TSINTACCIYA CHAPTER 7 BY NIMCY LUV
TSINTACCIYA CHAPTER 7 BY NIMCY LUV
Jikin bango da sauri kuma ya saketa jin foot steps alamar wani zaizo, kama hannunta yayi ba tare daya kalli fuskarta ba ya fara janta zuwa upstairs Akeela tsoran da yay mata yawa ne yasa ko magana ta kasa,
Jikinta ya ɗauki ɓari sanin bata da wani mataimakin sai Allah yasa tabi bayansa babu gardama amma tuni hawaye ya fara bin kyakykyawar fuskarta,
Da wani irin ƙarfi cike da Zallar mugunta yake janta zuwa samansa, suna isa bakin ƙofa ya sanya fararan hannunsa masu ɗauke da wasu kwantaccen gashin dogwaye luff dasu, cikin nutsuwa ya murɗa handle ɗin ƙofar tare da turawa tsayawa yay bakin ƙofar still bakinsa na motsawa alamar tasbihi yake, idanunsa ya buɗe sosai tare da saukewa a saman laɓɓanta wanda suke jajirrr dasu sunyi pink yirrrr dasu, da sauri kuma ya ɗauke idanunsa yana taɓe fuskarsa shiga cikin parlon nasa yayi, Akeela kanta a ƙasa ta riƙe bakin buhhh ɗinta wacce ta tsaya mata iya cinyoyinta gaba ɗaya fararan dogayen ƙafafu wanta ana ganinsu, wani ajjiyar zuciya ta sauke tana ƙara ƙamƙame Jikinta bakinta na rawa sosai, ba tare da tunanin komai ba taji ya sanya hannunsa tare da fisgarta zuwa cikin parlon nasa, maida ƙofar yay ya rufe binta yay da kallo from head to toe kafin a hankali ya shige zuwa ciki,
Kai tsaye wajan fridge ɗinsa ya nufa a hankali ya durƙusa tare da sanya hannunsa ya buɗe fridge ɗin power horse ya ɗauka tare da ice cream da cake wanda cinsu ya zame masa kamar masifa.
Saman doguwar kujera yaje ya zauna tare da zube kayan hannunsa a kan center table, cikin nutsuwa ya sanya hannunsa ya zame jallabiyar jikinsa nan da nan murɗaɗɗan jikinsa ya bayyana, ko ina na jikinsa a murɗe yake Musamman Physique chest ɗinsa ga wasu manyan nonuwa da yake dasu nipples ɗin nan sunyi yirrr dasu, tsakiyar ƙirjinsa duk gashi ne wanda sukai masa kyau matiƙa.
Cake ɗin ya ɓare a hankali yay Bismillahi tare da buɗe bakinsa ya sanya, zaƙi da kuma daɗin cake ɗin ya haddasa masa lumshewar idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya, baya yay tare da jingina da jikin sofar gently kuma ya miƙa hannunsa ya ɗauki remote ya kunna channel ɗin N.c.c ya fara kallon Labarai gyara zama yay sosai ganin an nuna zaman majalisa wanda ake a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York a ƙasar Amurka KENA BETANCUR POOL/AFP.
Idanunsa ya buɗe sosai ya zubawa zauran idanu wanda ake taron cikinsa wato United Nations.
Shugaban zauran Akeem ya kalla mai suna Abdul-ƙhadir Azeem (Chief of Staff) fuskar mutumin babu walwala kana kallonsa kasan ba kirki zai ba, a hankali kuma aka nuno shugaban lafiya wanda yake faɗin.
“June 19th was officially designated as World Sickle Cell Awareness Day,The international awareness day is observed annually with the goal to increase public knowledge and an understanding of sickle cell disease, and the challenges experienced by patients and their families and caregivers, kowa ya san cewa wannan rana a ita ake Wannan taron kuma ake tattaunawa da masu ciwon skila tare da family nasu, while mun ware manyan likitoci guda mace ɗaya namiji ɗaya wanda za suyi muhimman bayani akan wannan ciwo na sikila, mutum na farko shine Dr Abdul-hakeem Bukar Bello, sai kuma Dr Meema Ahmed Adil President’s daughter, wanda za’ai taron ne a babban asibitin dake Nigeria a garin Kano wata Asibitin Murtala Muhammad, Wannan zaure na United Nations ya ware adadin kuɗaɗen kimanin 100.25m domin taimakawa masu wannan ciwon” shiru yay saboda tafin da aka ɗauka.
A hankali Akeela ta buɗe idanunta tare da sauke idanunta akan cineme ta kalli mutumin dake bayani, she’s was shock da taji labarin domin kaf Duniyar nan ta ɗauka cewa ita ɗaya kawai take da wannan wahalalliyar ciwon.
Samun kanta tayi da son jin ragowar zan can, ana August gashi ance june kenan da sauran lokaci sai wata shekarar ma, cos already time ya shige.
A hankali Akeem ya ɗauki ice cream ɗin ya fara sha, a ransa yana ta tunanin Wacece Dr Meema ganin irin wannan sabgar bai damesa ba yasa kawai ya cire tunanin hakan a ransa.
Shi ya riga daya mance da itama gaba ɗaya a ɗakin, hakan yasa yaci gaba dayin abinda ya shafe sa, a lokacin kuma tunanin ƙauyen ne a ransu ya ɗauki niyyar a wannan weekend ɗin zai je yaga Meke going.
A can downstairs kuwa Abbu ne kwance a bedroom ɗinsa Mami na gefensa tayi shiru tunani fal a ranta, abu biyu ne ya shige mata ga rashin Adnan ga kuma matsalar mijinta, a koda yaushe suka zo kwanciya 5mins yay masa yawa wajan kawowa, tana da ishasshiyyar lafiya a lokacin da shi burinsa ya cika ya samu gamsuwa a lokacin ne ita kuma masifar sha’awar ta zata motsa, ta rasa da waye zatai sharing damuwar ta, ita kaɗai take fuskantar Wannan problems ɗin na rashin gamsuwa ko hadda sauran mata kamar ta.
Kuka ta fashe da shi da sauri Abbu ya buɗe idanunsa tare da miƙewa yace “Mami” bata kallesa ba kuma batai shiru ba ganin hakan yasa yace “please dan Allah stop cry Meke damun ki? What happened to you Khadijertou?” Cikin kuka tace “what should i do? Eh? Jina nake kamar zan mutu You older than me, buƙatarka na biya shikenan, You doesn’t care about me ya nake I’m ok ko mene, na samu nutsuwa ko yaya? Kullum cikin ciwo nake me kake so nayi eh?”
Kallonta yay yama kasa Magana daman yasan wannan zan can ne baki ya buɗe zai magana tace “look! Abbu baka sona is Okey, amma kana son nabi maza ne? Abinda banyi da ƙuruciya ta ba sai yanzu, idan problem ɗin daga nine I’m ready to accept it kuma na gyara na nemi magani, amma zama haka ba zai yiwu ba, I’m so horny bana iya bacci wallahi billahi ni da ace ka raɓeni gwamma na zauna hakan nayi managing kai na hakan nan, amma ace 2mint da kwanciya mutum ya samu gamsuwa ni kuma ko ohhho! wacce kalar azalce haka ta hauni” kuka ta fashe dashi sosai tana riƙe cikinta dake matsananci ciwo zuwa Mararta.
Kasa magana yay sai miƙewa yay kawai tare kama hannunta ya jawota tare da bata side hug.
Akeelah
Hawaye ne ya sakko daga cikin idanunta zuwa saman fuskarta cikin tausayin kanta ta ƙara ware idanunta akan t.v tana jin bayanin da ake, a hankali shugaban lafiyar yace “zamu sakko da wannan taron wanda zamu gabatar soon, saboda yawan mace mace da kuma tarin masu sikila da muke dasu yasa dole a gabatar cikin wata mai kamawa in sha Allah period zamu sanar da mouth, day, time”
Jiki a sanyaye ta miƙe a hankali kuma ta zare hular kanta tare da wani irin baza gashin kanta ya sakko har waist ɗinta ta zama kamar wata ƴar India she look like Maheyk.
Jikinta yana wani irin Kaɗawa ta ƙanƙame Jikinta waje guda walking slowly ta nufi inda Akeem yake zaune ya shagala da shan ice cream ɗinsa yana danna system ɗinsa hankali kwance ba zato ba tsammani yaji Akeela tayi wani irin..
Faɗawa jikinsa tare da sakin wata gigitacciyyar ƙara wacce ta sanya Akeem saurin ware narkakkun idanunsa tare da sauke ganinsa a kanta, wani irin murɗewa jikinta yake tamkar ba mutum ba, ga wani rawa haɗi da kyarma da ɓari da naman jikinta ya shigayi kana ganin Akeela kasan she’s not on her right sense, irin something is fishy ɗin nan.
Gajiyayyun idanunsa kawai ya sauke akanta yayinda zuciyarsa ta shiga wani irin masifafan harbawa fuskarsa babu walwala ko kaɗan, baƙin ciki da haushin yadda ta faɗa masa jiki yafi masa komai ciwo, cikin ɓacin rai bai ba duba condition ɗin da take ciki ba ya wani irin Miƙewa tsaye da sauri tare da sanya hannunsa ya fisgota haɗi da mannata jikin bangon parlon nasa, idanunsa na wani irin ruwan zallar bala’i ya mannata da jikin bangon tare da sanya hannunsa a wuyanta ya shaƙeta yadda Jikinta ke rawa haka nasa ke rawa, yama kasa magana saboda tsananin ɓacin rai, cikin tsananin ɓacin rai ya buɗe bakinsa cikin wata kakkausar murya yace “you’re mad jakaness, jikina sa’anki? Eh? I’ll killed you village gal” ya faɗa jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa raɗa idanunsa yay Wani mahaukacin jaaa gaba ɗaya ya fita a hayyacinsa ba zaka ɗauka mai hankali bane saboda yadda yake huci kamar kumurcin Maciji.
Cikin wata iriyar Murya mai tsanani taushi da kuma amsa kowa Akeela ta buɗe bakinta tare da faɗin “mune zaka kashe ko ita? Duk abinda zakai a yanzu mu zakaiwa domin ita ɗin bata da wani laifi mune ne muka ziyarce ka” wani irin kallo yay mata har zuwa lokacin idanunta a lumshe suke suna zubar da ƙwalla, girgiza kai yay yana wani irin taune bakinsa cikin ransa yake faɗin “za’a rina gayyar aljanu kawai” ɗago idanunta yay wanda sukai wani irin bala’in jaaa kafin a hankali Murya babu wasa yace “open your eyes” girgiza masa kai tayi zaka ɗauka tasan abinda ta keyi kafin tace “i can’t” cije baki yay yana wani ƙara shaƙe mata wuya cikin ɗaga murya yace “Open your eyes” da sauri itama ta sake girgiza masa kai tace “ban mu iyawa” kafin Akeem yay magana Didi wacce ta shigo tayi saurin faɗin “tsinannu gantalallu, to ubanwa kuka ajjiyewa a Jikinta? Wallahi Ii”ilafi ƙurash, tub! tub! tub! To basai kuci kanku ba Allah kurwarta ɗaci gareta” ta faɗa tana riƙe zani dake neman faɗuwa a hankali Abbu ya shigo sai Mami kana Ummi ta shigo sanye da hijab idanunta akan Akeem kasa magana tayi dan she can’t believe ace wai Akeem yayma Akeela haka.
Cikin ɓacin rai Abbu yace “Well-done Abdul-hakeem Bukar Bello, Well-done” ya faɗa yana ƙarasawa wajan da sauri Akeem ya saki wuyan Akeela tayi wani luuu zata faɗi cikin zafin nama Abbu ya rungome ta a jikinsa yana ƙara kwantar da ita cike da ɓacin rai a kuma karon farko na rayuwarsa ya kalli Akeem yace “what nonsense! Eh? Kasheta zakai eh Dr nace mekai mata da harta suma haka eh?” Shiru Akeem yay kansa a ƙasa idanunsa a lumshe wani irin baƙin ciki da kuma tarin tsanar Akeela ya ƙara nunkuwa cikin zuciyarsa, a karo na farko na rayuwarsa ta dalilinta a yanzu ta sanya mahaifinsa yana ɗaga masa murya a all his life har kawo yanzu bari wannan bata haɗa shi da Abbu ba amma yanzu da girmansa da komai har ƴar ajjiye akan Wannan yarinyar mai kama da TSINTACCIYA a idanunsa mahaifin zai masa faɗa,
Ummi dake tsaye tace “Akeem” a hankali ya ɗaga idanunsa wanda sukai jajirr ya kalleta kamar bazai magana ba sai kuma yace “Ummi..,” wata tsawa ta daka mai wacce tunda yake bata taɓa yi masa irinta ba kafin tace “shut up! Akeem this is not how I train you ƴar Uwarka jininka? Eh Akeem? Where is your heart da har zaka sanya hannunka ka shaƙe wuyan yarinya nan, U hate her is your problem amma baka da ikon da zaka sanya hannunka a kanta idan har ba kuskure ta aikata ba, ko dan ciwonta ai ka daga mata haba, bata zo nan daka a wulaƙanta ta ba, baka san Wacece ita ba ko Do you know what gal has been through? Ka ban mamaki baici ace kayiwa jinin Baffa haka ba, da kasan waye Baffa da bakaiwa abinda ya haifa haka ba wallahi zan baka mamaki” Mami wacce ke tsaye ranta duk ya ɓaci domin har cikin ranta take jin faɗan da akewa Akeem wai kuma akan wannan Yarinyar cikin jin haushi tace “haba Ummi it was a mistake wanda kowa nayi kunsan Akeem ba mai shiga sabgar mata bane, inside of ku tambayi dalilin zuwan ta part ɗinsa sai ku hau yaro da faɗa” da sauri Didi tace “A toh! Yau ni naga ruwan masifa ai she daman indo ba ƙaunar yaron nan kike ba? Kai ma da laifinka wallahi idan nace ka kaf faɗin gidan nan nine kawai ke sonka to daman idan bani ba wazai so ka ai nice dolenka” Kai Akeem ya ɗaga tare da kallon Abbu a hankali kuma ya kalli Ummi da sauri kuma ya nufi saman sofa ya ɗauki car key ɗinsa ya nufi fita waje, cikin sauri Ummi tace “Akeem where are you going ina ne zaka nine kayiwa zuciya?” Ko tsayawa bai ba bare ta sanya ran cewa zai dawo, hankalin Abbu ne ya tashi domin yana masifar son Akeem kamar ransa, ya rasa Adnan bazai saken da zai rasa Akeem ba salati Didi ta fasa tace “Huuuu! Jama’a mun shiga uku wanne irin gantalallan Bukari ya samu ne? Anya ba’a sauya maka shi a asibiti ba wannan baƙar zuciya har ina, to wallahi sai dai kaci kanka tass” wani irin Miƙa Akeela tayi a jikin Abbu bakinta na motsawa a hankali kuma tace “Abbu Hamma Akeemmm kada ya fita” da sauri Didi tazo tana dungure mata kai tace “Annamimiyya mai zubin munafukan farko ashe kina ji kikai shiru waike salammiya” yanayin Akeela yasa Ummi saurin cewa “Abbu anya ba mutanan ɓoye bane kuwa?” Kafin Abbu yay magana Akeela ta fasa wata gigitacciyyar ƙara tare da zabura ta nufi waje da gudu, cikin sauri Abbu ya mara mata baya yana faɗin “Akeela! Akeela!!” Ganin yadda take gudun kamar barewa Abbu bai san lokacin da yace “Babyna, Babyn Abbunta Stop” daga Ummi har Mami babu wanda yasan me yake nufi, cikin zafin nama kuma Akeela tai waje gaba ɗaya kasancewar ƙofar a buɗe take saboda ficewar Akeem daga cikin gidan.
Kai tsaye gate ta nufa shima yana buɗe gaba ɗaya ta fice daga cikin estate ɗin tana sharara uban gudu, daga ita sai Nightgown gashinta duk a zube tamkar mahaukaciya a haka ta nausa kan titi babu ko slippers.
Fitowa Abbu yay zuwa complete ɗin yana faɗin “Bala, Isa, Rabi’u” ya shiga kiran driver da gatekeeper da mai shukar Flowers, amma gaba ɗaya babu ko wanne bacci duk suke, jin shiru yasa Abbu komawa da gudu cikin gidan dai-dai lokacin kuma su Afaf suka fara daga baccin da suka fara domin duk da wuri suke bacci.
Car key ya ɗauka ya fito da sauri Mami tace “Ina zaka at this time?” Bai ko kalleta ba ya nufi wajan ɗaya daga cikin motocin sa ya shiga key yay mata ya fita da gudu tare da barin estate ɗin, kuka Didi tace “Bukari ka kawo masifar duniya gidanka” cikin damuwa Ummi tace “Didi Aljanu ne da Yarinyar wallahi kuma sune suka tashi” wani zaro ido waje Didi tayi tace “Muhammadur Rasulullah s.a.w shine ke kuwa kikai min shiru itana da surutu yau na shiga wallahi gidan zan bari” juyawa Mami tayi ta shige ciki Ummi ba haka da gudu Didi tabi bayansu har zaninta na faɗuwa.
Akeem kuwa yana fitowa kai tsaye motarsa ya nufa idanunsa a Lumshe ko ganin gabansa ba yayi, wani irin zafi da tafasa zcuiyarsa ke masa, yana shiga motar ya jata da gudu bayan ya danna wani hargitsastsan horn da dauri Isa ya tashi daga baccin da yake ya buɗe masa gate fita yay da motar yana ƙara gudun motar tafiya yay mai nisan gaske har yabar gaba ɗaya cikin Rail way ɗin kafin ya nemi hanya yay parking motar, kansa ya kifa akan string motar yana sauke wani zazzafan numfashi jikinsa duk rawa yake amma har kawo lokacin fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki ba sai idanunsa kawai da suka sauya kala.
Akeela kam gudu kawai take tana bin sahun motar Akeem tun tana gudu kaɗan har ta fara mai yawa, kasancewa gudun ba nata bane na Iskane yasa itama ta fice daga cikin Rail way ɗin,
Akeem na zaune cikin motar yana sauke numfashi a hankali ya ɗaga kansa dai-dai lokacin da Akeela tazo ta gaban motarsu ta shige, bayanta yabi da kallo yana ganin yadda take gudu tamkar mahaukaciya tun yana iya ganinta har ta ɓace masa da gani, taɓe bakinsa yay a hankali yay baya tare da kwanciya a jikin kujerar motar yana maida numfashi tare da dafe kansa wanda matsanancin harba masa.
Duk inda Abbu yake tunanin ganin Akeela ya duba amma babu ita tashin hankalin mara misaltuwa ya sauka akan fuskarsa, yasan Akeem tun inda yake sai kula da kansa Amma Akeela waye ta sani a wannan garin? Musamman Wannan hargitsastsiyar unguwar tasu, jiki babu ƙauri ya koma gida har wayewar gari basu runtsa ba,Didi data rufe idanunta zata buɗe da sauri tana faɗin “Muhammadur Rasulullah s.a.w” washe gari wajan ƙarfe 8 na safe lokacin tuni Abbu ya gama bada cigiyar Akeela both side t.v Redio, a hankali motar Akeem take shigowa cikin estate kai tsaye kuma gate ɗin gidan su ya nufa yana zuwa Isa ya buɗe mata gate ya shiga tun kafin ya fito daga motar cikin ɓacin rai da kuma tashin hankali Abbu ya nufi kan Akeem gadan gadan domin rashin Akeela dai-dai yake da rasa rayuwarsa….¹⁴ ¹⁵