TAIMIYYAH CHAPTER 2 BY Ayshat Ɗansabo✍🏻

TAIMIYYAH CHAPTER 2 BY Ayshat Ɗansabo✍🏻

 

 

Lokacin da TAIMIYYAH suka dawo gida daga asibitin ana ta kiraye-kirayen sallan zuhur ne,hakan yasa Sani wuce wa masallacin kusa da gidan,ita kuma TAIMIYYAH ta nufo sasan Iya jikinta gaba ɗaya ya saki ga wani zufa da ke keto mata alamun alluran da akai mata ya fara aiki sosai wajen saukar da Zazzaɓin gaba ɗaya,kaman ance ta kai dubanta ga sashen adana motoci na gidan,idanunta suka sauka akan motar Abie ɗinsu,ƙatuwar baƙar LEXUS tuni taji zuciyanta ya fara gudu wani daɗi ya lulluɓe zuciyanta,domin tayi kewansa matuƙa don sun rabu da shigowa garin shi da matansa da qanninta ,ta cigaba da takawa cikin takun tafiyanta wanda take dafe da ƙafanta na hagu,lokacin da ta sanya kanta a sashin Iya shi kuma Abie na shirin fitowa don zuwa masallaci,kaɗan ya rage suyi karo TAIMIYYAH tai baya don bashi hanya,cikin rashin sa’a hannunta dake dafe da ƙafanta me lalura ya zame,tai kaman zata kifa Abie ɗin yayi saurin taro ta yana faɗin “Subhanallah! ki dinga kula Zainab.”

TAIMIYYAH da duk murnan ganinsa ya gama cika ta tai murmushin da suka bayyana kyawawan haƙoranta,cikin zallan murnan daya kasa ɓoyuwa take faɗin “Sannu da zuwa Abie,i miss u so much tare da su Ummie kazo?”

Alhaji Sameer ya gyaɗa mata kai yana sakin murmushi yake faɗin “We ol miss u too dear,tare muke ya jikin naki hope kina samun sauƙi sosai?”

Ta gyaɗa kai da shagwaɓa take faɗin “Naji sauƙi sosai Abie bari in shiga daga ciki na ga masallaci zaka sai ka dawo.”

Daga haka ta raɓa shi ta wuce ya bi bayanta da kallo,yana kallon yadda take tafiya wanda shi yake ganin kaman a wahalce take takawa,tausayin ƴar sa da ƙauna irin ta uba da ƴa ke ratsa sa,sai da ta ɓacewa idanunsa sannan ya juya ya fice daga sasan baki ɗaya.

A cikin sasan Iya kuwa TAIMIYYAH na shiga falon Iya bakinta ɗauke da sallama,idanunta suka fara sauka akan qanwarta Nahar,yarinya ƴar shekaru bakwai zuwa takwas,Iya da Ummie da ke zaune cikin falon ne suka amsa sallaman TAIMIYYAH,yayinda Nahar ta rugo da gudu wajen TAIMIYYAH tana faɗin “Oyoyo! Anty TAIMIYYAH.”

TAIMIYYAH da tayi saurin jingina da jikin kujera don kar Nahar ɗin ta kadata,tayi saurin sakin murmushi tana ware mata hannuwanta Nahar ta shige,ta rungume yarinyan tana faɗin “Welcome My Baby i miss u.”

Raudha yayar Nahar ce ta iso itama tana ma TAIMIYYAH oyoyo,TAIMIYYAH ta rungume su duka sunata murnan ganin juna,Raudha zatai shekaru goma sha ɗaya,kallo ɗaya zakai mata kasan sun haɗa jini da TAIMIYYAH,domin kamansu ɗaya da Iya har farin fatan,yayinda suka ɗakko manyan idanun Abie farare tas,sakin su TAIMIYYAH tayi tana nufan wajen su Iya,Nahar ta biyo bayanta tana faɗin “Anty har yanzu Abie ya kasa sawa a gyara miki ƙafanki ki dinga tafiya irin yanda mukeyi,kuma a daina ce miki gurguwa yadda su Anty Zuhrah ke kiranki.”

Ummie ne tayi saurin buge bakin Nahar ɗin a lokacin da ta iso wajen,yayinda TAIMIYYAH tai murmushi tana duban Nahar ɗin da muryanta me raunin daya fallasa cewa maganan Nahar ya taɓa zuciyanta,ta furta “Nahar ba laifin Abie bane domin bashi ne zai iya sawa ƙafan ya gyaru ba,ni haka Allah yaso ganina karki damu kinji,ni Allah bai nufa in dinga tafiya irin yadda kuke yi bane kuma ki daina ɗaukan maganan da su Anty Zuhura ke faɗi kina sawa a ranki kinji ko?”

Yarinyan ta gyaɗa kai alamun gamsuwa yayinda TAIMIYYAH tai ƙasa tana gaida Ummie,Ummien ta amsa da kulawa duk da cewa fuskanta babu wani alamun ɗoki ko murnan ganin TAIMIYYAN,domin irin matannan ne marasa sakin fuska,sam bawai ta damu da TAIMIYYAN bane kanta da ƴaƴanta kawai tasani,shiyasa tun lokacin da Abie ɗin ya auro ta ya nuna son ta riƙe TAIMIYYAN ta bijera masa,domin a ganinta zama da irin su lalurace kawai da ɗawainiya duk da cewa babu abinda yake gagaran TAIMIYYAN a hakan babu abinda bata iyawa,hatta da ɗaukar ruwa a bucket da duk wani aikin ƙarfi gwargwado tana iyawa,babu abinda ake taimakonta dashi sai ƙalilan,sannu da dawowa Iya taiwa TAIMIYYAH tana tambayanta yadda sukai da likita,TAIMIYYAH ta sanar da ita cewa allurai aka bata uku anyi ɗaya saura gobe da jibi,Iya tai mata fatan samun sauƙi daga haka ta zame jikinta ta nufi ɗakinta don yin wanka da sallah sabida yadda take jin zufa ya jiƙe jikinta bazata iya komiba ba tare da ta sake wanka ba.

Lokacin da ta fito wankan samun su Nahar tayi sunyi ɗai-ɗai a bed ɗinta,suna faman kallon ƙaton photo album dake aje saman Bed side na gado,kallo ɗaya tai musu ta saki murmushi tana wucewa wajen kayanta,doguwar riga mara nauyi ta saka me taushi bata shafa komi ba a jikinta,ta zura Hijab ta tada sallah,bayan ta idar ne ta tasa kan su Raudha zuwa falo lokacin Abie ya jima da dawowa daga masjid,zama sukai gaba ɗaya aka shinfiɗa babban ledan cin abinci wanda aka jera manyan kulolin abinci duk da cewan zuwan bazata sukai bai hana Iya saka Ladi me aiki shirya abincika masu sauƙi ba,tare sukai lunch ɗin gunin sha’awa TAIMIYYYAH na jin farin ciki sosai na ganin ahalinta,duk da cewa sam babu cikakken wani shaƙuwa tsakaninta da Abie ɗin,amma hakan baya hana ta shiga farin ciki a duk sanda zai zo garin walau shi kaɗai ko da su Ummie ɗin,Ummie itace ta fara tashi daga wajen cin abinci tana sanar da Iya cewa zata wuce part ɗinsu,Iya tai mata Allah huta gajiya tai gaba su Nahar ko kallonta basuyi ba bare suyi yinƙurin bin ta suna nane da TAIMIYYAH domin Allah ya ɗaurawa yaran son Yayar tasu,ko don irin kulawa da ƙaunar da TAIMIYYAN ke gwada musu ne Allah masani,lokacin da Abie ya kammala cin abincin yayi hamdala tare da goge bakinsa da tissue,sai ya ɗaura manyan idanunsa akan TAIMIYYAH wacce itama ta gama cin abincin tana gogewa Nahar baki ne,cikin murya me nuna kulawa yake faɗin “Zainab yanzu kin gama NCE ɗinki sai kuma miye plan ɗinki na gaba,aure ko karatun zaki ɗaura?”

Kalman aure daya shigo cikin kalamansa yasa TAIMIYYAH saurin waro idanunta,cikin muryan da ke nuna kiɗima take faɗin “Abie aure kuma? Karatun dai zan ɗaura ni bazan yi wani aure ba waye ma zai auri gurguwa kaman yadda Umma ke faɗi.”

Ta ƙare maganan tana turo baki alamun shagwaɓa,Iya da ke zaune duk tana jinsu ta ɗago tare da saukewa TAIMIYYAH harara tana faɗin “Ashe ban hanaki irin waɗannan kalaman na banza ba TAIMIYYAH,don Allah ya yoki ahaka sai akace shikenan bazaki samu masoyin da zai aureki a haka ba,to bari kiji wanda suka fiki nakasama sunyi aure har sun haihu bare ke da babu abinda ma yake gagaranki,kije gidan Malam Inuwa ki kallon gurguwan da bata ko iya tashi ta miƙe a nannaɗe take amma tayi aure ƴaƴanta goma sha biyu zar sunanan suna taka doran ƙasa,don haka ki iya bakinki ki kuma daina ƙoƙarin ja da ikon ubangiji,ita wacce kike ji abakin nata tana cewa bazaki auru ba sai ki zuba mata ido ki ga idan itace ta halicceki da zata hana Allah ikon sa,ni a nawa ma babu wani karatun da zaki ɗaura Allah ya kawo me so kiyi aurenki kawai ki huta.”

Tunda Iya ta fara magana ko tari babu wanda yai har ta dasa aya cike da sababi da jin zafin Hajiya Saratu a ranta,Abie ne ya dubi mahaifiyan na su yana faɗin “A’a Iya idan har tana son cigaba da karatun kar a tauyeta,abata dama ta ɗaura idan yaso tana cikin yi Allah ya kawo me son sai ayi auren,amma zaman haka bazai yiwu ba,Zainab wani skull ɗin kike so gashi yanzu ana cikin wannan strike ɗin,ni kuma bazan so ki tafi wani gari ba sabida laluranki, karatunki a kusa da gida zaifi,don haka sai dai ajira aga janyewan yajin aikin malaman sai asan abinyi,idan akwai wani plan ɗin da kike dashi ina jinki tell me.”

Abie ɗin ya ƙare maganan idanunsa akan TAIMIYYAH da daɗi ya cika ta,na jin cewa Abie ɗin bazai hanata cika burinta na son yin karatu me zurfi ba,cike da ɗoki take faɗin “Abie zan fara yin wani Computer Skull kafin a dawo daga yajin aikin,ina so in samu certificate na Computer Training ɗin,kuɗin form da na registration kawai zaka bani,a can wajen Congo ne sai Sani ya dinga kaini yana ɗakko ni ko Abie?”

Alhaji Sameer ya jinjina kansa cike da gamsuwa yake faɗin “Eh hakan ma yayi kinyi tunani me kyau,karki damu zan baki kuɗin komi da komi,amma Iya tace an baki allurai uku meyasa kika yadda aka fara,kinsani sarai bana so ko kina manta alluran shine silan laluranki Zainab.”

Ya ƙare maganan da faɗa sosai wanda yasa TAIMIYYAH bashi haƙury,tare da sanar dashi magungunnan ne basui mata ba dole sai an haɗa da alluran,tare da su Raudha ya bar sashin zuwa part ɗinsu da suke sauka idan sun zo daga Lagos ɗin.Bayan fitan su Iya ta kalli TAIMIYYAH da ke ta faman murnan zata shiga Computer skull,ta maka mata harara tana mitan faɗin “Ayi dai mugani duk son karatun mutum da ƙinsa da aure indai lokacin mutum yayi dole yai auren ba.”

Kafin TAIMIYYAH tace komi suka jiyo amon muryansa,wannan dai muryan nasa me cike da isa yake doka sallama daga bakin ƙofar ɗakin Iyan,Iyan ce ta amsa sallama tare da bada izinin shigowa,qamshin turaren BENTLEY ya riga isowa cikin ɗakin kafin gangar jikinsa ya shigo,idanunsa ya sauke akan TAIMIYYAH da ta miƙe tare da dafe ƙafanta ta fara takawa don komawa ɗaki ta kwanta,baiyi magana ba har ta shige corridor ɗin da zai sadaka da Bedrooms ɗinsu,illa ɗauke kansa da yai ya maida dubansa kan Iya yana takowa cikin falon,a kujeran 2 seater ya zauna yana fuskantan Iya ya fara gaida ta,ta amsa fuska a sake tana faɗin “Yanzu Sadeek ka dawo tun jiya sai yau zaka shigo gaida ni,to kayiwa kanka ne aiko baka shigo ba ka zo don mutuniyar ka dana tabbatar kaji bata jin daɗi ko da yake naga yanzu ƴar wasan ɓuya kuke tunda uwarka bata ƙaunar jituwan da ke tsakaninku.”

Ta ƙare maganan cike da sababi hakan yasa Sadeeq sake haɗe fuska,yana wani taɓe baki yake faɗin “Ke dai Iya kin faye son nacin magana ɗaya,waya gaya miki wasan ɓuya muke ita ɗince dai bansan meyasa bata son haɗuwan mu ba yanzu ko don taga ta gama zama Big Girl ce oho.”

Iya ta taɓe baki itama tana faɗin “kadai ji da ƙaryan turancinka,ya wajen aikin naku ina fata dai komi na tafiya yadda ya dace ko?”

Sadeeq ya gyaɗa mata kai kawai,kafin ya miƙe ya nufi wajen cin abinci yana faɗin “Iya akwai abincin da zan iya ci anan,cikin gida tuwon shinkafa akayi ni kuma banso,ai na ga motar Abie ashe sun shigo.”

Iya ta amsa da “Eh aiko sai ga su babu sanarwa,sai ka duba akwai ragowan shinkafa da miya sai dai mayyan Salad ɗin ta juye shi ta kai fridge.”

Tuni ya gane wa take nufi don haka baice komi ba sai nufan hanyan ɗakinta da yai,Iya ta bi bayansa da kallo tana taɓe baki ba yau ta gama gane jikan nata ya kamu da son ƴar uwan nasa ba,sai dai bata ji ko sama da ƙasa zasu haɗene zata bar TAIMIYYAH ta aure shi,sabida ƙiyayyan da uwansa take gwadawa TAIMIYYAN,shiyasa tai biris bata taɓa nuna musu daga shi har TAIMIYYAN tasan abinda suke ciki ba……..✍🏻

DOMIN KARANTA CI GABA DUBA WANNAN LINK DIN👇

https://arewabooks.com/book?id=62d13b36e4924f3d4350f75c

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE