TSINTACCIYA CHAPTER 1 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 1 BY NIMCY LUV
Safiyar garin Lahadin yau ta kasance safiya mai ɗumbin tarihi ga dukkan jama’ar da suke yankin Kano kuma a sassa daban daban, Dalilin Kwantaccen baƙin hadarin dake garin, kasantuwar yanayin damu na da muke ciki, kuma farkon watan Agusta.
A hankali sassanyar iskar hadarin take Kaɗawa yayinda kuma dukkan baƙin hadarin yaywa samaniya tsinke, cikin nutsuwa baƙin hadarin ke joyewa zuwa jaa, alamar ko wanne lokaci ruwa na iya sauka.
Wata ƙaƙƙarfar iska ce mai tafiya da rufin gidaje ta fara fatali da dukkan wasu abubuwa marasa nauyi, ƙarfin isakar da rugugin hadarin ya wuce tunanin dukkan mai tunani da dukkan alama yau ruwan na musamman ne.
A hankali kuma gajimaren ke gudu yana haɗa jikinsa waje guda, cikin lokaci kaɗan samaniya tai wani irin jaa wanda ya wuce tunani mutane, ga wata ƙara da rugugi da hadarin yake, wanda ya haddasa tashin tsuntsayen daga saman bishiyoyi zuwa ma ɓoya.
Ƙarfin gudun isakar da kuma yadda take fatali da dukkan wani abu dake kan hanya, ya sanya dabbobi fara gudu suna kuka, yayinda abeben hawa suka shiga tsayawa a saman shimfiɗaɗɗan titin Sabon Garin!
“Shuuuu” haka sautin saukar ruwan saman ya bada Amo! Amon daya tsorata dukkan mutanan da suke waje, domin tunda aka fara damuna today is the first day! Da akai ruwa mai tsananin yawa wanda yake sauka da wata iska mai yaye dukkan rufin gidajen da basu da Kwari, saukar ruwan saman yay worse da yaywa al’amarin da yay Coursing wani irin hatsari mai munin gaske.
Saukar ruwan saman bai hanata ko da motsi ba, bare tayi Attempting na gudu zuwa wani wajan domin tsira da lafiyarta.
Tana zaune a saman wata kan bolar kasuwar Sabon gari, the way she’s acting zaka san cewa akwai wani abu da yake tattare da ita.
Farar macace mai matsakaicin jiki, ƙyakƙyawa ce sosai saukar long dark hair ɗinta zuwa gadon bayanta zai tabbatar maka cewa ita ɗin ruwa biyu ce wato _(Half-caste)_.
Dukkan sassan jikinta rawa yake yana wani irin ɓari, na tsananin dukan ruwan saman, a dai-dai lokacin da kuma saukar ruwan saman ya juye zuwa saukar ƙanƙara yasa tai wani irin firgita tare da ɗago kanta sama.
”Yasubuhanallah!” hasken fuskarta shi kaɗai zai tabbatar maka cewa wannan ko a mahaukatan ita sabon kamo ce, idanunta sunyi jajirrr Jikinta na wani irin ɓari ta tashi tsaye _”Ya hayyu ya ƙayyum”_ ashe tsirara take babu komai jikinta sai dugun gashin daya rufe asalin kayan fuskarta.
Idanunta ta ɗaga sama kamar mai tunani a hankali kuma bakinta ke motsawa yadda babu mai iya jin abinda take faɗa.
Cikin nutsuwa kuma sautin maganar ke fitowa fili tana faɗin.
_“Allahumma Innakaa, Afuuwun! Tuhibbun Afu-afuu Anniii”_
Sune kaɗai kalaman dake fita a bakinta, wanda Ubangiji ne kaɗai ya sahale mata faɗar su, da kuma ƙarfin Imanin da Zuciyarta ke dashi, amma banda haka yaya cikakkiyar Mahaukaciya mai yawo tsirara wacce ta maida kan Bola wajan kwananta, ruwan kwanta ya zama abin kashe ƙishinta, yayinda abubuwan kan Bolan suka zama abincin sawa a cikinta zata iya wannan salati¿ _ONLY GOD KNOWS_.
A dai-dai lokacin ne kuma wata haɗaɗɗiyar mota Rolls-Royce Phantom mai tintak tai parking a wajan, cikin nutsuwa kuma aka buɗe Murfin motar aka fita, wani Babban mutum kuma attajiri ne ya fito yana gyara zaman laimar dake hannunsa.
Idanunsa ya juya tare da sauke ganinsa akanta, wani irin lumshe idanunsa yay yana siɗe laɓɓansa da harshe kamar tsuhun maye.
Cikin wata fitinannan Murya wacce buƙatar kasancewa da mahaukaciyar ya gama narkar da ita, ji yake J ɗinsa na wani irin fisga saboda ganinta da yay naked a gabansa.
Frm head to toe yake binta da kallo!
Cikin zaucewa ya ƙara ji J ɗinsa ta fara fisga to Yarinyar tai bala’in haɗuwa.
A zuciyarsa yake faɗin.
“Young innocent pretty gril aka haukata haka? She’s different kyanta daban, komanta daban, that’s illiteracy ji ɓeta kamar ƴar sarauta, so pretty my Lord! Yasubuhanallah, masu haukata Yarinyar nan sumbin gata, na samu full chances zaɓe zai zo min a dai-dai, kalleta her body is so soft ga idanu ka manyan kaya, look at her. Snatch waist wallahi zama ƊAN MAJALISA _(Members federal house of Representatives)_ Dole!”
Ya ƙare zan can zucin yana wani sauke ajjiyar zuciya da shafa ƙirji.
Motsin da taji a bayanta ya sanya ta juya da sauri ganin mutum dake can nesa da ita yasa ta razana sosai.
Tsoro, firgici ya haɗe mata waje guda, Ada kafin shigowar sa cikin rayuwarta _DAMUWA_ ce, amma shigowar sa cikin rayuwarta a yanzu ya zama _ƘALUBALE!_
Kai ta shiga girgiza masa ta nayi baya, jikinta na kyarma da ɓari amma hakan bai hana shi ƙara kusantu ta ba, yana zuwa yasa hannu ya fisgota zuwa wajan motar, yayinda shima jikin nasa ya ɗauki rawa saboda wata kalar tsawa da akai.
Kokawar kwace kanta ta shigayi, hakan yasa shima ya fara tayata kokawar it was like he is enjoying.
Tana gab da ƙwace kanta ya wani dannata cikin motar tare da sanyawa motar lock yana shiga yaja motar da wani irin speed yabar kam bolar.
Fitowa yay daga cikin ƙaramin ɗakin da yake ciki, hannunsu riƙe da Magirbi daya saƙala a wuyansa, Dattijo ne mai matsakaicin jiki, yana da kamala sosai.
Cikin sauri ya rufe ɗakin saboda gaba ɗaya hankalinsa yay kan gonarsa.
Yana ƙoƙarin fita yaji matarsa na faɗin.
“Innalillahi, Malam!Malam! Malam kana ina ne”
Da sauri wanda aka kira da Malam ya tsaya daga tafiyar da yake, gabansa na faɗuwa domin daga yadda ake kiransa kasan bana lafiya bane.
Kallon Matar tasa yay yace “Ya..Ya Rabi wannan kiran hak ince dai komai lafiya ne?” Girgiza masa kai tayi tace “Malam inafa lafiya” gabansa ne ya sake faɗuwa kafin yace “Assha,Meke faruwa to, kinga sauri nake zani gona, kuma yau muna da baƙi a garin namu zasu taimaka mana akan Noman mu”
Numfasawa tayi tace.
“Malam ban ganta ba, tun dana farka ko karin kumallo banyi saboda fargaba yanzu ma gajiya nayi da zullumi nace bari na faɗa maka”
Da sauri Malam yace “Kamarya? Babu yarinya kuma kikai shiru kamar baki san ciwon Yarinyar nan ba? Kamar bake kika haifa ba?”
Girgiza kai tayi tace “wallahi Malam na ɗauka taje makara….”
Da sauri ya tare ta hanyar faɗin “Wacce makaranta Rabi? Bayan satin daya shige ta gama zana jarabawar shiga aji huɗu na sakandare? Wallahi duk abinda ya samu Yarinyar nan ki kuka da kanki, ba zan lamunci wannan shirman a gidana ba, idan baki son riƙe ta saboda da lalurar da take da ita ina da inda zan kaita ta zauna har abada ko mai kamannin ta baki gani”
Yana faɗin hakan yay cilli da Magirbin tare da yin waje.
Shiru Baba Rabi tayi cike da zullumin halin da Yarinyar zata kasance.
Tunda ya fita ko mai kama da ita bai gani ba, babu ma yara sam a unguwar dalilin ruwan da aka shimfiɗa a daran jiya, ko’ina na unguwar ya cika da ruwa, ko shi ya shiga wannan ruwan sai yay jinya amma ina yarinyarsa taje a wannan lokacin?
Abu kamar wasa har ya fara shige tunanin Malam, al’amarin daya ƙara tayar masa da hankali kenan, yarinya ɗaya tilo da yake da ita wani ƙaramin kuskure yana neman yi masa nesa da ita.
Yama manta da batun gona da kuma baƙin daza suyi a garin, tafiya yake sosai harya ƙarasa wajan wani tafkeken ruwa _(Wudil river)_
Kana kallon ruwan nan kasa duk wanda ya shiga ko kuma ya faɗa, ya faɗa kenan sai dai wani bashi ba, ruwan yay wani sama dan ma wai a hakan ya tafiya.
Baka ganin komai sai haske da hayaƙin ruwan har wani ambaliya yake ya cika yay tafff.
Tana tsaye a gaban ƙaton ruwan, kanta a ƙasa Idanunta a rufe, yarinya ce ko kuma nace matashiyar budurwa, ƴar kimanin shekaru 17 a duniya, baka iya tantance yanayin dirin jikinta saboda babban hijab ɗin dake jikinta.
Fararan hannunta da kuma yatsun hannunta da take motsa su ne zai tabbatar maka da cewa farar macace irin farin nan mai mugun kyau, da ɗaukar hankali.
Kanta yay tudu sosai kamar wacce tai acuci, fafaran ƙafafuwanta ko takalmi babu.
A hankali ta ɗaga kanta tare da buɗe idanunta wanda eyes lashes suka kwanta luff a saman fatar idanun, hannunta ta sanya tare da kama gefen hijab ɗinta ta ƙanƙame Jikinta waje guda.
Dadai ace ta auri wanda bata so, Tabbas gwamma kowa ya rasata, rayuwarta bata da amfani a yanzu damuwa tai mata yawa.
Mene Amfaninta ne a yanzu? Ada rayuwar ta tambaya ce? Amma rayuwarta a yanzu ta zama Amsa, duk da irin wannan abun bai hana duniya tai mata wani irin kallo ba, mene yasa duniya ke son yin juyin wainar fulawa da ita ne?
A hankali ta share hawayen dake silaluwa daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta, cikin siririyar muryarta mai raunin gaske tace.
“Am so sorry Baba, na kasa maka biyayya, I’m a bad girl ni ba ƴar ƙwarai bace, na ɗauka zan jure na ɗauka i can handle everything anything da zai farcing rayuwana, amma na kasa, Am sorry Ba..ba!!! Am sorry!”
Ƙafa ta ɗaga zata faɗa cikin ruwan taji ana faɗin.
“AKEELA! AKEELA!! AKEELA!!”
da wani irin sauri ta juya ganin Babanta a bayanta can nesa yana zuwa wajan, kai ta shiga girgiza masa ta kasa cewa komai.
Hijab ɗin jikinta ta tattare zuwa saman tana jan numfashi, Malam kuwa Murya ya buɗe ya shiga faɗin.
“Akeela ki tsaya bazan aura maki kuwa ba, Akeela Ruwa…”
Bai gama faɗin abinda yay niyya ba saboda wani irin bugawa da ƙirjinsa da yay ji kake “Tsundumm” ta faɗa cikin ƙaton kogin.
Wani irin suman tsaye Malam yay, komansa ya tsaya na wani lokaci, tashin hankali da makomarsa ya cika masa zuciya.
Da gudu har takalmansa na faɗuwa yay bakin Kogin duk da yadda idanunsa suke dishi dishi saboda ƙaran cin gani da yake da shi bai hana shi ganin wajan da Akeela ta faɗa ba, yana wani fidda ƙwayaye alamar numfashinta na fida saboda shigar ruwan cikin hanci da bakin ta.
Da gudu Malam ya kwasa zuwa bakin hanya yana faɗin.
“Jama’a ku taimakamin yarinta ta faɗa kogi, wai babu mutane a garin ne, jama’a!!!!”
Hannunsa ya ɗura akai har wani jiri ke ɗiban sa, babu mutum ko ɗaya a hanyar.
Sama da mintina 10 kafin Allah ya kawo wasu mutane wajan su biyar kana ganinsu kaga Manoma, da sauri Malam yasha gabansu yace.
“Bayin Allah ku taimaki ran baiwar Allah, yarinya ta na cikin ruwa, ko taimaka min kada ta mutu da haƙƙi na”
Kallon juna sukai kafin kuma gaba ɗaya suka bi bayansa saboda hannun wani da yaja.
Suna zuwa wani mai suna Isiya yace.
“Tab, ai wallahi idan kaga tayi rai sai ikon Allah”
Wani mai suna Sunusi yace “Wanne batun rai? Ai Isiya wannan Yarinyar Shikenan ta riga mu gidan gaskiya”
Wannan Maganar tasa Malam sakin kuka yana faɗin.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un, dan Allah ku daina faɗin haka wallahi yarinta tana raye bata mutu ba, gobe bikinta Tayaya ne za kace tamutu”
Isiya ne yace “To wallahi dai ku ruwa bai kashe ta ba, kifi ya cinye ta ko kada tab wannan maliyan ruwan ko ƙarshe bai dashi”
Jafar ne yace “To wama zai shiga wannan ruwan? Kasan bamu da wasu ƴan kwana kwana a wannan unguwar kafin su zoma komai ya faru” Sunusi ne ya ƙara leƙawa ruwan yace.
“Allah dai ya jiƙan musulmi, amma wannan Yarinyar tayi shahada mutuwar ruwa baiwar Allah kenan”
Da gudu Malam ya kwasa ya ƙara nufar kan hanya domin zuciyarsa ba zata jure jin wannan mugwayen alkaba’in akan Yarinyar kirki irin AKEELA ba.
Yana zuwa kan hanyar dai-dai lokacin da wasu haɗaɗɗun motoci suka danno kai cikin garin Wudil a kuma dai-dai Wudil river.
Motar farko wacce ta kasance Bugatti Veyron dark blue ce ta wuce da wani mugun sauri.
Kafin ɗaya motar mai ƙirar Lamborghini Aventador blue black ta marawa motar gaban baya.
Yana zaune a bayan motar idanunsa a rufe sanye yake cikin Modern fit suit nevy blue.
Sai wani Monk strap na shoe daya sanya, ya ɗaura Rolex Oyster Perpetual a hannunsa, ƙyakƙyawa ne amma baƙi, his Elegant black skin sai ƙyalli yake,
Babu wani abu mai haske jikinsa sai laɓɓansa da kuma idanunsa, he’s dark-skinned yet handsome guy.
Wasu irin idanuwa ne dashi masu sparkling cikin idanun duk mai kallonsa.
A hankali ya buɗe idanunsa jin driver na faɗin “Subuhanallah” idanunsa ya gama buɗewa sosai ba tare daya kalli Driven yace.
“What happened with the car?”
Cikin girmamawa yace “Ƙaramin Mai gida wani bawan Allah yasha gaban mu Allah yasa ban taka shi ba”
Yana latsa Wayarsa yace “Ok! Check him muga”
Fita yay yana fita Malam ya miƙe yana riƙe ƙafa yace.
“Yarinya ta dan Allah ka taimakamin ita kaɗai nake da ita”
Da mamaki Driven yace “Bawan Allah lafiya, baka san hatsarin mota bane zaka sha gabanmu haka”
Cikin kuka Malam ya bashi labari tare da faɗin
“Dan Allah ka taimakamin tayi wajan mintina ashirin da faɗawa”
Baya Driven yay tare da faɗin “Bari na faɗawa Karamin Mai gida”
Yana faɗin ya nufi wajan motar back seat tare dayin knocking.
Idanu BARR ADNAN (MD) ya ɗaga kafin ya buɗe glass ɗin motar ganin Driven sa yace.
“Is everything okay?”
Ajjiyar zuciya Driver yay yace “Wai Yarinyar sa ta faɗa wannan kogin na Wudil gashi babu kuwa kusa, shine yake neman taimako”
Kallonsa kawai Md yay kafin yace “Is she a kid?” “Wallahi dai ban sani ba, amma hankalinsa a tashe yake”
Malam dake can gefe yay saurin ƙarasu wa wajan yace.
“Dan Allah ku taimaka”
Da sauri Md ya ɗaga idanunsa domin idan ba gizo muryar take masa sai yaji kamar muryar Baffansa.
Da mamaki Malam yace “A’a Adnanu kai ne? Maza fito maza kaji”
Buɗe ƙofa Md yay ya fito fuskarsa ɗauke da Murmushi yace.
“Baffa wacce ta faɗa ruwa kamar haka?”
Girgiza kai kawai Baffa yay yace “a fara taimakon rai sai ai magana da baya”
Gaba Baffa yay Adnan Md na biye da shi of course ya iya ruwa amma wannan ruwan ya wuce tunaninsa, gashi dai bai shirya mutuwa ba, Amma yay zai ne? da P.a yana kusa da sauƙi ma.
Zare jacket ɗin sa yay tare da cire necktie ɗinsa, yana tattare hannun rigarsa yace “Baffa babu alamun mutum fa a wannan ruwan”
Zuciyar Malam ya buga da ƙarfi kafin yace “Wallahi tana nan ta faɗa ka jarraba”
Zare takalmin ƙafarsa yay yace “I’ll try my own best, firstly clam down kaji”
Gyara tsaiwa Md Adnan yay yana runtse idanunsa tsoro duk ya cikasa domin girman ruwan bana wasa bane da wani irin ƙarfi yay tsalle tare da faɗawa cikin Kogin….