TAGWAYE CHAPTER 14
TAGWAYE
CHAPTER 14
“Hajiya babu wata matsala jikinki ya warware, Sedai akiyaye gaba kada kisa’ke kai kanki ga fada ko hayaniya irin haka, Oga ya bamu umarni cewa mu gargadeki mukuma ja miki kunneh sosai da sosai, sabida acewarsa bakya Jin maganarsa ma barre kikarbi shawararsa, Amma gskya in asan samunsa ne kada kisa’ke ziyartar gidan Alhaji Sambo don gudun wata matsala makamanciyar wannan.
Da’idanun mamaki Ma’inah take kallansa har saida haushi ya addabeta sannan tadakatar dashi “Sabida kawai sunansa Zaid. Tafada abayyane sannan ta’kara taba baki tanacewa “Wai meye damuwarsa da lafiyata ma tukunna bayan duk wannan cin zarafin dayaimin cikin bainin jama’a yabatamin suna wai ni Ma’inah Sambo Maidugu Karuwa Kuma Yar Shaye shaye, how dare him, He is the worsed person I’ve ever known. Cikin hawayen takaici ta’karasar da’kalaman nata “Wallahi kuma duk wannan shirmen dayake faman yi ba zazuyi aiki akaina ba sabida har abada ba’zan yafemasaba, I hate him. Nan ta’kafe muryarta tafara dishi_dishi, inda ta’kara wata sabuwar hawaye tana tuna wulakancinda Zaid yaimata a office wanda ba’zata taba mantawa dashi’ ba harzuwa karshen rayuwarta.
Shiru likitan yai yake binta da kallo har tai shiru sannan ne yami’ka Mata takardan sallamarta daga asibiti batareda yatan’ka mataba haka yabar dakin cikin rudani dakuma bin umarnin Zaid cewa komenene tafada akansa kada suhukuntata.
Zaid na labe chan bakin kofa yana Jin duk abubuwnda take fadi shima ransa na bala’in baci idan ya tuno wannan kuskuren dayai inda yawulakan Tata cikin bainin mutane a wajen aiki cewa ita Yar Shaye ce kuma ‘karuwa. Abinda ke ‘kara bata masa rai kuwa idan yatuna musabbabin faruwar hakan duk ba laifin kowa bane fa’ce Maisha Sambo Maidugu domin tun tuni yarigada ya tabbatar dacewa Maisha ce yadauko abige yakai gidansa inda tai masa ‘karya dasunan Yar uwarta. Wannan dalilin yasa yake dada tsanar Ma’isha aransa.
Doguwar nunfashi yasaukar sannan ya’kara da tsaki “Me yasa nake irin wannan tunanin,
Zaid kadawo cikin hayacinka kuma kar’ka manta da alkawarinda kadauko wakanka cewa bazaka ‘kara yin soyayyaba har zuwa karshen rayuwarka, Muna is the only one you have,
She is your responsibilily Zaid wake up, Bakada hujjan tsanar Ma’isha a ranka sabida ita bakomai bace awajenka haka kuma zuciyarka batada hujjan San Ma’inah sabida ita kanta bakomai bace. Both the twins are good for nothing and useless kafi ‘karfinsu Zaid.
CEO lafiya kake magana kai kadei haka? Maganar Asad ne yadawo masa hayyacinsa, Inda Afirgice yagirgiza Kai “Babu komai l just don’t care, Muna itace kadei yakamata zuciyata tatuna. Me yasa?Asad ya’kara tambayarsa cikin mamaki “Kodei akwai matsala ce? No babu komai as far as my daughter is safe babu kuma abunda zai dameni bayan wannan.
Dashike Asad ya saba da halin abokin nasa Nan da nan yaga’ne tsarkuguwar dayai akan Ma’inah ce domin tun afarko ya rigada ya gane cewa abokin nasa ya’fara San Ma’inah sabida babu wata macen dayake kulawa kuma yake yawan tunani bayan ita, Sedei yanada tabbacin cewa wannan shegen dagin kan nasa dakuma abubuwnda sukafaru abaya ba’zasu taba barinsa ya gaskanta zuciyarsa haryafara soyayya ba. Da dukkan alamu kuma Ma’inah kyauta ce daga ubangiji kuma itace zatayi tsanadiyar dawowar farin cikin Zaid Insha Allah. Da wannan tunanin Asad yai murmushi sannan ya’kara fadan insha Allah. A bayyane. “Asad are u ok kaima naga kana maganar Kai kadei Kodei akwai matsala ce?
Dasauri ya girgiza Kai “No Dude go ahead kacigaba da tuna Muna after_all she is all you have.
Jinjina kai Zaid yai shima,jikinsa duk a tsargu yayinda yakecewa “You are right dude. Sannan yai shiru yafara bin abokin nasa da kallo Kuma. Babu abunda Asad ya’kara fadi bude kofar dakin yai Kai tseye yashige, shima Zaid haka yabiyosa duk dacewa ba’asan ransa yai hakanba. Shigewarsa keda wuya yafara tattara magungunan Ma’inah yanacewa; Miss tashi mutafi gida ya‘kamata kisamu hutu….
“Asad tun jiya kake zirga_zirga cikin asibitin nan yanzu ya’kamata kakoma gidanku domin kasamu hutu dawainiyar tayi yawa zakayi rashin lafiya, Za’muje gida tareda ita karka damu. Zaid yakatseshi cikin nunfashi daya.
‘Dan guntun murmushi Asad yai babu musu yajinjina kai “Toh se’mun hadu kenan.
Yana fadan wannan ya ijiye magungunan dama kamarjira yake akorosa babu sallama yabar musu dakin kai tseye Yana amsa wayarda akayimasa.
Ficewarsa keda wuya Zaid ya kwaso magungunan dama sauran ababe yanacewa” Wait for
me outside zanyi wata magana dawasu clients for like 5_10minutes…
Bai karasa furucinsaba Ma’inah takatseshi ”
Babu komai zaka iya tafiya Sir I will take care of myself. Da wannan tamike chak Bata kara wata ‘kalmar ba ahankali tasanya hijabinta tana kokarin ficewa.
“Ma’inah I’m sorry. Ya rike hannayenta dika biyu “I‘m sorry please try to forgive me.
Abunda yafada kenan.
Rabuwarta da Auwal, gidan babbar Aminiyarta “Mai_Jiddah” tanufa ganin babu inda zataje bayan nan. Dashike babu wata takura k0 matsi agidan, gidanta ne Halak Malak wanda saurayinta ya saya mata. Haka yawancin abokanan nata suke, sunada Maka Makan gidaje mallakinsu domin bata harka da ‘kananan mutane duk masu arzikine irinta, kamar yedda su abokanan nata basuyi da ‘kananan mutane suma.
Labarin gidansu gaba daya Maisha takwaso tafada mata har zuwa yanzu da alamu sun nuna Momcy kanta takoma bangaren Ma’inah babu mai yi da ita agidan, Danfaranta da Saminu yai duk ta jeromata, Shi Daddy ma tunda take bata taba rokansa kudi ya hanataba se awannan karon, atunaninta hakan yanuna cewa sihiri Ma’inah takeyi da Mahaifinta Saminu domin tarabata dasu, sukuma yi tsanadiyar karayar arzikinta
Tsit Mai_iidda take bin Iabarin daya bayan daya se bala’in jinjina kan da takeyi tun tuni
Idan Ni ce wallahi tuni na kauda ita cikin sha’fina tun ba yauba nabude wata shafin kuma ina dealing. Shiru tai nadan wasu mintuna tashiga tunani se chan ta’kara zuba mata Ido tanacewa “Abu daya zan tunasar dake Isha kada kimanta da sharudodin wannan kungiyar abokantakar tamu da masu kud’i muke harka wallahi ko yau akace Maisha ta lale batada arziki rabuwa dake zamuyi ko ajikinmu …..
Dakata Mai_jidda Maisha tazube kasa, kafafunta ta rike dika biyu tanacewa “Meyasa kike fad’in haka wallahi babu wanda ya isa yarabani daku Jidda kuma babu wanda zai shiga tsakanina da dukiyar mahaifina I promise, sabida duk na ‘wane Nice nan zan gajesu idan dattijon ya mutu, Dan Allah ko dawasa kada ki kara fadan irin wannan munanan maganganun sabida wallahi ni kaina rasa dukiya kan iya hallakani har lahira kamar yedda zan iya hallaka Dan Adam sanadiyar dukiya, Haka Kuma zanyi iya bakin kokarina don tabbatarda wannan kungiyar abokantakar nan tamu wallahi kune gata na gaba da baya ba’zan iya rayuwa babu ku ba ….. Da ‘karfi Maijiddah takifto kafafuwanta “Taya kikesan mu gaskantaki a kungiyar tamu bayan kin watsa mana kasa a ido Isha yanzu ko gidan kanki bakidashi bare mota wacce zata haura million Goma kuma na tabbata million Biyu kachal zasu daureki a yanzu.
Duk zufa ya jike Matajiki, Kar.. Kar… Kar…. kakeji rawan jikinta tsaban damuwar datashig
se yanzu ta tuno da sharudodin kungiyar tasu Kuma ko dawasa bazata iya rabuwa dasuba sabida duk fadin Duniya babu mai shiga gonansu yafito lafiya sabida yawan yan daba dakuma sauran Yan ta addan dasuke cikin kungiyar ko Gwamnati ba’ta shiga huruminsu,
abunda sukaga dama sukeyi sabida duk masu arziki ne nagani nafad’a babu matsiyaci cikinsu.
Bata bata lokaci kan wannan tunanin ba, mikewa tai wuf!!! cikin damuwa tawuce Wine
Cabinet nan ta ringimo kwalba daya tabuda, kamar yedda hawaye ke zuba a idanunta
haka take tura ruwan kwalba abaki tanakuma gwada layin Auwal wiski awayarta.
misscalls kenan yanzu babu amsa daga wiski. ’
Tausayinta Maijidda tashigayi ganin irin damuwar datanuna afuskarta nan da nan, Kai tseye tamike kwalbar dake hannunta takarbo “Ya Isa haka” maidoshi tai cikin sauran kwalaben sannan tadau key’n motarta “Ina Kuma Za’kije Jidda? Tambayarda Maisha tai mata kenan. “Taimakon ki zanyi ‘kawata I trust you, nayi miki alkawari cewa daga yau zanfara taimakamiki har zuwa ranarda Zaki mallaki iyayenki, ranarda Zaki rabu da Ma’inah har abada dakuma ranarda zatafl kowace rana farin ciki wato Ranarda zaki mallaki masoyinki Zaid dan Muhammadu.
Kace Maisha Bata taba yin farin ciki irin wannan ranarba, Nan ta ke tawashe hakori tana dariya, cikin sananin mamaki da Farinciki tai tsalle tasauke ajikin abokiyar tata “Na gode na gode na gode Besty, I trust you nasan kece zakiyi tsanadiyar dawowar farin ciki na thank you so much. Hakoran ta’kara washewa “toh dawanne zamu fara? Gidan Auwal wiski zamu fara zuwa sabida ayi sauri akarbo miki kudaden gidanki dake hannun kawunki Saminu daganan sei mu ‘kara sayan wata gidan sannan komai yabiyo baya kuma idan naga damuwa ko rashin kudi zatashige min hanya kawai barinki zanyi ki’kara gaba because l don’t care.
Tun shigewarsu mota Ma’inah take zaune Jugumm Tai ta’gumi tamkar wacce aka aikowa da sakon mutuwa, irin yedda Zaid yarike hannayenta dazun yake rokanta gafara tatuno kamar ba shiba duk wannan mugun kallon datake masa dukji taji sun gushe, Hoton ldanunsa alokacinda yakure mata Ido yake neman gafararta kawai yake yawo azuciyarta, gashin jikinta duk sun mimmike, Dogon eye lashes nasa dakuma hasken ldanunsa kawai
takeji ajikinta, tadaya Bangaren kuwa idan takoma kan dimples dinnan nasa wanda suke a bayyane ako wani alokaci dakuma gashin dasuke hannayensa, harma da d’umin hannunsa dakuma suran jikinsa duk na sha’awar ya mace ce ko ita wacece.
Haka tacigaba da kuramasa ido, duk dacewa zuciyarta na bugawa sosai bata denaba Haka
ta tilastawa kanta take ganin halittan Allah gwanin birgewa.
Tunda yashigo motar bai kulataba, waya yaketayi har Sanda suka iso gida. wannan ya’kira suyi magana wannan yasa ‘ke Kira se magana suketayi tamkar yafi kowa jama’a a duniya. Ma’inah koh tana nan tana sana,arta na kallon bata fasaba. Yana ijiye wayar tai sauri takauda idanuwarta inda tafara lekowa ta window se yanzu ta kula Gidan duk an chanza yayi kyau matuka ko ina flawowi kake gani. Damotar ta’su ‘kirar BMW XLR ta tsaya, Ana bude masa kofa yawuce kai tsaye yasa hannayensa yarike Ma’inah inda tafito cikin sanyin jiki. Sama da ‘kasa tafara bin gidan da kallo duk an chanza gwanin sha’awa “Welcome back Ma’inah Sambo Maidugu”.
A rubuce adeden kofar shiga kumada manyan baki aka tsara rubutun. Nan ne tai murmushi, duk wannan shirin sabida ita akayi ‘Thank you so much Sir. Ta’kara wata murmushin “I really appreciate. Tafada duk idanunta akan wannan sunan nata da aka rubuta a jikin kofa suke.
Murmushin Zaid yamaido mata “I’m glad you like my job Bae. Yakashe mata kyawawan idanun nan nasa tamkar a mafarki “Na’gode sosai. Ma’inah batayi wata wataba nan take farin ciki yamamayeta ta rungu’meshi gam! Tarike shoulders dinsa tamkar jinjira ta kwanta ajikinsa tana murmushi tareda hawaye duk alokaci daya.
Shushu waye kuma wannan? Daddy daman don ita yasa yau kabarni a makaranta bakaje ka daukoniba?
Muna ce kamar wacce aka jefo daga sama, tafad’a cikin nunfashi d’aya. Dasauri Zaid yasa ldanunsa a fiskarta duk hawaye takeyi kayan makarantarta duk datti.
Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun. Nan take yasa hannayensa ko kulawa baiyiba yajefo Ma’inah kasa inda kai tseye yai wajen diyarsa “I’m sorry Muna kiyafewa Daddy kinji’. Yana kokarin matsowa kusada ita tai sauri tajada baya “Daddy kar’ka tabani”. Bata kara ko minti d’aya awajenba aguje tashige bangarensu tana kuka.
Turetan da Zaid yai bata d’aga daga wajen ba anan tacigaba da zama tana binsu da kallon. Ganin hawaye a idanun Zaid yasa tamike nan take tafara zura idanuwana tsoro da tausayi duk yamamayeta alokaci daya “Zaid. Ta ambaci sunan sa ahankali sannan tafara karasowa inda yake.
“Itace tsanadiyar zubowar hawayen Muna, I hate you Ma’inah. Ya’kara kuremata ido yanacewa “Kece tsanadiyar zubowar hawayen yata Ma’inah Sambo Maidugu you are nothing but bad luck to us. Yana fadin wannan shima aguje yai cikin gida yabi sahun diyar nasa.
Nan Ma’inah tazauna bakin kofa tafara zubar da hawaye tana ganin duk kwalliyar da akama gidan dakuma sunanta da aka rubuta asaman kofar aka tsarata da decorations masu sananin tsada da walkiya duk wannan tatafl abanza…
MaiJidda Nan ne gidan Wallahi. Ma’isha ta’kara matsowa har kofa tana lekowa, cikin tsananin mamaki da damuwa, amsardei wanda aka basu tun afarko shi aketa maimaita musu cewa an sai da gidan. Sallati Maisha tafara saukarwa tafashe dawata dan banzan ihu tana rusa kuka “Shikenan Auwal ya danfareni kudi na million Uku na mallaka masa kawai sabida suyimin aiki, because I trust him ban taba tunanin zai iya tafiya da kudadena ba sabida shi ba matsiyaci bane he is Rich enough kuma kowa yasan hakan.
Rasa abun fada MaiJidda tai,jinjina Kai taketayi tun tuni ” Wai kina nufin Auwal Wiskin dakansa kika baiwa kudaden, abun mamakin anan shine kamar yadda kika fad’a Wiski is Rich enough banga dalilinda zaisa yadanfareki ba Maisha kodei yaudarata kikeyi.
Wallahi gaskiya nake fad’a miki duk ya kakkatse layin wayoyinsa gashi kuma munzo nan gidansa ance yaridaga ya tsayar wa Yar CBN president yazanyi besty na shiga uku. Maisha ta’kara rike hannayen Aminiyar nata tana neman mafita.
I’m sorry Besty. Maijidda tafad‘a cikin sanyin murya “Maisha bai kamata kifara kukaba tukunna, ki ijiye wannan case d’in ahannuna ya’kamata muyi handling case dinki na gida tukunna kamin muzo bangaren Saminu da Auwal. Babu musu ta amsa “hakane jidda. Sannan ta’kara tambayarta “toh yazanyi Ina neman mafita?
Gidanku zaki koma yanzu wajen Mahaifinki da Mahaifiyarki kinemi gafararsu, kinuna musu cewa har abada kinyi da’nasanin abubuwnda kika aikata, kicusa musu yardarki cikin zukatansu nan ne zamu nemi hanyarda zamubi murabasu da wannan Yariny’ar “Ma’inah. Maijidda ta amsa kai tseye kuma cikin nunfashi d’aya.
Babu musu Maisha ta tsai da machine inda tai gida kai tseye kamar yadda ta umarceta.
Tun tuni Miemah take zaune shiru cikin babbar falon Aunty Safeenah tana jiran dawowarsu dashike ta’kira Kawu Sambo alokacinda ta’iso ya shedamata halinda suke ciki a asibitin
kuma anjuma kad’an zasu dawo gida. Shiru dei duk ldanuwanta akan TV tana ganin tashan Arewa24 inda ake Shirin Dad’in Kowa. Aguje Maisha ta ‘karaso cikin gida tana ihun sunan Momcy, haka har tahauro falonta tai sallama Kai tseye Tashige. “Ma’inah? Metakeyi anan? Ta tambayi kanta cikin rudani. Aiko nan da nan ta’karaso ciki
“I can’t believe this crazy brat, Ma’inah meye kuma kikeyi anan gidan mu? nayi tsammanin kin koma gidan dadi kuna cin amanata tareda Zaid. Ta’kara fadi da mamaki a fuskarta.
“Zaid kuma? Miemah ta tabe baki. cikin sananin mamaki tamike tana tambayarta waye shi. Muryarta na karkaruwa, mamaki duk yacike Mata Ido “Miemah meye kikeyi anan “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun” Doura ahannu aka Maisha tai tafara Salati, kema gajiya kikayi da Matsiyacin Mahaifin naki kika dawo nan, to claim that Sambo is your real Father …….
Bata ‘karasa furucin nataba yayinda Miemah tadaga hannu, babu tsoro ta sauke Mata mari
afuska “Mind your tongue Maisha Sambo Maidugu.
“How dare you Miemah me tai Miki?” Muryar mummy ce tasa dukkan hankulansu takoma kanta. Dawowarta kenan ta shigo dedei lokacinda Miemah tasa hannu afuskar yarta ta shareta da Mari.
Kuka Maisha tasaka aguje tai wajen mahaifiyarta tana kuka tace “Mumcy ki taimakamin zata kasheni. Share mata hawaye momy tai tanacewa “yi hakuri Yata wallahi komawa
zatayi yanzun nan ba se anjimaba, Babu yadda za’ayi ta ta’kura miki cikin gidan mahaifinki tahanaki sakewa.
Babu inda zataje: Daddy yashigo falon kai tseye yakoma bayan Miemah yanacewa “Kamar yedda Maisha take Yata haka nadauki Miemah amasayin diyata duk daya suke awajena
sabida haka babu wanda ya isa ya koreta cikin gidan nan as far as I still remain the head of the family.
Hmm