TAIMIYYAH CHAPTER 3 BY Ayshat Ɗansabo Lemu
TAIMIYYAH CHAPTER 3 BY Ayshat Ɗansabo Lemu
Yana sanya kansa cikin ɗakin sassayan qamshin daya kama ɗakin ya doki hancinsa,ya ɗan lumshe idanu yana jinjina tsafta da son qamshi irin na TAIMIYYAH,halayyanta da ke sake saka shi jin ta aransa sosai da yaba ƙoƙarinta akan kula da kanta, duk da laluran ƙafanta sam bata da ƙyuiya da son jiki,kwance ya hange ta tayi ruf da ciki tare da tokare hannayenta da pillow waya riƙe a hannunta,sam bata ji sallamansa ba sai qamshin turaren BENTLEY da ya buɗe ɗakin,hakan yasa ta saurin tashi zaune tana sauke manyan idanunta akansa,fuskanta a sake take faɗin “Yah Sadeeq shigowa kayi,ina yini.”
Harara ya zabga mata yana takawa zuwa wajen stool da ke gaban madubi ya janyo ya zauna,idanunsa ya mayar kanta kafin ya buɗe baki cike da ginshira yake faɗin “Wannan yarinyan kin girma da yawa kin fara raina mutane ko? Ba kina kallo na shigo ba amma ki kai tahowanki sabida baki ƙaunar haɗuwan mu yanzu ko? to yau sai kin gaya min yadda akai na zama dodo har da kike guduna.”
Ya ƙare magana babu alamun wasa ko sassauci a face ɗinsa,hakan yasa TAIMIYYAH sake dubansa ya sake jefa mata harara,ganin hakan yasa ta tsuke baki tana faɗin “Kayi haƙury ni fa ba gudowa nayi ba,kasan banda lafiya to kwanciya na shigo yi ina jin jiri ne.”
“Allah ya sauƙe ya baki lafiya,amma meyasa tun wancen week ɗin dana shigo kika ƙi bari mu haɗu har na koma?”
Yadda ya tsare ta da ido yasa ta kauda kanta,ba tare da tace komi har sai da ya sake maimaita tambayansa sannan ta ɗago ido ta dube sa kafin ta shagwaɓe murya tana faɗin “Umma ce fa tace in daina shige maka inba haka ba duk randa ta sake ganina da kai saita ƙarisa ɗayan ƙafan nawa na zama gurguwan me sosai.”
Yadda ta ƙare maganan muryanta na ɗan rawa yasa jikinsa yin sanyi,cikin taushin muryansa me kauri yake faɗin “Amma sau nawa zance ki daina damuwa da maganganun Umma,haba Baby meyasa kike son kafa Hujja da Umma ni kuma kina azabtar da zuciyata why?”
TAIMIYYAH da tai ƙasa da kanta ta ɗago tana ƙoƙarin danne hawayen da ke son zubo mata,cikin rawar murya take faɗin “Dole in saka maganganunta araina Yah Deeku,Umma bata so na bansan miye laifi na don na kasance gurguwa ba,bani nai kaina ba inda ana ba ɗan Adam zaɓin ya zaɓi yanda yake son halittansa ya kasance bana ji akwai wanda zai zaɓi nakasa,amma ita sam ta kasa gane bani ce na zaɓi zamowa a haka ba,yanzu ba da bane Yah Deeku nasan ciwan kaina a yanzu,maganganunta suna ƙona zuciyata kaman yadda wuta ke ƙona itace,dole in kiyaye duk abinda zai dinga janyo min gorin halitta,kayi haƙury Umma uwace a guna amma zuciyata bazata iya juran yawan aibantani da takeyi ba,shiyasa tunda ta nuna bata son shaƙuwan dake tsakaninmu dole mu koyi nisanta da juna.”
Zuwa lokacin da TAIMIYYAH takai ƙarshen magananta tuni hawayen da take dannewa sun ɓalle,suna zarya a saman kyakykyawan face ɗinta,Yah Sadeeq da tunda ta fara magana ya tsura mata ido,ransa yai matuƙar sosuwa da hawayen da take zubawar,ya sani tafi shi gaskiya domin kaman yadda ta faɗi ne babu wanda yasan ciwan kansa da zai so jin yadda Ummansu ke kyaranta tana aibanta nakasanta kai kace TAIMIYYAN irin guragunnan ne da basa ko iya tafiya,cikin muryansa da ya bayyana raunin da zuciyansa shi ma yayi yake faɗin “Yanzu kina nufin sabida Umma ne zaki daina kulani bayan kinsan zuciyata ta riga ta kamu da ƙaunar ki Zainab,ya kike so inyi da wannan sabuwan ɗabi’an da sam bazan iya jure masa ba?”
Sanin bazata amsa masa ba yasa shi kai tsaye cigaba da faɗin “Lokaci yayi da zan fito fili insanarwa da Umma ke nake so,so kuma da aure ko hakan zai tabbatar mata da cewa alaƙanmu dake ya wuce shaƙuwa na ƴan uwantaka,zallan soyayya ce mara algus.”
Kukan da TAIMIYYAH ta sanya masa ne yasa shi tsura mata ido cike da mamaki,baki buɗe yake kallonta wani abu na yawo a cikin zuciyansa,cikin muryan kukan take faɗin “Ka dubi girman Allah Yah Sadeeq karka faɗawa Umma wannan maganan,wallahi kasheni zatayi nina sani,don Allah karka shigo da abinda kasan bazai taɓa yiwuwa ba,alaƙanmu ta tsaya iya na ƴan uwantaka, ka riƙe girmanka na Yayana wanda nafi so da shaƙuwa dashi,me sharemin kuka na da bani dukkanin ƙwarin guiwa,don Allah kada ka rusa wannan alaƙan ka shigo da batun da bazai taɓa yiwuwa ba illa jefa rayuwata cikin garari.”
Kuka takeyi sosai zuwa lokacin domin ita kaɗai zata iya gayawa duniya irin tsanan da Umma tai mata,ba ta ji ko za’a tashi duniya zata iya amincewa da Yah Sadeeq ɗin ya zama abokin rayuwanta,ta sani yana son ta don ya riga ya jima da fallasa mata sirrin zuciyansa,ita ɗince har yau ya kasa jin taƙamaimai miye a zuciyanta game dashi,baya hango kowace irin soyayya a idanunta daya wuce na ƴan uwantaka,irin na wanda shaƙuwa ya shiga tsakani,cikin tsananin ɓacin rai ya daka mata tsawan da yai saurin sata sake rushewa da kuka me ƙarfin gaske,ta kai hannu tana toshe bakinta ganin yadda ya taso yana nufota,ta shiga matsawa da baya-baya tana cigaba da toshe bakinta kuka nacin ta,zama yayi daga bakin Bed ɗin yana kai hannu ya janyota baki ɗaya zuwa jikinsa,kafaɗunta duka ya kamo yana girgizata yake faɗin “TAIMIYYAH me kike nufi da waɗannan kalaman,kina so ki gaya min tuntuni ni kaɗai nake haukata ke zuciyanki bata kamu da soyayyata ba? Ki sanar dani ni kaɗai nake shirme na kome?”
Yadda yake magana yana ɗaga murya da sake jijjiga kafaɗunta yasa TAIMIYYAH sake rushewa da kuka,sai dai kafin tayi wani yinƙuri sai shigowan Iya suka ji cikin ɗakin,ta tafa hannu tana salati tana faɗin “Me zan gani Saddeeku dukanta kai bata da lafiya kome,ko kaima ka fara kurɓe kurɓen zamanin nan da samari keyi ne bamu da labari? To sakarta tun ranka bai ida ɓaci ba,ka kuma sanar dani tun farko ma uban mi ya kawo ka ɗakinta?”
Sadeeq da ransa ya gama ɓaci sai ya saki TAIMIYYAH yana ballawa Iya harara yake faɗin “Bansani ba miye naki na shigowa nan ɗin kaman an kiraki.”
Iya takai hannu ta bige bakinsa tana faɗin “Yi min shiru mara kunya,kuma ka gaya min me tai maka da zaka tasa ta agaba kana jijjiga kaman ka biya sadakinta sabida tambaɗa da fitsara,to ahir ɗinka ka kiyayeta ince dai soyayya ce kakema wannan haukan,to inma son ta kake tun wuri ka cire bazata so ka ba,inma ta fara dole ta daina kowa yai ta kansa,indai ina raye TAIMIYYAH ba zata aure ka ba uwar ka taje can ta zaɓo maka matan aure amma ba dai Zainab ba,wuce ka kabar min sasa tun bansa an kira min uwar ka da uban ka sun maka iyaka daga shigowa nan ɗin ba.”
Yadda Iya ta rintse ido tana yayyafin masifa yasa Sadeeq ficewa cikin zafin nama,zuciyannan kaman ya faso ƙirjinsa sabida ɗaukan zafi,Iya ta bishi da tsaki kafin ta koma kan TAIMIYYAH tana lulluɓeta da faɗa kaman zata duke ta,cikin faɗan take cewa “In banda ke ɗinma banza ce uwar sa har nan tazo tai miki iyaka da ɗanta,amma shine zai lallaɓo ya tasaki agaba har da kama jikinki yana girgizawa baki fito kin bar masa ɗakin ba,yo ko dai kema son nasa kike? Aiko da kinyi asaran duniya kin kuma ba mutane kunya me zakici da mutumin da uwarsa bata da aiki saina aibanta halittanki tana kyaranki,to ahir ɗinki wallahi idan kika biyesa har ya yaudari zuciyanki sai dai ku mutu da son juna amma bazaki aure sa ba indai ina numfashi kuma na isa dake,shashashu kawai marasa hankali.”
TAIMIYYAH dai kuka kawai takeyi ba tace uffan ba har iya ta gama bambaminta ta fice,sai ta zame ta kwanta tana cigaba da kuka me tsuma zuciya,ita sam bata taɓa jin cewa zata iya son kowani namiji bama bare Yah Sadeeq ɗin,meyasa Iya zata ɗauki zafi da ita har haka? ta cigaba da kukanta zuciyanta na ƙuna ,kiran wayanta da akai ne yasata tsai da kukan bayan ta ɗauki phone ɗin ta ga cewa qawarta Haneefa ce me kiran,basu jima suna magana ba sukai sallama da juna,TAIMIYYAH ta nufi toilet ta wanke face ɗinta ta fito,dogon Hijab ta zura ta ɗauki phone ɗinta ta fito,a falo taci karo da Iya har lokacin bata fasa ƙananun mitanta da ta saba idan ranta ya ɓaci ba,kallo ɗaya taiwa Iyan ta ɗauke kai tana takawa zuwa ƙofan fita falon ba tare da tayi niyyan tankawa Iya ba,ganin da gaske fita TAIMIYYAH zatayi ba tare da ta kula ta ba,ya sanya Iya ɗaga murya tana faɗin “Au binshi zakiyi don na kore sa,ko kuwa gidan ubanwa zaki kina fama da kanki?”
TAIMIYYAH da takaicin Iya ya gama cika ta,ta juya ta balla mata harara kafin ta furta “Ni part ɗin Abie zani tunda yau abin naki akaina zaki sauke shi.”
Yadda TAIMIYYAN tayi magana cike da shagwaɓa da jin haushi yasa Iya sakin murmushi,tana faɗin “Oh’oh’oh me yai zafi daga faɗin gaskiya kuma ƴar nan,dawo kije ki kwanta tunda ba lafiya ne dake ba,ni ina jiye miki ne yadda uwarsa ta tsaneki me zaki ci dashi Allah na tuba,ko da kike a haka ai kinfi ƙarfin ajinsa ke ɗin matar manya ce.”
Wani hararan TAIMIYYAH ta ballawa Iya tana juyowa ta dawo cikin falon,kujeran kusa da Iya ta nufa ta kwanta tana faɗin “Nidai Iya wallahi fitinanki idan ya tashi yana bani tsoro,yaushe rabon da kika ga na kulasa amma sabida son ɗauramin laifi har da faɗin ko na fara son sa ne,ni bana son sa kuma bazan so kowa bama bare aje ana min gori,auren ma bazanyi ba ko zanyi kuma zanyi fatane Allah ya bani me nakasa irin tawa ta yadda ƴan uwa da danginsa babu wanda zai min gori,amma Yah Sadeeq bazan taɓa iya bashi zuciyata ba Iya don Allah ki kwantar da hankalinki,ni abinda kawai zakiyi ki birgeni ki samu Abbah da maganan kice masa baki son sake jin shi Yah Deekun ya tada maganan.”
Iya da ta tsurawa TAIMIYYAH ido tsananin tausayin ta na faman ɗawainiya da ita,ashe dai TAIMIYYAN na son auren gori take gudu sabida nakasan ta,zuciyan Iya ya motsa da wani irin yanayi me wuyan fassara,ji take da komi nata zai ƙare akan TAIMIYYAN ƙafanta ya dawo dai-dai da zata iya sallamawa,sai dai ita ɗin shaida ce akan irin yawon manyan asibitocin ƙashi da sukai tun TAIMIYYAN na ƙarama har kawo yanzu,amma ba’a dace ba ƙasar waje ne kawai ba’a fita da ita ba,ita da kanta TAIMIYYAN da ta gaji da wahala ta roƙi a ƙyaleta haka ubangiji ke son ganinta,Iya ta furta “To shikenan karki damu zanyi magana da Sanin,ni dai abinda nake so kisawa ranki gorin da ake miki bazai sauya komi ba,akan duk abinda Allah yai nufin kasancewansa,kada kisawa zuciyanki lallai sai me lalura irin taki zaki bawa dama,ina fa lura da dake sarai kina samun masoya kece kike kore su ashe sabida wannan manufan ne dake ranki? To wallahi ki kiyayeni angaya miki sai me lalura ne irin taki kaɗai zaki aura ki samu kwanciyan hankali da soyayya? Wannan shirmenki ne kawai ke dai ki dinga addu’an Allah yai miki zaɓi mafi alkhairy kawai.”
TAIMIYYAH kai kawai ta gyaɗawa Iya alamun gamsuwa da kalamanta,daga haka suka kulle wannan babin,Iya ta ɗakko mata zancen aminiyanta Hajiya Juwairiyyah,wacce suka rabu da saduwa da juna,cikin hiran Iya ke sanar da TAIMIYYAH da zaran ta sake samun sauƙi zasu kaiwa Hajjajun ziyara,ita dai TAIMIYYAH jin Iya kawai take yi amma sam a ranta bata son zuwa ko’ina, ita sam tafiye-tafiye basu dame ta ba…….✍🏻
Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*
*Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.*
_Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka_ 👇🏻
*DANNA LINK DIN NAN KASHA KARATU👆🏽👆🏽👆🏽*
*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
*Recharge* – inda ake shiga domin saka kudi cikin account.
*Balance* – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.
*Credit/Debit Card* – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.
A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).
——–
DOMIN SAMUN CI GABA DUBA👇