SOYAYYAR MU CHAPTER 5

SOYAYYAR MU

CHAPTER 5

Akwai wata rana a gidan Ammi, Aisha da Hanifa zaune a qasa a qaramin falo suna rubuta list din kayan da suke buqata na hada kek yayinda Nafisa take bisa kujera tana kallon TV.
Wayar Aisha ce tayi ringing, a wannan lokacin kuwa wayar tana kusa da kujerar da Nafisa take zaune don haka ne ta yunqura ta janyo wayar don miqa ma Aisha wadda bata ma ji wayar tana ringing ba.
Sunan Yusuf ta gani a fuskar wayar

A wannan lokacin ne Aisha ta ji qarar wayar ta nufo wurin Nafisa ta karba.
Ko da ta amsa wayar bayan sun gaisa ne yake ce mata zai zo anjima wanda ta amsa mishi sannan ta kashe wayar.
Nafisa ce tace “waye wannan Yusuf din?”
Aisha tace “Anty saurayi na ne wanda zan aura ” shine ake wani yi mishi yanga kamar ba”a so?”

Aisha a ranta tace bana ma son shi, qanin ki nake mutuwar so, kawai banda yadda zan yi ne.
Hanifa ce tace “haba Aisha ashe kin kusa aure shine ko da wasa baki taba gaya mana ba?” tace nima ai ban dade da sani ba tunda Baba na ya samu da maganar ba ni ba, kuyi haquri”
Nafisa tace “ikon Allah nima sunan dear dina Yusuf, zaki auri mai sunan shi kenan”
Aisha tayi murmushi a ranta tace “ke kin kira naki dear tunda kina son shi, ni kuma ban san wane suna zan kira nawa ba da bana so”
ji tayi Nafisa na fadin “gashi ma baku taba haduwa ba dayake yana zuwa library da kun hadu tunda yanzu yajin aiki suke yi a ma”aikatar su”.
Aisha tace “Allah sarki watarana zamu hadu ai”.
Bayan su Aisha sun cigaba da rubuta list dinsu ne Aliyu ya fito daga dakin shi riqe da kofin gilas na fresh milk.
Nafisa ce tace “babyn Ammi ina zuwa ne?” yace “nowhere anty” yayin da ya zauna a gefen ta ya sa ma Aisha ido.
Yadda yake kallon su ita da Hanifa zaka rantse yana kacici kacici ne akan wacce zai zaba.

Nafisa ce ta katse mishi tunanin shi inda ya ji tace “Aliyu ashe Aisha ta kusa aure shine bata fadi mana…”.
Qarar fashewar kofin gilas suka ji.
Suna dagowa sai suka ga hannun Aliyu yana jini a dalilin fasa kofin gilas din da ke hannun shi da yayi wanda bai ma san yayi ba saida Nafisa tayi ihu tace “subhanalillahi Aliyu garin yaya?”

Hannun ya kalla yayinda Aisha da Hanifa suka taso a rude, tuni idanuwan Aisha sun cook da hawaye.
Hanifa ce ta ruga domin dauko first aid kit yayinda Nafisa ta haura sama don kiran Ammi.
Hankici ya fiddo daga aljihun shi zai goge jinin, Aisha tayi sauri ta karba tana fadin “let me help you” tuni hawaye suka fara wanke mata fuska, wani sanyi ya ji a dalilin riqe hannun shi da Aisha tayi, kallon ta yayi yayin da ya tuno abinda yasa shi fasa kofin.
“Aisha zata yi aure!!”.

Ajiyar zuciya ya saki sannan ya karbi hankicin daga hannun ta tare da fadin “bar shi kawai thanks”
Anan ne Hanifa ta dawo riqe da akwatin first aid yayin da Nafisa da Ammi suka sauko a rude. Ammi tace “ko a kira likita ne?” yace “no need Ammi, ciwon fa ba wani babba bane”
Nafisa ce ta kira Hafsat tazo ta kwashe gilas cup din da ya fashe sannan ta kalli Aliyu tace “wannan jinin da yake zuba fa?”
Hanifa ce tace “idan aka yi dressing din ciwon jinin zai tsaya” shi dai Aliyu kallon hannun shi kawai yake yi yayinda tunanin shi yayi nisa. Gaba daya ma baya jin abinda suke fadi.

STORY CONTINUES BELOW
Hanifa ta riqe hannun shi ta duba sosai ta tabbatar babu gilas a ciki sannan tace ma Aisha wadda take ta goge hawayen da ke gangarowa daga idanuwanta da ta taimaka mata ta riqe hannun Aliyu yadda zata ji dadin sa mishi plaster.

Ba tare da bata lokaci bane Aliyu ya zare hannun shi daga hannun Hanifa ya miqe tare da fadin “thanks Hanifa ba sai kin sa plaster din ba”
Ya harari Aisha sannan ya wuce dakin shi. Ammi ta dauki plaster din ta bi shi dakin shi yayin da Nafisa ta kalli Aisha wadda take ta faman goge hawaye, mamaki tayi sosai domin dai ciwon da Aliyu ya ji ba wani ciwon da za”a yi ma kuka bane.
A ranta ne tace “Allah sarki Aisha, ta ma kasa boye son da take mishi”.

**************

Ammi ta sa ma Aliyu plaster a hannun sannan ta dafa goshin shi tace “ko a kawo maka maganin zazzabi ka sha ne?” yayi murmushi yace “haba Ammi, please stop, ciwon fa qarami ne i”m fine”.

Bayan Ammi ta fita ne Aliyu ya kwanta bisa resting chair dinshi ya runtse idanuwan shi, a fili ne yace “Aisha aure zata yi? Yanzu haka zan sa mata ido tayi aure?”

Wata zuciya tace mishi “toh me ya ruwanka? Kaima ba auren zaka yi ba?”
Da sauri ya bude idanuwan shi ya miqe, zuciyar shi ta cigaba da ce mishi “if you love her then tell her” a fili yace “do i?”.
Nafisa ce ta shigo dakin tare da fadin “bros ya hannun? Mu gani” ya miqa mata hannun ta kalla sannan tace “Allah ya qara sauqi amma me ya faru ne? Abinda na tuna shine ina gaya maka zancen auren Aisha sai kawai naji qarar fashewar kofin, ka tabbata ba maganar ta bata maka rai ba?”
Da sauri ya kalli Nafisa cikin mamaki.

Murmushi tayi tace “Albishirin ka, da idanuwa na naga Aisha tana kuka saboda ciwon da ka ji, ka sani cewa sonka take kuma kai ma nasan kana son ta amma girman kai irin naka bazai taba bari ka furta mata kalmar so ba”
Muryar shi qasa qasa yace “haba Anty feena, ni na ce miki ina son Aisha? Besides aure zata yi kuma nima shi zanyi there is no point talking about this right now” miqewa Nafisa tayi tace “shikenan bros, idan kana buqatar wani abu sai ka kira ni” yace “tanx sis”
Bayan ta fita ne ya cigaba da tunani kala kala a game da Aisha. Bai samu natsuwa ba sai da ya ji kiran sallah, bayan ya shirya ya fito ne don tafiya masallaci ya hango Aisha da Hanifa zasu haura sama.
Ko da suka hada idanuwa harara ya danna Mata ya wuce yayinda hankalinta ya kasa kwanciya.

***************

Aisha dai ko da ta koma gida hankalin ta ya qi kwanciya domin dai ta rasa dalilin da yasa Aliyu yake ta hararar ta bayan bata mishi komai ba, har kanta ya fara sarawa a dalilin takura ma kanta da tayi da tunani.
Wayar ta ce tayi ringing, ba wani bane face Yusuf.
Muryar ta qasa qasa ta amsa, yace mata yana waje, ba tare da tayi magana bane ta kashe wayar.
Tsaki tayi ranta a bace ta dauki gyalenta ta fita, sai da ta shaida ma Inna sannan ta wuce.
Sun dan taba hira wadda duk shi yake yin ta, ita dai saidai tace eh ko a”a.
Ckin hirar ne yake gaya mata cewa ana yajin aiki a ma”aikatar su, da sauri ta kalle shi tare da fadin “haba yajin aiki, tun yaushe?”
Yace “kusan sati biyu kenan yanzu ma ina dan bincike ne a library na wani aiki da zamu fara idan an koma”.
Jin wannan maganan ne kan Aisha ya qara sarawa, labarin Yusuf din Nafisa ta tuno wanda yayi daidai da wanda taji yanzu wurin Yusuf.
A ranta tace “ko dai…” sai kuma tace “no no no ban san inda mijin Nafisa yake aiki ba kuma ai Yusuf baya da mata…..”
Katse ta yayi tare da tambayarta “lafiya kika yi shiru?” Aisha ta dan dafa kai sannan tace “wallahi kaina ne yake ciwo” hankalin shi a tashe yace “kin sha magani?”
tace “a”a amma idan na shiga zan sha” yace “ayyah, Allah ya qara sauqi. Bari in qyaleki ki huta. Na manta ban tambaye ki ba, wai yarinyar nan har yanzu bata gama koyon girkin bane?” Aisha tace “tana dai qoqari”
yace “idan dai kin gaji ki bari hakanan. Ta dan yi murmushi tace “ai aikin lada ne tunda har a dalilin haka za”a raya sunnar manzo” murmushin yayi wadda bata kai ciki ba yace “Allah ya bada sa”a, ni bari in tafi. Allah ya qara sauqi” tace “ameen” ta shige gida.
**************

Ta tarar da Inna a Falo tana kallo, ta zauna kusa da ita sannan tace “Inna akwai panadol kuwa? Wallahi kaina ke ciwo”
Inna tace “aikuwa kamar jiya Zaid ya dauka bayan ya dawo daga makaranta, ki tambaye shi idan akwai saura. Allah ya qara sauki” Aisha ta miqe tare da fadin “Ameen Inna”.

Ta tarar da Zaid a dakin shi yana karatu. Yana ganin ta yace “hajiya Aisha matar Aliyu” nan da nan tayi murmushin jin dadi tace “Allah yasa haka” yayi dariya yace “ameen, ya aka yi ne yau kika biyo ni? Ko an fara Zou ne?”
Aisha ta zauna tace “ai yau bazan kalla cartoon dinnan ba, kaina yana ciwo wallahi. Yanzu ma panadol din da ka dauka ne jiya nake so” miqewa yayi ya dauko mata sannan ya fita ya dauko mata ruwa ya dawo ya miqa mata.
Bayan ta sha ne yace “Allah qaro lafiya matar Aliyu” yanzu ma murmushi tayi sannan ta dan kwanta kan kujerar dakin shi yayin da ya cigaba da karatun shi.
Aisha dai bata san lokacin da bacci ya tafi da ita ba, bayan kusan minti arba”in ne ta farka wanda a lokacin Zaid ya hau laptop dinshi yana ta browsing.
Addu”ar tashi daga bacci tayi ta ce “haba Zaid, shine ka bar ni ina ta bacci anan?” dariya yayi yace “haba gimbiya, ya za”a yi in tada ki bayan kan ki na ciwo. Nasan yanzu ya lafa ai ko?” tace “gaskiya ya sauka”.
Har ta miqe zata fita sai kuma ta dawo ta zauna kusa da shi tace “ni kuwa akwai abinda zan gaya maka amma kada ka gaya ma kowa” da sauri ya juyo tare da tattara dukkan hankalin shi gareta yace “ina jin ki”.
Aisha ta bashi labarin Yusuf din Nafisa da kuma zancen Yusuf wanda al”amarin ya daure mata kai.
A qarshe tace “ni yanzu ina so ne in tabbatar Yusuf din Nafisa ba shine Yusuf din da ke zuwa gidan mu ba”.
Zaid ya gyara zama yace “ina da shawara wadda nake tunanin zamu gano shi, gobe idan kika je gidan ki duba motocin da ke garejin gidan ki gani idan zaki ga daya daga cikin motoci biyu da Yusuf ke hawa.
Domin idan kin ga daya toh babu tantama ya fita da dayar. Sannan ki tambayi Hanifa cikin siyasa inda Yusuf din gidan su yake aiki, daga nan idan kin ji qamshin cewa shine gobe zan gaya miki yadda zaki kama shi gar da gar”.
Dariya Aisha tayi tace “shege mutumina, ashe dai kaima dan bala”i ne ban sani ba” shima dariya yayi yace “kar ki damu, idan ma shine zamu kama shi ai. Ni dama ba wani kwanta mun a rai yayi ba wallahi”, Aisha ta yamutsa fuska tace “balle kuma ni da za”a jona mun shi a matsayin miji”.

***************

Aliyu dai yana can har wani zazzabi yaso ya kama shi a dalilin takura ma kan shi da yayi da tunanin zancen auren Aisha da ya ji.
Yanzu kam ya tabbatar cewa son ta yake wanda kuma ya yanke shawarar barin abun a ranshi tunda aure zata yi.
Saboda razana da tayi da ganin shi da qyar ta saita murya ta gaishe shi, bai amsa ba ya juya. Dakin shi ya wuce yayin da Aisha ta taras da Ammi a falo ta gakda ta sannan ta tambaye ta “Hanifa tana sama ne?” tace “aikuwa sun fita da Nafisa siyo kayan da zakuyi amfani da su wurin hada kek”.
Aisha ta zauna zaman jiran su.
Wata qawar Ammi ce mai suna Haj. Hauwa tayi sallama. Bayan sun gaisa da Ammi ne Aisha ma ta gaishe ta.
Cikin fara”a ta amsa tare da fadin “hajiya ina kika samo “yar kyakkyawar balarabiya ne? Ko itace sirikar tamu ne?”
Ammi tayi dariya tace ” Aisha qawar Hanifa ce” da suke haurawa sama ne Ammi ta cigaba da fadin “ai Aliyu Hanifa zai aura” Hajiya Hauwa tace “masha Allah, Allah ya nuna mana”.

Aisha dai remote ta dauka ta canza channel zuwa cartoon ta cigaba da kallo. Tayi zurfi cikin kallon ne ta sa hannu a jaka ta ciro chocolate ta bare tana ci.
Aliyu ne ya fito daga dakin shi da niyyar fita zuwa gidan Suleiman, tsayawa yayi yana kallonta wadda gaba daya hankalin ta yana kan cartoon din da take kallo yayin da take ta cin chocolate dinta.
Ganin ta yayi kawai tana ta kwasar dariya wanda ta bashi mamaki matuqa.
Juyawa yayi ya kalli TV don ganin abinda ke sa ta dariya. Mamakin shi shine ya za”ayi mutum babba ya natsu yana kallon cartoon har su bashi dariya kamar wani qaramin yaro, wata zuciya ce tace mishi toh meye marabar ta da qananan yara.
Qamshin turaren shi da taji ne tayi saurin waigowa ta gan shi tsaye a bayan kujerar da take zaune.
Hannun shi ta kalla tace “ya hannun ka? Ya daina maka zafi?” murmushi yayi yace “dama nace yana mun zafi ne?”
zaro idanjwa tayi cikin shagwaba tace “akwai zafi mana, harda jini fa yayi ta zuba” wannan karon murmushi yayi ba tare da yace komai ba. Matsowa yayi kusa da ita yace “na ji ance zaki yi aure shine baki gaya mun ba?” cikin mamaki tace “ai ban san kana so ka sani ba” yace “saboda baki dauke ni a matsayin komai ba ko?”
Aisha ta bala”in jin dadin maganar Aliyu, tace “ba haka bane, na dai ga ba abinda ya dame ka bane….” katse ta yayi yace “ya dame ni mana” da sauri ta kalle shi yayin da ya cigaba da fadin “saboda ina….” bai qarasa maganar ba aka danna qararrawa.
Wucewa yayi don bude qofar.
Su Nafisa ne suka dawo. Yayi musu sannu da zuwa sannan ya fita.
Aisha dai shiru tayi tana tunanin abinda Aliyu yake so ya gaya mata wanda dawowar su Hanifa ya hana ta ji, Hanifa ce ta katse mata tunanin ta tare da fadin “Allah sarki Aisha yi haquri mun dade, hold up ne ya bata mana lokaci” ajiyar zuciya ta saki sannan tace “babu komai, sannun ku da zauwa”

suka amsa yayinda Nafisa ta tambaya “Ammi fa” tace “tayi baquwa suna sama” su Nafisa suka wuce sama don gaida Haj. Hauwa yayin da suka bar Aisha tana ta tunanin kalaman Aliyu.

*************

Shi kuma Aliyu ko da ya shiga motar shi kifa kai yayi kan sitiyari yana tunanin abinda ya faru yanzun nan, banda su Nafisa da suka dawo da ya gaya ma Aisha abinda ke zuciyar shi domin a yanzu kam ya fara tunanin lallai bazai iya haqura da ita ba domin kullum qara shiga ran shi take.

***********

Aisha da Hanifa sun shiga kicin sun fara hada kek, sun dan jima suna aikin kek din yayin da suke hira ne Aisha ta tambayi Hanifa “wai shekarar Anty Feena nawa da aure?” Hanifa tace “gaskiya zasu kai kamar shekaru biyar” Aisha tace “amma basu taba haihuwa ba?”
Hanifa ta saki ajiyar zuciya tace “ai lamarin rashin haihuwar Anty Feena abin mamaki saboda bayan auren su ba da dadewa ba ta damu akan rashin samun ciki, a dalilin haka har qasar waje an je don duba lafiyar su wanda likitoci suka tabbatar musu da komai lafiya. dukda akwai lokacin da ta samu ciki amma bai dade ba ya zube, tun daga nan bata sake samun wani ba. Anty Feena ta damu sosai akan rashin samun ciki, haka aka dinga kwantar mata da hankali akan cewa lokaci ne, idan yazo zata samu. A bangaren Uncle Yusuf shima ya kwantar mata da hankali tare da jaddada mata cewa rashin haihuwa bazai raba su ba tunda haihuwa na Allah ne, shi yake badawa kuma yana kallo don haka a duk lokacin da yaso zai basu haihuwa. Da wannan ne ta rage damuwa, gashi kuma har yanzu shiru”.
Cikin tausayawa ne Aisha tace “Allah sarki, Allah ya bata haihuwar yara masu albarka” Hanifa tace “ameen”.
Tambayar Hanifa tayi “toh shi Uncle Yusuf ina ne garin su?” Hanifa tace “shima bakatsine ne mutumin Bakori, iyayen shi sun rasu tun yana qarami” Aisha tace “Allah sarki,naji Anty Feena tana fadin sun je yajin aiki. Wanne ma”aikata yake aiki ne?” Hanifa tace “wata ma”aikata ce fa a nan Malali, National steel raw materials….”
tuni numfashin Aisha ya nemi daukewa jin maganar Hanifa, nan da nan ta fara zufa.
Da qyar ta saita murya tace “Hanifa tunda mun sa kek din a oven bari in je gida na tuna akwai wani aiki mai muhimmanci da na baro a gida, bari in je in qarasa, nan da minti sha biyar ki kashe, sai gobe”
kafin Hanifa tayi magana tuni Aisha ta fita, ko sallama bata yi ma su Ammi ba ta wuce.

*************

Jikin ta na rawa ta iso gida, ta taras da Inna da Zaid a falo. Inna ce tace “yau kin dawo da wuri lafiya dai ko?” Aisha tace “lafiya lau Inna, kek muka yi shine na baro Hanifa zata qarasa”.

Janyo hannun Zaid tayi tace “zo kaji mutumina” Inna tayi dariya tace “ku dinnan ba”a shiga tsakanin ku, yau shiri gobe fada. Yau dai ana shiri kenan har za”a qulla wata magana” dariya suka yi suka wuce dakin Aisha.
Bayan sun zauna ne Aisha tace “dan uwa magana dai ta fito, Yusuf dai shine na Anty feena”. Nan da nan ta bashi labarin komai da komai da ta gano.
Zaro idanuwa yayi yace “yanzu dama Yusuf mutumin banza ne maqaryaci? Wallahi ni dama haka kawai bana son gayen” ya gyara zama yace “listen to me sis, idan kuka yi waya zuwa anjima ki gaya mishi cewa gobe baza ki je gidan Ammi ba don zamu je kasuwa. Idan kika gaya mishi haka toh ina mai tabbatar miki cewa bazai je ko ina ba goben. Ke kuma sai ki je gidan don ku yi ido hudu da dan iskan”.
Dariya sosai Aisha tayi tace “gaskiya akwai ka da hikima, da ina raina maka wayau ashe dai big boy ne kai” dariya yayi yace “toh yanzu dai muje ki kai ni Mr Biggs kawai”.
Itama dariya tayi tace “idan dai zaka tuqa muje mu dawo kafin a kira magrib”.

Bayan sun fito ne suka ce ma Inna zasu je Mr Biggs har suna tambayan ta me take so, dariya kawai tayi tace “ku dai ku tafi kawai, kun qullo shirmen ku zaku yi mun iyayi”
Suka wuce suna ta dariya.

◇◇◇◇◇◇◇◇◇
Aisha dai bata gaya ma Salma halin da ake ciki ba tunda bata tabbatar da abinda take zargi ba, duk da bata son Yusuf bata so ace abun da take tunani ya zamo gaskiya domin ko kadan bata so wani mummunar abu ya samu Nafisa.+
Duk da bata taba ganin Yusuf din Nafisa ba tasan Nafisan tana bala”in son shi, kuma ga dukkan alamu bata san yana neman aure ba tunda da bakin shi ya gaya musu baya da aure, wannan yana nufin zai cutar da Nafisa ne ta hanyar saki ko wani abu makamancin hakan.
***********

Da daddare bayan sallan isha”i kuwa Yusuf ya kira Aisha a waya.
Sun dan jima suna hira ne ta gaya mishi zancen bazata je gidan Ammi ba gobe, ai kuwa har cikin ran shi ya ji dadi.
Bayan sunyi sallama ne ta koma falo, Inna ce take gaya mata cikin satin nan za”a kawo lefen Salma, don haka dukkan su zasu je katsina don karbar lefe.
Aisha ta zaro idanuwa tace “za”a kawo lefen Ummi shine bata gaya mun ba?, bari in je in kira ta a waya” Inna tana dariya tace “kun fi kusa, ku qarata”.
Aisha ta koma daki ta kira Salma a waya, tun kafin su gaisa ne Aisha ta fara masifa tana fadin “haba Ummi, lefen naki da za”a kawo shine baki gaya mun ba sai ji nayi?” Salma tayi dariya tace “haba sis, maida wuqar. Tun da rana nake trying wayar ki baya shiga, maybe network ne. Yanzu kuma aka ce mun line busy, ke da waye ne a waya? Aliyu?”
Murmushi Aisha tayi tace “mutumin da ko lambar waya ta baya da shi ta ya zai kira ni? Ai ni tunani na ma ko soyayya bai iya ba tunda dai ban ga suna yi da Hanifa ba” dariya sosai Salma tayi tace “kila bai son ta ne, ke yake so”
ajiyar zuciya Aisha ta saki yayinda tace “ni dai nake son shi kamar rai na, shi kam bai san ina yi ba. Congrats sis, Allah ya sanya alkhairi sai munzo karban kaya”
Salma tayi murmushi tace “Ameen Aisha, Allah ya nuna mana naki kema”

Aisha dai bata ce komai ba, Salma ce tace “da Aliyu, ba yusuf ba” da sauri tace “Ameen” suka fashe da dariya.

Su Ammi ma Mummy ta sanar dasu maganan kai kayan lefen Mustapha don haka ne suka shirya zuwa Katsinan idan ya rage kwana biyu.

************

Washegari Yusuf bai je ko ina ba domin ya sa a ranshi cewa Aisha bazata zo ba. Dayake ya kwana biyu bai je gidan Ammi ba saboda boyo da yake yi kar Aisha ta ganshi, a yau ya shirya ya je gidan.
Suna zazzaune a falon Ammi na sama suna ta hira har Ammi na fadin “yau wacce rana Yusuf a falona muna hira” dariya yayi yace “ai Ammi binciken da muke ta yi ne ya hana ni zama, yau ma dai hutawa zanyi ne shiyasa ban je ba” tace “Allah ya bada sa”a” suka amsa da “ameen”.
Nafisa ce ta kalli Hanifa tace “yau Aisha bazata zo bane?” tace “nima haka na gani, na ji ta shiru”
Hanifa tayi trying wayarta a kashe.
Yusuf ne a ran shi yake fadin “toh wai dama bata gaya musu cewa yau bazata zo bane?”
a fili ne yace “toh ko bazata zo bane yau?”

Hanifa ce tace “idan bazata zo ba ai tana gaya mun a waya kuma gashi ina ta kiran wayan a kashe. Jiya ma da wuri ta tafi wai tana da abun yi a gida” Ammi tace “shiyasa jiya ban san lokacin da ta tafi ba ashe, Allah yasa dai lafiya”.

***********

Aliyu ya dawo daga ofis, Hafsat ce ta bude mishi qofa, tayi mishi sannu da zuwa. Da bai ga kowa a falo bane ya tambaye ta “Ina Ammi?” tace mishi “suna sama”.
STORY CONTINUES BELOW
Dakin shi ya wuce ya watsa ruwa sannan ya shirya cikin designer sweatpant dinshi baqi da t-shirt, ya feshe kan shi da turare, gashin nan nashi ya sha gyara. Nan da nan ya fito a kyakyawan shi sak.
Ya fito daga dakin shi ya haura sama. Bayan sun gaisa da kowa ne ya kalli Yusuf yace “yau wacce rana Bros Inlaw a gida a daidai wannan lokacin” dariya suka yi gaba daya. Ammi ce tace “babyna a kawo abinci ne?” murmushi yayi yace “haba Ammi ban dade da na ci lunch din da kika aika mun da shi ba fa, shima ban cinye ba” Nafisa tace “haba Aliyu, wannan dan abincin ne har ka rage? Don Allah ka dinga cin abinci kada ulcer ta tashi kamar yadda ta tashi maka kwanaki”.
Yace “yi haquri Anty na, zan ci anjima” yana gama magana ne wayar shi tayi ringing, ya duba fuskar wayar yaga sunan manajan shi na Abuja.
Miqewa yayi yana fadin “mutum ya dawo gida amma ba zai huta ba”. Ya sauka ya bar su Ammi suna ta mishi dariya.

Aliyu zaune a falon qasa yana magana da manajan shi a waya, manajan ne yake gaya mishi ya aiko mishi wasu saqonni a mail din shi don haka ya duba yanzu saboda su cigaba da aiki.
Hafsat ya kira ya ce mata ta dauko mishi laptop din shi a dakin shi. Bayan ta dauko ne ya fara dubawa.
*************

Zaid ne ya kawo Aisha gidan Ammi yayin da yace mata zai je Maqarfi plaza, idan ta gama ta kira shi yazo ya dauke ta.
Ta danna qararrawa, Hafsat ta bude mata, suka gaisa.
Muryar ta da ya ji ne yayi saurin dagowa, sanye take cikin jallabiyya baqa mai kyau.
Tayi mishi bala”in kyau, haka itama yayi mata kyau har a ran ta tana fadin “Oh ni Aishatu zai kashe ni da kyan shi, why is he so handsome?”, bata san lokacin da tayi mishi murmushi ba wanda shima ya mayar mata da murmushin.
Da ta iso kusa da shi ne tace “ina wuni” yace “lafiya” ya maida kallon shi kan laptop dinshi. Don dai ta ji muryar shi tace “su Ammi fa? Ba tare da ya kalle ta ba Yace “suna sama”.
Tana haurawa sama ne ta ji ya kira Hafsat yace ta kawo mishi fresh milk.

Sallamar Aisha tasa Yusuf ya zabura, tuni ya fara zufa yayin da yake duqar da kai kamar munafiki.
Hankalin Aisha ya tashi ganin Yusuf zaune a gefen Nafisa. Da qyar ta saita murya suka gaisa da su Ammi sannan ta zauna.
Hanifa ce take fadin “ai na zata baza ki zo ba da na ji ki shiru” Aisha dai Yusuf take kallo wanda ya kasa hada ido da ita. Murmushi tayi tace “ai da bazan zo ba da na kira ki” ta juya ta kalli Yusuf tace “ina wuni” Yusuf dai gaba daya ya jiqe da zufa dukda AC da ke kunne a falon.
Nafisa ce tace “dear ana gaishe ka” da qyar ya saita murya yace “lafiya” Nafisa ce tace “yau dai ga dear ga Aisha, dama kai kadai ne baka san ta ba sai labarin ta da kake ji”. Da qyar yace “Allah sarki”.
Aisha kam gaba daya ta tausaya ma Nafisa domin dai ga dukkan alamu Nafisa ce ta damu da shi amma shi kam ko da wasa bata gaban shi, abinda ya zo mata a rai shine shin waye Yusuf? Mutumin kirki ne ko mutumin banza? Allah kadai yasan qaryayyakin da yake ma baiwar Allah Nafisa. Nan da nan idanuwan ta suka ciko da hawaye. Miqewa tayi tace musu “ina zuwa” ta fita.

***************

Tsaye yake riqe da kofin gilas na fresh milk yana waya da Bilal akan Project din za”a yi na Abuja wanda yana so Bilal din ya duba aikin tunda dama yana can.
Aisha ce ta sauko tana tafe tana tunani ba tare da tasan abinda ke gaban ta ba, kawai sai ta bige Aliyu wanda har kofin da ke hannun shi ya fadi ya fashe.
Ran shi a bace ya fara masifa “meye haka? Ba kya gani ne?” a lokacin ita har ta duqa ta fara kwashe fasassun gilas din.

Muryar ta qasa qasa tace “don Allah kayi haquri” jin yanayin muryar ta ne ya duqa ya riqe hannun ta yace “bar shi kawai Hafsat zata kwashe” ta miqe zata tafi ne yace “lafiya? Me ya same ki ne? Me aka yi miki?”
A guje ta ruga ta fita daga falon.
Cikin damuwa Aliyu ya kira Hafsat yace tazo ta kwashe cup din da ya fashe.
Yana shirin hawa sama ne ya ga Yusuf yana saukowa yayinda ya ce mishi “nayi baqo ne yana waje yana jira na, ina zuwa”.
Lokacin da ya haura sama Ammi ta wuce dakin ta don haka Nafisa da Hanifa kawai ya tarar a falon.
Tambayan su yayi “ina Aisha ta je ne?” Nafisa tace “yau da kan ka kake tambayar Aisha?” cikin damuwa yace “Anty feena ba haka bane, na ga ta fita rai a bace ne shiyasa nake tambaya” Ya kalli Hanifa yace “dan kira ta a waya mu ji inda take”.

Hanifa dai jin al”amarin tayi banbaraqwai domin dai bata gane me Aliyu ke nufi ba.
Ita dai Nafisa kallon shi take a ranta tana fadin “see this guy, yana fadin babu ruwan shi da Aisha amma gashi nan a gaban matar da zai aura yana nuna tsananin damuwa akan ta, kawai dai baya so ya amince cewa yana son Aisha ne”.
Wayar Aisha ta gama ringing amma bata dauka ba, da Hanifa ta gaya mishi ne yace ta cigaba da trying sannan ya fita daga falon.

Ya dauki laptop dinshi zai shiga dakin shi ne Hafsat ta dakatar da shi tace “Uncle dama da nake kwashe kofin da ya fashe ne naga jini shine nake tunanin ko ka ji ciwo ne” ya duba hannun shi yaga babu jini, nan take tunanin shi ya je kan Aisha.
Ba tare da yace mata komai ba ya shiga dakin shi ya ajiye laptop din sannan ya kira Bilal a waya yace mishi zai kira shi su qarasa magana anjima.
Ya fito daga dakin shi ne ya tarar da Hanifa zata zo wurin shi. Tambayar ta yayi “kin same ta?” tace “a”a” yace “bani lambar ta” Hanifa dai a sanyaye ta kira mishi lambobin Aisha yayin da taga tsananin damuwa a tare da shi.
Zuba mishi ido tayi tana kallon ikon Allah.

Lokacin da Aisha ta fita ashe saboda zurfi da tayi a tunani maimakon ta nufi hanyar fita sai ta wuce garden din gidan Ammi, ganin kanta kawai tayi a zaune cikin tsananin damuwa.

Tambayoyin da take ma kanta sune meye dalilin Yusuf na yi musu qaryan baya da mata? Idan yana da mata qin amince mishi za”a yi? Ita dai tasan har ga Allah ta ji dadi da ta gano qaryar da yayi musu, ko banza dai tasan babu zancen aure a tsakanin su toh amma kuma Anty feena fa? Duk son da take mishi ashe baya son ta? tana wadannan tunanin ne Hanifa tayi ta kiran wayar ta bata ji ba.
Fiddo wayar tayi don ta kira Zaid akan ya zo ya dauke ta, sai ta ga missed calls din Hanifa kafin ta kira ne taga wata special number na kiran ta har a ranta tana fadin “waye wannan kuma?”

Tana kai wayar kunnen ta ne ta ji muryar shi yana fadin “kar ki sake yi mun haka, kin san irin damuwar da na shiga na rashin amsa waya da kika yi? Kin sa ina ta tunanin wani mummunan abu ya faru da ke” daga Aisha har Hanifa da take sauraron shi sun girgiza da jin kalaman Aliyu.
Aisha kam don rudewa ma kasa magana tayi .
Ita dai Hanifa nan da nan jikin ta ya fara rawa, bata san lokacin da ta koma da baya ba ta ruga da gudu ta haura sama ta nufi dakin ta tana kuka.
Aliyu dai ya manta kwata kwata cewa Hanifa tana wurin, ya cigaba da magana “tell me, where are you right now?”
Muryar ta na rawa cikin shagwaba tace “ina Garden din Ammi amma yanzu zan tafi” yace “ki jira ni kada ki je ko ina, i am coming” ya kashe wayar ya kira Hafsat don ta kawo mishi first Aid kit.
Bayan ta kawo mishi ne ya fita.

◇◇◇◇◇◇◇◇◇
Hanifa kwance a dakin ta tana ta kuka, kasa kwanciyar ma tayi ta miqe tana ta kai da komowa.+
Tunanin yadda zata yi take domin kuwa al”amarin da ya faru ya tabbatar mata da cewa Aliyu ya kamu da son Aisha.
Kamar ance mata ta leqa ta windo kawai sai ta hango Aisha zaune a garden .
Dayake daga dakin Hanifa ana hangen garden din wanda dama lokuta da dama nan take zama tayi ta kallon Aliyu domin wurin zaman shi ne.

Hanifa na hangen Aisha ne ta ga Aliyu ya shiga garden din, nan da nan ta goge hawayen fuskar ta tana kallon ikon Allah.
*************

Aisha zaune a garden din yayin da kanta yake bisa cinyar ta tana ta sakin ajiyar zuciya.
Aliyu ya tsugunna a gaban ta yana kallon ta, qamshin turaren shi da ta ji ne tayi saurin dago fuskar ta wadda duk ta yamutse saboda tsananin damuwa da ta shiga.
Yace “mu ga hannun ki” cikin rashin fahimtar abinda yake nufi ne ta dago hannuwan ta tana dubawa.
Ganin jini ne ta miqe da sauri yayin da hawaye suka fara gangarowa daga idanuwan ta.
Hannun ta ya riqo yace “dawo ki zauna” ta zauna a rude tana fadin “wayo Allah na shiga uku” kamar dai yadda qananan yara suke yi.

Aliyu dai bai san lokacin da ya fashe da dariya ba. Abinda ya lura shine ba zafin ciwo yake ruda ta ba, jinin da take gani ne yake tada mata hankali.
Ita dai Aisha dama ta ji hannun yana mata zugi amma saboda tunanin da ya sha mata kai ne bata bi ta kan zugin ba, yanzu da ta ga jini a hannun ne ta rude. Aliyu ya ajiye first aid kit din a gefen ta sannan ya bude, da sauri ta zaro ido ta kalle shi tace “me zaka sa mun? Wallahi akwai zafi fa. Ka bar mun shi haka kawai” bai ce mata komai ba ya fiddo auduga da iodine, tun kafin ya sa mata ta qwace hannun ta boye.

Yanzu kam ya tabbatar Aisha bata da maraba da qananan yara.
Zama yayi gefen ta yace “yi haquri ki kawo hannun, close your eyes idan zan sa miki, bazaiyi miki zafi ba”
Cikin shagwaba tace “you promise?” yayi murmushi ya kada mata kai alamar eh.
Hannunta na rawa ta miqa mishi yayin da ta rufe idanuwan ta tana ta addu”a, yana riqe da hannun ta ne ya qura mata ido yana mamaki, a ran shi ne yake fadin “her childish behaviour alone gives me plenty of joy… I cant believe this”
Yana saka mata kuwa sai ya ji ta sa ihu tare da qanqame shi.
Wani irin sanyi ya ji ya ratsa shi wanda har ya kasa motsi.
Ita dai Aisha saboda zafin da ciwon ke yi mata bata ma san abinda tayi ba.
Hanifa dai tana sama tana kallon su.
Da qyar Aliyu ya samu natsuwa sannan ya banbare ta daga jikin shi, hawaye ne sharkaf a fuskan ta, plasta ya sa mata sannan ya fiddo hankici ya miqa mata.
Ta karba ta goge fuskan ta harda fyace majina, Aliyu ya yatsine fuska cikin ranshi yace “ya salaam”
Bai ankara bane yaga ta miqa mishi hankicin shi, kallon ta yayi yace a ran shi “this garl is crazy”
Ya sa hannu ya karba.
Hararar shi tayi cikin shagwaba tace “kayi mun alqawari cewa bazai yi zafi ba” yace “i”m sorry”.
STORY CONTINUES BELOW
Shiru tayi tana kallon shi cike da mamaki.
Tambayar ta yayi “baki haqura bane?” ita dai Aisha mamaki tayi wai yau Aliyu ne yake ce mata tayi haquri. Murmushi tayi tace “na haqura”.
Ba tare da ya kalle ta bane yace “me ya same ki ne kika fito hankalin ki a tashe haka? Wani ba lafiya ne?”
Ta girgiza kanta yace “ina sauraron ki”.
Tace “mun yi fada ne da saurayi na wanda zan aura” wani irin sanyi Aliyu ya ji a zuciyar shi.

Ji tayi yace “me yayi miki?” tace “ya yaudareni ne kuma ma dama ni ba son shi nake ba”
da sauri ya kalle ta yace “baki son shi shine zaki aure shi? Wa kike so toh?” runtse idanuwan ta tayi a ranta tace “kai nake so”.
Tambayar ta ya sake yi, ba tare da ta kalle shi ba tace “babu wanda nake so”
murmushi yayi yace “toh meye abun tada hankali tunda dama ba son shi kike ba?”
Aisha dai tunanin tayi ko ta gaya mishi gaskiyan abinda ke faruwa a game da Yusuf, wata zuciya tace idan kika gaya mishi kwanciyar hankalin Nafisa zai qare domin ba sai an fada ba tana bala”in son Yusuf sannan idan ta shiga mummunar hali hankalin su Aliyu da Ammi bazai kwanta ba.
A yanzu tunda kin gano Yusuf qila ya haqura ya rungumi matar shi su zauna lafiya ba tare da kowa ya san abinda ya faru ba.

Ji tayi yace “mu je in kai ki gida”.

**************

Hanifa tana hangen su suka fita daga garden din, komawa tayi ta fada bisa gado ta bude sabon babi na kuka. Hanifa tayi kuka har ta gode ma Allah, bayan ta dan natsu ne ta fara tunanin abubuwan da suka dinga faruwa tsakanin Aisha da Aliyu wanda suka tabbatar mata da cewa lallai akwai soyayya a tsakanin su. A qarshe ne ta wuce bathroom don watsa ruwa domin har zazzabi ya fara neman rufe ta.

****************

Tafe suke a cikin wata sabuwar BMW din shi mai kyan gaske yayin da su biyun suka yi shiru suna tunanin juna, gaba daya motar ta dauki sanyi.
Ita dai Aisha tana mamakin yadda sanyi baya damun Aliyu domin a yanzu haka har ta fara kyarma.
Gashi tana son idan ya nemi ya kawo ta gida amma kuma sanyin motar shi ita ce matsalarta, wata zuciya tace mata tunda son shi kike dole ne ki so abinda yake so kuwa.
Aisha tana ta chatting da Fiddausi a waya yayinda Aliyu ya sa mata idanuwa dukda kuwa tuqi yake yi.
Gani yayi ta yamutse fuska alaman ta kasa fahimtar wani abu, hakan ne yasa yace “lafiya?” kallon shi tayi cikin shagwaba tace “na kasa gane kan Internet Network dina ne, yana ta fluctuating”.
Wani ikon Allah shagwabar Aisha tana bala”in birge Aliyu, shagwabar ta tana daga cikin abinda yasa ta qara shiga ran shi. Murmushi yayi yace “toh meye abin bata rai?” ya miqa mata hannun shi yace “bani wayar in gani” a lokacin da ta miqa mishi ne suka iso gida.
Yana dubawa ne Aisha ta matsa daf da shi don ganin yadda zai gyara, bayan ya gyara mata ne ya miqa mata wayar, ta tabe fuska tace “ashe ma babu wuya”
Yayi murmushi yace “shine har kike neman kuka” itama murmushi tayi cikin shagwaba tace “bana sanin lokacin da nake kukan ne ai” yace “naga alama ai baki da maraba da qananan yara”

nan da nan ta turo baki tana neman yin kuka saboda ya kira ta yarinya.
Ganin haka ne yace “yi haquri, wasa nake. Kada ki fara mun kuka a qofar gidan ku a kama ni” ta fashe da dariya tace “ban isa in sa a kama ka ba ai, na haqura kuma nagode, bye”.
Bin ta kawai yayi da ido har ta shiga gida.
Ajiyar zuciya ya saki yace “yanzu saboda wani banza ya yaudare ta shine har ta shiga damuwa? Lokaci yayi da yakamata in fadi mata abinda ke zuciya ta” wata zuciya ce tace mishi “ya zaka yi da Hanifa?” Tsaki yayi ya tada mota yayi gaba abinshi.

***********

Aisha dai tana shiga gida ta samu su Inna a falo, nan da nan ta zayyana musu abinda ya faru. Inna dai salati tayi tace “yau ga dan iska, yanzu dama Yusuf dan duniya ne bamu da labari?? Toh wai ma meye amfanin qaryar da yayi? Wa ya fadi mishi idan maganar auren naku ya tashi muka tsananta bincike bazamu gano wannan zancen ba? Aikuwa dai bari baban ku ya dawo don dai kam babu ke babu shi”
Aisha da Zaid dai babu abinda suke yi banda dariya.
Zaid ne yace “ni dama bana son shi wallahi” Aisha tace “balle kuma ni da za”a jona mun shi”.
Miqewa tayi ta wuce daki ta bar Inna tana ta zage zage yayin da shi kuma Zaid ya cigaba da shan dariya.
Aisha ta kira Salma a waya ta bata labarin komai da komai hatta abinda ya faru tsakanin ta da Aliyu wanda ta ji dadi matuqa.
Salma ta zagi Yusuf sosai itama sannan ta yi ma Aisha addu”ar Allah ya sa Aliyu ya kasance mijin ta.

◇◇◇◇◇◇◇

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE