TSINTACCIYA CHAPTER 6 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 6 BY NIMCY LUV
Kuka Meema ta sanya wanda ya ƙara tayar da hankalin President Ahmad Adil,cikin damuwa yace “he looses his memory? I understand,but problem ɗin fuskar fa? How long zai kasance cikin rashin sanin wane ne shi?” Kafin Dr yay magana Meema tace “i don’t understand Dad,loosing memory kamar ya?” Cikin nutsuwa Dr ɗin ya kalleta kafin yace “everyone forgets things atimes,how often have you misplaced your car keys or forgotten the name of a person you just met,some degree of memory problems as well as a modest decline in other thinking skills,is a fairly common part of ageing,there’s a difference,however between nrml changes in memory and memory loss associated with alzheimer’s disease and related disorders,and some memory problems are result of treatable condition Madam Meema Ahmed Adil” shiru tayi idanunta yay rau rau zai kawo ruwa kafin a hankali tace “kenan bazai iya tuna waye shi ba? Balle ya tuna abinda ya faru dashi,more explanation please” farin glass ɗinsa ya ɗauka tare da sanyawa cikin nutsuwa yace da Meema “he looses his memory,he can’t remember anything about his life,and normal age-related kin gane ba? Memory loose doesn’t prevent you from living a full productive life for example,you might occasionally forget a person’s name,but recall it later in the day,amma tunawa lokaci guda it’s difficult,you might misplace your glasses sometimes,or maybe you need to make lists more often than in the past to remember appointment or tasks. These changes in memory are generally manageable and don’t disrupt your ability to work,live independently or maintain a social life” Dr ya ƙare maganar yana sauke numfashi baya jin hausa ko kaɗan hakan yasa dukkan wani bayani da zai yi dole sai dai yay da yaran nasara Ingilishi kenan.
Kasa magana Meema tayi bata san mene yasa ba amma wani mugun jin tausayin mutumin take kafin a hankali tace “alright yanzu dole sai the same abinda ya faru da shi ya sake faruwa zai iya tuna waye shi?” Ta faɗa abinda Dr ɗin ya faɗa,jinjina kai yay kafin yace “sure” miƙewa President Ahmad Adil yay yana kama hannun Meema kafin yace “Dr ka shirya komai na tafiyar cikin week ɗin nan za’a fita dashi” ya faɗa yana jan Meema zuwa waje,kallonsa tayi tana kwaɓe fuska kafin tace “Dad” ba tare da ya kalleta ba yace “what again Meema?” Idanunta na kawo ruwa tace “Dad i want see him please! Please Dad” tsayawa yay yana kallonta kafin yace “Look Meema wannan ba age ɗin soyayya dashi bane,infact kin girme masa respect yourself ok?” Ƙasa tayi da idanunta tana jin ranta babu daɗi kafin tace “Dad ni fa ba?” Tsareta yay da idanu kafin yace “kefa mene? Uhm gayan naji” girgiza masa kai tayi kafin tace “nothing” kama hannunta yay tare da shiga cikin mota securities suka rufa masu baya.
Can cikin gidansa suka nufa bayan sun ƙarasa Meema ta fito da sauri ba tare data tsaya Dad ɗinta ba,murmushi kawai Dad yay domin hakan da tayi yasan fushi tayi.
A bakin shiga lift ya sameta tana ganinsa tai saurin shigewa tana danna 3rd floor,rabuwa yay da ita ya nufi wata daban yana shiga ya danna shima,a parlor ya sameta tana maƙale jikin Mom tana surutai wanda ita kaɗai ta san mene take cewa,kallon juna sukai shi da matarsa kafin Mom tace “yanzu kuka fita lafiya amma ji har abin ya motsa” cike da so da ƙaunar ƴar tashi ya kalli Meema wacce zufa ke yanko mata sai surutu take ita ɗaya murmushi yay kafin ya ƙarasa tare da kama hannunta yace “Allah sarki Mamana,Ubangiji yana sane dake kinji nothing will happened to you again,ina nan kinji i’m always be by your side kinji” ya faɗa yana yin gaba da ita tare da nufar side ɗinta,suna zuwa ya zaunar da ita bakin bed kafin ya fara bin bedroom ɗin da kallo,a hankali ya ɗauki wayarta tare da kunnawa yace “ke ƴar gidan shugaba ce,President’s daughter,ya kike son maida kanki middle class ne eh? U have to be classes lady irin manyan matan nan,ni da na keso ki fara fita kina rage min wasu manyan ayyukan tunda kinga ba ni da wanda zai taimake ni ba ni da wani babban ɗa,soon zaki fara fita zuwa wasu Company,wai ke nan sunan babbar likita,a haka zaki zama babbar baƙuwa a wajan taron sickler day ɗin,haaaa! Taɓ su Meema ƴan ƙasa na gari a nan tare dasu I.d card voters card anya kin taɓa voted na Dad ɗinki ma?” Murmushi tayi masa tana ƙwace jakarta bai kulata ba,a hankali ya zauna a gefe ganin wayar nata empty ba komai gata sabuwa dal iphone 13pro max,transfer kati yay mata na 50k kana ya sai mata data cikin sauri ya shiga play store tare dayi mata download na I.G whatsapp,twitter sai wattpad da okoda books tare da games da app na qur’an da azkar,buɗe mata komai yay da wani special name Meema_ President’s daughter,wayarsa ya ɗauka tare da yi mata sending na picture ɗinta,ɗora mata shi yay saman profile kana ya bata yana faɗin “yanzu kika fito Mamana,oyah tashi ki fara duba wayanki gashi nan ki yi abinda kike so na tura maki 500k a acct naki” dariya ta masa tace “thank you Dad i love you” Murmushi yay mata yana miƙewa yace “love you too Meema,kinfa girma good 32 to 33 yrs amma abu ya saki gaba kamar yaƙi please ki yita addu’a,ki samu kiyi aure kamar ko wacce mace i don’t know what wrong with your mother bata damu ba sam,ina cikin mutane hankalina na kanki ki taya ni kula da kanki,ahha! Ba na son facebook domin zaki iya gani ana zagin Dad ɗinki ranki ya ɓaci,ina yin abinda naga zan iya,amma kin san halin mulki,mai makon jama’a su tayamu da addu’a sai su bimu da zagi,bayan bama da laifi domin na saman su ke take komai,ki kula da kanki akwai guards naki guda ashirin duk inda zaki,make sure tare kuke,ok?” Jin shiru yasa ya juya,ashe tuni bacci ya ɗauke ta shi kaɗai yake abinsa,girgiza kai yay tare da ƙarasawa wajanta ya gyara mata kwanciya,a hankali ya shafa kanta tare da sumbatar goshinta,fita yay yana rufe mata ƙofar bedroom ɗin.
Washe gari Dad da wuri ya fita zuwa wajan meeting wanda zai zauna da ƴan majalisu na dokoki wato _(National assembly)_ na ƙasa baki ɗaya,akan lafiya musamman ciwon sikila wanda ya zama kamar Annoba.
A hankali Meema ta fito sanye da silhouette da VGOLD palazzo trousers wanda yake da faɗi sosai daga ƙasa kamar skirt daga waist ɗinta kuma ya ɗame ta irin sosai ɗin nan ba zaka taɓa cewa tayi shekaru har 33 ba,tayi rolling kanta da wani haɗaɗɗan vail,a hankali take tafiya kamar wata ɓarauniya tazo dai-dai parlor taji ance “mrng mai satar hanya” ajiyar zuciya ta sauke tare da faɗin “Mom” sai kuma ta juya tana murmushi,zama tayi tace “mrng Mom?” “Mrng how are you? Ina zaki haka ko breakfast baki ba?” Shiru tayi sai kuma tace “kamar nayi ko? A’a banyi ba,kai na yi” girgiza kai Mom tayi tana ajiye system ɗin gabanta,wato al’amarin Meema kullum ɓaci yake kamar da sauƙi sai kuma ta ƙara komawa ruwa “bama ki tabbar kinyi ba kenan ko,eh?” Taɓe baki tayi domin Mom faɗa gareta yanzu zata hargitsa ta,miƙewa tayi ta fice daga cikin gidan baki ɗaya.
A can waje kuwa wata mota ta shiga cikin sauri guards suka nufota,da sauri ta ɗaga masu hannu driver yaja da gudu tana faɗin “aso rock clinic gulps za kai dropping nawa” ta faɗi hakan tana buɗe network ɗin wayarta,kai tsaye wattpad ta shiga ta fara dube dube domin tun sanda Dad yay mata settings ɗin komai bata taɓa wayar ba sai yanzu,har ta shige wani book sai kuma ta dawo baya taga ansa _Our secret_ (Sirrin mu) shiga tayi tana zaune ta karanta Episode 1 to 5 lokacin da tazo wajan da Airah ta kewa Sheikh kiss kanta yay wani mahaukacin sarawa a firgice kuma tai wani irin….
Dafe kanta Jikinta ya shiga mahaukacin rawa jijiyoyin kanta suka mimmiƙewa, wasu abubuwa suka fara gilmawa ta cikin idanunta a hankali kuma take lumshe idanunta cikin nutsuwa bakinta yake motsawa a hankali take furta _“Ya hayyu ya ƙayyumu”_ shine kawai abinda yake faɗa drivern ne ya ɗan tsaya da gudun da yake tare da juyawa ya kalli Meema cikin girmamawa da bata matsayinta yace “Madam is everything okay?” Jinjina masa kai kawai tayi a hankali tai baya tana kwanciya a jikin kujerar motar da sauri kuma ta ɗauki wayar ta tura ta cikin hand bag ɗinta.
Ganin sauyin yanayinta yasa Driven ya fara da ita a hankali har suka isa clinic ɗin fitowa yay da gansa sosai mamaki ya kamasa ganin bacci take hankalinta kwance babu abinda ya dame ta, ya daɗe tsaye a kanta yama rasa mene zai mata, a hankali ya fara buga kujerar da take kai yana faɗin “Madam! Madam!” Idanunta ta buɗe tana ya motsa fuskarta ba tare data kallesa ba ta fito daga cikin motar kai tsaye cikin haɗaɗɗan Clinic ɗin Wanda Manyan likitoci suke ciki tana shiga Dr dake kula da mutumin ya fito Murmushi Yay mata yace “wlcm Madam Meema Ahmed Adil” Murmushi tayi masa wanda ya sanya yay ƙasa da kansa domin kwarjini gareta sosai ga shirme da manta abubuwa gaba ɗaya kanta bashi da saiti “how can i help you?” Taji Dr ɗin ya faɗa cikin ƙasa da murya tace “please ina son nai magana dakai prvtly firstly kuma ina son ganin sa please kaji?” Jinjina mata kai yay kafin yace “follow me” bayansa tabi tana sakin murmushi a cikin wani haɗaɗɗan room mai masifar kyau ba zaka taɓa cewa mara lafiya bane a ciki waje ya bata ta shige ciki idanunta na kansa, yana kwance flat gaba ɗaya an sanya masa wasu na’ura a jikinsa fuskar nan nashi manne da bandeji kansa ma haka, baƙi ne his Elegant black skin ɗin nan nashi sai ƙyalli yake, babu abu mai haske a Jikinsa irin foot ɗin sa da tafin hannunsa a hankali kuma Numfashinsa ke sauka, he’s dark-skinned yet handsome zai iya shekaru 29 to 30 kujera taja ta zauna kusa dashi a hankali ta kama hannunsa idanunta na kawo ruwa cikin ƙasa da Murya tace “you’re my brother as frm today, I’ll take good care of you kaji babu abinda zai sameka, i love You irin so na ƴan uwa in sha Allah zaka tashi you’ll be fine ji nake kamar na sanka tun can baya” Shiru tayi kafin ta ƙara riƙe hannunsa tace “Nima zaka zaka kula dani ko? I’m scared ina jin tsoran mutane, kaga nan nima wai babba ce fa kullum Dad sai yace na zama babba classes lady zaka kuya min komai ai ko? Zaka dinga zuwa mall mall dani da park za muna hira ko?” Ta faɗa hawaye na sakko mata, mamaki ne ya kama Dr domin yaji ana faɗin Meema bata da wani cikakken hankali shiyasa mahaifin nata baya fita da ita amma the she’s talking yanzu zaka ɗauka mai cikakken hankali ce Allah Al-hakkamu kenan.
Murmushi ta saki jin ya riƙe hannunta dake cikin nasa, juyawa tayi ta kalli Dr hawaye da dariya na kwance mata tace “You see ba? I’m lucky wallahi he loves me I’m so happy” ta faɗa kuka na ƙwance mata kamar wacce ta tuna wani abu kuma ta miƙe tsaye tana kallon Dr kafin tace “let’s go” fita yay tana biye dashi a baya har office ɗinsa zama yay kana ta zauna tana faɗin “i need your help Dr but kada Dad yaji please” jinjina mata yay kafin yace “what the you want?” Shiru tayi tana tunani sai kuma tace “Ina son a sawa wannan mara lafiyar fuskar wani” idanunsa ya ware yace “fuskar wa kikeso asa masa to?” Ya faɗa cikin harshen turanci “bani da photon sa amma dai ina da photon a idanuna da zuciyata” Wayarsa ya ɗauka yace “ok bari na kira arteries muga” tana zaune yay waya not too long wani mutum ya shigo ɗauke da kayan drawing ajjiye komai yay a hankali Meema take masa bayanin komai tana faɗa yana zanawa Murmushi tayi tana jin wani mugun daɗi na ratsa Zuciyarta ta sauri Dr ya miƙe tsaye idanunsa akan zanan cikin ɗaga murya yace “wannan ai photon tsuhun ɗan majalisa ne (Members federal house of Representatives) Hon Bukar Bello..
A hankali yake sakkowa daga strains ɗin benen yana sanye da wata ɗanyar shadda fara dal da ita ɗinkin babbar riga da jamper, ya ɗura wata half jaddara a saman sumar kansa wacce tayi kwance lubb da ita, ƙafarsa sanye cikin wani Black half shoe na Gucci mai tsananin kyau.
Yana tafe yana maƙala Rolex ɗinsa na A.lange & Sòhne yay wani irin mahaukacin kyau idan kaga Akeem zaka ɗauka wani Balarabe ne fuskarsa tai wani fresh ga wata haiba da zallar nutsuwa fuskar nan babu yabo babu fallasa as usual yana tafe yana lumshe idanunsa tare da motsa bakinsa.
Abbu dake downstairs yace “Akeem yau dai ka makara kamar ka manta yau Friday” caraf Didi ta amshe zan can tana faɗin “yoooo Allah na tuba zuciya ce babu alkairi, mugun abu yay masa yawa faɗa yake nema dani saboda an faɗa masa ni sallamammiya ce irinsa to ba’a gantale nake ba, wallahi Bukari ina faɗa maka kaji tsoran ka nemawa ɗan ka magani gani kuke ina wasa amma billahi wannan yaron ba lafiya ce dashi ba” Murmushi Abbu yay yace “Didi kunfi kusa da mijin naki fa” wani zaro ido tayi tace “wa ɗin? To wallahi li’ilafi ƙurash banda a ido aka haifi Audil wallahi da cewa zanyi ba jinin ka bane, saboda tsabar maita ka kalli yadda yake jajir dashi kamar wannan yaron na yama sunan Film ɗin…” Ta faɗa tana kallon Afaf wacce ta fito daga part ɗinsu da sauri Afaf tace “Shuria khana, na Film ɗin maheyk” tafa hannu Didi tayi tace “Yawwa Shimam irin albarka shifa kai Muhammadur Rasulullah s.a.w wlh mugun halinsu ɗaya” A hankali Akeem ya gama sakkowa tsittt wajan ya ɗauka sai muryar Didi ta fara faɗin “Astagafirullah satali saboda Annabi albarkacin juma’a” Murmushi kawai Abbu yay a hankali yay gaba Akeem ya fara masa baya kamar wasu abokai kai tsaye mota suka nufa gaba ɗaya kuma back seat suka shiga driver yaja sun ɗan fara tafiya Abbu ya kalli Akeem yace “Ina son sanya Akeela makaranta what’s your opinion?” Taɓe baki yay ba tare da yace komai ba ganin hakan yasa Abbu faɗin “Abdul-hakeem” marai-raice fuska yay kamar zai kuka yace “for God sake Abbu mene nawa ni” da mamaki Abbu yace “Akeem! what wrong with you? Ƴar uwar taka jikinka itace Meye ruwanka cikin lamuranta Are You at of your sense?” Haɗe fuska Akeem yay ba tare da yace komai ba a yanzu haushin yadda Abbu yake son fifita shi da village gal ɗin nan ya keji cikin damuwa Abbu yace “ashe zaka iya wulaƙanta jinin ɗan uwana jinin Baffanka har haka Abdul-hakeem? Akeela is your sister kamar Aleema da Afaf mene yasa kake haka ne?” Ɓata rai yay yana sauke numfashi kafin yace “Abbu ni kawai i hate her ne” wani sassanyan numfashi Abbu ya sauke yana mai jin daɗin hakan a ransa shi kaɗai yasan mene zuciyarsa ke faɗa masa a haka suka ƙarasa babban masallacin juma’a dake nan nasarawa gra.
A can gida kuwa su Akeem na fita Akeela ta fito a sanyaye kamar wata munafuka tana sanye da wata haɗaɗɗiyar open abaya blue black ta ɗura wata hula mai gashi a kanta, cikin nutsuwa ta ƙarasa shigowa ciki ganinta yasa Ummi faɗin “Daughter kin fito?” Ƙasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannunta Miƙewa Mami tayi tare da barin main Parlo ɗin gaba ɗaya taɓe baki Didi tayi tace “to ita dai rayuwar guda nawa take? Ban dai gantalewa da son zuciya irin na mutum, idan ka riƙe ɗan wani baka san wazai kula da naka ba fisabilillahi mugun abu ƙarara” Murmushi Ummi tayi tace “have a sit daughter” Afaf ce ta kama hannunta tana faɗin “Ummi wallahi tsoran Hamma Akeem take kamar ranta” taɓe baki Aleema tayi tace “ba dole ba, mutum sai faɗa da miskilanci wallahi gabana har faɗuwa yake idan na jisa kai wallahi munyi missed Hamma Adnan Allah ya dube mu” Ummi dake Miƙewa domin haɗa lunch tace “Za kuyi bayani bari yazo” da sauri Didi tace “Tsila (Akeela) ke dai babu ruwanki da shiga tsabgar wannan mutumin kada kuma ki biyewa su Shimam wallahi shawara nake baki bani da mugun abu ko kaɗan” ita dai Akeela da idanu kawai take kallonsu kafin tai magana taji ƙamshin turarensa da kuma zazzaƙar muryarsa yay sallama cikin parlon Abbu na bayansa da sauri ta kulle idanunta ƙirjinta na wani irin bugawa, babu wanda ya kalla cikin parlon part ɗin Mami ya nufa tana zaune a Parlon ta watching TV Akeem yay sallama Murmushi tayi tace “wlcm Hero” shigowa yay tare da zama saman sofa yana ɗan lumshe idanunsa kafin a hankali yace ” Ma’ul khair Mami” Murmushi tayi tace “yawwa yaya aiki?” Yana lumshe idanunsa yace “Allahamdulillah Mami” kafin Mami tayi magana Amani ta shigo tare da faɗawa jikinsa tana faɗin “Abbie na” satar kallon Mami yay yaga basu take kallo ba da sauri ya rungume Amani yana bata peak a goshinta yace “little na” dariya tayi tace “Abbie na kayi kyau kamar new Aunty” ware idanunsa yay irin bai gane ba ɗin nan tace “Abbie Anuty Akeela tana da kyau” haɗe fuska yay yace “لاأريدالشوشرة” (ban son surutu). Shiru tayi masa domin tasan halin Abbien nata miƙewa yay Mami tace “Uba da ƴar duk babu kunya ka daure dai kayi wani Auran a samu more children’s” shafa fuskarsa yay tare da ɗaukan Amani ya fita, ita kaɗai ce a parlon duk sun tafi taya Ummi shirya Lunch can nesa da ita ya zauna domin yunwa ya keji shiyasa ba zai iya komawa part ɗinsa ba, buɗe ido tayi a hankali tare da sauke ganinta a kan ƙwantaccen sajansa wanda yay mata masifar kyau bata taɓa ganinsa da manyan kaya ba kenan sai Friday Friday yake sawa? Ta tambaya a ranta, wani irin sahihin kyau yay kamar Balarabe Amani dake jikinsa ta zame tace “Abbie ka ganta tana da dimples irin nawa da naka Allah” Murya can ƙasa dai-dai kunan Amani yace ،أنت” إجلس معتزلا” Wato _Ke! Zauna dai-dai_ jin abinda yace tayi shiru tare da komawa ta zauna tana jan gemunsa.
Fitowa Abbu daga part ɗinsa idanunsa akan Akeela ganin Akeem zaune a parlo abinda bai taɓa ba kenan yasa kawai ya nufi dinning room gently Akeem ya miƙe da sauri Amani ta zame hannunta ta nufi wajan Akeela ogan kuwa tunda ya zauna bai kalleta ba, tana jin Ummi na kiranta kasa tashi tayi domin jinta take wani uncontactable a cikin su.
Bayan sun kammala yin lunch ɗin Akeem ya haura sama Abbu kamar yay ihu ya keji domin tun safe bai samu damar yin magana da Akeela ba bare yaga ƴar shagwaɓar data saba yi masa.
Da daddare bayan sallar Isshā duk suna zaune a parlo iya yaran Aleema, Afaf da kuma Akeela Amani tuni tayi bacci ya jima da shigowa amma gaba ɗaya basu san ya shigo ba hankalinsu na kan film ɗin This is fate da ake na karan da firita, gyaran murya yay yana zuba hannayensa a cikin hannun jallabiyar jikinsa da sauri gaba ɗaya suka juya tare da kallonsa a kusan tare da Afaf da Aleema suka shiga faɗin “lailatan Sa ida” wato barka da dare haɗe fuska Akeem yay cikin wata tsawa yace “duk Shegiyar dana ƙara gani da Wannan kayan uhm” ya faɗa yana duban ƙananun kayan dake jikinsu bakin Aleema na rawa tace “Ayyah Hero banmu ƙara sawa” wata tsawa ya daka mata yace “ku ɓace min da gani” Akeela tafi kuwa firgita jikinta na wani irin ɓari ta miƙe zata gudu da wani irin sauri yasa hannunsa ya riƙe wist ɗinta tare da wani irin juyo da ita ya haɗata da…..