Tar tallah2

YAR   TALLAH

          CHAPTER2
*Mun tsaya ne a inda*
*Inna mai danwake ta daga hannun nata ta saki taga ya tafi ragwaf alamar ba rai*
*Inna laure ta kwasa da gudu tana gyara  daurin zani fadi take iya karfinta  na shiga uku ni laure*
Zamu tashi a
ta isa bakin randa ta ciko tasa da ruwa taxo ta sheqa mata gaba gaba daya yarinyar ta firgita, ta tashi tana fadar wayyo inna kiyi haquri mai dan wake ta riqeta ke yi shiru da  allah aita kyalekin,
Inna laure ta sauke wani nannauyen numfashi ta shiga zare na mujiya
Mai dan wake ta miqe tana fadin ni na tafi amman dan allah laure ki dinga kula kisan irin dukan da zaki dinga musu don karkije ki daure kanki da kanki
Inna laure ta sake jan kwaron numfashi kafin tace  insha allahu zan kiyaye mai dan wake ta fice abinta
Laure ta juya ta shige dakinta ta barsu a nan
Saude ta rarrafa ta nufi dan uwan nata
Wanda ke zaune ya hada kai da gwiwa yanata faman kuka
Saude ta raba jikinsa ta kwanta ya qara janta a jikinsa sosai
Bata jima da kwanciyaba barci ya dauketa sai faman jan ajiyar zuciya take
Akai akai
Malam bala yayi sallama ya shigo gidan nasa hannunsa sagale dana iklima yarinyar da bazata wuce yar shekara goma  sha daya ba
Qanwar saude ce don ita yanxu tana shekara sha biyu ne a duniya
Malam bala ya shigo tsakar gidan tare da miqama iklima baqar  ledar dake hannunsa ta karba ta shige dakin mahaifiyarta tana tsallen murna
Malam bala ya kalli rabiu fuskarsa ba yabo ba fallasa yace bakin munafiki kallon uwar me kakemin? Me mugun halin tsiya hala wani abun kukai aka dakeku ko?
Inna laure ta hankado labule ta fito kamar an bankadota ai daman jiranka nake malam wallahi yau saika biyani kudina in dorama yarinyarnan tallah ta boye kudin wai tace an kwace
Na rantse da allah ban daukar asara
Malam bala yace ai daman tunda na gansu zazzaune anan nasan wata ta’asar sukayi
Yan iskan yara masu tsinannan hali wanda sukai gadon
Halin tsiya niko yarannan dada inda zan kaiSu
wallahi dana kaisu na huta da bala,in su
Tace ahto nidai kudinane sai an biyani
Babu mai doramin asara alalata ta murtala biyuce da goma
Malam bala yace toya zanyi ai dole na biyaki tunda allah ya hadani da jarababbun yara
Kiyi haquri idan na dawo daga kasuwa gobe saina biyaki miqomin buta nayi alwala
Laure taja kwafa ta juya ta koma dakinta ta dauko masa butan ya nufi bayan gida
Ta watsama rabiu harara sannan ta wuce dakinta ta samu iklima ta zazzage baqar ledar sai diban kilishinta takeyi
Ta miqa hannu zata dauka yar tasa kuka tana tirje tirjen qafafuwa inna laure tayi saurin ajiyewa
Ga abinkinan sarkin rigima, Ai nasandai duk cinki baki iya cinye wannan kilishin
Yarinyar ta turo baki irin na shagwababbun yara taci gaba tacin abinta
Duhun magaribane ya fara ketowa sauro suka fara duduma a jikin  rabiu ya lallaba ya kwantar da saude saman siminti sannan ya sake
lallabawa ya nufi dan akurkin dakinsu ya shinfida musu yar yagalgalallan tabarman kaba irin mai cin jikinnan
Sannan ya dawo ya lallaba ya dauketa da qar
Ya kaita dakin ya kwantar da ita ita kadai ta mamaye tabarman don haka shi saman simintin dakin ya kwanta babu ko filo balle abun rufa
Ga duhun dakin. Ya runtse idanunsa dukda yanada yakinin yunwace ke kwankwasarsa bazata barshi yayi barci ba
Tunanin mahaifiyarsu ya fado masa kamar yaddah kullun yakeyi kafin ya kwanta
Wasu hawaye suka cika masa idanu masu zafi tabbas yasan wahalar da sukesha somon tabice
Akan wanda mahaifiyarsu tasha a gurin mahaifinsu
Nasiharta gareshi itace ta dawo masa tamkar yanxu take masa su tace
Rabiu don allah don annabi ko bayan raina. Ka kula da rayuwar qanwarka karkabar rayuwarta ta gurbata a duk halin da kuka tsinci kanku a ciki kaga ita mace ce dole tana buqatar taimakon wani wanda zai jibanci lamarinta
Nasan kaima kana buqatar taimako amman a duk yanda rayuwa taxo rabiu yinta ake
Nasan kodani ko bani dole ku rayu bakuda mataimaki sai Allah.
Rabiu kuyitayimin addu,a in rayu kodan saboda ku. Nima inason in rayu sbd ku
Baisan sanda kuka ya kwace masa ba saida yaji saude jikinsa tana jijjigashi.
Tace yaya kuka kake?
Yayi saurin hadiye kukan tare da goge hawayensa
Ya lalubo hannunta ya riqe kafin yace ba kuka nakeba dariyace nake na tadaki ko?
Tace a,a yaya yunwa nakeji cikina sai cixona yakeyi tun safe banci komaiba na tafi tallah har yanxu
Ya salam ya fada a fili sbd rashin sanin abinyi
Saude ta kwantar da kanta a kan cinyarshi tace kaji cikina sai kuka yake ko yaya?
Bai tanka mataba ta qara girgizashi cikin muryar kuka tace yaya abinci zanci
Rabiu ya kwantar da murya yace dakinyi haquri kin kwanta kinga da safe ba saiki karya ba
Tace wlh bazan iya barciba yace to lallaba ki kwanta ina xuwa
Ta zame daga jikin nasa sai shi kuma ya miqe ya fita
Duk suna kwakkwance a tsakar gida cikin gidan sauro sbd lokacin zafine
Sai radio ce keta faman babatunta a banza
Rabiu ya lallaba sadab sadab ya isa har inda suke ya dauko langar fura ya lallabo ya shigo
Dakin ya zauna yana fadin tashi saude ga fura na samo miki kisha
Ta tashi da hanzarinta ya lalubo bakinta ya kafa mata langar furar tasha iya shanta sannan shima yasha kadan ya rage sauran ya lallaba ya tafi don mayarwa
Yana qoqarin ajewa kenan iklima ta farka tana fadin laure zansha fura
Rabiu yai saurin durkusawa a wurin jikinsa nata faman bari
Inna laure ta tashi tana haska fitila da niyyar dauko langar furar
Taga mutum a durkushe wuri guda
Ta fasa wani uban ihu wayyo allah malam barawo barawo
Malam ya tashi a firgice ya rarimo adda yana ina yana ina ? Kafin ya fito daga ciikin gidan sauron rabiu ya kwasa a guje yayi dakinsu yana famar rawar jiki
Malam ya fito yana ina barawon yake laure?
Tana rawar murya tace nan nan na ganshi duqe wlh
Malam bala yaja tsaki to idan nan kika ganshi yana ina ?
A,a ka. Haska mana ya dauko touch light ya tafi yana haskawa har zuwa zaure ya dawo yana fadin kedinnan
Wallahi kinada matsala. Yanxu haka inuwar wani tsuntsun kika gani kinxo kin rikita mutane da wani barawo barawo
Laure tace malam nifa mutun na gani anan duqe
Yace to idan da mutum kika gani da ban ganshiba ko laya yayi ya bata? Don Allah ki koma ki kwanta kinji
Laure tace niko malam wlh bazan iya rintsawa ba don da idona naga mutum nan tsugunne
Malam bala ya shige gidan sauransa yana fadin ai saikiyita zama ke kadai
Sai a lokacin hankalin rabiu ya kwanta ya saki wata ajiyar zuciya ya lallaba ya kwanta abinsa
Bai jima da kwanciya ba bacci barawo ya sacesa
Qarfe shida na safe laure ta hankado kofar dakin nasu ta gansu sai sharar barcinsu kawai sukeyi wani takaici ya kamata ta juya ta debo ruwa cikin kwanon sha ta daga labulen ta sheqa musu a firgice duk suka tashi sukai wuqi wuqi kamar ya,yan zakaru
Inna laure ta tabe baki cikin masifa tace

Hmmmmm
Ya labarin
Ku kasance tareda.   *ABDULLAHI ISMAIL SALANKE*
Don kasancewa cikin nishadi a koda yaushe
*GOBEMA DA LABARI*

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE