TAGWAYE CHAPTER 2

TAGWAYE 
CHAPTER 2
Sun taso cikin tsananin talauci da yunwa… 
A garin Maiduguri sukeda zama, dashike Alhaji Isma’il cikekken dan ‘kabilan Shuwa Arab ne, hakan yasa dawuya ka banbantasu da Larabawa. Saminu da Sambo suna da mugun kamanni wanda duk duniya babu mai banbantasu se mahaifinsu Alhaji lsma’il. 
sana’ar saren itacenda Malam lsma’il keyi yake taimakamusu suna iyaci so biyu a rana wataran so daya. Tun kamin rasuwar mahaifiyarsu burinta shine tsakanin Yan biyun nan 
nata daya daga cikinsu yayi karatun boko kuma yasamu cikekken ilimin boko mai anfani, ‘Dayansu kuma yasamu cikekken ‘karatun Arabiya mai anfani. Hakan yasa Malam lsma’il yayi tsayin daka da tsana’o’i iri daban daban sabida yayi kokarin cika burin marigayiya (Matarsa) kuma mahaifiyar yayansa. 
Shakuwar dake tsakanin Saminu da Sambo shakuwa ne wanda ko a tarihi babu wanda yatabajin y’an uwa irinsu, Saminu ya so dan uwansa Sambo fiyeda yaddah yakeson kansa domin ko’da ya kwan biyu baisa abinci abakinsa ba bazata dameshiba inhar Sambo yana samun abun ci da sha. Hakama Sambo kwata kwata bai damu da kansaba ako yaushe burinsa shine yaga dan uwansa Saminu cikin farin ciki da annashuwa. 
Shekarunsu goma sha biyu aka rabasu, inda Malam lsma‘il yakai Saminu karatun almajiranci achan garin Nijer, Sambo kuwa yacigaba dazama tareda mahaifinsa yana zuwa makaranta. Tun yana kukan rashin dan uwansa har yadena da lokaci suka tafi Akwai shi da ‘kokari a makaranta, duk malaminda ya tambayesa dalilin dagewarda yakeyi kuwa cewa zayyi yana ‘kokari ne ya kammala karatunsa yayi kudi domin yaje garin Nijer yanemi dan uwansa Saminu. Ana_nan ana_nan Sambo yakammala karatun sakandari. Suna shirin tara kudin zuwa jami’a tsausayi ta riskesu, Malam Isma’il yayi hatsarin Mota acikin gari, nan take bai kara minti daya ba yabar duniya. 
Alhaji Sambo yayi matukar kukan rashin iyaye da rashin dan uwansa Saminu domin bayan rasuwar mahaifinsu yatafi kasar Nijer sama da kasa ya nemeshi amma babu alamarsa. 
Da gadon mahaifinsa yacigaba da karatu harzuwa karshe, inda yayi nasaran samun scholarships zuwa ‘kasar Amurka ta tsakiya, anan yakammala ‘karatunsa har zuwa PHD. Yafara kasuwanci mai zurfl cikin Amurka, Lokaci na tafiya kasuwancinsa na ‘kara bunkasa har yafara aika kayansa zuwa kashashe daban daban, yayi suna a duniya babu wanda baisan Alhaji Sambo Isma’il Maidugu ba sabida yawan confanunnukansa dakuma ‘kayansa dake shiga dafita cikin ‘kasashen duniya. 
Kasuwanci ce tahadashi da Safeenah Yarwani balarabe a garin Jiddah dake birnin Saudi Arabia, Soyayar shekara guda sukayi sannan aka daura musu aure suka dawo Nigeria (Abuja) dazama. Sun shafa tsahon shekaru Allah bai basu haihuwa ba, likitocin duniya duk sun dubasu amma babu wata mafita. Chan… Wani abokin kasuwancin Alhaji Sambo ya kwatanta masa wani kwararren malami dake ‘kauyen Agadas wanda aikinsa yake tamkar yankan wuka. Magani kurun zai basu kuma da yardan Allahsun rabu da matsalar 
rashin Haihuwa har abada. Alhaji Sambo ya gamsu da maganar abokinsa, Washe gari suka shirya tareda Safeenah zuwa garin Agadas tareda Abokin nasa Muktar. 
Garin agadas tanada nisa matuka, sunsha hanya kamin su Kai ‘kauyenda Muktarya kwatanta musu. Amma abun mamakin shine wanda sukatarar amasayin malamin. 
Suna isa sega dan uwansa Saminu yafito cikin wani dakin bukka. “Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun Saminu ashe rai kanga rai” Alhaji Sambo ya dafa kai cikin rudani, yayinda yake faman share hawayen dake kokarin zubomasa. 
Littafin dake hannun Malam Saminu ne yafado kasa inda yafara zubarda hawaye Shima yana kokarin komawa cikin bukkansa. Damke hannunsa Alhaji Sambo yayi, A wannan lokacin ya kasa rike hawayensa zubowa suke tamkar lalataccen fanfo “Dan uwana baka ganeni bane? ” 
Fisge hannunsa yayi yakoma cikin bukkansa batareda yatankamasa ba, lrin damuwan daya bayyana a fiskar Alhaji Sambo yasa Safeenah da Muktar rudani da mamaki, duk dacewa sunajin labarin Saminu daga wajen Alhaji Sambo amma abun mamakin shine ‘wani dalili yasa Saminu yake gujewa dan uwansa dasukayi shekara da shekaru basa tare 
Shigewar da Saminu yayi bai sake fitaba har seda gari yawaye, Matarsa ce tafice kofar gida ta tsami ‘Dan uwan mijinta (Sambo) anan wajen dasuka tseya basu motsa ba, ballentana su tafi. Sambo Yana tseye awajen abun tausayi, rigarsa duk ta jike da hawaye, hancinsana yoyo, Sabida yawan kuka dakuma kwana dayayi a tseye, domin shi kwata kwata bai saba wahala ba ya taso cikin gata. Babu yedda Muktar da Safeenah basuyi dashiba amma yaki sauraron su. A hakan suka tsaya tareda shi suna basa hakuri har zuwa wayewar gari. 
Tausayinsa ya matukar mamaye zuciyar Aisha (Matar Saminu), ta ‘kasa rike hawayenta, Alokacin tafashe dakuka tana nunashi da dan yasa “kwarai da gaske mijina yayi gaskiya domin kamar yadda yafada kunada kamanni matuka, Sedai a yanzu kafishi kyaun gani Sabida kana rayuwa cikin daula kuma kana more rayuwarka ba kamar shiba Wanda duk wahala ta cinye mai jiki, Kai ko kana chan da iyalinka kunacin gadon Bawan Allah wanda bai taba aikata muku komai na ……. 
Dakata Malama; Safeenah ce ta dakatar da ita ‘Meyasa kike zarginsa da laifinda bai aikataba, Mijina Sambo mutumin arzikine domin ya nemeku sama da ‘kasa bai ganekuba, hakan yasa ya janye domin azatonsa ‘Dan uwansama ya barduniya shima baya Raye… Safeenah kidena tsawatar mata: Sambo ya katseta cikin karkarwan murya ‘Hakika na san kinfi kowa sanin Son danake yiwa dan uwana Saminu Sabida ke Matata ce kuma ako yaushe muna tare,Amma tunda har yau Matar Saminu dakanta ta zargeni da cin kudin gadon dan uwana, Kuma Saminu ya gujeni, kawai inaga ya kamata mukoma gida domin ni kaina ba jimawa a duniyan zanyiba… 
Juyowarsa kenan Saminu yafice, dama chan Yana laBe cikin daki yana sauraronsu. Yana fita ya rungume dan uwansa Yana hawaye ‘Dan uwa ina mai neman afuwarka, kayi hakuri kagafarta mana ni da mata ta wallahi munyi kuskuren zarginka damukayi…. 
Daga nan ne suka nemi afuwan juna, suka deideita tsakaninsu. 
Saminu bai bukaci dukiya gun dan uwansa ba duk dacewa shi attajirine, iya gadon mahaifinsa yabukata wanda shi kansa ya san Abban su bawani attajirin mutumi bane amma Sedei ya dan taramusu Dukiyar iya karfinsa domin namijin zuciya gareshi. 
A ranar. Sambo ya gayyatosu gidansa dake Birnin Abuja, inda suka tattara kayyakinsu shi 
da Matarsa suka koma Abuja tareda Sambo. Bayan sun koma Gidan ne Sambo 
yafada masa matsalarsu na rashin haihuwa anan suka cigaba da zama har na tsahon wata guda Yana basu magunguna tareda Matarsa Aisha domin itama tun lokacinda ya aureta suka tseda jijiyoyin haihuwarta sabida Saminu bayason yayansa sutaso cikin rayuwar Talauci da damuwa kamar yadda yataso. Domin shi tun yana dan ‘karami burinsa shine Yayansa sutaso cikin rayuwar daula dajin dadi
Ahaka Saminu yacigaba dabasu Magunguna iri daban daban har na tsahon wata uku. 
A rana d’aya Aisha da Safeenah suka dauki ciki. A ranar ne kuwa Saminu ya sai wata madeideicin gida a asalin ‘kasarsu (Birnin Maiduguri) inda suka koma chan tareda Matarsa. Sambo kuwa sukayi masa alkawari cewa idon cikin Aisha ta ‘kai wata tara zasu dawo gidansa domin tahaihu achan asha bikin suna tare. 
Saminu ya tsaya chak da kasuwanci a Birnin Maiduguri har yayi shaguna a gurare daban daban yasamo yara masu kulamasa dasu, A hakan har yafara zuwa Kano yana tsaro Kaya masu yawa Ana dawo dasu Maiduguri. Ana_nan ana_nan har Cikin Aisha takai wata Tara. Bai Manta da alkawarinda yayiwa dan uwansa ba, cikinta wata Tara da kwana biyu suka koma Abuja Gidan Alhaji Sambo. 
A ranar uku gawatan goma, Safeenah da Aisha duk suka haihu Kuma a asibiti daya (Landlord Sambo Private Clinic) dake Abuja,. Asibiti ce mai zaman kanta mallakin Sambo Maidugu. Aisha ta haifi lafiyayyen ya mace kyakkyawa Mai kamada mahaifinta, Safeenah kuwa tasamo Tagwaye mata kyawawa suma masu kamada mahaifinsu, amma daya daga cikin tagwayen nata (Ma’isha) an haifetane da cutar lukemia Wanda ake ‘kira Blood Cancer. Sambo da Matarsa duk sun rude, hankalinsu yayi masifar tashi, Safeenah tunda tahaihu sana’ar kuka takeyi bata motsi k0 magana. Aisha ta sauka lafiya amma tausayin Safeenah yanata kwanciyar hankali. Saminu kuwa kukan dayakeyi ta kusan fin na mahaifin yarinyar domin gani yake kamar da wuya Ma’isha tarayu. 
Nan da nan likitoci sukayi saurin aikasu wata babbar asibitin ciwon Cancer a babban birnin America, inda sukayi shawarar barin Yarsu Ma’ina gun Aisha da Saminu ta shayar dasu (Ma’inah da yarta Miemah). 
Sambo, Safeenah da Jaririya duk suka wuce zuwa America. Aisha, Saminu da jarirai kuma suka koma Maiduguri…. 
Aisha da Saminu sun rike Ma’inah rikon Amana tamkar Yarsu Miemah, Sun nunamata so da ‘kauna matuka dakda cewa basu nunamata sune mahaifanta ba. Ako yaushe Sambo da Safeenah sukan ‘kira ahadasu da Yarsu Ma’inah suyi magana. 
Ma‘isha kuwa jikinta yayi fighting cutar. Shekarar ta biyar tarabu da ita, Likitoci suka tabbatar musu cewa Yarsu ta rabu da ciwon. 
Jininta ya zamto babu ciwo tamkarjinin duk Mai lafiya. Ta taso cikin gata da matukar soyayyan lyayenta, ko dawasa basa son ganin bacin ranta hakan yasa suka boye mata cewa tanada Twin sister, Nunamata sukayi itace kadei Yarsu Kuma Yar gatan Abban ta. 
A ‘kasar Nigeria kuwa. Ma’inah da Miemah sun girma gwanin bansha‘awa.’ sherunsu biyar suka kammala Nursery schl a wata babbar Makaranta acikin Maiduguri. Sunada kamanni matuka wanda hakan yasa ake musu la’kabi da TOD Sisters “Twins of Destiny” duk dacewa kowa ya san iyayensu dakuma asalinsu. 
Sambo yakan ziyarcesu bayan kowani ma’ko domin yaga lafiyar yarsa. Safeenah kuwa takan ziyarce sune bayan kowani mako biyu. Ma’inah ta saba da Iyayenta na asali sosai Kuma tana ‘kaunarsu matuka sedei tunda take a duniya bata taba yin ido hudu da Yar uwarta ba, Kai ko muryarta Bata tabaji ba. Duk da hakan tana matukar Son Yar uwarta Kuma ako yaushe burinta shine Ma’isha tadawo suci gaba da rayuwa tare da ita dakuma Teddyn ta (Miemah). 
Sambo ya dauki nauyin biyan kudin Makarantar yarsa Ma’inah dakuma Yar Dan uwansa Miemah domin duk daya suke awajensa.
Aisha tana matukarji da yanyan nan nata Miemah da Ma inah domin a dalilinsu yasa kowa ke kiranta da momin Twins Sabida Kamanin Ma’inah da Miemah kamanni ne wanda ba kowa ke iya banbanta suba. 
Ma’isha ta girma a ‘kasar amurka tayi ‘karatu har takammala primary school achan. Ta taso cikin shugwaba, son kudi, son rayuwa,jiji da kai da kishi. Domin ko dawasa ba ‘tason 
mahaifinta da mahaifiyarta su kula wani bayan ita. Burinta shine duk Dukiyar Iyayenta yakare a kanta ita kadei ‘she hates second partner… 
Ma’inah da Miemah kuwa sun kammala primary school dinsu ne a wata babbar British school dake Abuja Kuma Makarantar takwana ce, ma’ana Boarding school… 
 Ma’isha ta kammala Primary school tayi graduation, Mahaifinta yaga alokacin ne yafk chanchanta su bayyana mata sirrin da suka Dade suna boyewa, sedei shi kansa yasan hakan zayyi wahala matuka 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE