TSANGAYAR MATI CHAPTER 4

TSANGATAR MATI 






CHAPTER 4




Assalamu Alaikum mutan gidan.” Fadin ‘yar doguwar dattijuwar kuma tsamurmura mai sharba-sharban tsagu a gefen bakinta, baka ce wuluk kamar danta Mati. Mati ne a gaba d’auke da k’aramar akwatin kayanta, ita kuwa tana biye da shi a baya. Abule ta soma fitowa daga d’aki sai Nene daga bandaki suka saki baki suna kallonta. ‘lkon Allah, wai na kwance ya fadi.‘ Cewar Abule kenan a kasan ranta ganin shigar da surukarta su tayi, wata karamar Atamfa Super ce ajikinta an mata dinkin riga da siket sai wani babban mayafi data yafa a kafada ba rufin kai ba. Fuskarnan tasha farar hoda, ba’a gane wa sakamakon bakin fatarta da ya ciza saidai kuma kana gani zaka rantse yanayin hunturu ne wanda yayi sanadin da fatar fuskar nata ya bushe yayi furu-furu, ga uban jan janbaki data lafta a lebbanta masu tudu. A hankali Nene ta maida dubanta ga Abule, akayi sa’a itama ta kalleta sai kuma suka sauke ajiyar zuciya kam kowaccensu ta shiga rububin tarbarta da amsa sallamarta. “Waalaikumussalam, lale marhaban.” Fad’in Nene kenan ta karasa bakinta a washe ta karbi akwatin Inna, caraf itama Abule ta sanya hannu da zummar kwacewa ta kai nata dakin. “A’a menene haka? Yaushe akayi daren kuma da har ace gari ya waye? Malama sakarmin.” Cewar Nene tana k’ara jogana akwatin a jikinta. Dole Abule ta saki tana harararta ta karasa wajen Inna cike da kissa ta ce. “Maraba Inna.” Inna ta hau karewa Abule kallo, eh kam ta yarda da rahoton da Aminiyarta Ladidi ta kai mata game da Amarya d’an nata. Ta tabbatar mata tafi: Nene tsafta kuma ta ga alama. Sai dai kuma ta kasa fahimtar me yaja Mati ga aurenta? Wannan abu a dunkule haka? 
“Yauwa sannunki kema.” 
Ta fadi tana mai karasawa ta zauna a saman tabarmar da aka shimfid’a. Nene za ta yi ciki da kayanta ta yi saurin dakatar da ita. 
“A’a ‘yarnan dakata.” Zani na kuncewa tana sake daurawa ta karkata kugu ta tsaya gami da dire akwatin tana jan majina. 
“Na’am, to.” Inna ta yamutse fuska. “Ai kuma sai dai wannan karon ki hakura don a d’akin ita ‘yar uwar taki zan sauka. Na gayamaki bana son kwana kan wannan gadon naki mai warin hammatan wanzamai, da kyar idan kin chanja wannan tsohon zanin gadon wanda na gama yayinsa tun jegon mijinki. Bawa abokiyar zamanki akwatin naga nata kamun ludayin.” 
Ai sai Abule ta kece da dariya, kallon banzan da Inna ta watsamata ne ya sanya ta nutsuwa. Nene ta cika tayi tam! Yau ita Inna za taci wa fuska akan Abule? Lallai ya dace ta zage damtse. 
Tana numfarfashi ta zauna, Inna ta dubeta sannan ta kara duban Mati. 
“Wai ni Mati wacece mejuna biyun a matanka?” Mati ya hau washe baki. “Ai duka biyun ne.” 
Inna ta kwalalo idanu cike da mamaki tana duban Nene, karshe ta sauke idanunta akan Abule da ta zauna tana wani sussunne kai ita a dole kunya. Sai kuma ta hau tafa hannuwa da shewa. 
Farin ciki ya cika su don a zatonsu ta yarda suna da cikin. Sai dai ga Inna kuwa sam zuciyarta bata amince Nene nada ciki ba, shekaru nawa da aka yita rade-radin ba tada mahaifa, ai kuma ta saka ayar tambaya. Dabara tazo wa Inna. “Yau naga abin al’ajabi, to ai shikenan, zama ya kamani a kauyen nan duk da bana so, amma zan zauna har naga ‘ya’yanka Mati.” 
Hanjin cikin Nene da Abule ya kada sai’ dai kowaccensu tayi fuska. Mati kuwa wani dadi ne ya mamaye zuciyarsa ganin burinsa ya kusa cika. 
Abule ke da girki ita ta shiga hidima da Inna, Nene kuwa d’akinta ta fada tana tunanin mafita nan gaba. 
Bayan kwanaki hudu da zuwan Inna ana zaman lafiya kowacce ta ciki na ciki. Karshe kuma sai Mati ya tsuro da wuni a dakin Abule wai hira da Inna, haka za tayi ta tsinkayo dariyarsu. 
Da abin ya isheta ta shirya ta nufi gidan ‘Yar Magaji don neman mafita. Tana isa ta zayyanemata komai, ‘Yar Magaji ta buga uban tsaki. 
“Kece ai ki kayi sake da baki mallake Mati tun fari ba, yanzu da komai zaizo maki da sauki Jin haka Nene ta gyara zama. “To yanzu ya za’ayi.” 
‘Yar Magaji ta dan yi jim, sai kuma ta saki dariya ta mike ta fada daka. Can sai ta dawo dauke da kulli ta mikamata. Nene ta haujujjuyawa. “Na menene?” 
‘Yar Magaji ta dan murza hanci tsabarwarin da bakin Nene yake yi kamar na ‘yan ga ruwa. 
“Kinga wannan, kasar karkashin gadon ma’auratan da suka tsufa tare ne suna soyayya, matukar kin yi turare da shi na kwanaki uku Mati ya kusanceki to an gama.” Nene ta girgiza kai. “Matsalar mun fi wata biyar bai nemeni ba, ni kinsan na tsani a maisheni jaka.” Wani kallo ‘Yar Magaji tayi mata sai kuma suka kwashe da dariya ‘Yar Magaji na kauda kai. “Dad’ina dake ba dai warin baki ba.” 
Nene ta muskuta tana shafa bakin. 
“Um to yana iya da abinda yafi karfin wuta?” 
Tabe baki ‘Yar Magaji tayi. 
“Ke kika so, ni yanzu dai kinsan ina jiran kaso na, makira ai ina shigowa daman naga yanayinki na gane makircinne ya motsa.” 
Nene ta dara. Suka gama kulle-kullensu dai Nene ta koma gida da zummar soma gabatar da aiki. 



Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE