TAIMIYYAH CHAPTER 4 BY Ayshat Ɗansabo Lemu

TAIMIYYAH❤️✍🏻 *

Kwanaki biyar da suka biyo baya TAIMIYYAH ta samu sauƙi tayi garas,don ta gama amsan alluranta har tana harkokinta,tun safiyan yau da ta tashi tana jin cin Meat pie,sai dai basu da nama ya ƙare dole sai ta aika an siyo gashi Nura almajirin Iya kwana biyu bai zuwa ya tafi gida,bayan tayi wanka ta shirya wajen ƙarfe sha ɗaya har da rabi,ta samu Iya a ɗaki don sanar mata zata fita cefanan yin Meat pie ɗin ta dawo,don kuɗi sosai take dashi a hannu,sabida duk idan Abie zai koma yana barin mata kuɗi sosai a hannunta,gefen gadon Iya ta samu ta zauna ganin Iyan akan dadduma alamun idar da sallan walhan ta kenan tana addu’a,wayanta da taji yana ring acikin ƙaramar jakan hannunta ta ciro,ganin sunan Mubarak yasa ta share kiran tare da maida wayan silent,Mubarak wani course mate ɗinta ne da sukai NCE tare,shi a dole son TAIMIYYAH yake da gaske sai dai ita kuma bai taɓa birge taba,mutuncinsa da take gani da irin taimakonta da yake yi akan karatu yasa ta kasa blocking ɗinsa,Iya ta waiwayo ta zubawa TAIMIAYYAH idanu,wacce ke sanye da Hijab kalan Pusha Pink daya haske farar fatanta,tayi kyau ƙwarai duk da cewa babu komi akan face ɗin illah manyan fararen idanunta da ta sanyawa kwalli,sai bakinta da sai ka kalla da kyau zaka gane ta goga lip gloss,wani kuma zaiyi zaton pink ɗin janbaki ta saka domin pink lips gareta.

“Sai ina kuma da hantsinnan TAIMIYYAH?”

Iya ta jefa mata tambayan har lokacin idanun Iyan na kan TAIMIYYAH,TAIMIYYAH ta dubi Iya tana sanar da ita inda zata da abinda zai kaita,Iya ta gyaɗa kai tana faɗin “To shikenan sai kin dawo ki kula da kyau,ni bana son yawan zuwa kasuwan da kike da Nura na nan ma babu inda zaki gaskiya,ga ɗari biyu can saman madubi idan kinga Goro me kyau ki siyo min.”

TAIMIYYAH da ta miƙe tana me dafa ƙafanta ta fara tafiya take cewa”Bar shi Iya akwai kuɗi sosai a hannuna bayan Goran ma har Gautan Yalo idan na gani duk zan siyo miki.”

“To Allah yayi albarka TAIMI na,Allah fito min da suruki nagari.”

Cewan Iya tana bin bayan TAIMIYYAH da kallo,cike da so da ƙauna haɗi da tausayinta me zurfi,a ciki TAIMIYYAH ta amsa addu’an Iya tana cigaba da takawa har ta fice daga ɗakin,lokacin da ta fito haraban gidan sai ta dubi part ɗin Abie da ke kulle,ta cigaba da tafiya tana jin kewan su Nahar na ratsata don kwanaki biyun da sukai ba ƙaramin ɗebe mata kewa da sanya ta farin ciki sukai ba,sam bata kula da fitowan su Zuhura daga Sashin su ba,sai da ta kusa fita daga gate ɗin gidan sai ji tayi kawai an janyo Hijab ɗinta ta baya,ta waiwayo tana sauke idon ta akan Basma,kafin ta buɗe baki don musu magana Zuhura ta riga ta da faɗin “Dallah! Malama bamu waje mu wuce sauri muke kinzo kina wannan shegen tafiyan naku na guragu,salon a bangajeki ki faɗi ki janyo ma mutane masifa,yanzu gaba ɗaya na ga wani tashen girman kai kike ji tunda Yaya ya zubda ajinsa yace ke yake so,ko mai zaici da gurguwa bansani ba,ko da yake kila kyawu da dirin jikin yake mawa,inma hakan ne banda abinsa idan Kyan da nonuwan ke ruɗansa ga lafiyayyun ƴan mata nan da suka haɗa komi mitsuww!”

Zuhura ta ƙare maganan da jan dogon tsaki,Basma na taya ta yayinda TAIMIYYAH da suka ja gefe tayi saurin durƙusawa ƙasa,tuni hawaye sun fara zarya a face ɗinta,har suka fice daga gate ɗin ta kasa koda motsawa,kanta na duƙe tana ji zuciyanta na mata wani irin zafi kaman ya kama wuta,ko kaɗan bata fiya ganin laifin su Zuhuran akan duk irin cin mutuncin da suke mata ba,tafi ganin laifin Umma domin a wajenta suka fara gani,itace ta koya musu hakan duk da cewa TAIMIYYAN age mate ɗin Zuhura ne watanni biyu kacal ke tsakaninsu,amma ace har Basma da take qanwan bayanta ta san taci zarafinta akan kawai ta kasance me nakasa,wasu hawayen masu tsananin zafi suka sake wanke face ɗinta,tayi saurin buɗe jakanta tana ciro hanki da ke ciki ta shiga share hawayen ,tana rarrashin kanta kaman yadda ta saba,don wannan ba shine karon farko ba,idan zasu haɗu so dubu to tana da tabbacin sai sun goranta mata sunci fuskanta,taso fasa fitan kawai ta koma amma sai tayi tunanin Iya zata tsare ta da tambaya,da zaran ta gaya mata yadda sukai da su Zuhuran kuma to abin bazai kyau ba domin Iya wanke ƙafa zatai ta je taci mutuncin Umma da su kansu su Zuhuran,wanda hakan bakomi yake sake janyowa TAIMIYYAN ba sai tsantsan tsana,don haka kawai ta miƙe duk jikinta yayi sanyi ta cigaba ta kawa har ta fice daga gate ɗin gidan,idanunta sun rine sabida kukan da tayi amma bata da zaɓi haka ta cigaba da tafiya bisa yadda Allah ya nufeta da takawa,ta miƙo layin nasu sosai tana cigaba da tafiya,wasu yara da suka zo wucewa ne suka zuba mata ido suna kallonta,ƙaramin cikin su ne ke cewa “Laah! Gurguwa ce kunga yadda take tafiya.” Ya ƙare maganan yana kwatanta ma ƴan uwansa yadda TAIMIYYAH ke dafe guiwanta tana takawa,TAIMIYYAH da ke cigaba da tafiya duk tana jinsu yadda suka biyo bayanta suna ta kwaikwayon tafiyanta,idan tace zuciyanta baya shiga ƙunci to tayi ƙarya ,sai dai babu yadda ta iya haka ubangiji ya nufe ta da kasancewa,kuma bata isa ta hana a kwaikwayeta ba,sai dai tunawa tayi da cin mutuncin da ƴan uwanta na jini sukai mata a yanzu yanzu,yasa takaicin yaran raguwa a ranta domin tana ganin gara su yara ne masu hankali ma sunyi bare su,har ta iso bakin layin su inda zata iya samun abun hawa zuciyanta a cinkushe yake babu daɗi sam,bata wani jima a tsaye ba ta samu abin hawa tai gaba abinta.


GRA,Zaria.

Babban gida ne wanda tun daga nesa me kallo zai san gidan na manya ne masu hannu da shuni,tsananin haɗuwan ginin da tsaruwansa zai sa me kallo yasan cewa ƙwararru a harkan ginin zamani ne suka zana asalin taswiran ginin,ginin upstairs ne da tsayawa misalta tsaruwansa ɓata lokaci ne,daga cikin ƙaton parking space na gidan motoci manya guda uku ne aje,za kai tafiya me nisa kafin ka isa asalin main entrance na shiga cikin gidan.

Daga ciki gidan babban falo ne a ƙasa,mai ɗauke da ɗakuna guda uku kowanne manne da toilet a ciki,an zuba kaya na alatu wanda ƙwararrun Interiors ne suka tsara komi bisa muhallin daya dace,yanayin yadda aka tsara falon da irin kujerun dake cikinsa da sauran kayan decor na ɗakin,zai tabbatarwa me kallo ba ƙananun kuɗi aka narkar ba, daga hannun hagu wanda nan ne aka aje 3 Seater,wani kyakykyawan magidanci ne ma’abocin kyawu da cikar haiba,Black Beauty ne wanda fatarsa ta rine da hutu da jin daɗin rayuwa,hakan ya haifar ma lafiyayyan fatansa da wani irin fresh,yana da dogon hanci zar tare da manyan dara-daran idanu,abinda ya ƙarawa kyawunsa armashi shine gashin giransa baƙi siɗik wanda suke a cinkushe,kame yake cikin kujeran ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,a shekaru bazai gaza shekaru talatin da bakwai zuwa da takwas ba,daga saman cinyansa ƙaramar laptop ne yana faman latsawa,dukkanin nutsuwansa yana ga aikin da yake a cikin computern,sanye yake cikin wata Farar Jallabiya,wanda kana kallo zaka san manyan kuɗi aka aje kafin a ɗauke ta,dukkanin wajen ya cika da qamshin turaren RALPH LAUREN,takun takalman dana fara jiyowa daga ɓangaren matakalan benan dake kallo cikin falon yasani kai dubana wajen,idanuna suka fara hango min fuskan matar da ke sakkowa daga stairs ɗin sanye cikin kayan bacci riga da wando da suka fiddo suranta a fili,baƙace sai dai tana da matsakaicin kyawun fuska,don kai tsaye bazaka kirata kyakykyaba,haka kuma bata da muni akwai ta da cikar halitta me ɗaukan hankali,ko kaɗan bata da makusa,matashiyace da bazata gaxa shekaru ashirin da takwas ba a duniya,amma duk wanda yai mata kallo ɗaya zai iya bata shekaru ashirin da biyu sabida yanayin kula da gyara da jikin ke amsa a kowani lokaci,gaba ɗaya tunda ta doso tsakiyan falon qamshin turarukan da tai anfani dasu masu sanyi da daɗin qamshi suka cika wajen,abinda yasa magidancin tsayawa cak! daga latsa Cumputern da yake ya ɗago manyan idanunsa masu cike da kwarjini ya zube akanta,fuskansa babu yabo ba fallasa yai mata kallo biyu yana me ɗauke kai ya cigaba da aikinsa,ita kuma ta cigaba da takowa cikin takun da ke nuna yanga da kwarkwasa don janyo hankalin wanda akeyi dominsa,ko da ta iso inda yake kai tsaye ta zauna kusa dashi tamkar zata shige jikinsa,gaba ɗaya gangar jikinta ya gama mannuwa da tasa,ta miƙa hannu da nufin ɗauke Laptop ɗin dake bisa cinyansa,yayi saurin kai hannunsa yana dafe nata hannun, tare da ɗago ido ya zuba mata,fuskansa na tsukewa hakan yasa ta janye hannun nata,cikin muryanta me cike da iyayi ta fara faɗin “Haba A.Maleek magana fa mu ke daya kamata ace ka bani lokacinka ka saurareni,amma shine zaka sakko nan ka zo ka zauna kana faman sabgan gabanka,meyasa yanzu ni bani da ƙima da darajan da zaka xauna ka saurari matsololina? A gaskiya A.Maleek na fara gajiya da halin ko inkulan da kake nuna min.”

Tunda ta fara magana ya tsaida abinda yake ya zuba mata idanunsa dake rikitata,yana jifanta da wani irin kallo da ita kaɗai tasan ma’anansa,kafin amon muryansa ya fito cike da Isa da izza yake faɗin “Suhailah ni za ki zo ki tasa kina ɗagawa murya,si’anki ne ni ko ni ɗin ɗanki ne? karki bari ki fusata zuciyata a wannan karon har kija in ɗauki matakin da ba zai mana daɗi ba,ke kike ɗaukan maganan da kika zo dashi tana da muhimmanci,ni a wajena maganan banzace tunda bazaki bi abinda nake so ba,don haka ki barni inji da tarin matsololi da ciwan kan da kike bani,oya tashi ki bar nan wajen tun raina bai ɓaci ba,kuma wannan ya zama karo na ƙarshe da xaki sake zuwa min da raini makamancin wannan.”

Ya ƙare maganan yana nuna mata hanyan inda ta fito,idanunta ta sauke akansa kaman zatayi magana amma yanayin yadda ta ga ya haɗe fuska yana jifanta da kallon da ta fi tsana a wajensa, yasa ta juyawa da sassarfa ta nufi hanyan stairs ɗin,da bibbiyu take takawa har ta haye,ya bita da wani mugun kallo kafin yaja ƙaramin tsaki yana miƙewa tare da ɗaukan laptop ɗinsa da wayansa ya rufa mata baya zuwa saman,ɗakinsa direct ya nufa yana aje Laptop ɗin da wayansa,ya fara cire jallabiyan jikinsa yai jifa dashi bisa Bed,ɗakin yabi da kallo zuciyansa na ɗaukan zafi,sam Suhailah bata damu da gyaran ɗakinsa ba,abinda kawai tasani ta ciyo wanka tazo ya biya mata buƙatanta su sha bidirinsu ta kakkaɓe jikinta tabar masa ɗakin,sai lokacin da ta busa iska sannan zatai gyaran ɗakin,idan kuma tayi sai ta ɗauki wani dogon lokacin kafin ta sake,sai dai shi idan yana gari ya dage yai gyaran ɗakin da kansa,don bai lamunci wani ƙato ko ƙatuwa su shigo masa ɗaki da sunan gyara ba,Bathroom ya nufa don yin wanka kaman yadda saba baya iya bacci idan baiyi wanka ba,lokacin da ya fito kintsa jikinsa yayi ya sanya wasu kayan bacci masu taushi ya zura slippers ya fito,kai tsaye kitchen ɗin dake nan upstairs ɗin ya nufa,don haɗo shayin da zai sha kafin ya kwanta,da kansa ya tafasa ruwan zafin ya zuba duk abubuwan da yake buƙata,cikin Mug ya juye bayan ya tafasa ya fito zuwa wajen dining ɗin da ke manne da corridor ɗin shiga Kitchen ɗin,Sugar ya ɗiba da slice bread guda biyu ya nufi ɗakinsa,bayan yayi ma ƙofan shiga ɗakin Suhailah kallo ɗaya ya ɗauke kansa,koda ya kammala shan shayin nasa bakinsa ya je ya wanko yazo ya kwanta,ba tare da yana jin cewa zai bi takan Suhailah wajen nemanta zuwa ɗakinsa kaman yadda yakanyi a wasu lokutan ba,don shi yana ɗaya daga cikin irin mazan da sam basa son raba shinfiɗa da matansu koda sun samu saɓani ne,sai dai yana ganin a yanzu lokaci yayi daya kamata ya fara biris da lamuranta ko zata saitu tasan abinda ya dace da ita,addu’an kwanciya bacci yayi ya shafa yana fata yau yayi bacci ba tare da yayi mafarkin da ya saba yi a ƴan kwanakin nan ba,mafarkin dake tsaya masa arai ya kuma rasa gane kan inda mafarkin ya dosa,lumshe idanunsa yayi bayan yaja blanket ya rufe jikinsa……..✍🏻

Littafin TAIMIYYAH paid book ne da zai zo akan 500 naira only,ga masu buƙatan yin payment zakui min magana ta wannan number ɗin 08167768704, ko kuma ku turo kuɗin ku kai tsaye ta wannan account ɗin 0504192664 aisha ibrahim dansabo GTbank.*

Sai ku tura shaidan biyanku ta wannan line ɗin 08167768704.

Masu account da Arewa books,zaku dinga siyan sabbin shafuka dalla-dalla akan farashi me sauƙi,ga yadda zaku siya pages a arewa books kamar haka 👇🏻

YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

Balance – Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

Credit/Debit Card – Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za’a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba “Proceed”. Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).


Akwai

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za’a gansa a Balance.

Ɗansabo ce

DOMIN KARANTA CI GABA DUBA👇

https://arewabooks.com/book?id=62d13b36e4924f3d4350f75c

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE