TAGWAYE CHAPTER 6

TAGWAYE
CHAPTER 6
Daga nan babu Inda Ma’lnah ta tsaya se gida, Inda tayi parking motarta tashige, zuciyarta na bugawa tana zaro idanuwa tamkar wacce aka sako daga gidan yari. Kana ganinta ka san akwai tsoro atattare da ita kuma ko kad’an hankalinta ba’a kwance take ba. Ahaka ta ‘karaso falo tana tafiya jugum… Jugumm tana tinani ‘kala ‘kala a zuciyarta ‘lnna lillahi wa Inna ileihi rajiun’ shine taketa nanatawa tana kokarin kauda tunanin Zaid dayake shirin addaban rayuwarta. 
“Sannu da Dawowa Ma’ina ga abincinki nan mun kammala, na shirya Miki a dinning” Mariya tafada. yayinda a firgice Ma’inah ta kad’a kai tanacewa ‘Banajin yunwa ki tattara abincin ki mayar dasu kitchen; Tana fadan wannan tahauro sama, inda tashige dakinta a gajiye ta fada kan gado, tana rintse idanuwa babu wanda tafara gani se Zaid ‘Auzu billahi Mina Sharrin Shaidhanin Rajim’. Daga nan tamike a tsorace ta daura alwala tafito tanata nafiloli wanda ita kanta batasan adadinsu ba tana rokon Allah. Dauki
‘Karfe shida ta_yammaci Momy tadawo daga wajen aiki. Tashigo tana waya da Ma’isha; A’uzubillahi baby kice dei yaukam bakisamu interview’ba… ‘Momcy ke dei bari. Mutanen chan ba suda mutunci wallahi saura kadan mu kaure da fad’a dawani soja awajen, kinajima Momcy wai Kashim ya tseyarwa wani Confanin anya zan samu aikin kuwa?‘ Zaki samu Isha’ta kin manta nasiharda Momcy take miki ako yaushe ‘Do not loose hope’, Kuma don Allah Isha kidena wannan halin naki na fadace fadace kinsan wasu mutane ba mutunci ne dasuba, zasu iya su dake ki Kuma ko ajikinsu…. 
Ta karasa kalmar ne akan gadon ta inda takecewa; lsha kiringa bin duniyan nan a sannu kinji. ‘Kuttt Ma’isha tafashe da dariya momcy kema kinsan diyar taki ne bata daukan ‘Shit, I love you momcy bye bye. Anan ta katse wayarta, Inda Momy tashige bathroom tayi wanka tareda daura alwala, Tana fita tayi sallah raka’a Uku Mangriba, tareda Nafiloli. Bata ta’shi kan sallayar datake ba, tadauki addu’oin “Askar” tana ‘karantawa. Alokacin Daddy yayi sallama yashigo “Safeenah yau naga Ma’inah ta sauya ko meke damunta? “Ma’inah kuma? meya tsameta?” Ta ajiye littafin dake hannunta tana tambayarsa cikin rudani. a Mikewa Daddy yayi yana girgiza kansa alaman abunda yake tunani ya tabbata ‘Wato ke Safeenah kwata kwata na fahimta baki damu da Ma’inah ba, Ki tuna yarkice ya kamata kifini sanin halinda take ciki Amma k0 ajikinki…. Dasauri momy takatse shi ‘Dakata Abban Ma’isha taya zaka zargeni da laifinda nasan ban aikata ba, kafi kowa sanin irin son danake yiwa Ma’isha da Ma’inah su kadei na mallaka taya zan kaurace musu kuma taya zanki basu kulawata bayan dukansu ni kadei ce Uwar dasuke alfahari da ita… “ldan Ina Miki maganan Ma’inah ba nason kikawo min sunan wata Ma’isha saboda naga kin dau dukkan soyyayar ki kin daura akanta bayan dukkansu Yayanki ne kuma alhakkine akanki, dole ki kula dasu dukkansu biyun …… 
Hawaye momy tafara zubarwa “Amma dai Kaikanka ka san dalilin dayasa nake bin lsha a sannu kuma ba’nason ganin bacin ranta saboda irin rayuwar data taso aciki ka fi kowa shagwabata kuma wannan Chanjin rayuwar datayi hanyace ta bacewarta, inba ahankalin muka bitaba wallahi tuni ta ‘kauracewa hanyan kwarei Kuma lsha gyaran Likitoci ne ba cikekken lafiya gareta ba. Ma’inah kuwa Allah yasani Ina santa har cikin zuciyata kuma Ina bata Kulawa dedei ‘karfinda Allah yabani. 
Ya Isa haka ba‘nasonjin wannan kame Kamen naki, wace irin Kulawa kike bata? Shin yau kin tambayeta batun interview datayi awajen aiki wanda ‘tunda safe tafita gidan nan bata sake dawowa ba. Daddy yanata zuba yana sauke haushinsa akanta har tseda abun ya isheta, takatse shi; Ya Isa haka mana haba, na tambayi Isha Kuma tace yau babu aiki, Kashim ya tseyarda wani a Confanin. Kumafa banjima da dawowa gida ba kafahimceni Mana… Anki a fahimta; Daddy ya daka mata tsawa “Nace Miki idon muna magana akan Ma’inah bansan kisa sunan Ma’isha Kuma idon ‘karya kike Shirin tsaromin tuni nayi magana da Y’ata tarigada ta fadamin cewa ta’samo aiki a confanin KSM kuma a masayina na Mahaifinta na tayata Farin cikin hakan. Da wannan maganar Daddy yatura kofa hartseda takusan ballewa yayi waje yanata mita shi kadei. Mommy ma tashi tayi tabiyoshi abaya, shi koh dakin Ma’inah yayi kai tseye yashige. Tana kwance kan gado yasa hannu yajanyota, momy na ko’karin masa magana amma ko kad’an bai saurareta ba. Ma’inah ma tana ko’karin tambayarsu abundake faruwa amma Daddy ya hanata yin haka, janyota yayi batareda ya sanar da ita inda suke zuwaba, tana tambayarsa har tseda suka sauko ‘kasa yace; wani wuri za’mu, wajenda na tabbata Baki taba zuwa da Umman kiba. Ya bud’e mata kofan mota tashige shima yashiga a driver’s seat yafara tuki. 
“Alhaji Sambo baka fahimceni ba, me yasa kake zargina da laifinda nasan ban aikata ba, Ninasan zafin haihuwa sabida Nice na tsunguna na haifeta ita da yar uwana duka, toh meyasa zan fifita san d’aya akan d’aya?“. 
Anan Mommy tazauna tacigaba da kuka har tseda aka ‘kira sallan Isha. Ganin basu dawoba yasa ta tashi cikin tsananin kuka da damuwa tad’aura al_wala. A falon tayi sallah. 
Tana idarwa ko hijabin dake kanta bata chanzaba, haka tashige mota ta kama hany’an 
gidan yarta Ma‘insh. Tana isowa tayi parking awaje, Inda tayi kokari ta’karaso da kafafunta. Tunda tashigo take ko’karin yaye damuwar dake bayyane a fuskarta amma abun yacitura. 
Ma’isha Koh alokacin tana kwance a tsakar parlour tana kallon series film a tashan Zee World inda ake nuna ‘My Golden Home‘. Masu kula da ita suna dannana mata jiki suna yimata abunda turawa suke kira Masage. 
Tanajin sallaman Momy tamike cikin sananin Farin ciki tarungume ta; Momcy sannu da zuwa Ina Daddy? Ta tambayeta da mamaki a fuskartakarta. Sabuwar hawaye Momy tasa’ke, sabida tun Ma’isha na ko’karin tambayarta abunda ke faruwa har tagaji daga baya tadena tana rarrashinta ahakan har tseda zuciyarta tad’anyi sanyi tajanyo yarta jikinta tana shafan kekkyawan fiskar d’iyar nata. Ayayinda ta kwaso dukkan labarin abunda yafaru ta sanar mata. “Momcy wallahi kinfi ‘karfin wulakanci Kuma ko Daddy yayi kad’an ya wulakantaki ballentana wata ‘karamar al_hakki Ma’inah banza, sha Sha Sha“… Da wannan magana Ma’isha tamike cikin bacin rai tajanyo hijabinta “Momcy karki je ko ina, zauna anan kijirani wallahi ko ina suka shigo yau Sena biyosu na koyama wannan la‘a nanniyar hankali. Tana fadan wannan momy tariketa; Ma’isha dake da Ma’inah duk y’ayana ne kuma yana matukar konamin Rai idon kina zagin Y’ar uwarki wanda kukejini d’aya uwa da uba sabida itama ni ce nahaifeta Kuma k0 kad’an ba zanso wani yazageta hakaba,And beside ba tada lafi anan Daddynku ne yake zargina kuma bai shawaran cetaba ballentana ki zargeta da wani laifin… 
“Momcy ya Isa haka, nidei abunda na sani kawai shine babu wata Yar iskarda ta Isa ta batamiki rai takwana lafiya, saboda ke mahaifiya tace Kuma ni Ma’isha Sambo Maidugu kowa yasanni ba’na daukan shit kuma bana barin bashi… Janyota momy tayi, tazauna kusa da ita tanacewa; I love you soo much lsha, bazan iya rabuwa dakeba yata Koda kuwa duniyar nan duka zasu gujeki k0 surabu dake I will always be with you my Child. 
Murmusawa Ma’isha tayi, taturo baki taredacewa; I love you too mumsy, kizo muje d’aki mukwanta rabu dasu let them go to hell ba damuwarmu bane.
Sun shafa tsahon lokaci suna tafiya, se chan Daddy ya gangara cikin wata kataparen restaurant mai suna Chinese food and Drinks. Ma’inah tana zaune shiru kaman mara lafiya cikin mota har seda suka sauko cikin restaurant din tayi magana; Daddy me mukeyi anan? wajen nan abincinsu nada tsada sosai. Tafada cikin sanyin murya. 
Daddy ya rike hannayenta sukaje wani wuri na musamman suka zauna kan wasu kujeru masu tsananin kyau Sannan yayi odan abinci kala daban daban da kayan mar Mari masu kyau da tsada. 
“My dear karki damu da tsadan wannan wajen na san yau bakici abinci ba, shiyasa mukazo nan to spend some quality time with my princess and also to celebrate. Saboda haka don Allah kiyi kokari kici wani abu kinji’. Daddy da hannunsa yad’auki abinci yana bata abaki. “To celebrate what?” Ma’inah ta tambayeshi cikin rudani. 
Murmusawa Daddy yayi “aw harma kin manta maganar samun aikinda kikayi a confanin KSM. Sanda yayi magana ta tuno ‘karyar da tamasa cewa ta samo aiki a confanin KSM wanda alokacinda yatambayeta batada wani zabi ‘karyar kawai itace mafita tunda hartanada hope gobe da yardan Allah idan taje Kashim bazai sallameta ba. Gyada Kai tayi “Aw maganan aiki, eh fa hakane gobe da yardan Allah zan fara zuwa. Bayan sun kammala cin abinci, sun biya ta super market inda Daddy ya sayo mata sabbin ‘kayayyaki nazuwa aiki dama sauran abubuwan bu’kata. Daga nan ne suka koma gida karfe goma_sha_daya da rabi dedei. 
Ma’ina kai tseye tawuce d’aki da kayayyakinta, Daddy koh ya yi niyan zuwa dakin Matarsa amma dayaga lokacin barcinsa ya’yi kawai yawuce dakinsa shima ya kwanta. 
Ma‘inah tana shigowa tazuba duk kayayyakin dasuka tsayo kan kujera inda tayi wanka tafito Kai tseye takwanta tana kokarin rufe idanuwanta tayi barci amma ta’kasa, Ahaka tamikejiki a sanyaye tadaura alwala tafito tana addu’oi. 
Banaso mu sake haduwa dashi a rayuwata, idanuwansa sun hanani barci, zuciyata ta ‘kasa sukuni tun lokacinda muka hada ido dawannan kekkyawan hallitan,Ya Allah karabani da sharrinsa, inma Aljani ne ya Allah rabani dashi har abada. 
Daga nan tayiwa annabi sallati ta tofa, bayan ta kammala karatun alQur’ani ta kwanta k0 barcin zai ‘kara daukanta. 
Ai kuwa tana fara gengedi idanuwan Zaid suka sake dawo mata ‘lnna lillahi wa Inna ileihi rajiun wannan wani irin masifa ne’. Haka tamike ta ‘kara daura al_wala tacigaba da Sallah harzuwa wayewar gari. 
Bayan ta idar da sallan asuba, tashige bathroom tayi wanka cikin mintuna ‘kalilan tasanya Kaya ko Hoda bata shafa a mkarta ba, haka tashirya“ 
Tana fitowa suka gaisa da Momy larai (Ma’aikaciyar gidan) tawuce d’akin momy domin sugaisa. Koda ta kwankwasa taji shiru ta’san momy tarigata tafi wajen aiki, ba tareda sanin cewajiya momy bata kwana a gidan nasuba. 
Daga nan ne tawuce garrage, lnda tashige motarta tafara tuki, har izuwa yanzu ko’kari take ta kauda tunanin Zaid amma abun ya citura har ta kai Confanin aikin nata. 
Tayi parking motarta adedei wajen daya chanchanta, tafice cikin sanyin jiki tayi cikin office inda taketa mamakin girman wajen dakuma tsarin ginin ‘Gaskiya wurin babba ne sosai kuma agaskiya bata taba ganin irin gininba ko a television se yau’ Masha Allah”. Wannan tunanin take har takai wajen receptionist. 
“Madam you are welcome to ZMZ Builders how may I help you?”… Idanuwarta ta zaro kororo kororo, gabanta yafad’i cikin mamaki tace; What Zaid Muhammad Zabir kike nufi? Ko dei kunnawa ne sukaji ba dedei ba. 
lnda maganardatayi yayi dedei da lokacinda Zaid da bo’
sawansa suke shiga, 
Yana jin sunansa ya tsaya chak! ba tareda ya fiskanceta ba yace; Show some respect, confanina Keke so call me Boss or CEO… Daganan yawuce babban ofishinsa dake ‘kebe asaman bene. 
Se yanzu Ma’inah tadaga Kai sama inda taga arubuce ZMZ Builders da manyan baki Wanda ko’da makaho ne idanuwansa zasuja idan yasasu asaman rubutun sabida hasken wuta dasuka sarrafa awajen. 
Hadiyar miyau tayi. Tajuya, tana tambayan receptionist “taya hakan yafaru bayan ta’san confanin a KSM? 
Kai tseye receptionist tayi mata bayanin komai dalla dalla cewa an tseyarwa Zaid Confanin ta zama mallakinsa. Bata ‘kara ko kalma dayaba, haka ta kwaso littatafanta tayi waje sabida babu yedda zatayi tasake haduwa da Zaid bayan abubuwnda sukafaru jiya. 
Kanta duk tabi ta d’aure, tinaninta duk sun ‘kare, Haka tashige motarta tasa key, tana kunnata tinanin ‘karyar datayiwa Dady jiya yadawo mata “Inna lillahi wa Inna ileihi Fitowa tayi asulale ta kwaso dukkan littatafanta, Zuciyarta na bugawa takoma cikin company. lnda tasa’ke komawa wajen receptionist ta tambayeta wurinda zataje ayi mata interview, Sama tanuno mata tana cewa, tahaura zuwa ofishin CEO anan zatabi layin interview, Sannan susake bin layin screening a ofishin assistant. Ma’inah tana dago ‘kanta tahango CEO tseye asaman stairs yana duba aikace aikacenda ake tapkawa a ‘kasa. Da sauri tasauke idanuwarta kasa tafara ambaton “Inna lillahi wa Inna ileihi rajiun” Ya Allah karabani da wannan Ghost din don darajan Annabi …… 
IYA ABUNDA YA SAWWAKA AYAU KENAN ‘ KUBIYON| CIKIN LABARIN KUJI YEDDA CIGABAN ZATA KASANCE. 
CHAPTER 7 SPOILER 
Ma’lna Sambo Maldugu. Seketerin CEO yadanna kararrawa ma’ana lokacin interviewn ta yayi. Kai tseye aka bude mata kofa tamike jikinta yana daukan zafl tashige tana rabe rabe. Rasa abun fada tayi muryanta na karkarwa tace; Sannu ina wuni. Se yanzu Zaid yajuya da kujerarsa  ya d’aga ido ya kalleta ‘You again? Yafada cikin mamaki. 
Kanta na kasa ta gyada kai ” I’m sorry Zaid kayi hakuri wallahi nafi kowa bukatan wannan aikin I’m sorry ka kaddara bamu taba had’uwa ba kuma…. 
Excuse me…. Zaid yadakatar da ita; kin cika hayaniya and I hate talkatives saboda haka don’t think zamuyi aiki tare dake just get out. 
Kuka Ma‘inah tasaka, cikin damuwa tasauka kan guiwowinta tana rokansa “l’m Sorry Zaid please ka taimakamin k0 wani irin aiki kabani nayarda zan karba hannu bibbiyu kayi hakuri ban…. 
“Excuse me, ya isa haka  Yana fadan wannan yadauki littatafanta yaduba kai tseye yasa hannu inda yamikomata wata takarda yanacewa; Welcome to Zaid Muhammad Zabir Builders Company daga yau kece Masinja’ta bcoz I don’tthink you will fits in any other position bayan wannan Sabida haka nabaki zabi “TAKE IT OR LIVE IT”. 
Hmm kunji fa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE