TAGWAYE CHAPTER 18
TAGWAYE
CHAPTER 18
A kwance take kan gado tana rusa kuka iya son ranta, sedei har zuwa yanzu ta’kasa gaskanta maganar da Momy tafada mata, tun tuni taketa faman trying layin iyayenta duk basa shiga. Layin Mai gadin gidansu ta gwada sekuma tai sa’a bugu d’aya ya d’aga muryar wata tsohuwa taji tanacewa‘ Mai wayan ya rasu jiya aka tsinci gawarsa cikin gidan dayake gadi yanzu Yan sanda suna neman Mai gidan ruwa a jallo sabida dashi da Matarsa duk sun gudu, a daren sukabar gari ana zarginsu da laifin kisa. “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Gabobin jikin Miemah ce sukayi sanyi yayinda tasake wayar tafadi ‘kasa “No this can’t be true, I must protect my family, Abba ba’zai taba kisan Kai ba, akwai wata shiri ta musamman dake ‘kasan duk wannan abubuwnda suke faruwa damu and I swear anyone responsible must pay.
Shiru tai nadan wasu mintuna tana tunanin hanyarda zatabi tai solving all this complicated challenges dake faruwa da Iyayenta domin bayan jin wannan bayananda tsohuwar nan dstai, ta’kara tabbatarmata cewa there must be someone who is responsible, Ma’ana akwai wanda yake bayan duk wannan abubuwnda dasuke faruwa dasu Kuma tayi rantsuwar musulmi cewa ko Wanene se tayi iya bakin kokarinta antono masa asiri ya tafl gidan yari, Kamar yedda yasasu damuwa da wahala yazama dole shima yaje gidan yari domin achan tafi dacewa daduk mutane mai hali irin ta’su.
Da wannan tunanin Miemah tadauki jakarta, Karamar school bag ce tad’ansa kaya basufi kala Uku ba tasanya hibinta Sannan tafita Momy ce tatarar a falo kamar kullum tareda Maisha suna cin abinci a dinning. “Se Ina kuma mai kafar Kaza. Momy ta tsei da ita. “Maiduguri. Miemah ta amsa mata kai tseye tace’ I need to protect my family akwai wani makiyinmu dayake shirin sa iyayena cikin damuwa yazama dole in tona masa asiri Kuma wallahi ko wanene sai yaje gidan yari is a promise Miemah bata faduwa I always win sabida haka wannan ma zanyi winning da yardan Allah. Momy Bata tankamata ba, ita koh tanafadan wannan takama hanyarta “Momy amanarta Daddy yabari a hannunki, Maisha tamike cikin nunfashi daya tace‘ Kada kibarta tatafi Daddy zaiyi fushi damu, Mommy kiyi sauri kisa masu gadi surufe gate kada subari taje ko ina. Cikin yanayin ko inkula momy tace’ Isha kyaleta taje na tabbarmiki kamar yedda tabar gidan nan haka zata dawo ta samemu kyaleta Kawai.
Momy kamar ya? Tadawo babu inda zataje. Maisha tashige gaban Miemah aguje tatareta “Dawo, bazaki janyowa mahaifiyata damuwa agun mahaifinaba sabida haka maza koma daki babu inda Zakije.
“Toh Sannu Uwata; Miemah ta tabe baki tanabinta da kallo “Anyway yanaga kin tsargu kodei kece makiyar tamu danake magana ….. Bata karasa kalamanta ba Maisha ta katseta “Me kike nufi? Ja da baya tai ahankali tace’ Mun kyaleki tafi’, kuma agaidamana da shugaban polisawan duniya.
Zasuji. Abunda Miemah tafad’a kenan sannan takama hanya tai tafiyarta.
Aguje Maisha tadawo, shigowa falon tai tamkar korota ake Momy tanamata magana amma ko ajikinta haka tahaura sama kamar jirgi “Isha se Yaushe zaki girma kibarwannan guje gujen naki ne? Ke da Mainah dei babu abunda yabanbantaku se son gudu da wasa. Momy ita kadei take duk wannan maganganun, Maisha bata dade sosai cikin d’akinba tasauko aguje tawuce momy a falo tafita. “Ko ina take saurin zuwa oho Isha busy body. Haka
momy tamike itama tashirya tafita sabgoginta
Paaaaa! Paparpapaaa!! Pwaaapwa!!! Pappappapapaparrr!!! ‘Karan bindigogin dake tashi cikin asibitin Britian City Hospital dake Abuja kenan deden Karfe Sha biyu na dare. Ko Ina ana watsewa marasa lafiya duk sun tashi sabida wannan tashin hankali suna faman ceton rayukansu, Likitoci duk sun watse cikin damuwa da sananin tashin hankali. Dakyar Muhammad Zabir dake kwance cikin dakin Emergency Aminity room yamike inda yaballe robanda aka sanya mishi a hanci, ya ballo drip dake hannunsa yana kokarin ceto rayuwarsa ko ta ina gudu ake rasa inda zai fara zuwa yai gashi wuyansa a daddaure baya iya motsa jikinsa sosai bare yagudu. Haka ya labe karkashin wata drawer a tsorace yatoshe kunnuwarsa, Karan bindiga dei se matsowa take. Alh Zabir yamike cikin damuwa yana kokarin gudu kawai yaji bullet a kafarsa, ahaka yai kokari yaja har sanda yashige wani ofishi sannan ya rufe dakyar ya kwanta cikin Wardrobe din files yasamu yalabe, Bai dade da shiga gurinba ya Suma. ’
Ta Gangaren Gidan Alh Zabir kuwa ‘Karfe Biyarda minti hamsin bayan Sallan asuba Zaid yana kwance tareda Munah a d’akinsa yana ganin News bayan dawowarsa masallaci Kawai
Sai yaga an rubuta labari da dumu duminta a headline ma’ana breaking News…
Innalillahi wa Inna ileihi rajiun’ wuf yamike kai tseye ya dauki Munah dake barci yasata a kafada haka ya gangaro kasa cikin damuwa yahadata da Security akaita bangaren Mamy Nan da nan yatara yan sandansa suka hau convoy zuwa BCA hospital dake birnin Abuja, babu abunda Zaid yake tunani aransa sai lafiyar mahaifinsa kuma ko shakka babu Mahaifiyar sace take bayan duk abubuwnda suka faru sabida daman kowa ya san dacewa fitowarta gidan Yari ba alkhairi bane duk dacewa y’an Sandan China data Nigeria duk sun hada kai suna fafutukar nemanta dawuya sugano ta, Hajiya Turai tamkar Ramin kuregece mai yawan kofofi, tanada hanyoyin buya daban daban, she is a multi billionaire woman kudi ba komai bace awajenta, kai idanma ana lissafa masu kudin Duniya sedei asata a ta Uku ko Hudu (Top 5). Tanada dukiya da ‘kadarori masu d’inbin yawa wanda Mahaifinta yamutu yabari dashike itace kadei Y’ar daya mallaka dukiyar Mahaifinta gaba d’aya tagada Wanda alokacinda mahaifin nata yake raye yafi duk duniya Kasuwanci da Kudi, Atakaice dei mahafiyar Zaid Attajirace sosai.
Alh Muhammad Zabir Zuri’arsa gaba da baya talakawa ne, dakyar ya kammala karatunsa daga farko har zuwa karshe sabida yanayin da kasar tamu take ciki ayanzu idan kai karatunma da kwalinka babu aikin gwanati da mutum zai samu sedei kaita zirga zirga da takarda babu mafita, Amma dayake Alh Zabir Namijin zuciya gareshi aikin makanikancin gyeran motoci yafara ahankali ahankali har yazama babu wanda yakaishi iya makanikanci
kap birnin AbuJa wani Mai gida ya samu attajiri Shi yai masa hanya yakoma China yaci gaba da sana’arsa awata babbar confaninsa na gyaran motoci achan.
Nan suka hadu da Hajiya Turai Mafiya, sayan mota yakaita chan inda tagansa, kallo daya tai masa ya kwanta mata arai babu tsoro ko wata fargaba tafuskance shi kai tseye tai expressing feelings dinta sannan tacemasa Sonsa take tanaso a daura musu aure. Alh Zabir yayi matukar mamakin Jin wannan maganar daga wajen Babbar yarinya, kuma yarinya mai wadata irin Hajiya Turai. Afarko ya tsorata da bukatar Turai sedei daga baya bayan yin shawara da iyayensa dakuma sauran Yan uwansa suka karfafamasa guiwa akan auren sabida acewarsu Aurenta zai zame musu alkhairi zai kuma fitardasu cikin kuncin rayuwar dasuke fuskanta. Mahaifln Turai Balarabe ne d’an asalin ‘Kasar UAE (Dubai) Mahaifiyarta Kuma Yar Kasa Nigeria alokacinda Zabirya Aure’ta marainiya take gaba da baya haka yamaya gurbin uwarta dakuma Ubanta sunyi zaman soyayya da nishadi arayuwar aurensu, Hajiya Turai ta dourashi a kasuwanci, da dukiyarta suka bude konfanunnuka masu dinbin yawa Alh Zabiryayi suna sosai. Sunyi Zaman wadata ya’kuma riketa amana. ’
Bayan sun haihu, Turai ta doura Zaid cikin Kasuwanci tun yana dan karaminsa sukafara business tareda ita dakuma mahaiflnsa, Ya taso cikin wadata da more rayuwa wannan yasa yanzu baya ganin dukiya amasayin komai, sedei duk investment dasuka bude Turai tayi maintaining sunan mahaifinta a takardun akuma accounts din da mahaifinta yamutu yabari kadei ake Tara kudaden duk dacewa sunada damar diba iya abunda sukeso.
Ana nan ana nan da shekaru sukatafi sosai Yan Uwan Alhaji Zabir suka ba’sa Yarinya Y’ar uwarsu ya_aura sabida akarfafa dankon zumunci alokacin ya’rigada yayi suna ya’kuma tara arziki masu dinbin yawa dashike akwai shi da saukin kai bayason batawa y’an uwansa Rai, babu musu ya amince da maganar aure yana China aka daura auren a Nigeria babu wanda yafadawa, a tsammaninsa idon yayi hakan ne zai fiyemasa kwanciyar hankali a gida kuma labarin zatazowa uwar gidansa Turai kai tseye dole ta amince.
A ranarda Amarya ta tare Uwar gida tana Sanfransisko a ‘kasar Amurka ta dade achan tunda tadauki cikin Munah takoma, achan tai goyon ciki tahaihu har yarta tai shekara daya da labarin auren yazomata ba shiri takoma China Ki’shin fitar hankali take dashi nan da nan taji Zabir yafita aranta ta tsanesa kuma ji tayi ya yaudareta ya wulakanta ta, Ba shiri takoma China, tanazuwa ta turo mutanenta Sha’shin Amarya suka hallakata, Bayan taje duba gawan ne suka hadu da Mijin nata shima ta Tsare shi da Adda a wuya kai tseye, Daman niyar kashesu duka tai. Tana rikeda diyarta Muna ayayinda takefaman gudu suka
hadu da danta Zaid, anan ta danka masa amanar Muna, yarasa gane dalilin hakan karbanta yai Kawai yakura mata ldo har tabacemasa. Tun kam tafito Alh Zabir ya kokarta ya Kira yan Sanda aka chapkota nan takoroshi gidanta, Zaid shima yayi Allah wadaran halin Mahaifiyar tasa haka suka koma Nigeria yakai Abba asibiti yanajinya shiko yacigaba da aiki a sabon confanin da ya tsayo a Nigeria (ZMZ) An kamo Mahaifiyarsa an mata daurin rai da rai a gidan yari ta Chinese duk da hakan tana nasaran tseremusu sau dayawa tai excaping sabida kawai tasamu tacinma burinta na hallaka Alh Zabir tareda kwasan dukkan dukiyarta da sukejuyawa shi da dansa Zaid sabida tun ranarda Zaid yataso yake bin bayan Mahaifinsa haka shima yasa ya fita a ranta. Hajiya Turai tanada Bosawa dayawa agari susuke taimaka mata Kuma takan iya bribing ma’aikatan Gidan yarin kansu domin ataimaka mata ta tsere sabida tarigada ta Sha alwashin cewa se ta maida Alh Zabir Talaka kamar yedda yake a da kuma se sunsha Wahala sun gano darajar ta agaresu musammanma danta Zaid, tanaso yasha wahala ya dandani rayuwar talauci nan zai gano anfaninta agunsa sabida itace ta rufamusu asiri suke abubuwanda sukaga dama a duniya.
Sau dayawa tana attacking dinsa amma ba’tasamun nasara, wannan barin gidan yarin datayi takai sau biyar kenan gashi kuma ta inda ta bullo musu ayau.
Aisha tayi kwana biyu cikin daki sedei Saminu yaturomata abinci ta Window kamar yedda yafad’a Sallah ma turomata ruwa yake tai alwala cikin d’akin sannan tai Sallah, sabida tananan akan bukanta na dole se ta fadawa Sambo abunda ke faruwa domin yadauki mataki. Saminu ko shima yana nan akan bakansa cewa babu wani mahaluki a duniya wanda zai bata sunan Maisha a idanun mahaiflnta.
Karfe hudu ta la’asar bayan Aisha tayi Sallah, kukarta tacigaba Kawai taji an bankado kofa kamar daga sama Saminu yashigo yana wani zazzaro idanu tamkar Barawo mai ritaya. Mikewa tai cikin bala‘in tashin hankalin tana tambayarsa Laflya.
“Yazama dole mugudu mubar wannan kauyen tunda wuri yan Sanda suna nemanmu ako wani lungu da tsako, suna zarginmu da laifin kisan Kai. Saminu yafada cikin nunfashi d’aya. Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Kisan kai? Ta daura hannu aka “Wa muka kashe? An gano gawan mai gadin gidanmu a ranarda mutanen Maisha suka taho sanda suka kasheshi kamin sukaraso ciki. Saminu ya amsa mata cikin tsananin rawan jiki.
Gyara zama Aisha tai “Wallahi, wallahi babu inda za’ni, wai ni Alhaji wani irin halitta ce kai haka kawai kasa kanka cikin damuwa ka ringa gudu tsakanin kauyuka kana buya alhalin babu laifinda ka aikata, Kuma kamar yadda nafada cewa babu inda za’ni hakanne, I’m not a criminal meyasa zan ringa buya ina kauracewa yan Sanda Allah ya kiyaye.
Dakata Aisha, yazama dole ki taso mubar wannan kauyen. Saminu yai saurin katseta cikin tsananin bacin rai yace; Idanfa Yan sandan nan sukayi nasaran kamomu ko kinaso ko bakiso dole ki amince da laifinda suke zarginmu na kisan kai ko da wasa kadaki sake sunan Maisha tafito daga bakinki idan kinyi kuskuren yin hakan kuma. Shiru yai nadan wasu mintuna sannan yanufota a hankali yace; wallahi Aisha se na hallaka ki Mark my word.
Da wannan maganar Saminu yamike Kai tseye yai dakinsa anan ya kwaso akwatunansu yasa cikin mota, Babu musu Aisha ta taso a tsorace tashige suka kama hanya.
Maisha ta tara duk yan ta’addanda sukaje Maidugun gidan Saminu. Tare da Auwal dakuma sauran manyan Gayun abokanan nasu suka hadu a gidan Mai Jiddah suna musu gargadi cewa kada susake sunan Maisha ya bayyana a kunnen yan Sanda sabida babu wacce tabasu umarnin kisa son saukinsu yasa suka kashe mai gadi ba’tareda an umarcesuba, komawa Maiduguri kuma ta ‘kamasu inda zasuje suyi iya bakin kokarinta don ganin sunan Maisha k0 sunan wani cikin kungiyarsu bata fito amasayin suspect ba.
Mikewa Maisha tai cikin sananin damuwa da bacin rai tace” Gashi yanzu mun tashi a tu’tar babu, Yan Sanda suna investigating gidan dakuka anso min, niba kudi ba kuma abunda yafi komai bakin ciki shine babu yedda za’ayi ku bayyana kanku amasayin ku ku keda takardan gidan bare ku sayar da ita sabida yin hakan zaisa Yan Sanda su zargemu
amasayin mu muka kashe Mai gadi. Mafitar kawai itace kubi ko tawani hanya kusamu
hujjoji na musamman wanda zata iya tabbatarwa Yan Sanda cewa Saminu da Matarsa su
suka kashe mai gadi sannan suka gudu sukabar gari you just have to frame them kusamo evidence masu yawa cikin sirri ku Maka musu, Wuya bata kamaceniba su sunsaba da wuyan acikinta suka taso Sabida haka karkuji komai nice Nabaku umarni. ’
Nima Nabaku umarni” Mai Jiddah tafad’a babu tsoro tace‘ Kun samu goyon bayanmu duka ku tabbata aiki yayi Kyau ko nawa kuke bukata zamu biya.
Se yanzu Auwal yai magana” Ku tabbata kuma wannan Yarinyar da Maisha tace ta fara zarginta bata samo komai akantaba kada kubari tasamo koda hujja guda ce akan Maisha. Sunanta Miemah Maisha tafada cikin bacin rai.
Angama: Commandern yan daban ya tsara musu zakuma muyi kamaryedda kuka fada, ku kaddarama Saminu da Matarsa sun gama shiga gidan yari, Miemah kuma da yardan Allah kamar yedda tatafi cikin bacin rai haka zata dawo cikin bacin rai.
Da wannan maganar yasa yaransa agaba suka tafi. Nan ne Maisha tai nunfashin kwanciyar hankali.
Ma’inah, Ma’inah, Ma’inah. Jitayi kamar a mafarki ake kwala mata kira Ashe dei Barci take Mamy ce tashigo tana kokari ta tashe ta. A firgice Ma’inah ta taso tana Salati “Ma’inah taso mutafi, Aunty Rahila ta janyota, batasan hawaba bare sau’ka haka ta mike cikin sananin mamaki tabi sahunta ko hijaba bata sakaba haka suka fito Dama mota na jiransu a waje shigewa sukai kai tseye tana tambayarsu abunda ke faruwa Amma babu wanda yake mata magana cikinsu, Cikin motan Aunty Nasibah, Anisa da Muna duk suna ciki, Convoy sukayi tareda y’an Sanda suka hauro titi. Mainah tana mamaki, tsoro yasa ta’kasa cewa komai se gudu suke tamkar barin ‘kasar zasuyi, Suna isa wata asibiti duk sakayi coner d’aya bayan d’aya suka karaso ciki. Mainah ta rasa abunda yakawosu wajen sedei taga rundunan y’an Sanda cikin asibitin tareda y’anjarudu da dama sunata zirga zirga aciki.
Fitowa sukayi alokaci d’aya suna gudu Muna se kuka take Aunty Nasibah na rikeda ita. Duk dacewa Mainah batasan inda suka nufoba haka tabiyosu abaya itama a guje har Sanda suka karaso cikin wata kantamemiyar d’aki babu kowa awajen se tarin likitoci suna aiki kan wani Mara lafiya, dakuma Zaid dake zaune a wata kujera yana kuka.
Kuka sakafayi dukkansu yayinda Aunty Nasibah tatambayi wani d’an jarida yedda abun yafaru. Kwaso labarin yai daga farkonta har zuwa karshe ya tsanar musu. Nan ne Ma’inah ta
tabbatarda cewa wannan Mara lafiyan Mahaifin Zaid ne, taya hakan yafaru? daganan tausayinsu ta’kara shiga zuciyarta sosai da sosai.
” K0 shakka babu Mahaifiyata itace tai sanadiyar faruwar wannan matsalan sabida haka yazama dole ku ganota zata iyayin abundama yafi wannan idan an kyaleta.
Haka Zaid yake fada duk an jaridu dakuma y’an sandarda suke kansa suka amsa. Mainah kam mamaki yarufeta awannan gurin duk abubuwnda takeji suke fada wani banbaragwai haka takegani, Wacece wannan Mahaifiyar tasa? Tambayarda take zagawa aranta kenan.
Bayan sun zauna a asibitin har na tsahon wasu awowi likitoci da Yan Sanda sukace ya’kamata tafi gida tareda shi mara lafiyan sabida acewar yan Sanda chan gida zai fiyemasa kwanciyar hankali akan nan asibiti sabida ako yaushe mutanen Hajiya Turai zasu iya dawomusu. Zaid ya amince da maganar haka akasashi amotar ambulance su Ma’inah kuma sukabi abaya da motarsu. Yan Sanda sun rufe musu baya har Sanda suka iso gida.
‘Karfe shida da minti talatin ana Kiran Sallah Magriba jirginsu Miemah tai landing a Maiduguri Airport. Daman batada wani ‘Kaya daga ita se dan karamin jakarta haka tafito, Allah Yayi kuma tanada dan kud’ade a hannunta. Adedeta tashiga, tafada addreshin gidansu aka kaita Kai tseye. Tana isa ta hango motocin y’an sanda suna shiga da fita cikin gidan Nan taja da baya cikin daba’ra ta haye ta Kofar Bayan gida anan tasa Ido tana lekansu acikin gidan babu kowa cikin se Yan Sanda.
Daga nan gidan makwabciyarsu tawuce dama sunyi cewa idan tazo anan zata sauka har zuwa ranarda gskiya zata bayyana.
Maisha tana ‘karasowa gidansu taga ko ina walkiya yake an gyara gadan da decorations masu tsananin Kyau da tsada. Mamaki take har Sanda tashige, tazuba ldo tanabin ko ina da kallo ko meye dalilin hakan ta’kasa ganewa. Gidan shiru babu wanda tagani awaje bare tasamu tatambayesa abindake faruwa. Kodei Farin cikin tafiyar Miemah yasa momy tasa aka shirya gidan haka. Babu abunda Maisha bata saqa ba . Aiko tana bude kofa taji flawowi daga sama sun fado kanta Sannan aka haska wutan Falon.
Ma’aikatan gidan tagani duk sunyi shiga iri d’aya sunacewa Happy Birthday in Advance Maisha Sambo Maidugu. Tama manta cewa gobe ranar haihuwarta ce, Se yanzu takai idonta sama inda taga hotunanta ne akota ina dakuma hotunan Ma‘inah duk sun manna aka rubuta Happy Birthday in advance Twins. Maisha ta’yi bakin cikin ganin Hotunan Ma’inah aciki sedei kawai batsarwa tai tafara nuna farin ciki tanakuma godemusu.
Momy tana fitowa Maisha tai wajenta cikin farin ciki ta rungumeta sosai tanacewa ” Momcy
thank you so much you are the best Mother in the whole wide world.
Mumy na murmushi tace’ Na’gode sosai baby, gobe da yardan Allah akwai liyafa ta
musamman na shirya muku dake da Yar uwarki a babbar filin taron Ofishinmu, Na san bazakiji dad’in hakanba sabida Baki taba fitowa agun taro tareda Yar uwarki Mainah ba,
Please Ma’isha do it once for your Mother‘s Happiness.
Maisha na binta da kallo har Sanda takammala abunda take fada sannan ta girgiza kai tanacewa” Allah ya kiyaye, Momcy gwara ki chanza shawara wannan kam bazatayi aiki a kai naba I’m sorry, Kada ki manta cewa duk duniya babu wacce nafi tsana irin Ma’inah, Ita tai tsanadiyar gushewar farin ciki na, Ma’inah ta rabani da Mahaiflna wanda yafl kulawa dani fiyeda kowa a duniya. Momcy kinfi kowa sanin cewa Daddy bai taba barin gefena ba alokacinda sunan Ma’inah bata bayyana a Zuri’ar muba.
Hawaye ne sukafara zubowa a idanuwan Maisha yayinda takecewa; Alokacin, dake da daddy baku taba barin gefena ba ako yaushe kuna taredani kuna kuma nunamin dukkan soyyayarku. akan wani dalili rana tsaka zaku bayyana wata yarinya from no where kuce Yar uwa tace, Wallahi ba’zan taba amincewaba kuma Ma’inah ba kowa bace awajena.
Tana fad’an wannan tawuce dakinta a guje tana hawaye.
IYA ABUNDA YA SAWWAKAA YAU KENAN ‘
®NEXT CHAPTER SPOILER®
Mainah tanafita tsakar gida ta hango mutane masu bakaken kaya suna dirkowa daga sama aka daurosu da igiya suna sauka daga saman jirgin Helicopter da bindigoginsu, Nan da nan suka fara har6i “TaaTatatattataaa” cikin Tsananin damuwa da tashin hankali Mainah takoma ciki a tsorace, daman ba kowa a gidan daga ita sei Anisa se Kuma Abban Zaid tareda likitocinsa. Anisa tanajin sautin bindigogin tafito a tsorace suka rungumejuna tareda Ma’inah jikinsu na karkaruwa suka labe karkashin dining (teburin cin abinci) Sautin matsowa take tamkarya ki ake cikin gidan nasu. Dashike duk bangunan kidan bullet proof ce babu wani bullet din dake shiga ciki, Ganin Kofar Falon nasu abud’e yasa Ma’inah ta tashi jikinta na rawa taje tana faman rufe Kofarsausayi tarisketa, sake bindigar akayi kai tseye tashige deden gefen cikinta, Haka tafadi awajen tafita hayacinta. Mikewa Anisa tai cikin tashin hankali “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ Ma‘inah Karki mutu. Tafada da karfi cikin damuwa da tashin hankali ……