TAGWAYE CHAPTER 15

TAGWAYE





CHAPTER 15





Bayan Ma’inah ta sha kuka a kofar Part din Zaid, Tamike jiki a sanyaye tai bangarensu duk dacewa tanasan tashige bangaren nasa domin taduba halinda yakeciki tareda Munah amma babu halin yin hakan sabida ko kad’an bata mance da maganarda Asad daya fada mata alokacinda tazo gidanba cewa Zaid ba yasan ashigemasa bangare kuma kowa nabin umarninsa agidan Aunty Rahila ce kadei take da damar zuwa tareda shi Asad din dakuma diyarsa Munah. 
Ako yaushe alakar dake tsakanin Zaid da Munah takan bata mamaki dakuma rudani, tun ranarda Asad yafada mata cewa Munah Yar Mahaifiyar sace tafara tunanin cewa akwai wata boyeyyen lamari tattare da Zuri’ar tasu. Amsoshin da‘take san samu akansu shine, Wacece Mahaifiyarsa? a ina take? Kuma shin a ina Mahaifinsu yake wanda ako yaushe takanji suna maganarsa amma bata taba ganinsaba ko sau daya. Shin Zaid shi kadei neh dan Muhammad Zabir kodei yanada yan uwa? Meyasa Aunty Rahila tamaye gurbin Mahaifiyar Zaid? Wani dalili yasa Zaid yai adopting ‘Kanwarsa Munah? Kuma meye dalilinda yasa Zaid yakeda yawan fushi akoda yaushe sabida ga dakkan alamu Mutumin ‘kirki ne bashida hayaniya. 
Duk wannan tambayoyin sunada amsoshi sedei a boye suke babu wanda yasani se Zuciyar Zabir dakuma Allah Subhanahu Wata’ala. 
““ Innalillahi wa Inna ileihi rajiun, Innallllahi wa Inna ileihi rajiun’. Hayaniyar dataji akeyi cikin falon Aunty Rahila ce takatse mata tunanin, Nan ta kula cewa harma ta ‘karaso bangarensu. Babu abunda kakeji cikin falon se koke koke da alamun tashin hankali a tsorace Ma’inah tasa ‘kafa zata ‘karaso ciki kenan taji muryar wata Mata tanacewa “How did she mannage to escape? (Ya akayi tabar gidan Ya’rin?) Don Allah Wannan maganar ta tsaya anan kada asake Zaid yasani, Kuma dole se an kamota takoma gidan yari. 
Aunty Rahila kuwa se aikin kuka takeyi bata cewa komai. Nan da nan Gaban Ma’inah yafadi tafara zazzaro idanuwa tana harde da hannayenta kwata kwata ta rasa abundake faruwa agidan kuma da dadukkan alamu akwai matsala babba wacce Kuma ba’asan Zaid yasan hakan. Tausayin Zaid ne ya’kara shiga ranta sabida wannan al’amarin ne yadada tabbatar mata cewa akwai babbar matsalar dake damin Zaid wanda kuma idan Allah ya yarda zata shige rayuwarsa domin tayaye wannan matsalar dake daminsa takuma sanya farin ciki arayuwarsa. 
Da wannan tunanin tasake juyowa kai tseye tai hanyan waje, zuciyarta na bala’in bugawa, gabanta na faduwa,jikinta na karkaruwa har takai bangaren nasa (Zaid). Inda Kai tseye tabude kofa tashige. Wannan ake ‘kira al_jannatud duniya mansion ne guda ginin Zamani mai cikeda guraren sauke gajiya da kayan more rayuwa. Sake Baki Ma’inah tai tanabin gidan da kallo cikin tsananin mamaki. Bata taba tunanin haka gidan takeba har Saida tashige taganewa idanuwarta nan taga’ne cewa wannan matsayin da ake nunawa Zaid matsayin sane sabida yanada gata tun agida. 
Da wannan tunanin tacigaba da shigewa tana dudduba ko ina tana mamaki har Sanda wani dan Sanda ya tsei da ita “Madam ina Zakije? Kai tseye ta amsa masa cewa “wajen Zaid tazo’. Ya San da zuwarki neh? Kada kai tai “A’a bai saniba. Daganan mutumin bai sake cewa komaiba, wayarsa yadauka kurun yakira layin Zaid yana ‘kiransa. 
Dasauri Ma’inah ta dakatar dashi “Ba se ka kirashiba Zan koma yanzu. Juyowa tai asulale 
tai hanyan waje inda wannan securitin yasa’ke tsei da ita Yana mikomata wayar dake hannunsa. Da ldanun mamaki tace Me zanyi da ita? Yace kuyi magana. Ya amsa mata. 
Hannunta na karkaruwa ta karbi wayan tasa a kunne, muryan Asad taji yanacewa Ma’inah kiyi sauri kikaraso ciki akwai matsala. Wace irin matsala? Tana tambayansa yakatse wayar batareda ya amsa mataba. Haka Mainah tamiko masa abarsa cikin tsananin damuwa ta’karaso ciki tana shiga Compound din tafara tambayan Security inda zata tsameshi. Yashedamata cewa Yana PoolSide. Sannan yanuno mata bangaren sabida Pools sunada yawa cikin gidan. Kai tseye ta’karaso wajen. 
Ahankali ta’karaso, inda tahango shi cikin ruwa yanata kaiwa da kawowa. Yayinda Asad yake zaune kan dayan zujerun dakejere agefen wajen yana kokarin kwantar masa da hankali. Ma’inah tana karasowa wajen yamike cikin sananin damuwa yace; ko zaki taimakamin nidei nayi nayi dashi yaki fitowa Kuma tinda yadawo yake cikin ruwa sabida akwai wata mumunar labarin dayazo mana wanda kwata kwata bai kamata Zaid yaji wannan labarin ba. Kuma yakan iya kwana cikin ruwa idan ransa yabaci. 
Ta’yi niyar tambayarsa abundake faruwa kawai sei tafasa sabida wasu dalilai, ahaka ta tsaye ta ‘kasa cewa komai tana binsa da kallo tanakuma sauraran duk rarrashinsa da Asad yakeyi ayayinda Zaid yake dada nitsewa cikin ruwa. Hawaye ne yafara zubowa a idanuwan Ma’inah alokacin. Wata siririyar murya sukaji tun a nesa take ambaton “Yaya Zaid. Ahaka harta’karaso inda suke, se yanzu Ma’inah tamaida idanuwarta akanta “Wata santaleliyar Yarinya ce sa’ar ta, Kalar Ajeboters, dagani kuma tanaji dakanta sosai. Anisa, Meye kikeyi anan? Asad ya 
tambayeta cikin sananin mamaki afuskarsa shima. 
Babu abinda yarinyar tafada zuwa tai har kusada ruwan ta tseya taredacewa; Yaya na rokeka dan darajan Allah da Annabi kafito, ka dade cikin ruwan nan Yayana zakayi ciwo. Idan kuma kai ciwo wa zai kulamaka da Muna. Yanajin sunan diyarsa ya mike tseye duk dacewa idanuwansa na hawaye ahaka yadaure yafito dagashi se wata ‘karamar wando. Nunfashin kwanciyar hankali Anisa tasau’kar yayinda tanufi inda yake tana kokarin rike hannayensa ya kifto, Nan ne Asad yataho da towel yana ‘kokarin sharemasa jiki inda Ma’inah koh tai mutuwar tseye tana binsu da kallo tanakuma hawaye. Zaid bai tseya ko ina ba se wajen Ma’inah kai tseye yarungumota ya ‘kara fashewa da sabuwar hawaye abun tausayi. 
Murmusawa likitan yai yana ‘kara tabbatarwa Daddy cewa sakamakon Miemah ta nuna 
bata daukeda kowace irin ciwo. Wanda tun tuni yake aikin tsanar dashi ya’kasa yarda… 
Har gida Daddy ya gayyato likita, inda yakawo masa sakamakon goje gojen jininda akayiwa Miemah Kuma gojin ta tabbatar musu cewa Miemah bata d’aukeda ko wani irin ciwo ajikinta. Ya gamsu da maganar likitan sedei ya’kasa gamsuwa akan cewa d’an uwansa yayimasa ‘karya ne kawai dan yasamo abun hannun shi. Ransa duk a bace ya tsallami likita sannan yasa layin Saminu awayarsa kai tseye yafara ‘kira, babu amsa da dukkan alamu ya’san abunda yasa ake kiransa shiyasa bai dagaba. Cikin sananin bacin rai yakoma dakinsa… 
Yau tin da yammaci Momy, da diyarta Maisha tareda ma’aikatan gidan suke busy cikin kitchen suna girke girke iri iri, gidan duk ta dauki kamshin nau’in abincin dasuke girkawa. Bayan Sallan Maghriba suka kammala sannan suka shirya dinning dakansu suka had’a komai da komai gwanin birgewa. Turaren wuta suka ballbado cikin falon tana tashi ko ina kanshi kakeji sannan akazo ana shirya falon da kwalliya ababen walkiya da sauransu. Duk wannan shirin dasukeyi Miemah batasan dalilin ba sabida Ma’isha da Mahaifiyarta duk sun had’e mata fiska babu wacce take mata magana cikinsu. Ahaka tacigaba da kallon TV datakeyi tanakuma sace ido tana ganin shirye shiryenda ake tapkawa. Bayan sun kammala komai da komai zuwa sukayi cikin d’akunansu kowa ya rangwad’a ado suka fito gwanin sha’awa. 
Miemah tanazaune cikin falon kuma babu wacce takanka’ mata cikinsu. Wutan falon suka kashe duk baisa tabar wajen ba haka tacigaba da zama tanakuma binsu da kallo ayayinda Maisha tashige d’akin Daddy bayan wasu mintuna suka fito tare inda nan take wutar falon ta haska “Surprise” Momy da Ma’isha duk saka fada alokaci daya. lnda Daddy ya’kara zaro idanuwa yana bin falon da Kallo “Family Re_union” abunda aka rubuta kenan sannan akasaka hotunansu iya su ukun duk hotunan lokacinda suke Amurka ne, yawancin sukuma hotunan Maisha ce tun tana Yar karamarta a gadon asibiti duk sauran hotunan nata da 
aka mammanna agadon asibiti take. 
Daddy Yana ganin wannan yafashe da kuka nan ta’ke ya rungume Maisha yana zubarda hawaye yayinda yake kuma tuna lokacinda take fama da ciwon ajikinta. Mommy ma kanta kukan takeyi inda duk suka hadu suka rungume Yarsu suna kuma hawaye alokaci d’aya. Ma’isha koh hannayenta tasaka ta’kara rungumesu tana murmushi. 
Sake Baki Miemah tai tana binsu da kallo, itama kanta dakyar ta rike hawayenta domin 
hotunan datagani ta matukar bata tausayi, Tausayin Maisha ce tafara shiga zuciyarta nan ta’ke. 
“Wannan hotunan dakake gani su suke hanani kauracewa Y’ata Maisha shiyasa ko menene tai nake goyamata baya sabida kowa yasan cewa ta sha ba’kar wahala abaya bai ‘kamata ta‘kara shan wataba, Kuma idan zaka tuna wannan ne alkawarinda muka dauka alokacin da Ma’isha tarabu da Ciwon Wanda Kai Mahaifinta ka ‘kasa cikawa. Mummy tafad’a cikin nunfashi daya. Bata ‘karasa furucintaba Daddy ya rike hannayenta yanacewa “l’m sorry 
Safeenah kiyafemin. Ya rungumeta suka Kara wata sabuwar hawaye. 
Ma’isha tananan tseye tana aikin murmushi, Wayarta tadauka Kai tseye ta haska musu hotu bata matsa awajenba taturowa Ma Jiddah hotunan sannan takoma gunsu tanacewa ‘kukan ya Isa haka mana, mun shirya mana abinci iri iri akan dining ya’kamata muje muci koh. 
Babu musu suka rike hannayenta suka zauna kowa da kujerarsa. “Miemah ya kika zauna achan ba ya, come and join us. Daddy yafad’a cikin nunfashi d’aya yayinda yakejan santin abincin dayake ci. Tasowa Miemah tai, bata ‘karaso wajenba Maisha tamike cikin sananin Bacin rai tace’ Daddy bamusa sunanta cikin wannan abincin ba, kawai idan tanajin yunwa taje kitchen tai girki da hannayenta. Ta waina idanuwa sannan takoma tazauna. 
Bakiji abunda take fadi bane, kodei kurma ce ke? Momy tadakatar da ita, inda babu musu tajuye tana hawaye takoma d’aki Kai tseye. Daddy yana kokarin magana amma da zaran yaga hotunan nan kawai saiyai shiru yacigaba da cin abinci sedei hawaye ne suka ‘kasa katsewa a idanuwarsa. 

IYA ABUNDA YA SAWWAKA A,YAU KENAN 
PART 17 SPOILER 
A daren Daddy yaje wajen aikinsu Ma’inah sukayi sallama dajuna sabida zai koma America yacigaba da kasuwancin sa, Bai dade awajenba yadawo gida duk dacewa Ma’inah ta dan bata masa lokaci da koke koke domin zatayi kewarsa sosai. Amma dashike cikin daren zai tafi nan da nan ya sallameta. 
Maisha Tasha Kwalliya tareda mahamyarta sun fito pes!! Gwanin ban sha’awa suka fito falo inda akwatunan kayansa suke wajen. ‘Daya bayan d’aya masu aiki suka kai kayan mota sannan Daddy yafito daga baya. Yanafita yaje d’akin Miemah yace itama ta taso sutafi airport tare kada abarta agida ita kadei. Babu musu ta sanya hijabinta suka fito tare. Momy da Yarta duk kallon Mara hankali sukemata, suna fita wajen motoci suka shige, dukkansu akujerun baya suka zauna yayinda dreba yake tuki a gaba. Momy tana manne da mijinta tana hawaye ganin zatayi kewarsa sosai idan yatafi hakama Maisha Jugumm take zaune cikin Motar har tseida suka karaso Airport. 
Aikin kuka Momy takeyi har Sanda jirginsu ta fire sannan suka kama hanyan gida. Ma’isha tana nan tana Bata hakuri har suka ‘karaso gida inda duk suka fito babu dadi jiki a sanyaye. Karfe Goma Sha d’aya alokacin kowa yayi barci. Maisha ce tabude kofan falon Mummy 
tashiga itama tashige sannan taja kofa zata rufe kenan Miemah tasa hannu tanacewa “Me 
kike korinyi bakya gani ne? Babu abunda Maisha tafada Jan kofar tai tarufe Miemah na tseye awaje. 
Momy koh, kojuyawa batayiba haka tamike Kai tseye tatafi dakinta. Ita Maisha ma bata joyoba ta kulle kofan tai dakinta. 
Anan ba ‘kin kofan Miemah ta kwanta tana hawaye ga sanyi gakuma babu komai akasan 
daga tiles se tiles, sanyin iska na busa ta tako ina ….
Wacece Anisa? Ma’inah ta tambayi Asad cikin rudani. Kai tseye ya amsamata cewa “Tsohuwar Budurwar Zaid ce.

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE