TSANGATAR MATI CHAPTER 2

TSANGAYAR MATI 

CHAPTER 2


Daga waje kuwa Nene na jin haka sai tayi wuf ta fito daga maboyarta, can baya take zagayawa ta hau kan dan dutse tana kasa kunne a karamar tagar dakin Abulle. tana yi tana leka bayanta ko wani zai taho wucewa kasancewar daga nan ana hangen waje a dalilin gajartar katangar. 
‘Dakinta ta shige da saurinta, jiki na rawa ta hau sauke kwallayenta tana fadin; “ldan sammako ku kayo, ni asubanci na yi.” 
Ta fiddo wani maganin gargajiya wanda tayi mugun tsanar warinsa, sannan ta mai da kayan ta afka garin kusan rabi a baki. Kan kace mene cikinta ya murda ga yunkurin amai da ta soma. Ai a guje ta fito ta isa gaban makwararar ruwa ta hau sheka aman iyakar karfinta tana nishi yanda ta tabbatar zasu tsinkaya… 
“Nifa kamar kakari nakeji.” Cewar Mati yana kallon Abule. “Kai fa dadi na da kai haryanzu baka bambance kukan Jakinka dana Akuyar Delu.” “To idan ma itance kinyi zaune salon tamin ta’adin da ta saba?” 
Ya fada yana mai mi’kewa tsaye, itama da sauri ta mike tana mai rufa masa baya. 
Ita dinma jin tahowarsu ya sata zubewa gefen kwatamin tana mai rike cikinta da fadin “Wayyo! Mati…” Da gudansa ya ‘kara so wajen yana mai janyeta gefe. 
“Ikon Allah! Nene ashe kece. Sannu me kika ci ne haka?” “Ba komai tun safe nakejin tashin zuciya da rashinjin dadi.” Ta fada da kyar tana sauke numfashi. 
“A‘a irin wannan ciwon ai bana shiru bane Nene, karki manta da haka Sahura ta mutu da irin shirun nan.” “To Mati ana ta kai wa yake ta larura? Taimaka min zakai Abule ta dubomin ‘Yar Magaji,ji nake kamar ana daka yaji a kirjina.” “Huu’umm!” Abule ta fada tana tafa hannu. “Ai wallahi da aiken kishiya gwamma najibgi Uwar miji. Kai ni banma yarda da wannan ciwon ba. Saboda Allah Mati bakaji warin tazargaje ba?” 
Ta fada tana mai daddaga hanci sama. “Me kike nufi ne? Kinga Abule bansan fitina, ya mutum na halin ciwo kina kawo shashanci. ldan na isa dake to maza ki jeki dubomin ‘Yar Magaji.” ‘ 
Mintuna kadan Abule ta dawo da ‘Yar Magaji biye da ita ta rataya wata tuttumar jaka me kama da ta wazirin Sarkin kutare. Kallo daya tama Nene makaryaciyar zuciyarta ta kisa mata menene, dan haka ta kalli Mati da murmushi. “Malam ai ba wata lalura ba ce mai girma, karuwa ce zaku samu, a takaice dai Nene ciki gare ta har na tsawon wata biyu.” “Kan babban bala‘in can! Alkur’an wannan karya ce.” Abule ta fadi tana mai buga tsalle gefe, kafin kuma tayi barin da Nene ke kwance. “Ke Nene kiji tsoron Allah, ina ce ba shekaranjiyar nan muka gama rikici kan tsumma na da kika yaga kikai kunzugu da shi ba?” “Wayyo Ni Abule! Yau na ga abinda yafi ‘karfina, wai cikin ma har kinsan yayi wata biyu sai kace wacce kika hada iri da Mayu. ke kam ‘Yar Magaji anyi tantiriyar ma’karyaci wallahi. 
Matar da ake rade-raden Aljanu sun sace mata mahaifar ne keda ciki?” 
“Ke! Ke! Abu kin cika mana kunne da shegen karadi. Ki tsayamana abu abin a sannu idan ma karyar ce ai ‘Yar Magaji zata fadi. “Wane irin abi-sannu Mati? Ai fa magana ta riga ta kare, Nene dai ciki gare ta, maganar ganin jini kuma wanann a bayyane yake, ko Magaji ka tambaya zai idar maka wannan zance. Lalle ne akwai Matan dakejini da ciki. ” 
“Ke kuma Abule da kika hada Ni da Maita ina jin dai tsohonki shine Bazawari na? Dan haka bushiya dai ba zata wa Kunkuru gorin kafa ba , ko zaki mutu dai Nene ciki gare ta na wata biyu.” 
“Kai kuma yanzu ya rage naka sai ka dinga mata abinda take so. Ni kaga tafiyata.” 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE