TAIMIYYAH CHAPTER 1 BY Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
TAIMIYYAH CHAPTER 1 BY Ayshat Ɗansabo Lemu✍🏻
*MABUƊI*
*Ina me farawa da godia ga Allah subhanahu wata’ala.Da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna asama,ina roƙo Ubangiji yayi riƙo da hannuna wajen rubuta dai-dai,ya kuma yafe kusakuran da zasu iya kasancewa aciki Ameen.*
*SADAUKARWA*
*Na sadaukar da wannnan littafin gaba ɗayansa zuwa ga duk wata me nakasa,especially masu matsala irin na TAIMIYYAH,ina roƙo ubangiji yasa nakasan ta zame muku alkhairy da ɗaukaka a rayuwa.*
*Page 1*
Matashiyar budurwa ce kwance ƙudundune cikin bargo, jikinta na faman karkarwa alamun zazzaɓi ne ya yi mata kamu me kyau.
Daga gefenta wata dattijuwa ce wacce shekarunta ya fara nisa sosai,don a ƙalla za ta yi shekaru sittin da biyar zuwa sama.Farace tas dattijuwar me tsagen kalangu a fuskanta hagu da dama,kyakykyawa ce wanda a kallo ɗaya za ka zaci cewa Bafulatana ce.Sai dai ba hakan ba ne Bahaushiya ce ziryan, Ubangiji ne kawai yai mata baiwar kyau da farar fata.Hannu ta kai tana janye bargon da budurwan ta ƙudundune a ciki,cikin muryan da ke nuni da tsananin kulawa take faɗin, “Tashi TAIMIYYAH ki ƙoƙarta ki yi wanka ko za ki daina wannan rawan sanyin,idan kin karya yanzu sai Sani yazo ku koma asibitin watakila waɗannan magungunan kaɗai ba za su wadatar da ke ba sai an haɗa da alluran dai da ba a so.”
Ta ƙare maganan tana ƙarisa ya ye bargon da budurwan ta rufa da shi.Nan take kyakykyawan fuskan budurwan da aka kira da TAIMIYYAH ya bayyana,tare da jikinta baki ɗaya wanda take sanye da rigan bacci Ash colour me kauri sosai.Kamannin ta da tsohuwar da ya bayyana sosai zai baka tabbacin idan ba ƴar ta ba ce to akwai alaƙa ta jini me ƙarfin gaske da ke tsakanin ta da dattijiyar matan.Abinda kawai dattiyar zata nuna mata shi ne fuskan manyance ,amma hatta farar fatan na ta irin na Dattijiyan ne.TAIMIYYAH ta yamutse kyakykyawar fuskarta tana sake lumshe manyan idanun ta,muryan ta can ƙasa da ke ɗauke da ƴar shagwaɓa take faɗin,”Wash! Allah Iya ba ki ji kaina ba kaman zai cire wallahi.”
Iya ta dube ta cike da tausayi da kulawa tana faɗin “Sannu kiyi haƙury zai bari,yanzu tashi ki shiga wankan na haɗa miki ruwan ɗumi sosai da za ki ji daɗin sa,Allah ya baki lafiya TAIMI na.”
Budurwan ta amsa da “Ameen.” Tana miƙewa tsaye da ƙyar sai lokacin na kula da cewa tana da tsayi dai-dai misali wanda bai cika yawaba.Sam ba ta da jikin ƙiba sai dai jikin a murje yake cike da tsoka da cikan halitta me ɗaukar hankali.Ta sake lumshe manyan idanunta sabida ciwan da kanta ke yi,kafin a hankali ta kai hannunta na hagu ta dafa guiwan ƙafanta na hagun.Tana me fara takawa zuwa toilet ɗin da ke manne cikin ɗakin.Dattijiyar Iya ta bi bayanta da kallo ƙaunar budurwar da tausayinta na sake ratsa ilahirin jinin jikinta.Tana matuƙar tausayin TAIMIYYAH sai dai ko kaɗan ba ta nuna mata cewa nakasan da ta samu na ƙafa yana damunta.Domin ita kaɗai ce a kullum ta ke ba TAIMIYYAN tabbacin haka Ubangiji ya so ganin ta.Tashi tayi tana me ficewa daga ɗakin mintoci kaɗan ta dawo ɗakin hannunta ɗauke da Mug da ta ciko da zazzafan Kunun gyaɗa da ya ji madara sabida sanin TAIMIYYAH na matuƙar son sa.Dai-dai lokacin da TAIMIYYAH ta fito daga toilet,tana ɗaure da ƙaton towel da tsayinsa ya sauka har zuwa guiwanta.Ƙafafunta na bi da kallo wanda na lura ɗaya ya sirance ɗaya kuma lafiyayye,ta yadda ruwa ke gangara a jikinta kaɗai zai baka tabbacin Allah yai mata baiwa da sulɓin fata,taiwa Hajiya Iya kallo ɗaya tana sakin murmushi.A hankali ta ciga da dafa ƙafanta na hagu tana takowa zuwa cikin ɗakin,da alamu wankan da tayo yasa ta fara jin daɗin jikinta.Iya ta ɗaga kai ta dube ta tana faɗin “Sannu kin ji daɗin jikin ko? ga kununki nan sai ki daure ki fara sha kafin Ladi ta gama soya miki dankalin.”
TAIMIYYAH ta ɗaga manyan idanunta ma su haske ta dubi Iya,cikin sanyin muryanta me daɗi take faɗin “Naji daɗi Iya nagode da kulawa,amma ina ga abar dankalin wannan ɗin kaɗai ya isa.Amma zuwa anjima don Allah ki min faten tsaki da kanki irin wanda ki ke yi ya yi ɗan tsamin yakuwannan shi kawai nake son sha.” Ta ƙare maganan da shagwaɓa sosai a muryanta.”
Hajiya Iya tayi murmushi me faɗi tana faɗin “To shikenan ba ki da damuwa za’ayi insha Allah.Yanzu dai sha kunun ki sha magungunan,sai a sake kiran Sanin ku koma asibitin,ki tafi da duka magungunan sabida su gani ki kuma buɗe baki ki yi magana agaban likitan ba na son wannan miskilancin na ki idan kina ciwo ki ƙi magana.”
Hajiya Iya ta ƙare maganan da mita,wanda hakan yasa murmushi me faɗi suɓucewa daga face ɗin TAIMIYYAH. Wacce ta kammala shafa mai tana ƙoƙarin saka Rigan da ta ciro,ba tare da ta yi magana ba har Iya ta fice.Ta sanya doguwan rigan atamfa Red wanda akai wa adon zanen manyan Flawer da milk and black,ya yi mata kyau sosai tare da haska kalan skin ɗinta,ba ta shafa komi a face ɗinta ba sai lip balm me taushi,qamshin Body mist da tai anfani da shi ne ya cika ɗakin baki ɗaya domin ita ɗin ma’abociya son qamshi ce na ajin ƙarshe.Zama tayi tana ɗaukan Mug ɗin da Iya ta aje tana fara shan kunun a hankali cike da nutsuwa,magungunan ta sha bayan ta shanye kunun.Wani zufa ta fara ji na keto mata hakan ya sa ta miƙe tana ƙara ƙarfin gudun Fan ɗin da ke aiki a ɗakin.
Tsaye ta yi a gaban dogon mirrow ɗin ɗakin tana kallon fuskanta da ya rame sosai a kwanaki biyu kacal da fara ciwan na ta.Sai fararen manyan idanunta ma’abota haske da ɗaukan hankalin mai kallonta,domin wasu irin idanu Allah yai mata baiwan su ma su ɗaukan hankali.Ƙirjinta ta kalla tana me waro ido waje ganin cewa ta manta ba ta sanya Bra ba,gashi fita za su yi sam bazata iya fita ba bu shi ba.Sabida Allah yai mata baiwan cikar ƙirji,sai dai ba wai irin sunyi girman da har suka rankwafa ba ne,kawai dai bata iya fita haka babu Bra dake tare su ajikinta.Wannan sabo ne da ta yi wa kanta tunda ta isa sanya Bra ɗin.Don haka kai tsaye wajen da ta ke aje su ta nufa ta ɗakko tana sauke zip ɗin riganta zuwa ƙasa ta sanya.Wayanta da ke aje bisa gado ya fara ringing,sai ta nufa wajen don ganin me kiran,ganin sunan Sani ya ba ta tabbacin ya zo kenan,ta ɗaga wayan tana gaida shi tare da ba shi tabbacin fitowanta yanzu.
“Iya ga Sanin can ya iso za mu wuce.”
TAIMIYYAH ta faɗi hakan tana kallon Hajiya Iya dake zaune saman ɗaya daga cikin kujerun da suke qawataccen falon na ta.Iya ta ɗaga kai tana sauke ganinta akan TAIMIYYAH da ke sanye da dogon Hijab kalan Red da yai mata kyau sosai.Ta saki murmushi tana faɗin “To sai kun dawo ki kula ki kuma buɗi baki agaban likitan bana son wannan miskilancin naki,kice ma Sanin idan kun dawo ya shigo ina son ganin sa.”
TAIMIYYAH ta amsawa Iya tana miƙewa hannunta ɗaya riƙe da ƙaramin hand bag da ta sanya magungunan da aka ɗaurata akai,ɗaya hannun na dafe da guiwan ƙafanta na hagu,wanda ke bada tabbacin sai da taimakon dafa guiwan shanyayyen ƙafan take iya takawa tana tafiya,a dukkanin cikar halittan ta babu inda ke da naƙasu sai wannan ƙafan na hagu daya shanye ya silance,kyakykyawace da ta mallaki duk wani cikan halitta me ɗaukan hankali,ahaka ta dinga takawa har ta fice daga falon Hajiya tayo waje,idanunta suka shiga ƙarewa haraban sasan Iya kallo kaman me son gano wani abu,kafin ta cigaba da takawa bisa tsarin yadda ubangiji yaso tafiyan nata ya zamo ahaka har ta fito daga sashin Iya baki ɗaya,ta iso ainihin haraban gidan me ɗauke da part guda biyu duk da na Hajiya Iya ne cikon na ukun,tafiya ta cigaba dayi zuciyanta na karyewa a lokacin da idanunta ke hango mata matar da ta fito daga ɗaya part ɗin,bayan matan wani matashi ne ke biye da ita riƙeda da wata ƙatuwar leda a hannunsa,TAIMIYYAH tayi saurin yin ƙasa da kanta tana cigaba da tafiya har ta iso dai-dai inda Hajiya Shuwa suke tahowa,hakan yasa TAIMIYYAH dakatawa daga tafiyan tana jiran ƙarisowan Hajiya Shuwan wacce suke kira da Umma,matar wan mahaifinta ne wacce taiwa TAIMIYYAN wata irin muguwan tsana.
“Ina kwana Umma.”
Sune kalmomin da suka fito daga bakin TAIMIYYAH a lokacin da su Umman suka iso suna shirin gitta ta su wuce,sai dai gaisuwan da ta aikawa Umman yasa Umman dakatawa tana zubawa TAIMIYYAH ƙananun idanunta,fuskanta babu ɗigon fara’a ko kaɗan,tai mata wani malalacin kallo memakon ta amsa gaisuwan TAIMIYYAN sai cewa tayi “Ikon Allah su gurguwa kenan ance baki da lafiya,ke kuma haka Allah ya yoki irin jaraba ga nakasa ga yawan ciwo da wanne za’aji? kuma a hakan ake so wani yazo yace zai kwashi jaraba,ga gurgunta ga yawan cuta kaman sikila,to mu dai kurwan mu kur kada arasa me so ace wataran za’a cinnama lafiyayyun ƴaƴan mu gurguwa raguwan cuta.”
Ta ƙare maganan da jan tsaki tana yin gaba abinta bayan ta kalli ɗan lelen ɗan nata ta maka masa harara tare da yi masa sign da ido alamun ya shige gabanta,ba tare da ta kuma kallon TAIMIYYAH da tai ƙasa da kai zuciyanta na shiga wani irin ƙunci mara misaltuwa ba,manyan idanunta tuni sun fara tara hawaye, ciwan kan da take riritawa taji ya dawo sabo,cikin ɗan hanzari ta dafa ƙafanta me laluran ta fara cigaba da tafiya,sai dai taku biyu tayi taji sassanyan qamshin turaren BENTLEY na isowa hancinta,kaman yadda kafin tayi wani yinƙuri yayi saurin tare gabanta,manyan idanunsa masu kama da nata ya sauke akanta,wani abu na yawatawa cikin maƙoshinsa,cak! TAIMIYYAH ta tsaya still bata ɗago face ɗinta ba don qamshinsa ya gama bata tabbacin ko waye domin kaf gidan shi kaɗai ne mamallakin irin wannan turaren me qamshin da ke kashe jikinta, amon muryansa me cike da ginshira taji cikin kunnuwanta yana faɗin “Kiyi haƙury Sis da halin Umma please! watarana sai labari ko kaɗan bana so kisa wani damuwa a zuciyanki haka Allah ya halicceki kuma yaso ya ganki, mu da ita babu me halitta haka kuma babu wanda isa ya sauya halittan wani face wanda yayisa,ya jikin naki?”
Ya ƙare maganan da jefa mata tambaya,hakan yasa TAIMIYYAH yin jarumtan maida ƙwallan da suka cika idanunta,sai dai duk yadda ta so ɓoye halin da zuciyanta ke ciki ƙaramar zazzaƙan muryanta dake rawa ya fallasata,cikin sanyin muryan da ke kashe zuciyansa take faɗin “Naji sauƙi Yah Sadeeq zazzaɓin ne yaƙi tafiya shine yanzu zamu koma wajen ganin likita,ina kwana dafatan mun tashi lafiya.”
Ta ƙare maganan da gaida shi tana me ɗago manyan idanunta ta sauke akan face ɗinsa,sai dai ganin ita ɗin yake kallo yasa ta sake ƙasa da kanta,tana jin yadda idanunsa ke cigaba da yawo akanta,kafin ya furta “Okey! Allah ƙara lafiya yi maza kije tunda yana jiranki zuwa anjima zan shigo sasan Iya sai muyi magana,take care Angle.”
Ya ƙare maganan da wani karyayyen sauti daya motsa zuciyan TAIMIYYAH,hakan yasa ta gyaɗa kanta tana lumshe idanunta da buɗesu lokaci guda ta cigaba da takawa zuwa parking space inda take hango motan Sani,ya bi bayanta da kallo tausayinta da matsananciyan ƙaunarta na sake kassara zuciyansa.
Ko da TAIMIYYAH ta isa wajen motan Sani baya ta buɗe ta shiga don tana buƙatan kwanciyane sabida yadda kanta ke sarawa,sam baiyi ƙorafi ba domin matsayin driver yake bashi da damuwan duk inda zata zauna ɗin,sannu yai mata yana tada motan bayan TAIMIYYAH tayi ƙarfin halin amsa masa,zuciyanta na mata bitan baƙaƙen maganganun Umma wanda inda sabo yaci ace ta saba da yadda Umma ke kyaran halittan ta da kushe nakasanta tamkar itace tayo kanta a hakan,ba haka Allah yaso ganinta ba, hawaye masu ɗumi suka silalo mata ta kai hannu ta share tana son ƙarfafa zuciyanta kaman ko yaushe,don ganin maganganun basuyi tasiri a zuciyanta sosai ba,sai dai har suka isa asibitin ABU da ke zaria zuciyanta babu daɗi,zuciyanta ya sake nauyi tana tambayan kanta wai har sai yaushe ne zata daina fuskanta gorin halitta da cin fuska daga wasu cikin ahalinta akan yadda Allah ya yota? da ƙyar ta lallashi kanta ta samu ƙwarin guiwan shiga cikin asibitin don ganawa da likita.
A ƙalla ta shafe kusan awa guda kafin ta fito tana faman liliya inda akai mata alluran,domin bayan dukkanin bayanai da taiwa likitan sai ya sanar da ita dole ta amshi allura guda uku wanda zaa jera yi kullum guda ɗaya,ba don rai yaso ba ta amince domin allura na daga cikin abinda family ɗinta suka tsana akira za’aiwa ƴaƴansu tun bayan laluran data samu TAIMIYYAN wanda ta sanadin allurance ta samu wannan nakasan na shanyewan ƙafa ɗaya,wanda hausawa ke kira da shan inna wanda kuma take fuskantan ƙalubale me tarin yawa daga ƴan uwanta da wasu baren daban ma,kai kace itace ta janyowa kanta laluran da kanta ba Allah ne ya ɗauro mata ba…….
Hello! my people gani da sabon salo sabon tafiya irin wanda Ɗansabo bata taɓa zuwa dashi ba,labarin TAIMIYYAH labari ne mai cike da ban tausayi, haɗi da darasi me tarin yawa ga zallan ƙauna da soyayya me motsa zukata,kada ki bari abaki labari a wannan karon kowa ta ƙoƙarta ta mallaki nata akan fara shi me sauƙi da zan faɗi nan gaba kaɗan,ku dai ku cigaba da bibiyata a shafukan da zasu biyo baya don jin ya rayuwan TAIMIYYAH zai kasance.
DOMIN KARANTA CI GABA DANNA WANNAN LINK DIN👇