TAGWAYE CHAPTER 24 B
TAGWAYE
CHAPTER 24 B
Suna shiga Sha’shin, Maisha sai taji tamkar America ta’koma, “Wayyo Allah Zaid I love you’ subucemata kalmar tai tafada a bayyane, Matar dasukazo wajen da’itane tai murmushi “Hajiya Ma’inah ai nan wajen ma karamin wajensa kenan agaskiya dei kinshiga zuri’ar Arziki, Hajiya Turai mafiya babu wanda zai goda dukiyarsa da nata .
Ma’isha tana murmushi sosai yayinda takashe murya tanacewa” Suru’kata kenan. Kwarai da gaske” Matarta amsa mata. Wannan maganar suke har suka kai wata makekiyar waje “Mainah Zaid Zabir” arubuce asaman dakin, Maisha ta’kara karantawa sau biyu, alokacin haushi ne ya’kara shiga zuciyarta sosai, sedei datatuno aurensa zatayi kawai sai tadanji sany’i aranta.
‘Da’kinda aka rubuta Ma’inah Zaid Zabir din ne suka shige, wedding gowns ne bila adadin dama sauran ababen kwalliya da kayan alatu na mata acikinta, Wani dan Sandanda suka tarar cikin dakin ya gaidasu “Hajiya sannufa maraba Mrs Zaid zaki iya shigowa. Matar dasukazo tare ce tace’ Mainah anan Zaki zabi wedding gown duk kalar wacce kikeso akwai ankawosu dazun nan aka shirya miki komai yanzu zabi ce tarage Miki. Ma’inah…. Ma’inah… Mainah.
Maisha tana shigowa dakin tai mutuwar tseye tana ganin kayyakin, kai harma ta’kasa gane
wacce zata zaba
Toya zanyi, Wayar ya karba kai tseye yafara daukanta tamkar camera man, Maisha ko sai styles din hauka taketayi.
Today is my day Maisha Zaid Zabir, wannan hotunan tasaka a WhatsApp status dinta tai hashtag ”Gimbiyar ZMZ. Nan take abokananta duk suka sace hotun suka sassaka a status d’insu suma kada ayi babusu “Besty Gimbiyar ZMZ, Masha Allah Gimbiyar Zaid. Kowa da abinda yake rubutawa a ‘kasan hoton.
Hajiya ankusan daura aurenfa, ya’kamata kiyi sauri mukoma, mutane sun ciki gida saura kiris a daura aurenku. Maisha Tana murmushi sosai yayinda ta amsa “To muje koh.
Zaid yayi zaman jiran wannan Madam din amma haryanzu ba labarinta, Clifford sai ‘kara bashi hakuri yake amma ayanzu kam kawai gajiya yai yami’ke “I’m sorry Clifford agaskiya na gaji”, Sai yanzu Clifford yaji kwanciyar hankali “Toh ai hajiyan ta ‘karaso Sir. Yana juyowa sai ga Ammi agabansa (HAJIYA TURAI MAFIYA) mahaifiyarsa. ‘Kasa magana yai, nan da nan yai loosing balance dinsa yafadi kan kujerar dake bayansa.
Da kaga matar Baba kaga Dollar dakanta, Kalar arzikice kana ganinta kaga ajebota ta karshe Ka’yan dake jikinta gown ce kwalliyar cikin gown d’in stones ne Gold asalin Zinari,
sarkokinta dama warwaron dake hannunta se haske suke suna karban ido, idan ka ganta zakace gold abar banza ce sabida ba komai bane awajenta ita.
“My Son kada kaji ciwo, Tai sauri tarikeshi “Dubekafa, Zaid Kai ne kuwa, duk kabi ka lalace,
Innallllahi wa Inna ileihi rajiun duba yedda kayi baki ‘Dana ne haka ina gaskiya Zabiryaci amanata, Zuwa nayi indauke ka mutafi na’gaji da barinka tareda mahaifinka kana lalacewa cikin talauci, Allah na tuba rayuwa a Nigeria kuma rayuwace Zaid duba yedda kakoma wallahi Allah ya Isa tsakanina da Zabir l hate him.
Kifto hannunsa yai, cikin mutuwar jiki yace “Ammi just Surrender please, yafada yana hawaye masu tsananin zafi abun tausayi. Rungumeshi Hajiya Turai tai tana hawaye itama, yana kokarin kaucewa amma ta riskeshi sosai “Sweetheart don Allah kabini Mutafi, kada kakoma wajen mahaifinka sabida kaima wataran tabbas sai ya butulceka kamaryedda yaci amanata kaima haka zaici amanarka wataran …..
Ammi Ya Isa haka Ba’zan taba barin mahaifina sabida son zuciyarkiba, He is my father,
i love him Ammi try to understand me I will never leave my father.
Ya ‘kara d’aga muryarsa da karfi kamar ba shiba cikin tsananin bacin rai yace” I repeat,
Ammi take note of this, I will never leave my father’s side because of you. Yafad’la cikin
sananin bacin rai yana nunata da dan yasa. Ayau idan kaga Zaid dawuya kaga’neshi sabida yedda zuciyarsa takoma Baki Kirin tsaban bacin rai, fuskarsa har takoma Ja zurr!, bazakama taba tunanin Zaid yana irin wannan bacin rai ba. “
Calm down son kada kadaga murya yan Sanda suna nemana ako ina zasu iya kamoni idan sunga’ne hayaniya muke.
Tabe baki Zaid yai “So What? Duk da na’uran sanyi dake aiki awajen, Zufa Zaid yake hadowa “Ammi I’m your Son amma kin tafi kin barni, kin koromu daga gidanmu na China kawai sabida na ce bayan Mahaifina zanbi, Ke ‘kanki kinsani shine yakeda gaskiya Wallahi Kuma da kece kikeda gaskiya da tuni nabi bayanki. Ammi kinbani mamaki sabida ni ma bai’kamata kiyi trusting dina ba, yanzu zan ‘kira yan Sanda azo akamoki kowa ya huta da bala’i irin naki.
Bai ‘karasa furucinsaba Hajiya Turai ta tsinke shi da Mari a fiska ” How dare you, why can’t you go ahead kakira yan sandan Mana suzo su kamani meyesa baka fitarda wayarka kafara kiransu tun yanzu ba, Go ahead Zaid ka kirasu suzo sukamani su maidani gidan yari. Ta kara d’aga murya da karfi tace’ Go ahead Zaid, Go ahead. Da wannan maganar tajuye tareda Clifford Esthen suka fara tafiya cikib masifar Gacin rai.
Dasauri Zaid yashige gabansu, Ammi tanajiran abunda zaiyi sai kawai taji ya rungumeta yana hawaye sosai yayinda yakecewa” Sorry Mommy, I’m so sorry, Forgive me.Tasa duk ‘karfinta ta tureshi daga jikinta “ls too late Zaid wallahi dakai da mahaifinka sai kun gwammace wulakanta iri na Hajlya Turai Maflya, You must pay.
Tana fadan wannan suka kama hanyarsu. Yayinda Zaid yami’ke cikin tsananin kunan zuci yafice shima, Sanda Drebansa yafito yarikeshi sukaje mota yabude masa kofa yatayashi zama, shiko yakoma driver’s seat yafara tuki. “Ina zamuje sir,. Ganin Babu amsar da Zaid yabashi tasa dreban yai hanyan gida kai tseye.
Suna Isa gida Zaid yahango mutane bila adadin cikin compound d’in gidan nasu ba’yan yawuce first gate, Maza dattijai sunata kaiwa da kawowa wasuko azaune suke kan kujeru wasu suna kan darduma a ‘kasa. Tsaban yedda ranshi ya Gaci ko kallo biyu baiyiwa mutanenba, guntun tsaki yaja yayinda yamaida idanuwarsa cikin mota, Ahaka har suka iso bangarensa. Ganguna yaji ana bugawa dawasu wakoki cikin gidan. Haushi tamkar hadiye ransa. ‘
Yau lafiya kuwa nakejin banguna da tashin kida haka ta Gangaren nawa. Bata fuska yai yace: bayan kuma kowa ya’san babu abunda nafi tsana a duniya irin hayaniya. Haka ya’kara tambayar kansa “Cikin gidan Zaid Muhammad Zabir din ne yau ake irin wannan sautukan? Mamaki duk ya ishi Zaid so yake kawai ya’karaso cikin gidan yaga wainar da ake tauyawa. Dasauri yasa drebansa yafara tuki, suna shiga, yafito cikin sananin mamaki yaduba gidan sama da kasa duk an sa decorations se walkiya take anata buga ganga masu waka sunata waka harma da yan rawa. Kai tseye ya tambayi wani dan sandansa lafiya meke faruwa cikin gidan?
Mahaifinka ne yasa aka shirya komai, duk wannan mutanen gayyatarsu yasa akayi da ‘kansa. Mahaifina? ‘kara daure masa kai mutumin yai, amma bai ‘kara tambayarsa komai ba, aguje yanufo Sha’shin Mahaifinn nasa, yana shigowa falon, wasu yan kauye ya tarar sunata ci tamkar basu taba ganin abinci a rayuwarsu ba. Zaid Yana shiga suka mike, Zuuuu! suka kewaye shi tamkar masifa “Ga ango, Ga ango, su ango ansha kanshi, Mintuna ‘kalilan yarage a daura aurenku. Toshe bakinsa yai harma da hanci, Yana ja da baya ahankali ahankali baiso ya amsa musuba daman cikin Gacin rai yake, maganar ta’su ‘kara batamasa rai suke, irin maganganun dasukeyin yasa shi dole yace”
‘Wai mekuke nufi ne? Aure kuma? Dani dawa?
Mutanen hada Baki sukayi alokaci daya sunata dariya “Laaaa jimun Ango tamkar bai saniba, ‘Daurin aurenka mana da Malama Maisha yar gidan dattijon arziki Sambo Maidugu. Mu nan dakake gani mahaifinkane ya gayyacemu
What., Mahaifina ne Kuma yashirya auren? Why didn‘t he inform me.
‘Kara hade rai yai, filuskarsa tamkar gobara ce takeson tashi’. “Ammi is right, my mother is absolutely right Daman ta cemin wataran Baba sai yaci amanata kamar yedda yaci amanarta, You are right Ammi na tabbata hada baki sukayi tareda Maisha sukeson su aikatamin wannan cin mutuncin, I swear, wallahi Maisha se ta fahimci true colors dina, Lokacin saninta ko waye Zaid Muhammad Zabir tayi.
Mutanen tseyawa sukayi jikinsu na karkarwa tsaban yedda sukaga ran Zaid ta baci, daya bayan d’aya suka fara barin wajen.
IYA ABUNDA YA SAWWAKA A YAU KENAN
®NEXT CHAPTER SPOILER ®
Waliyai sun zauna, kowa yayi shiru za’a fara daura auren Zaid da Maisha kenan akaji jiniyar yan sanda. Motocin sojoji sai shigewa suke babu fashi tamkar bala’i harma da motocin ya’ki rundunar sojoji duk Zaid ya’kira gidansa ayau, Sai gangarowa wajen suke basa karewa.
Take jama’a suka mimmike kowa na zura idanuwa, Sojojin suna fita suka fara tattara mutanen babu wanda suka tankawa cikinsu, tattarosu akeyi daya ba’yan d’aya anasa su cikin mota, dattijai sunata kuka da babban rigunansu ake kwasosu anasa su cikin mota, da matsayin su amma ayau wulakanci ta faru anan wajen daurin auren Tas! sojoji suka kwashesu babu wanda suka bari awajen. Sannan sukaja motarsu sukatafi …..
Hmm