TAGWAYE CHAPTER 17

TAGWAYE 


CHAPTER 17A tseye take, jikinta na rawa sanyi ya shigeta sosai, hijabin dakejikintane yake dan rufemata jiki yana taremata ruwan da iska ke hurowa kan Varrendern. Ruwan tazo da iska mai sanani dakuma Thunder wanda take matukar tsorata Miemah. Kuka take tana tuna Mahaifiyarta. Ako yaushe idan ana ruwa irin wannan a gida, Kwantawa take gado daya tareda Umman nata ta jata har kusa da ita, Umma na bata labari har zuwa lokacinda zatayi barci mai kwanciyar hankali. Gashi yau itace aka bari a waje cikin wannan Bakar daren ana ruwa kuma babu wandake kusa da ita. 
Ata Gangaren Mommy kuwa ta dade tana barci mai kwanciyar hankali, a tsakar dare ‘Karar Thunder tatasheta, A firgice tataso nan tabude window taga irin ruwan saman dake zubowa awaje. Maisha tatuno lokacinda take ‘karama tana tsoron ruwa musamman ma ruwan dare, Snow itace kad’ei abinda take sha’awar gani itace kuma likitoci suka hanata wasa aciki sabida yanayin lafiyarta. Ruwan hawaye ne ta sirnano a idanun momy yayinda tatuna irin wahalhalun da Maisha ta fuskanta har na tsahon shekara biyar. Da wannan tunanin tamike babu inda ta tseya se dakin ‘diyar nata inda ta tsameta kwance kan tattausar gadonta tana barci, Kwantawa tai ta rungumeta kamar yedda suka tsaba kwanciya alokacinda take ‘karama,sata a tsakiya suke ita da Daddy su rungumeta tamkar kwai sannan suyi barci. Ahaka mommy tai har zuwa wayewar gari. 
Ana Kiran Sallah Maisha tabude ldo, ganin Mummy akusa da ita yasa tai murmushi, ahankali tacire hannayenta data daura akanta tamike a nitse tashiga ban daki ta daura alwala tafito tana tada Sallah Mommy ta taso inda tashige ban daki itama tai alwala tafito nan dakin Maisha tai Sallah tana idarwa suka koma dakinta ita da Ma’ishan duka. 
Dama ta kosa gari yawaye domin tai sauri tashirya zuwa airport sabida irin wannan 
abunda yafaru da ita ayau wanda ko a mafarki bata taba tunanin hakan zata faru da 
rayuwar taba. Alkhawari ta dauka cewa bazata ‘kara koda second guda a gidan ba ana 
Kiran Sallah idan an bude kofa zatashige ta kwaso kayanta tawuce airport, duk dacewa 
jirgin se la’asar zata taso ahaka zatayi zamanjira har zuwa lokacin. Ai ko tana idar da 
Sallah aka bude kofan Parlour, Kai tseye tashige, tana shigowa kuwa da Momy sukayi karo “Innalillahi wa Inna ileihi rajiun‘ abunda momy tafara fada kenan cikin mamaki tace’ daga ina haka? cikin wannan lokacin jiki duk a jike. Zuba mata ldo Miemah tai, bacin rai yasa ta’kasa fadan komai haka ta chanza hanya tana wucewa. ‘ 
“Wace irin rashin tarbiya ce wannan, ki kwana a gidana, Sannan ki taso ba Gaisuwa Ina Miki magana kuma kina wani hararata tamkar sa’ar kiceni. “Allah yabaki hakuri” Miemah tafada zuciyarta na tafasa tace’ lna kwana. Momy Bata amsa mataba kallonta tai daga sama har ‘kasa sannan ta tabe baki tanacewa‘ Karki zaunamin cikin gida haka, ki chanza wannan jikakkun Kaya ko kifito Rana tabusar dake, Yara ba hankali wallahi Allah ma yasoni da Ma’inata tadawo hannuna tun dawuri da wayasan irin tarbiyar da zata kwaso tadawomin dashi gida tunda dei gashi Yar cikinsuma basu bata tarbiyan ba. 
Miemah tanajin duk wannan munanan maganganun datake akan iyayenta amma batace 
mata uffan ba, haka tawuce daki kai tseye tafara chusa kayanta cikin akwati. 
Tunanin da Mommy take tun wayewar gari itace hanyarda zatabi tafadawa Maisha dawowar Miemah gidansu, ba’tason abunda zai bata mata rai dedei da kwayar zarra, Haka tacigaba da lissafai iri iri aranta. Bayan Miemah ta kammala shirya akwatinta, tai wanka tachanza kaya, Ji’kakkun kayan data cire haka ta chuso cikin akwati tasau‘kar kasa, Momy tana zaune a falo tashigo tana Jan ‘jakarta tace’ Se anjuma. Tabe baki momy tai tana zuba mata ido “Ina kika kinkimo akwati kike zuwa haka? Gida” Miemah ta amsa mata kai tseye. ‘Bakida da labarin Sa’tar da mahaifinki yai neh? Momy tabita da wannan tambayar. 
Miemah ta‘san da maganar sabida tana yawo agari kowa yasan dacewa dan uwan Alhaji Sambo ya saci kudi kuma an ‘kaisa ‘kara kotu sedei tarasa gane dalilinda yasa Aunty Safeenah take mata irin tambayar, kodei so take ta’kara chusa wata bakin cikin aranta bayan abin kunyanda Mahaifinta yai. 
Na sani; Ba’ tason maganar tai tsaho iya abunda tafada kenan. “Kotu ta zartarwa Mahaifin naki hukuncin biya, yanzu ta kar6i dukkannin abunda ya mallaka bashida ko sisi har gidan chan naku ta Maiduguri sun karbe, Atakaice dei iyayenki sun koma wata kauyenda se Allah yasan a ina take suna rayuwarsu achan, sabida haka Kawun ki yayi magana da Mahaifin naki jiya yace anan Zaki cigaba dazama har zuwa ranarda zasu bayyana. 
“Ba gaskiya bace, Iyayena suna gidanmu Kuma babu wanda ya isa ya amshe mana gida, tamu ce. Jakar dake hannunta tasake, yayinda tai loosing balance tazube kasa, kunnuwarta sunyi matukar kad’uwa dajin wannan mumunar labarin, sedei zuciyarta ce ta’kasa gaskanta abunda taji. “Ba gaskiya bace Umma da Abba suna gida Kuma babu abinda kotu ta zartar akansu. Jikinta na rawa tasa hannu a jaka tazaro waya, Hannunta na karkarwa takai layin Ummanta,ta’ kira layin yakai sau goma babu amsa cewa suke ” The MTN number you are trying to call is not reachable at the moment please try again later Thankyou. Ma’ana babu Network a wajen dasuke. 
Duk da na’uran sanyi dake aiki awajen Zufa ce ke zobowa ajikin Miemah tamkar ruwa, Layin Abba ta’kai Kai tseye tafara trying shima the same thing “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun‘. 
Maisha na tseye achan baya tana bin duk wannan abubuwnda suke, duk dacewa bataji dadin dawowar da Miemah tai gidansuba tayi matukar farin cikin ganinta datai cikin 
wannan yanayin because they need to suffer just as she did, Ta godewa Allah dayasa 
Momcy ba irin Matan nan bane masu makalewa yayan dabanasuba, And the best part of it is that she trust her mothers love more than anything else in the world. 
Hotunan dasuka dauka a shakatawarsu tajiya Ma’inah take gani d’aya bayan d’aya awayarta. Tana kai hotonda suka dauka dikkansu “Daddy yana tseye a tsakiyarsu yana dariya, Miemah na rike da hannunsa itama ta washe baki SOsai tana dariya sekuma ita Mainah wacce tafisu duk wangale baki tana manne da mahaifin nata tanakuma Dariya tamkar Albishirin kujerar Makkah akayi mata Kuma dei babu duk sunyi Kyau babu laifi. 
“Kinfisu kyau’ Murya taji abayanta kwatsam ta waiwayo, da sauri tacire Hoton takife wayarta ganin Zaid ne abayan nata babu wata fargaba ya’kara maimaita abunda yafada “Ma’inah cewa nai kinfisu kyau a Hoton meyasa kika cire? Rasa abunda zata amsa masa tai ganin maganar tazo mata banbaragwai haka, yaushe ma suka Saba da juna har yake magana haka tamkar sun saba yin irinta, mema ya banbantasu da Miemah wanda har yakecewa ta fisu kyau a Hoton, idan Kuma Daddy yake nufi toh ai duk kyausa suka dauka. 
Ma’inah; Se yanzu tatuno magana yai mata “Na’am, Ta amsa ba’tareda tafuskance saba sabida tun ranarda sukayi Ido hudu ta’kasa sukuni daga nan kiyayewa take sabida kada su’kara had’a Ido dashi. Bata taba ganin idanun wani mahaluki a duniya wa’inda sukeda matukar Kyau da Jan hankali irin idanun Zaid ba hakan yasa take tilastawa kanta kada su’kara hada Ido dajuna, domin Bata iya barci cikin nitsuwa da kwanciyar hankali idan taga cikin kwayar idanunsa. 
“Ma’inah na fuskanci cewa k0 yaushe idan nayi miki magana kina shiga wata tunani daban ko meyasa? Zaid ya’kara tambayarta cikin nitsuwa kamar yedda yasa’ ba. Zuciyarta ne yafara bugawa yayinda tabude Baki ahankali tace: Babu komai. 
“Alright yayi Kyau” ya tabe ‘karamin bakinsa yana tambayarta “Ina Mamy? 
Muryar Anisa sukaji tafito daga d’akinta tanacewa “Yayana yaushe kashigo? Wajensa tai kai tseye ta rungu’meshi, Babu abunda Zaid yafada hannunsa yad’aura abayanta yanacewa” Anisa yakike? Lafiya Yaya. Tashafa fiskarsa “Zaid I miss you so much. 
Ya Isa haka, yaja baya cikin sanyin murya kamar yedda yasaba yace: Ina Mamy. 
Ta fita” Ma’inah ta amsa masa cikin sanyin jiki yayinda takebin Anisa da kallo. Tana bashi amsa yafita, Anisa takuremata ido cikin bacin rai tace‘ Wa yasoma bakinki cikin maganar, gashi yanzu kinsa ya tafi Yar shishshigi kawai. 
Babu abunda Ma’inah tafada, Tasowa tai kai tseye tai dakinta anan takwanta kan gado tana tinani iri iri aranta har barci tafara daukanta. Ta fara gengedi barcin batayi tsaho ba. ‘Karar wayarta ce tafirgiceta tana duba fiskar wayar sunan momy tagani, Nan ta ke farin ciki ya dibeta Momy ce yau take nemanta. Nan take tadaga “Mommy”. 
Baby yakike? Momy tafada cikin sanyin murya “kinajin dadin gidan Zabir kuwa? ldanfa kinasan dawowa you are free my dear, Daddy ya koma America zaki iya dawowa gida if you miss mommy. 
Murmusawa Ma’inah tai “Yes i miss you momy amma babu komai Mamy tana kula dani iya gwargwado anan. 
Muryar mummy tanuna bacin randa tayi kan wannan maganar da Ma’inah tafada sedei kawai batsarwa tai tace’ yayi Kyau take care of yourself. Da wannan takatse wayarta. 
Haduwa sukayi cikin kebebbiyar wajenda suka tsaba ansar kudi. Maisha tayi matukar mamakin gayyatarta da Auwal wiski yayi bayan bacewa dayai kwana da kwanaki tana nemansa babu labarinsa. Ba wata magana mai tsaho sukayi ba iya gaisuwa dayai mata sannan yamika mata wata Jaka yanacewa: Naji maganganu suna yawo cikin kungiya kina batamin suna Wai ni Auwal wiski na danfareki, Maisha you really disappoint me wallahi ko da wani ne yafada miki hakan bai kamata kigasganta shiba Sabida Nafi ‘karfin haka 
wallahi nafi karfin ace na danfareki,. Danfaran ma Ma’isha narasa Wanda zan danfara se ke. 
Me kake nufi? Ma’isha tai saurin katseshi. Jinjina Kai Auwal yai yanacewa” Babu komai wannan jakar Million bakwai dinki ce muka anso miki gun Saminu Maidugu. 
Dasauri tasa hannu takarbi jakar tana wani irin murmushi na farin ciki da annashuwa “Shege Auwal, gaskiya ne abunda ya’kara karfafa kungiyar nan ta’mu itace hadin kai ba a shiga sabgarmu a kwana lafiya. Allah dei albarkacemu gaba daya. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE