TUN KAFIN AURE COMPLETE
TUN KAFIN AURE💐1
Motsi kadan sai ta daga labule ko zata ga shigowarsa amma shiru. Dawowa tayi falo ta shimfida abin sallah don tana gudun kada ya dawo ya shige daki bata sani ba. Tayi raka’a takwas duk biyu tayi sallama ta sake tashi ta daga leka wajen, wannan karon ruwa akeyi kamar da bakin kwarya tayi ajiyar zuciya…daya daga cikin lokutan amsar addua kenan sai ta koma kan abin sallar ta fara addua. Tana yi tana kuka bukatar tata bata wuce Allah Ya shirya mata Junaid ba. Jin alamar shigowar mota gidan yasa tayi saurin kashe fitilar falon ta koma gefe ta tsaya. Bata dade ba taji ya bude kofar a hankali ya shigo da sanda kamar wani barawo. Mamaki ne ya kamata yadda yake da key din kofar bayan ta rufe ta sannan ta kwashe duka keys din. Yana kokarin hawa sama ne yaji ta haske masa fuska da touch light din wayarta….wane dan kut….maganar ce ta makale a bakinsa ganinta a tsaye fuskar nan kamar bata taba dariya ba. Duk da a buge yake amma sai da gabansa ya fadi.
Saukowa yayi yace Mommy ina wuni…wunin uwarka Junaid? Nace wunin uwarka. Matsowa tayi ta cire hannu ta kwada masa mari har sau uku sannan ta koma ta zauna idanunta cike da hawaye.
Bai iya cewa komai ba don yasan bashi da gaskiya. Yana kallo tana masa kukan nan da ya tsana har cikin zuciyarsa yake jin abin. Mommy ya kira ta a hankali bata ko kulashi ba sai da tayi mai isarta ta tashi ta haska masa agogon bango. Karfe nawa yanzu ta tambayeshi. Hudu da minti ashirin ya bata amsa kansa a kasa. Mu je kayi wanka kawai tace masa. Ba musu ya hau sama tana bayansa yana tangadi amma yana iyaka kokarin dannewa wai kada tace ya sha wani abu. Suna zuwa kofar dakin tace idan kayi wanka kayi alwala ka sauko ina jiranka.
Daki ta wuce ta kalli maigidanta da yake ta uban minshari ta ja dogon tsaki. Ita kam kudi bai zamu musu komai ba sai silar watsewar tarbiyar yaronta. Allah Yasa ma yaran basu da yawa su uku ne. Babbar Nafisa tayi aure itama mai bin Junaid din
Hamida tana gidan mijinta. Shi kadai namiji ya zame mata jarabawa a gidan duniya. Mijinta Senator Rufai Bukar ya rike mukamai da dama har zuwa lokacin da ya fara siyasa yanzu haka karo na biyu kenan da aka sake zabarsa sanata. Ko kadan bashi da lokacin iyalinsa saboda tafiye tafiye idan yana kasar kuwa daga office sai bacci. Baya taba bincikar halin da yaransa ke ciki amma duk karshen wata zasu ji alert mai kauri a account dinsu. Gaba daya lalacewar tarbiyar Junaid bata gabansa. Alwala ta sake sannan ta tashe shi ya sauko suyi sallah a kasa tare da maaikatan gidan tunda ana ruwa.
A falon kasan ta tarar da shi yana nafila tace cikin takaici ko kunya baka ji ka gama aikin sabo ka zo ka tsaya gaban Allah kana neman biyan bukata. Masu aikata laifi bisa kuskure ma suna tsoron haduwa da Allah amma kai naka lamarin kana sane kake takewa. Alhaji dake saukowa daga bene a lokacin yace ni kuwa bana so yaro yana kokarin shiryuwa kina sagar masa da gwiwa… Alhaji kenan ta fada tana shimfida abin sallah wallahi ina dada baku shawara kai da Junaid kuji tsoron Allah. Akwai ranar kin dillaci ranar da dukiya bata da wani amfani. Daga mata hannu yayi to malama naji zan masa fada ince dai shikenan ko.
*********************
Hafsi! Hafsi!! Hafsi!!! Dagewa tayi ta sakar mata duka a baya. A gigice ta dago kai Ummati lafiya kika doke ni. Kujera ta jawo ta zauna kusa da aminiyarta, naga kin zurfafa a tunani ne. Tunda ansa rana ya kamata ki rage tunanin Saif haka. Ki kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Ke ko tunanin exams kike? Nima da tawa ‘yar brain din ban tsorata ba sai ke. Ajiyar zuciya Hafsi tayi ta kalli kawarta Ummati wai kinsan ya mukayi da Saif kuwa jiya? Me ya faru ta tambaya cike da zumudi. Ita dai soyayyar Hafsi da Saif tana burge ta. kamar abin arziki ya nuna min hotunan wasu abokansa da sukayi da matan da zasu aura sai daga baya yace ai tunda ansa rana muma yana son muje muyi. Dadina dake sokonci kin manta mun taba hirar dake lokacin da muka ga na Aliya Yunusa duk muka ce muna so. Ke kanki kin yaba da kyan da suka yi. Gara da kika ce yabawa kinsan ko da wasa bazan iya tambayar Mama ba ma balle Baffa. Bazasu taba barina naje ba shiyasa ma na cire abin a raina, amma ina fada masa haka da fushi ya tashi rai a bace.
Ummati ta dafa kafadar Hafsi bari mu fito daga exam dinnan sai muyi shawara. Karatu suka cigaba har malamansu suka shigo ajin aka fara jarabawa.
Suna tsaye a bakin gate din makarantarsu Health Technology dake cikin birnin Kanon dabo. Ummati ta zunguri Hafsi tana waigowa ta danyi murmushin yake. Kana ganinta kasan tana cikin damuwa. Ke na samo mana mafita fa. Nan take hankalinta Hafsi ya kwanta har suka samu adaidaita sahu suka tafi gida.
TUN KAFIN AURE💐 2
A tsakar gida ta tarar da mamanta tana dinki. Bayan sun gaisa Mama ta tambayetajarabawa. Alhamdulillah tayi sauki sosai. Hmmm kinji ki wai tayi sauki sosai to a bita da addua dai. In sha Allah ta bata amsa tare da shigewa daki. Tunani kawai take yi na yadda zata gabatar da plan din da suka yi da Ummati idan ba haka ba sai dai Saif yayi hakuri. Amma tasan halinsa sarai na fushi. Gado ta fada tana juyi. Idan akwai abinda ta tsana bai wuce fushin Saif dinta ba. Ina ma dai yayi hakuri har zuwa lokacin aurensu sai ayi kowanne hoto yake so ta fada a ranta.
Sauransu jarabawa uku su gama makarantar gaba daya sai dai har yau ta kasa fadawa Mama. Hafsi ta rasa me yake mata dadi domin kuwa daren jiya da Saif yazo baram baram suka rabu. A cewarsa bai taba tambayarta komai ba sai wannan ta gagara yi masa. Da bacin ransa tayi bacci ‘yar wayar daren ma da suke yi yaki kiranta da ta kira kuma yaki dauka.
Shewar Ummati ta jiyo tare da kannenta Amira da Anisa. Da sauri ta fito ta jawo hannunta suka koma daki. Ummati ta kalle ta to sarauniyar masoya yau kuma me ya faru? Tunda naji muryarki kamar zaki yi min kuka nasan an taba zuciyar. Ba kya ma tausayina wallahi naga abin har dariya yake baki. Plate din abincin da Hafsi ta zuba amma tunani yasa ta kasa ci shi Ummati ta dauka tana ci…bakinta cike da abinci tace bana tausayinki zan zo yau. Ai don nasan Baffa yana gida yau ba aiki ne ba bari zaiyi ki fito ba. Ni fada min me ya faru. Hafsi ta zauna kan dadduma tace akan zuwa daukan hoton nan ne fa. Kwarewa Ummati tayi tana kokarin yin magana. Amma dai ke anyi banza wallahi Hafsi, ina ce tun last week muka rufe zancen nan. Ajiye plate din tayi ta tashi ina zuwa…ganin zata fita Hafsi ta bita da gudu tsaya don Allah ina zaki. Ko sauraronta bata yi ba ta shige kitchen wurin mama. Mama kinga Hafsi ko…dago kanta tayi daga tsintar waken da take yi me tayi miki kuma ku da ba kwa rabo da fada. Wai nace mata ranar da muka gama exams tunda ta safe gare mu ranar tazo muje daukan hoto shine tace wai bazata ba. Mama tun shekaranjiya nake mata magana tana kin bani amsa shine nace bari nazo kawai na fada miki. Kun fiye shirme ke da yar uwar taki meye abin fada a nan. Kinsan halin Baffanku sarai baya son fice fice ba gaira babu dalili nasan abinda take tsoro kenan. Ummati wadda ta zauna a kasa tana taya ta tsintar waken tace Mama dama wai na tarihi nake son muyi ranar tunda kinga ni Bauchi zan….karasa mana bauchi zamu kaiki ko. Tashi tayi zata gudu Mama tace ba komai zan fada masa ranar da ku ka gama din sai kuje kuyi hoton shikenan ko. Nagode nagode nagode abinda ummati take ta fada kenan har ta fita daga kitchen din. Ita kuwa Mama dariya take sai dai bata san me yaran ke kullawa ba.
********************
Kwance yake kan makeken gadonsa yana zukar wata irin taba mai kauri da tsaho, bai ankara ba kawai sai ganinta ya yi a tsaye bakin gadon. Ah sis saukar yaushe…harara ta galla masa kafin ta fizge tabar. A jikin wandonsa ta kashe ta ai kuwa ba shiri yayi ihu tare da mikewa yana kokarin cire dogon wandon. Sis don mugunta sai ki kona ni me nayi miki kuma daga zuwanki. Ko da ya cire wandon saman gwiwarsa ya fara alamun tashi. Ta zauna ai kadan ma ka gani wutar can tafi wannan. Jin yanayin maganarta yasan mommy ta kai shi kara wurinta ne. Daure fuska yayi yace to idan kinzo ganewa idonki ne kinyi sa’ar gani sai ki fita….rayuwa kowa da tasa so please let me be. Duk ranar da na gaji ke zan fara sanarwa. Yana gama magana ya shige toilet tare da banko kofar da kafa daya. Har zuciyarta taji sautin ta mike a sanyaye. Zuwan Junaid America certificate kala kala ya samu banda na school harda na shaye shaye, neman mata da tsabar kin ji. Baya ganin kowa da gashi ciki kuwa harda mahaifin nasu da ya dage sai dansa yayi karatu mai tsada.
Dakin mommy ta shiga ta zauna a gefen gado tayi tagumi tana jira mommyn ta idar da sallah. Ya dai Nafisa kunyi magana da kanin naki. Hmm mommy ai lamarinsa sai addua kawai ta fada tana tabe baki. Nan ta labarta mata yadda suka yi. Mommy tace to ni dai na gaji zan sanar da Hajiyan Dangi halin da ake ciki kafin yaron nan ya dauko mana magana. Zaro idanu Nafisa tayi cikin tsoro tace Hajiyan Dangi….wai .
TUN KAFIN AURE💐 3
Cike da murna Hafsi ta kira Saif ta sanar da shi an bata izini a gida amma sai ta gama exams. Yayi matukar farinciki da jin hakan. Hafsi kyakkyawa ce ga kyan jiki. Tun farkon haduwarsu yayi ta fama da samarin da ke sonta kala kala Allah Ya taimake shi ta zabe shi kuma yayi saa mahaifinta bashi da wasa wurin sa ido akan lamuran ‘ya’yansa. Duk da kasancewarta ba fara ba saboda babanta mutumin maiduguri ne amma yanayin fatarta mai kyau ne kamar ‘yar hutu. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara saboda haka Saif yake godewa Allah da wannan tsaleliyar budurwar take sonsa.
‘Yan ajinsu suna ta faman rokonta su tsaya ayi hoton tarihi ciki kuwa harda Ummati amma ita duk hankalinta yayi gaba. Gefe ta jawo kawar tata. Ummati wai kin manta da abinda ke gabanmu ne yau kin tsaya sai hira kike yi. To sarkin azarbabi ko dan jan aji ai kya yi masa yasan kema kina ji da haduwa. Ki bari muyi sallama da mutane cikin mutumci. Da kyar Hafsi ta bari sukayi hotuna sannan suka wuce gida. Cike da doki tayi wanka ta debo kayan sallarta da wasu kaya masu kyau har kala hudu ta zuba a leda. Tana cikin shiryawa Saif ya kirata. Tana dauka ya suma magana.
(Matar baku shirya bane? Na kusa karasowa gidanku fa)
Ji tayi gabanta ya fadi don bata fada masa da yadda aka barta ba. Kashe murya tayi cike da shagwaba.
( Saif kada ka zo please Baffa zaiyi fada. Ka jira mu a bayan layin su Ummati idan ka iso yanzu zan fito nima.)
(Ai duk yadda kika ce haka za’ayi matar. See you soon)
A gaggauce ta fito ta ce Mama zan je gidansu Ummati daga can zamu wuce. To Allah Ya kiyaye amma don Allah banda bude jiki gaban mai hoto. To kawai ta amsa tana sauri ta fita. Hafsa! Taji mama ta kira ta ….a hankali ta juyu tace baki karbi kudin hoton ba da kudin mota ko duk saurin ne. Da gudu gudu ta koma ciki ta karbi kudin tayi godiya sannan ta fita.
Tana zaune gaban motar Saif suna ta hira sai dai gaba daya ta kasa sakin jiki sosai saboda basu gama fita daga unguwarsu ba. Karshe dai fakewa tayi ta duba kasan takalminta ta sunkuyar da kanta har sai da taji sun hau titi sosai. A gaban wani sabon gidan hoto da ake ji dashi a kano Treasures suka tsaya. Zata bude kofa ta fita Saif yace haba matar ai nine mai bude miki kofa daga yau, tunda gashi nayi sa’a kin shiga motata. Ummati da ke baya tayi shewa lallai ma Saif wato ni ko oho. To Allah bazan fito ba sai nima wani cikin ku ya bude min ai nima ina da nawa rabin ran. Dariya duk suka yi sannan suka shige ciki. Zama suka yi a reception ya gama magana da receptionist sannan yayi joining dinsu kafin azo kansu. Wai Saif yau babu aiki ne ka fito yanzu? Matar kenan Lukman na bari ya kama min kafin mu gama. Dayake aikin sa kai ne ba. Da haka nan nace ka zo a wannan lokacin cewa zaka yi aiki aiki. Ledar hanunta ya kala yayi saurin dafe kai kinsan har na manta ba taho da kayan canjawa ba. Bata fuska tayi don Allah da gaske kake? Dariya yayi mata sannan yace ina son shagwabarki matar kinga yadda kika yi kyau kuwa…buga kafa tayi a kasa ni fa da gaske nake yi Saif….nima da gaske nake yi Hafsah ya kwaikwayeta. Zanyu kuka fa dariya yakeyi sosai sanan ya tashi ke wasa nake yi suna mota just give me a minute.
Bayan ya dawo suka shiga aka bar ummati tana jiransu idan an gama na masoya sai ayi na kawaye kamar yadda ta fada.
Suna shiga mai hoton ya ce da Hafsi cikin hausar da bata gama zama a bakinsa ba zaka yi cire wanan veil ko yana nuna mayafinta. Saif ta kalla da alamar tambaya yace ta cire akwai wanda zasuyi nan gaba da mayafin. Nan fa aka rinka hotuna kala kala…babu wanda jikinsu baya taba na juna tun Hafsi tana dan jin kunya har ta saki jikinta. Sunyi kusan kala goma suna canja kaya dama ga ta gwanar kwalliya da daurin dankwali. Mai hoto yace da Saif, Alaji ba zakiyi na english wears ba amarya? Dariya Hafsi tayi tace kaji min mutum baza muyi ba. Saif yace ni nayi tunanin zaki zo dasu fa matar. Juya masa idanu tayi mai hoto yana kallonsu wannan sai bayan biki. To na yarda ya amsa mata sai tana shirin daukan mayafinta sai kawai taji saif ya cire mata dankwali ya kuma fizge mayafin ki dan baza gashinki sai muyi a haka a madadin kananan kayan tunda naga wannan rigar ta kama ki yadda yake maganar wani kasa kasa. Daure fuska tayi sosai Saif meye haka ya zaayi nayi hoto a haka. Ita saboda ma yanayin rigar bata yadda sunyi hoto da kayan ba mayafi ba. Fitted gown ce a jikinta wadda ta bude daga kasa. Saman kuwa ya kama mata kirji sosai gashi gaban yana da dan zurfi ana ganin saman kirjinta.
Shi kanshi Saif ya kadu da ganin surarta banda mai hoto da yake gefe yana ganin bati. Please matar ko daya ne ki bari muyi please, please. Bata son bata masa rai amma ba karamin haushi taji ba. A haka ta bari aka yi guda daya da kyar ta tsaya gabansa bayanta a jikin kirjinsa ya sakalo hannuwansa duka biyu ya ta gaban cikinta. Wani irin yanayi duka suka tsinci kansu shi da kansa yace ya isa guda dayan.
Da rashin fara’ar nan aka dauke su tare da Ummati wanda zasu nuna a gida. Bayan an wanke musu ya bada wayarsa aka tura masa. Ita Hafsi dama tata wayar ba wata mai tsada bace tace bata so. Wanda aka wanke ma cewa tayi ya rike duka a wajensa. Ganin duk ta bata rai bayan sun shiga mota yace Ummati ta bata hakuri. Ko da ummati taga dalilin fushin duka ta kai mata a baya shegiya Hafsi irin wannan pose haka ko ni da Lawal bamuyi irinsa ba. Hawayen da take kokarin boyewa ne suka sakko ba shiri. Saif na gani ya tsaya da ribas din da yake shirin yi da mota…. matar don Allah kiyi hakuri nima sai da nace muyi abin duk ya dameni. Bani da niyar wulakanta ki, ummati ki sa baki mana. Haka suka yi ta bata hakuri har ta dena kukan amma a zuciyarta ba karamin tsanar kanta tayi ba da ta biye masa irin wannan runguma haka kamar an shafa fatiha. Ga wani bakon feelings da takeji tunda ta hada jiki da Saif abinda ko hannunta bai taba rikewa ba. Anya tayi wa kanta adalci kuwa. Da wannan tambayar a ranta suka isa unguwarsu.
Kamar yadda suka tafi yanzu ma a bayan layi suka sauka. Haka ta shiga gida sukuku kannenta suka karbi hotunan da tayi da Ummati suna gani. Baffa ne ya kula da yanayinta Hafsa me ya faru ne duk kinyi wani iri. Kago murmushi tayi Baffa kaina ke ciwo. Daki ya shiga ya samo mata magani Mama tace sannu ai abin ne da yawa ga karatu, kinyi jarabawa sannan kuma baki huta ba kin sake fita. Ai zan baki hutun kwana biyu kafin ki cigaba da tayani dinki kinga sun taro. Baffa ya harareta nifa na gaji duk kin mayar min da yara teloli. Kowa dariya yayi harda Hafsi da ta kakalo ta dole.
TUN KAFIN AURE💐 4
A hankali yake tuki kamar yana tausayin kasa. Fitsararrun matasan Abuja ne suka cika wurin maza da mata wanda abin takaici ‘ya’yan musulmi ne mafiya yawan cikinsu. Kallo ne ya koma kan hadaddiyar motar da ya shigo da ita tun kafin a gane waye a ciki. Wuri ya samu yayi parking yana fitowa aka fara ihu da tafi
Juni! Juni!! Juni!!!
Junaid ji yayi kansa ya kara fashewa. Sanye yake da wani matsatstsen jeans baki da bakin takalmi mai kyau. Farar riga ce a jikinsa mai dogon hannu amma bai balle maballi ko daya ba ana ganin bakar singlet din da yayi zanzaro da ita. Hannunsa wani agogo ne mai tsada ga bandana ya daura a kansa wanda ya tara gashi ya aski gefen hagu da dama. Kana ganinsa kaga yaron da ke ji da kudi, kyau da tsabar rashin tarbiya ko rashin sanin ciwon kai.
Junaid Rufai Bukar kenan dan senate president din Nigeria wanda yake fantamawa son ransa saboda kudi da kuruciya da ke cinsa.
Tun shigowarsa harabar club din take kallonsa kamar tsohuwar mayyar da ta kwana da yunwa. Tana son namiji mai kyau a rayuwarta gashi tun da ta fara zuwa club din bata taba ganinsa ba. Yana ta gaisawa da maza da mata tana binsa da ido har ya shige ciki. Itama binsa tayi ta sami wuri a gefe ta zauna don matan da sukayi kansa suna da yawa. Sai da taga an fara rawa ta je kusa da shi suka gaisa. Amma ke bakuwa ce ko ya tambaya yana mika mata cup cike da juice wanda aka sirka da kayan maye. Yes ta bashi amsa. Matar ta hadu don ba ya kirata yarinya ba, yasan da kyar idan bata girme shi ba. My name is Tilly beauty…sunan ya dace da ke kuwa. Ni suna na Junaid. Hmm amma naji ana kiranka Juni. Cire glasses dinsa ya yi kana mata wani shuumin kallo Juni friends dina ke kirana. Nima ina son zama daya daga cikinsu. Then you can call me Juni. Haka hira ta balle tsakaninsu karshe da suka fara buguwa da kyar suka karasa daya daga cikin dakunan da ake bayarwa haya a cikin club din.
Ganin baccinsa yayi nisa ta dauki kayanta ta saka ta kare masa kallo gaskiya Juni yana da kyau ga kudi…just what she needed. Takarda ta samu ta rubuta sunanta da phone number ta ajiye masa sannan ta fita. A waje ta hadu da kawarta Rosie suna haduwa suka tafa. Aiki yayi kyau Rosie sai munji daga gareshi. Shegiya Tilly baki da kyau fa Rosie ta fada tana dariya.
*******************
Da kyar ta samu Baffa ya barta taje gidan yayarta Hadiza kwana uku bayan ta gama exams. Suna kitchen sai hira suke yi Saif ya kira Hafsi a waya. Tashi tayi ta koma daki Hadiza tana ta yi mata tsiyar ta gudu kada aji hirarsu.
Kan gado ta kwanta sannan ta amsa wayar.
(Hello matar kin wuni lafiya?)
(Lafiya kalau ya aiki?)
(Ba dadi gaskiya. Ni missing dinki nake yi sosai yau.)
Yar dariya tayi domin itama kwana ukun da basu hadu ba tun ranar da suka je daukan hoto bata ji dadi ba. Babu abinda yafi damunta kamar yadda ta kwadaitu da son sake jin ya taba ko da hannunta ne. Ya Allah Ka kara tsare mana imaninmu.
(Ina gidan Yaya yanzu amma anjima bayan laasar zan tafi.)
dadi yaji har ransa domin kamar yadda take son kasancewa tare dashi abin yafi daga wurinsa. Karshe dai yace zaizo ya dauketa.
Bayan ta idar da sallah ta zauna gaban mudubi fuskar nan tasha fenti. Hadiza ta kalleta Hafsi amma dai kinsan bai kamata ki fita da irin wannan adon kan titi ba ko. Saurin mikewa tayi to yi hakuri Yaya na yau ne kawai nayi shaawa. Saif na zuwa yayi mata waya tayi sallama da yayarta wadda har kudin mota ta kara mata. Tana rufe gate din gidan ta tsaya ta feshe jikinta da turare mai kamshi abinda bata saba ba domin tasan rashin dacewar mace ta tsaya gaban saurayi tana kamshi irin wannan banda zunubi a addinance. Sai dai ita kanta ta rasa gane dalilinta na yin hakan. Annabi SAW yayi gaskiya da ya fada mana cewa shaidan yana gudu a jikin mutum kamar yadda jini yake gudu. Shi aikin sabo da kadan muke farawa sai a hankali ya zame mana jiki. Mu kiyaye don Allah da yadda muke langabewa jikin maza ayi hoto wai da sunan pre-wedding pictures. ‘Yar uwa idan baki aure shi ba meye makomar rungume rungumen da ku ka yi duk da sunan wayewa?
TUN KAFIN AURE💐5
A mota Hafsi ta sami Saif yana jiranta. Tana shiga wani kamshi mai dadi ya bakunci hancinta tare da sanyin AC. A kunyace ta zauna tare da gaishe shi. Matar kinyi kyau sosai ga kamshi mai dadi da kike yi. Fari tayi masa da ido har na kai ka kamshi Saif? Har kin fini ya bata amsa yana dariya.
Yana tuki suna hira bata ankara ba taji ya kama mata hannu ya dora akan gear ya hada ya rike. Tana kokarin kwacewa ya matar kina son muyi accident ne kike neman canza min gear? Cikin muryar shagwabar da ta saba magana tace da hannuna fa ka hada Saif. Au hannunki ne ma ba nawa ba. Naka ne mana amma ba’a gama baka ba sai an daura aure. Ku mata komai sai an daura aure ne? Ko kin manta ansa mana rana. Ai yanzu abinda ya rage tsakaninmu kadan ne.
Suna shiga unguwar ta fada masa su bi ta bayan layinsu Ummati sai ta sauka. Ba musu layin suka shiga da yake a tsuke yake ba mutane sosai. A nan Saif ya sami damar kebewa da Hafsi don a gidansu akwai idon jama’a. Rikota yayi ya hanata fita….matar ni fa duk kin rikita min lissafi tun ranar saturday da muka yi hoto. To yanzu me kake so ayi. Wayarsa ya dauko yana nuna mata pictures din. Hafsi ta sami tarbiya daidai gwargwado kuma shima Saif din ya fito ne daga gidan mutumci sai dai koyi da tarbiyar nasara yasa idanunsu ke neman rufewa. Ganin hotunan yasa suka fara shiga wani yanayi. Yadda ya riketa kamar ba zai saketa ba yana kokarin hada bakinsa da nata itama kuma bata yi yunkurin hana shi ba.
Tun shigowarsu layin Mal Aminu ya gane motar sai dai bai gane yarinyar da ke gaba ba saboda yadda take ta kokarin rufe fuskarta. Ganin motar ta shige wata kwanar ba hanyar gidansa ba yasa yayi mamaki kamar ya wuce sai yaga anyi parking dinta a karkashin bishiyar darbejiya shiru ba’a bude kofa ba. Karasawa yayi ya tambayeshi gidan wa yake nema tunda dai a iya saninsa gidansa yake zuwa a unguwar.
Jin ya fara kissing dinta jikinta yayi sanyi hankalinta gaba daya ya tashi. Ashe akwai ranar da zata aikata irin abinda take ji a labari tana ganin bakin masu aikatawa. Wai a zamanin yanzu a haka ne kawai masoya zasu nunawa junansu kauna. Wazu hawaye taji sun zubo mata. Hankalin Saif ya tashi…matar kiyi hakuri wallahi rudin shaidan ne amma bani da mugun nufi a kanki. Yana cikin share mata hawaye suka ji an bude kofar gefen da take zaune…..idanu ta bude a tsorace ganin waye a tsaye cikin rawar murya tace BAFFA!.
*******************
Yau ma a cikin maye ya shigo gidan anyi sa’a ma wurin shabiyu da rabi na dare ya shigo. Fito ya shigo yana yi yana karkada keys din hannunsa. Kamar daga sama yaji kira…Junaidu….ba don namiji bane da gabansa sai ya fado kasa yadda ya mugun tsorata. Cak ya tsaya kamar gunki. Don ubanka juyu ka kalleni. Mommy da ke zaune a gefe shiru tayi. Babu wanda baya tsoron Hajiya Ramatu. A kano take aure a gyadigyadi wurin da aka fi sani da dangi, shiyasa ma ake kiranta da Hajiyan Dangi.
Tsawa ta daka masa bazaka zo ba ne. A hankali ya dawo ya zauna a kan kafet. Hajiyan Dangi doguwar macece kamar mahaifisu ga jiki. Ita kadai ce mace a gidansu kuma ita ce babba. Allah bai bata haihuwa ba sai dai ta rike yara da yawa daga danginta har na mijinta. Cikinsu harda Senator Rufai kaninta. Mace ce mai riko da addini kuma mai sa ido akan tarbiya. Yanzu Junaidu wannan wannan rayuwar ka daukarwa kanka? Tana magana ta soma hawaye gidan malamai manyan mutane muka fito amma saboda giyar kudi na dibanka kana neman lalata rayuwarka. Ta kalli Mommy yanzu sai da lamarin ya baci haka kika sanar dani. Mommy dai hakuri ta ba ta. Bandanan kansa Hajiyan dangi ta fizge. Gobe kaje ka aske wannan shegen kan kuma kazo ka nuna min. Ko ci kanka bai ce mata ba haka ya tashi ya basu wuri. Yana shiga daki tabarsa ya kunna ya fara busa hayaki kai ka ce bakinsa salansar mota ne. A haka Junaid ya tuna bai yi sallar laasar, magriba da isha ba. Tsaki ya ja tare da mikewa ya nufi toilet. Haka ya yi alwala irin yadda kwakwalwarsa ta karanta masa sannan yazo ya fara ramuwar sallolin da bai ma san abinda yake karantawa ba.
A dakin da take sauka kuwa Hajiyan Dangi ce ta yanke shawarar ba zata koma kano ba sai kaninta Rufai ya dawo daga Australia sunyi magana akan Junaid. Babu abinda taki jini kamar yaro yaki ya rinka keta dokokin Allah ba tare da an dauki mataki akansa ba.
TUN KAFIN AURE💐6
Jikinta ne ya hau bari kamar wadda akayiwa wanka da ruwan sanyi a watan december. Iya karfinta ta sa ta fito daga motar har tana ture baffan nata. Da gudu ta tafi gida kafarta ko takalmi babu. Saif kasa motsi yayi a cikin motar ya sunkuyar da kansa. Baffa bai ce masa komai ba ya juya ya nufi gidansa.
Yadda ta shigo a firgice yasa Mama saurin tashi. Hafsa lafiyarki? Me ya faru? Me ya sami yayarki? Ko daya cikin tambayoyin bata amsa ba durkusawa kawai tayi a gabanta tana kuka. Amira ce ta kula da kafarta ta dama tana jini. Mama kinga kafar Hafsi jini take yi. Subhanallahi ke ko hatsari ku ka yi a hanya ne? Ana magana kinyi shiru kamar wata bebiya. Cikin Hafsi har wata kara yayi da jin sallamar Baffa. Bai jira an amsa ba yaja hannun Hafsi zuwa dakinsa. Garammm ya banko kofar har gaban su Mama ya fadi. Ihun Hafsi kawai suka ji tana bawa Baffa hakuri. Tuni Mama ta karasa bakin kofar dakin tana bugawa. Su Amira kuwa sai kuka don tun suna jin kukanta har murya ta dashe. Babu irin magiyar da Mama bata yi masa ba amma yaki budewa.
Baffa ya bude kofa Hafsi na kwance a kasa Mama ta shiga dakin hankali a tashe. Baffan yara me ya faru…ke Hafsa me kika yi? Da kyar Baffa ya iya fada mata tana ta kuka. Ita kam Hafsi hawayenta ba na zafin duka bane kawai. A yau tayi dana sanin abinda ta aikata. Tayi Allah wadarai da maza da matan da basa jin komai lokacin da suke hada jikinsu da juna alhali babu aure a tsakaninsu. Yau ina ranar son zuciya da biyewa shaidan da mukarrabansa wadanda suke tallata irin wannan watsewar da sunan wayewa. Mama da bata zagi yau duk wanda yazo bakinta dankarawa ‘yar tata take yi. Tashi ki bani wuri mara mutumci tasa kafa ta haure ta. Jiki a sanyaye haka ta fita tana share hawaye.
*******************
Yau kwana biyu kenan Junaid yana wasan boya da Hajiyan Dangi da mommyn sa. Tun sallar asuba yake fita sai tsakar dare yake dawowa. Hajiyan Dangi lamarin ba karamin bata mata rai yake ba. Sai da ta cika sati a gidan Senator Rufai ya dawo. Bayan ya huta cikin dare wuraren karfe tara yaje dakin da yayar tasa ta sauka.
Hajiyarmu babbar Hajiya zama da tashi cikin girma. Kirarin da ya saba yi mata kenan yau ma bayan yayi sallama tun kafin ta amsa ya fara. Murmushi tayi tana kallonsa Rufai bazaka girma ba. Ai indai ina ganinki bazan girma ba Hajiya. A kan kafet ya zauna kusa da ita. Bayan sun gaisa tace Rufai kayi min laifi gaskiya. Nasani Hajiya kiyi hakuri don Allah. Lamarin Junaid ba karamin bata min rai yake yi ba amma na rasa yadda zanyi da yaron nan. Dole ka fadi haka mana tunda aiki yafi maka akan rayuwar iyalinka, wannan karon cikin fushi take maganar. Kana gefe kana turowa yara kudin da yafi karfin aljihunsu dama me kake tsammani ga yaro da kudi. Shiru yayi don sam baya iya mata musu kuma ma yasan gaskiya take fada masa. Tace to ni na yanke shawara ayi masa aure kawai. Tun zuwana garin nan yaron nan yake gudu na. Anya zaka iya haduwa da Allah akan yadda kayi wasarairai da amanar da Ya baka na yara? Ni bama wannan ba Rufai kaga Allah Ya baka matsayi a cikin al’ummar kasar nan kuma ni da kai munsan ba iyawarka bace tasa ka samu. Zabi ne kawai na Allah saboda haka ina dada baka shawara kamar kullum ka tsaftace dukiyarka. Ka kiyaye haram don ita kadai zata wargaza duk wani al’amarinka. Kafin ta gama magana idanun senator sun cika da kwalla. Dukiya kam suna kai suna wasa da ita son ransu. Ya Allah Ka bamu ikon gyarawa ya fada a zuci.
Gyara zama yayi to Hajiya wa kike jin za’a aura masa? Sayyada ta bashi amsa a takaice. Sayyada ya maimaita shima ban gane ta ba. Bama ka santa ba. Yar wajen Atika ce kanwar Baba(maigidanta). Tun da ta gama secondary ta dawo hannuna bana ma zata gama Buk. Yarinyar tana da hankali da nutsuwa kuma bata daukar wulakanci shiyasa nake ganin zata taimaka wajen shawo mana kan Junaidu. Har zuciyarsa yayi murna. Yace Allah Ya shige mana gaba kuma don Allah a taya mu addua.
Junaid yasha fada wurin mommy karshe tace yaje ya bawa Hajiyan Dangi hakuri. Yana zuwa bakin kofar dakin yaji maganar da suke yi da babansa. Wata dariya ce taso kubuce masa…wa yaga Junaid da auren dole. Ai ko zai dena holewarsa a waje zancen aure bai ma taso ba. Juyawa yayi a hankali tare da yankewa kansa shawarar barin garin a washegari daidai lokacin da yaji Alhajinsu yana cewa idan Hajiyan Dangi zata koma kano zasu tafi tare.
TUN KAFIN AURE💐7
Tamkar mujiya haka iyayenta suka mayar da ita. Babu mai kula ta sai kannenta suma a tsorace don sun fuskanci su Mama fushi suke da ita kada abin ya shafe su.
Zaune take kan abin sallah tana addua bayan ta idar da sallar walha. Idanunta duk sun shige ciki ga ramar da tayi saboda rashin cin abinci. Sallamar Mama taji ta dago kai a hankali ta amsa. Ko kallonta bata yi ba ta shige tana tashin Anisa ta sha magani saboda ta kwana da zazzabi. Mama ina kwana, an tashi lafiya? Kau da kai tayi amma har zuciyarta tana tausayin Hafsi. Ta kuma yarda kaddara babu yadda bata zuwa ga bawa domin duk cikin ‘ya’yanta ita ce mutum ta karshe da zata yi tsammanin zata aikata abinda tayi. Auta tashi ki sha magani kinji ta fada tana shafa kanta…mama baki ji Hafsi tana gaishe ki ba ne. Tsaki tayi naji…karbi ki sha sai ki koma baccin. Ficewa tayi ta koma dakin Baffa ita ma kukan tayi na tausayin halin da yara harma da manya ke fadawa a wannan zamanin.
Fitar mama kenan Amira ta fito daga toilet ta tsugunna gaban Hafsi. Wai ni don Allah me kika yiwa su Baffa ne Hafsi? Anisa dake kwance tace yanzu ko gaisuwarta ma Mama bata amsa ba. Share hawaye tayi babu komai ku dai cigaba da taya ni addua. Tana gama magana ta tashi ta tafi dora girki don yau duty dinta ne. Ko da ta fita kannenta shawara suka yi karshe suka kira yayarsu Hadiza a waya aka sanar da ita abinda ke faruwa.
*******************
Juni ba wayarka bace take ringing tun dazu. Tsaki yayi ya sha giyar dake hannunsa kyale shi Old Man dina ne. Ai tun shekaranjiya dana bar Abuja yake nemana wai ni zaiyi wa aure…what a joke. Chuks ya kalle shi ku fa hausan nan haka kuke sai ku auri yarinya ku sakata a family way at a very young age. Chai, its disgusting. Karshe ta sami VVF wurin haihuwa kuyi mata saki.
Hannu Juni ya daga masa kai Chuks dakata bana son wulakanci. Gara mu aure muke yi da wuri kai at what age ka fara having sex. Wata irin dariya yayi har mutanen dake cikin club din suka fara kallonsu…my friend I was 13 fa. Wata yarinyar neighbour dinmu ce na ma girmeta. Ita ta koya min. Juni yace ka gani ko ashe kune manyan ‘yan iskan. Kun iya bibiyar kananan yara amma idan musulmi sunyi aure sai ku ce child molestation. Hypocrates kawai.
Abeg no insult me Juni…..ai kaine ka fara zagin hausawa nasan karshe kan musulmi zaka koma.
Ha! Kai ai baka son islam Juni you drink like a fish and sleep with every prosti…kafin ya karasa Junaid ya kai masa naushi a baki. Kan kace kwabo bakin Chukwuma ya fara jini nan yan uwansa suka tarar wa Juni ashe akwai ‘ya’yan hausawa. Cikin karamin lokaci sai fada ya kaure tsakanin musulmi da kishiyoyinsu na wani addinin. Ana ta fashe fashen kwalaben giya. Karshe dai sai da police suka shigo cikin lamarin duk aka kama su.
Tilly na kwance akan gado tare da wani hamshakin dan kasuwa taji waya. tayi mamakin ganin sunan Juni ta dauka cike da farinciki. Nan yayi mata bayanin yadda suka yi da police amma jin ko dan waye kuma ya jika su da kudi sun sake shi. Karshe dai yana bukatar account number dinta zai turo mata da kudi ta biyoshi Lagos. Ko sallama bata yiwa mutumin da suke tare ba ta tashi bayan taji alert….lallai Juni na ji da kudi.
*******************
Cikin kuka Mama tayiwa Hadiza bayanin abinda Hafsi tayi. Itama kukan take…wallahi Mama yanzu irin wanan masifar ake fama da ita. Ana zance ana shafar juna karshe inda kaddara ayi ciki. Mama tace abin ne ba kama ba don ni na haifi Hafsa ba amma wallahi nayi mata shaidar alkhairi. Allah Yasa mufi karfin zukatanmu. Amin Mama amma don Allah kuyi hakuri don idan muka nesanta kanmu da ita sai tayi wani abin ma babu wanda ya sani.
Hafsi da Ummati suna ta shawarwari Hafsi tace kinsan har yau babu waya ko text din Saif. Idan na kirashi ba waya a kashe abinda ya kara batawa Baffa rai kenan don shi so yake a sanar dashi a matso da bikin. To aje gidansu mana don bai isa ya jawo mana jangwam ya tsallake ya barmu a ciki. Ke ummati kila a tsoro yaji. Ai ni dadi na dake shegen son saurayi. Ni wallahi daga yau kara kama kaina zanyi har sai anyi aure.
TUN KAFIN AURE💐 8
Juni dear….yes Tilly ya amsa mata yana daga kwance. Jin tayi shiru ya taso ya dafa bayanta Tilly ya akayi ne? Ko akwai abinda kike so ne? No tambayarka kawai zanyi. Nawa ne kudin hotel dinnan ne per night? N150,000. Wage baki tayi ko wane kwana daya? Eh menene wai duk kin wani rude. Gani nayi kudin da yawa kuma gashi yau kwanan mu hudu banda abinci da kudin da kake kashewa a club. Wani shekeke ya kalleta kin ma raina ni to ko don ban biya ki naki kudin bane…yana gama magana ya mike daga shi sai gajeren wando ya jefo mata cheque. Ganin kudin dake jiki dubu dari biyar ba shiri ta rungume shi tana ta murna. Hmm kudi a kasar nan yana hannun masu shi suna kashewa kadangarun bariki da kayan maye wani lomar tuwo ta gagare. Masu kudi a rinka cin halal dai.
*******************
Hajara tana kwance tana chatting da kawayenta a group taji shigowar messages. Tana dubawa hotuna ne kamar bazata bude ba don bata da data sosai sai ta bude daya. Zumbur ta mike ta bude sauran. Babu shakka ita ce a duka hotunan biyar. Wadda ta turo cewa tayi ga wani style din pre-wedding pictures. Nan da masu cewa sunyi kyau da masu zaginsu. Wani gumi ne taji yana karyo mata lallai baa shaidar mutum, yarinyar da kullum take shigar mutumci ita ce a haka. Tsam ta tashi ta dauki mayafi ta sauka kasan gidanta wurin makociyarta. A’a Hajara shigo mana ina kitchen…a sanyaye ta karasa dama wani abu zan nuna miki a waya. Maimakon kiyi min forwarding, menene mu gani. Ruwan ruden tuwon da take ne ya fallatso mata a hannu da gefen fuska saboda tsabar rudewa. Na shiga uku ni Hadiza me zan gani haka. Hajara tace a group na gani shiyasa na nuna miki don nasan wace Hafsi. Muciyar ta karba ganin yadda hannun Hadiza ke rawa ta karasa mata tuwon. Daren ranar bata yi baccin kirki ba. Mijinta zai tafi office ya ajiyeta a gida duk da bata fada masa abinda ke faruwa ba yasan babu lafiya.
A falo ta hadu da Baffa zai fita ta gaishe shi. Lafiya dai Hadiza irin wannan sammako ko duk saurin ki taya ni cin kosai ne. Murmushin karfin hali tayi. Baffa akwai wasa sai dai baya sake wa yara suyi yadda suke so. Ganin bata biye mishi ba ya mike muje ciki. Mama na shafa mai suka shigo dakin. Hadiza lafiya kuwa…nan taji tsoron nuna musu hoton sai dai tasan yadda irin hotunan nan ye kawo a social media. Wasu mutanen basu da aiki sai ture turen abinda bai shafesu ba karshe su kunna wuta mai wuyar kashewa. Wayar ta mika wa Mama shima Baffa ya zauna kusa da ita yana gani. Hankalinta bai tashi ba sai da taga ‘yarta babu ko dankwali ta shige jikin namiji sai kace kanin uwarta ko na ubanta. Nan take numfashin Mama ya fara sama sama dama ita haka take idan ranta ya baci. Haka ta fita daga ita sai daurin kirji ta shiga dakin ‘yan matan. Wayar chaja ta fizgo daga jikin bango ta fara tsula mata. Hafsi ji tayi kamar a mafarki ana dukanta tayi saurin tashi. Yaya Hadiza ta gani sai kannenta. Cikin rashin fahimtar laifinta ta fara rokon gafara. Sai a lokacin Baffa ya shigo ya dakatar da dukan. Kyaleta haka ku zauna. Wayar Hadiza ya bata hoto daya ta kalla ta kama kafar Mama tana kuka…don Allah ku yafe min wallahi bazan kara ba. Ki ma kara mana don ubanki…wai ni dame muka kuskure miki ne Hafsa. Lokaci guda kin fara taka rawar gangar shaidan. Wai ma yaushe akayi wannan hoton? Shiru tayi ba amsa. Nace yaushe akayi hoton nan…lokacin…lokacin. Hadiza ce ta katse ta lokacin me? Uhm lokacin da muka ce miki zamu daukar hoto da ummati. Nasan za’a rina cewar Baffa. Dama nasan da taimakon wani a lalacewar da kika soma yi. Amma wallahi ba a gida na ba. Gidansu Saifullahin zani in nunawa mahaifinsa, ki kwana cikin shiri aurar dake zanyi cikin kankanin lokaci mutuniyar banza. Nan dai ya hada duka yaran nasa sun sha fada da nasiha. A dakinsa kowa yace da Mama ta tabbatar ta tuntubi Hafsi ko babu wani abu da ya shiga tsakaninsu domin shi yanzu ya tsorata da halin yaran zamani.
TUN KAFIN AURE💐 9
Wani irin kuka ne mai tsuma zuciya take yi tunda Mama tayi mata wannan tambayar. Wai ko wani abu ya shiga tsakaninsu??? Lallai ta jawo wa kanta tunda an fara zargin ko lalacewar tata ta kai nan. Gabadaya filon ta gama jika shi da hawaye dadin bakin cikinta ma rashin duriyar Saif. A wannan yanayin Ummati ta shigo itama kukan take yi don a falo Mama da Maman Ummati suka hada su ana ta fada gadon itama ta hau suka jeru kamar masu gasar kuka. Iyayensu sunyi fushi sosai. Tayi nisa da tunani kamar daga sama taji wayarta na ringing. A firgice ta tashi don tasan ko waye me kiran. Ringtone dinsa daban ne….ummati ce ta doke mata hannu da sauri tana kokarin dauka. Ta galla mata harara to banza mara zuciya..duk abinda ya samemu a dalilinsa sai yau zai wani nemeki. Cikin muryar data dashe saboda kuka tace bafa ki san me ya same shi ba. Don Allah ki bani wayar Ummati. Ni wallahi haushi kike bani mtww karbi ni ta dangwara mata wayar ta koma gefe. Ba zancen fita don iyayensu mata suna falo ana ta maida zance.
(Matar ina kika shige ina ta waya.)
Kaji rainin hankali yau fa kwanansu shadaya bata samunsa a waya(kai zan yiwa wannan tambayar. Sai da kaga matsala ka guje ni Saif) kuka ne yaci karfinta.
Shima a hankali yake magana( kiyi hakuri ni kunyar sake haduwa dake da kuma Baffa nayi. Matar ina tsoron zama sirikinsu har abada Baffa bazai dena ganina da wannan tabon ba)
Wani irin faduwar gaba taji (me kake nufi? Baffa fa sun taho gidanku tare da baban ummati)
(Nasani na kuma nayi musu bayani. Tun ranar da ya ganmu na sanar da umma don bana son rufafa a maganar aure. Kunya tasa na guje ki don naci amanar Baffa. Kiyi hakuri muyi rabuwar arziki amma bazan iya aurenki ba.)
Yana kashe wayar wani kuka ya kwace mata har su Mama suka shigo. Ummati suka fara tambaya tace bata san me ya faru ba. Kasa fada musu tayi tana ta kuka. Gajiya suka yi da tambayar aka kyaleta. Sai da Baffa ya dawo ya sanar da Mama yadda sukayi mahaifin Saif yace aure ba fashi tare da basu hakuri shi kuma dan yace bazai iya sake kallonsa ba. Zai fadi haka mana tunda yaso gurbata mana rayuwar yarinya. Suna ta maganganu Hafsi na jinsu daga daki tana kara tsanar kanta da abinda tayi.
******************
Junaid mutum ne mai son jindadi, bashi da magana sosai sai ta zama dole. Ko kadan baya daukar raini wannan kuma hali ne ya tarar da dukiyar da ya taso cikinta. matashi ne dan shekara 30 ga tsaho ga kyau ga fatarsa mai kyau saboda tana shan hutu. Gashin kansa da saje kuwa a kwance yake don kudin da ake ajiyewa don gyara shi daban ne. Yana son kula da gashin kansa ko kadan baya son abinda zai bata shi.
Yana kwance kan kujera kansa a cinyar Tilly tana fara shafa masa kai. Doke mata hannu yayi yana magana kasa kasa ki dena taba min kai I hate it. Dan tabe baki tayi to yi hakuri naga ko wanka baka yi ba meye abin bacin rai don na taba? Tashi yayi ya bude fridge ya dauko lemon gwangwani ya fara sha. Ki shirya muje party amma bana son wannan faratan naki kamar mayya ya juya mata baya ji yadda kika kusa kwashe min baya. Yi hakuri Juni ta fada tana murmushi bari na cire su nayi wanka.
Lallai ma yarinyar nan wallahi kinyi kadan abinda ya fada kenan lokacin da ya fito daga wanka ya kama Tilly tana satar masa kudi. A fusace ya karaso gabanta tasha mari hagu da dama. An fada miki bani da hankali ne? Kumatu ta rike tana kuka ni ka mar Juni? Ke ‘yar waye da bazan mareki ba? Barauniya kawai get out of my room. Kafa yasa yana kai mata duka tana ta ihu. Da kyar ta rarrafa ta fita ya jefo mata jakarta waje ta ce zaka san ni kayiwa haka Juni sai na bata maka rayuwa. Ta mike da kyar tana dingisawa mugu ko kudina bai bani ba duk kwanakin nan dana yi.
*******************
Dai dai yake kallon mutane kowa da budurwarsa ana ta sha’ani. Shegiya Tilly da nasan haka take ai da tun wuri na nemi me rako ni nan. Kai da wa kake magana Juni? Shafa kansa yayi zancen zuci ne ya fito fili birthday boy…Imi dan wani gwamna ne abokin Junaid ne tun suna secondary duk watsewarsu tare sukeyi. Ina babe din da na ganku tare ne jiya? Tilly barauniya? Ai na bata takardar sallama dazu….sata fa tayi min don rainin hankali. Imi da buduwarsa suka fashe da dariya ai abokina ka fiye kwashe kwashe ne. Ya rungumo yarinyarsa ya Simy akwai wata a kasa ne kada yayi kwanan kadaici yau. Kai kyale ni kawai. Maybe na tafi portharcout gobe. Dont worry I will pay bana son ganinka so quite. Wayarta ta dauko ta mika masa ga hotunan wasu nan duk kawayena ne idan ka zaba kayi min magana. Bakin ruwan suka koma ana ta wasa da raye raye shi kuma yana kallon ‘yan mata kala kala a wayar. Tsaki yayi zai kira Simy ta karbi wayarta sai kawai yaci karo da hoton da ya daga masa hankali. Zuciyarsa ce take bugu da sauri da sauri…he wants this girl at all cost abinda kawai yake fada a ransa kenan.
TUN KAFIN AURE💐 10
Jikinsa har tsuma yake bai taba ganin macen da ta sace masa zuciya ba kamar wannan. Fatansa daya wannan saurayin daya rungumeta ba mijinta bane. Tura hotunan yariyar yayi daya gani a wayar ya tashi da sauri ya je wurin da Imi da Simy suke ta rawa yana mata liki da dubu daya. Janyo hannunta yayi suka fito daga wurin rawar Imi ya jawo wata suka cigaba. A irin wannan rayuwar ana tafka kazanta da tsabar rashin kishi. Muna mantawa akwai ranar da zamuyi accounting for every second da muka rayu a duniya.
Rawar ta cigaba da yi a gabansa ganin hakan ya sake janta suka kara nisa da mutane. Yarinyar nan nake son duk wani information a kanta. Ta dan nutsu ta kara kallon hoton wai wannan kake nufi? Eh mana are you blind? No…sai tayi dariya sorry. Gaskiya Juni bansan….katse mata magana yayi kada kice baki santa ba. Kudi ya dumbuzo daga aljihunsa ya damka mata a hannu. Ki nemo min duk abinda ya dace …ya sake kallon hoton…my God she is so pretty. Kallonsa tayi Juni wannan fa pre-wedding pictures ne. Maybe ma anyi auren don na kusa wata da ganinsu. A wani group aka saka na ma manta wadda tayi sending. Ai sai ki sake sending ki tambaya. Look Simy bani account number dinki. Washe baki tayi yanzu kayi magana. Zan nemo ta ko tana gidan miji ne sai tazo ta kashe maka kishi…kanne masa ido tayi ta tafi. Simy ‘yar shekaru goma sha tara karamar yarinya ce da iyayenta suka kyaleta take irin rayuwar da take so saboda yanayin aikinsu. Tana abinda taga dama babu me tsawatar mata a cewar su kuruciya ce ke damunta. Wai kuma yar musulmi kenan babu ko tsoron mutuwa.
******************
Kallon ‘yan uwanta take ana ta hayaniya. Kanta har wani sarawa yake don ciwo. Wai nan lefenta aka kawo shine har yanzu mutane basu gama tafiya ba. Dakinsu ta nufa kai tsaye wata kakarta tace ai tunda kika dawo bamu watse ba ki tsaya ki kalli abin arziki. Ai ni kam wannan miji yayi ina ma ina da sauran kuruciya. Dariya duk aka sa Hafsi ko sai hawaye. Auren da zaayi ba dadin rai. Abinda komai Baban Saif ne yayi don yace shi ba karamin mutum bane aure ya zama dole. Shi kuma Saif kamar bai taba cewa yana sonta ba alaqar tasu yanzu ba yabo ba fallasa. Da gaske yayi nadamar abinda ya aikata sai dai kunyar iyalin Baffa yasa har ransa baya son ayi auren. Allah Yaso shaidan baici galaba a kansu ba da da wane ido zai tsaya a gaban mahaliccinsa? Ko matasa nawa ne ke tuna irin wannan a lokacin da suke matse ‘ya’yan mutane suna aikata haramun?
Ita kanta Hafsi tana tsoron rayuwar da zasuyi. Da wane ido zasu rinka kallon juna. Ba don zuwan Baffa ba da kila shikenan. Rayuwa kenan wasu na nadama wasu kuwa zuciya ta gama bushewa a aikin sabo. Tir da wannan rayuwa ta shaye shaye da zinace zinace. Ya Allah Ka kara shiryamu Ka bamu wadatar zuci.
TUN KAFIN AURE💐 15
Hajiya da maigidanta sun rasa yadda zaayi a dauko Junaid saboda Baba baya iya tuka mota idan dare yayi. Suna ta shawarwari ne suka ji karar motar sa. Da sauri suka fito motar duk ya buge ta a hanya har fitila daya ta lotse. Haka suka kama shi yana ta tangadi sosai suka shiga dashi dakinsa. Hajiyan dangi sai kuka take jin yana ta sumbatu yana cewa ko a aura masa pretty ko ya saceta ta karfi. Haka Hajiyan Dangi ya zauna dashi har yayi bacci shi kuma Baba ya kira senator Rufai ya sanar dashi halin da ake ciki.
Jirgin karfe 7 na safe suka biyo shiyasa kafin karfe 9 sun iso kano. Motoci uku ne suka je tarbar maigirma senate president da matarsa Hajiya Salama.
Gyadigyadi suka nufa gidan Hajiyan dangi. Mommy tana ganin Hajiya ta soma kuka. Bana son irin haka Salama baki san hawayen iyaye cuta ne ga ‘ya’yansu ba? Share idon tayi tace kinga irin yadda nake fama da yaronnan ko. Ni fa har cewa nayi baban nasu ya dena saka masa kudi a account amma yaki. Hajiya tace abar maganar nan yanzu bari mu gani ko ya tashi. Su hudu iyayen suka dunguma zuwa dakin da Junaid yake mahaifinsa ya bude kofar ya tarar dashi a kwance yana ta busa taba. Kwarai yayi mamakin ganinsu ya tashi da sauri…mommy na sannu da zuwa. Hannun daya kawo zai tabata ta doke tare da jan tsaki. Yasan fushi take yayi murmushi kawai ya kalli babansa. Oldman ya hanya? Wannan karon Hajiya ce ta doke masa baki. Uban naka kake kira oldman kuma junaidu? Dole kayi ta ganin ba daidai ba a rayuwarka tunda iyayenka ma basu da kima a idanunka. Da ace ka maida hankali kan addini da kasan cewa iyaye sun fi karfin wasa. Duk zama suka yi Senator Rufai ya cire hularsa yasa hannuwansa ya dafe kansa. Ya rasa yadda zaiyi da Junaid fitinarsa kullum karuwa take. Hajiyan Dangi ce ta labarta musu dukkan abinda ya faru game da yarinyar da Junaid yace yana so mai suna Hafsa. Ya maimaita sunanta a ransa yafi a kirga. Baya jin komai game da maganganun da suke yi. Hankalinsa ya tafi can tunanin yadda zai mallaki yarinyar nan mai suna Hafsa.
A wace unguwa suke? Ita ce kalmar da yaji daga bakin mahaifinsa. Da sauri yace sabontiti. Shi kuma wanda zata aura fa? Nan ma Junaid ya bada amsa. Alhaji zaka nema min aurenta? Wallahi nayi maka alkawarin zan shiryu indai na aureta. Hajiyan dangi tace Rufai me kake shirin yi ne? Shima Baba cewa yayi hala ka manta haramcin neman aure akan na wani? Mommy dai binsu ta rinka yi da ido don itama bata san me mijin nata yake nufi ba.
TUN KAFIN AURE💐 16
Senator Rufai dai bai iya basu amsa ba ya fito ya shiga mota kafin a tayar Junaid ya fito da gudu ya shiga shima. Yana zama senator yace sai ka kwatanta wa Bulus hanyar gidansu yaron. Yaron kuma Alhaji? Ba nema min auren zaka yi ba? Junaid just do as you are told kaina har ciwo yake. Ba gobe ne daurin auren ba? No sai saturday.
Gidan ya fara cika da ‘yan uwa da abokan arziki yan daurin aure da biki. Da gudu ya shigo gidan har yana zubar da abincin dake hannunsa wata yayarsu ta janyo shi. Adnan saurin me kake yi ne haka? Yauwa yaya ina baba? Ya amsa yana ta haki. Wannan mutumin da ake nunowa a tv na gani a waje sun zo a cikin motoci masu kyau sai wani mai bindiga yace babanmu suke nema. Kai mai bindiga fa kace…eh wallahi amma na hango na tv din mai kudi ne fa. Jin kamar yana shirme Zainab ta leqa wajen da kanta ai kuwa babu karya wasu jeeps ne guda uku duka bakake amma ta tsakiyar tafi kyau. Ga mutane sun sha suit kowa rike da bindiga.ba shiri ta koma cikin gida ta nufi dakin baban su sai dai a hanya suka hadu har Adnan ya isar da sako. Shima dai mamakin yayi ya matsa wurin daya daga cikin guards din yace shine mai gidan. Yana kallo yaje wurin motar tsakiyar sai ga wasu mutane su biyu sun fito. Ba ko shakka senate president ne Rufai Bukar yasha wata ash shadda kana ganinshi kaga kudi da tsantsar jindadi. Dayan kuwa saurayi ne kyakkyawa amma fa kayan jikinsa kamar anyi wasan kura dashi. Guard din yace ciki zamu shigo. Nan Alh Bashir yace to cikin hanzari yayi musu jagora. Suna shiga jamaa sai binsu ake da ido har falon sa. Maman su Saif ta bi bayansu. Ganin waye bakon ta fito da sauri ta bada kudi a siyo lemuka da ruwan roba.
Alh Bashir ya sake gaishe da senator sai yayi mamakin ganin da kansa ya taso ya bashi hannu. Bayan sun gama gaisawa yace ni sunana Rufai Bukar. Ranka ya dade ai tuni na ganeka ni sunana Alh Bashir. Senator ya kalli Junaid dake zaune kan kujera ba zaka gaishe shi ba. Nan take ya sauko ya gaishe shi. To nasan zaka yi mamakin ganina tare da dana a gidanka ba tare da an sanar da kai ba. Haba ranka ya dade ai nasan dole ce ta sa. To akan maganar yarona ne Junaid… ..haka dai senator ya labartawa Alhaji komai na halayyar dansa da Hafsa da ya gani yana so. Ikon Allah kawai yake fada sannan yace idan na fahimci inda zancen ya dosa so kake Saifullahi ya hakura kenan. Hular kansa ya cire ya dago kai idanunsa da kwalla Alhaji ina tsammanin Allah baiyi maka jarabawar haifar dan da….kai Junaid ku fita. Suna fita ya cigaba da magana wadda sai da hawayen da yake kokarin boyewa suka zubo. Junaid yaro ne me hazaka tun kuruciya amma yanayin aiki da jindadin kudi yasa na sangarta shi. Yaronnan ya janyo min magana fiye da yadda baka zato ga shaye shaye ga….da dai sauran aikin sabo. A bisa amana nake fada maka sirrina Alhaji wallahi wallahi mulki da kudi jarabawa ne sosai daga Allah. Ban farga da munin share lamuran yarana ba sai da naji waazi daga bakin wasu malamai kamar su Daurawa, Kabir Gombe dasu Dr Sani Rijiyar lemo. Nasan nayi barna mara iyaka har ina tsoron ranar mutuwata. To a yau bani da burin daya wuce yaron nan ya shiryu ina ganin wannan zai zama sanadiyar samun rahma a gareni. Da gaske mutumin nan kuka yake Alhaji Bashir ya fada a ransa ganin hawayen senator. Naji dukkan bayaninka ranka ya dade amma yarinyar ba tawa bace. Na sani kuma nasan haramcin nema akan nema. To idan haka ne ko zaka yarda na kira mahaifinta dashi yaron. Ai mai nema ke bi kayi mana jagora gidansu kawai.
********************
Baffa don Allah ka yafe min nasan nayi kuskure wanda bana fatan sake maimaitawa. Hmm Hafsatu kenan ki sani kaza tana taka danta ba don bata sonshi ba sai don ta koya masa hankali. Hakika muna cikin wani zamani da ake tallata zina kamar kayan miya, wanda bai siya ba ma kallon banza ake masa. Amma ina so ke da ku ma…ya kalli Amira da Anisa lallai ku tuna wutar Allah mai radadi ce kuma baya bata da kadan. Sai ka aikata abu ka manta ma dashi watarana ya dawo ma lokacin da baka tsammani. Ki je na yafe miki Allah Ya yi muku albarka. Da farinciki suka tashi dukkansu balle ma Hafsi zuciyarta fes fes. Suna fita Alh Bashir ya kira Baffa ya sanar dashi zai zo gidansa da baki nan da lokaci kadan idan yana gida.
TUN KAFIN AURE💐19
Kwanaki uku kenan tana binsa yanzu ta gama gano gidan da yayi masauki abinda ya rage mata yadda zata sami damar yi masa abinda bazai taba mantawa ba har abada. Idan ka bari motar nan ta bace mana bazan biyaka ba yau…dreban taxi din ya kara gyara mirror din gaban mota yadda zai ganta da kyau. Mace har mace sai dai babu alamun mutumci a tare da ita. Kallonta yake yana hadiyar yawu saboda irin shigar da tayi ta matse dukkan jikinta ga kamshi kamar wadda tayi wanka da turare. A bakin gate din wani asibiti yayi parking inda yaga motar da suke bi ta shiga. Tafiyarta kamar da gayya don ta tada hankalin maza…a zuciyarsa dan tasi Allah Ya isa yayi mata shi ba aure ba kullum yana yawo da ita a gari.
Junaid ya kara kyau saboda shaye shayen da ya dena yan kwanakin nan. Bayan sun gaisa da likitan ya sanar dashi irin tests din yake so ayi masa wanda suka hada da HIV da hepatitis. Haka ya zauna aka debi jinin yasa kida a kunnensa yana jiran result. Ba karamin farinciki yayi ba ganin komai is negative. Tabba ba kowacce mace yake muamala da ita ba kuma yana amfani da hanyoyin kariya amma dai gaskiya ya tsorata. Ana bashi result dinsa wani tsalle yayi da ihun murna. Yana fita Tilly ta fito daga inda ta boya tabi layin ganin likita. Da kyar da salon bugun ciki taji abinda ya kawo Juni asibitin. Allah Ya kama ka Juni boy sai ka gane baka da wayo a hannuna.
******************
Baffa da Mama sun yanke shawarar Hafsi ta tafi gidan kanwar mama dake aure a Funtua har sai yaji makomar Junaid. Haka ta tafi ba musu ita duk abinda zai sa su manta da laifinta na baya nema take shiyasa suka yi shawara da ummati kan cewa bazata musa musu zancen auren dan senator Rufai ba. taso kwarai taga ko waye Junaid dinnan sai ta hakura ganin iyayenta basa yi mata zancensa.
A gajiye Tilly ta shiga gidan aminiyarta Rosie. To mutanen banza daga ina kike tun safe ba hi ko hello. Harara ta galla mata Ke ni bani abinci kizo muyi magana akwai gist fa. Rosie ta washe baki hala kin samo hanyar bi ta kan wannan shegen dan sanatan? Fadi ki kara Tilly ta amsa tana fari da ido. Yanzu dai cikina is empty.
Wata gyatsa tayi me kara sannan tasa kafa ta ture plate din abincin can gefe. Tana sakace hakori tace Rosie yar mutan Gaya kina ji na. Ni da tun dazu na matsu ki gama cin abincin, to ya akayi? Nan ta bata labarin yadda ta bishi asibiti da test din da yayi. Ni bansan me ya faru dashi ba these days amma naga baya zuwa wuraren shakatawa. Da na yanke shawarar na biya doctor din su fada masa yana da HIV to sai nayi tunanin kada yaje wani ya sake aga negative. Tunda ta fara magana Rosie take dan tunani. Ke banza magana fa nake. Ki fada min yadda zanyi ya aureni mu kwashi namu national cake din. Ai ki kwantar da hankalinki sister. Ki bani two months kawai sai muje gidansu. Two months kuma? Yi min bayani mana. No ki bari idan har naga titin da nake so mubi mai billewa ne zaki ji komai. Ke dai ki cigaba da sa ido don mu tabbatar da inda yake ko yaushe.
*******************
Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah. Senator Rufai ya mayarda Alh Bashir wani abokin shawara don har yau Mal Aminu bai gama sakewa dashi ba. Alh Bashir yasha fada masa idan har suka dage zasu iya sawa ya aikata alkhairi a ragowar tenure dinsa. Shi kuwa Junaid a kano ya cigaba da zama wurin Hajiyan Dangi ya rage shaye shaye sosai. Har mamaki yake bai taba ganin Hafsi da idanunsa ba amma sai bin dokoki yake saboda ita kamar wanda aka asirce.
Saura sati uku bikinsa da Hafsi ta dawo kano. Baffa kam sai da yaga result din tests har daga asibitoci biyar ya gamsu tare da bawa Junaid damar yazo ganin Hafsi.
******************
Ba wata kwalliyar kirki tayi ba don ma yayarta Hadiza ta matsa mata ne. A falon gidan Baffa yace su zauna yadda mutane zasu rinka wucewa. Hafsi murmushi tayi daya fadi haka lallai laifi Allah kadai ke yafewa duka amma mutane abu kadan sai yasa su tuna baya. Tun kafin ta daga labulen falon gabanta ke faduwa wanda ta rasa dalilin hakan. Da wannan muryartata mai kamar shagwaba tace Assalamu alaikum. kamar a dauke masa wutar jikinsa Junaid me cika idon yan bariki ya kasa amsa mata. Ido kawai ya bita dashi…..you are so beautiful,so pretty. Kin shigowa tayi ganin yadda ya rude saboda ganinta. Tsoronta daya kada ta shigo ya nemi taba ta. Karaso mana Hafsi ko….ya fada yana daga gira daya. Sunkuyar da kanta tayi kasa baka amsa min sallama ba ai. Dan bata fuska yayi ke da gidanku. Anyway wa alaikum salam. Tana zama ya tashi daga inda yake ya dawo kujerar kusa da ita. Wallahi kin hadu sosai ma kuwa. Can’t wait to have you. Gabanta taji ya fadi anya wanan ne Baffa ya aminci ta aura. sai ma a lokacin ta kare masa kallo. Don kyau dai yana da shi amma wani gashi ta gani ya danyi tsini daga tsakiyar kansa ga wani wando me fadi irin wanda black americans na ghetto suke sawa. Rigar jikinsa kuwa itama me fadin ce ta dan sauko masa. Nan take taji ta tsane shi bare da ta kalli wani kwantareren takalminsa. Yanzu fa sai ace duk kayan nan masu tsada ne ko ta fada a zuci.
Ganin yadda take kare masa kallo yasa yayi shiru shima yana dada kallonta. Can daya ji shirun yayi yawa yace yah nayi miki ko? Firgigit ta kalle shi bata fahimci zancen sosai ba kawai sai tace masa a’a. Ya zaro ido me kika ce? Kinsan yadda mata ke rububina kuwa? Ganin ya dauki wata hanyar sai ta katseshi da gaisuwa. Bayan yan mintuna tace zata shiga gida.
TUN KAFIN AURE💐 21
Yan uwa da abokan arziki sun cika gidan. Yan ganin kwal uwar daka ma suna nan zaune suga irin abinda zaa kawo wa Hafsi.
Akwatuna ne ake ta shigowa dasu gidan har goma sha takwas. Hajiyan Dangi ita ce tayi jagora ta nuna musu kayan. Akwati set biyu guda sha biyu na amarya ne komai na ciki me tsada ne harda set din gwal uku. Sai daya na baffa, na Mama, na ‘yan uwanta sai kuma wanda zaa bawa yan uwa da abokan arziki. Dukkansu shake suke da kaya. Ga kudin dinki dubu dari biyu. Wai a haka ma don kada su zake da yawa ne. Ranar bakunan mata sunyi magana har sun gaji kowa da abinda take fada. Mama dai dubu hamsin baffa ya bata na tukwici shima don su fita kunya ne. Wata yayarsa ta kira ta fadawa tare da dora nata dubu goma. Yayar da yake tana da dan rufin asiri ta kawo talatin itama Hadiza ta kawo goma suka cike dari. Hajiyan dangi mace mai kwarjini da kamala tace ko kwandala ba zasu karba ba yar da aka basu ma sun gode. Suna fita aka hau bude buden akwatuna ana kallon yadda ake wasa da kudi a kasar mu.
*******************
Hafsi tasha gyaran jiki sai sheki take ga lalle wanda mai lallen ma Hamida ce ta turo ta har gidansu. Ummati tace Allah Yasa kuyi zaman lafiya naga kamar basu da raina mutane. Haka akayi kamu a wani makeken filin senator wuri ya dauki mutane. Idan kaga Hafsi kamar wata yar tsana saboda mai kwalliyar ma tafiyayya ce. Tayi kyau har ta gaji. Su ummati ma da kannenta baa barsu a baya ba. Itama Batul Mamman sai wani shishshige musu take taga kudi.
Ranar dinner wasu kaya da mama ta kure basira ta dinka Hafsi ta saka. Ummati tana zuge mata zip din rigar Hamida ta shigo da wata riga da skirt na lace ne ko material gashi nan dai abin mai daukar ido golden brown. Tunda aka fara biki ta likewa su ummati sun zama kamar kawaye. Kayan hade suke da takalma da head and veil. Hafsi ta bata rai ni fa wanan zan saka mama ce ta dinka min. Hamida ta marairaice haba matar yaya anko yake son kuyi da kansa ya bayar aka dinka miki. Suka shiga ban baki ita da Ummati amma sam Hafsi taki yarda har zancen yakai kunnen mama. Nan tayi musu sulhu gobe idan zaa kaiki sai kisa nawan zan ga mai hanaki amma yau dai ki saka na angonki. Maman ummati tayi dariya to yar shagwabar Mama gobe dai zanzo da bokitin share hawaye.
Taro yayi taro wuri ya cika da mutanen da suka amsa sunansu a naija. Yan mata anyi dinkunan rashin mutumci suna tafiya kamar sanduna babu lullubi. Matan aure sai hura hanci wai kar a raina su. A mota aka tsayar da hafsi har Junaid ya iso. Ko da ya fito da shaddarsa golden brown bata gane shi ba. Duk da yasa hula ta kula yayi aski, ya gyara fuska gaba daya ya canja. Shima kallonta kawai yake har ya karaso. A kunnenta ya rada mata ni kada ki cinye ne da kallo, it has been three weeks, kin kara kyau kema. Cak ta tsaya saboda yadda yayi kusa da ita. Ana fara musu alamar su shigo cikin hall din taji yana kokarin kama mata hannu. Kokarin fizgewa tayi shi kuwa ya matse hannun ga zobba a hannun har ta fara jin zafi. A hankali tace kaci bashi wallahi. Ya sassauta rikon suka shiga.
Dinner tayi kyau kuma ko liki baayi ba wannan kuma dokar Hajiyan dangi ce. Tilly da aminiyarta Rosie ma sun sami shiga a wurin daukar hoto Junaid ya gansu. Tsoro ne ya kamashi ya hau adduar kada tayi masa wani haukan a wurin don bai ma tsaya tunanin yadda suka sami katin shiga ba. Bayan sun dau hoto ta bashi wani envelop congrats Juni boy. Hafsi ta dan kalle ta Tilly tace amarya mun dai rigaki lasar zumar muna fata tayi miki dadi yadda….junaid ne ya katse ta get out…ba musu ta kama kawarta suka fita don idanunsa sunyi jazur tasan halinsa sarai. Babu wanda ya kula sai Hafsi kowa na shaanisa.
Dreba ne a gaba sai Ummati baya kuma Junaid da Hafsi don ya nace shi zai mayar da ita gida. Tayi kokarin daurewa ta kasa can kasa kasa tace wace wannan matar ne. Dama ransa ya gama baci gashi yana son dena shaye shaye babu ko taba a aljihunsa ya harareta idan zaki bude baki kiyi magana ki bude sai wani kasa kasa kike da murya kamar wata mumina. Ummati ta juyu don taji me yace…zare mata ido yayi ke bana son gulma me kike kallo. Ba shiri ta juyar da kanta. Tooooh wannan ne mijin da Hafsi zata zauna dashi. Hafsi dai shiru tayi tana kallon fuskarsa. Sai tayi da gaske akan wannan mutumin. Abu daya ta sani dai da yana cikin farin ciki kafin yaga wannan matar. Babu ko sallama suna zuwa gida suka fita yace da dreba yaja motar su tafi.
Daki ya shiga hankalinsa a tashe yana tarrabin abinda ke cikin takardar da Tilly ta bashi.
Juni boy
Nasan kana cikin farin cikin auren da zakayi gobe nima ina taya ka murna. Sai dai ina me tabbatar maka gobe zanzo Abuja a tawagar amarya. Ga wedding gift nan.
Luv Tilly
Bude daya takardar yayi gumi ya karyo masa ganin reult ne dake tabbatar da Tilly na da ciki har wata uku.
TUN KAFIN AURE💐 22
Ko kayan jikinsa bai canja ba ya fita zuwa hotel din da abokinsa Imran yayi masauki. A waje ya tsaya yayi masa waya. Sai a karo na uku ya dauka ya sanar dashi yana wurin parking ya fito.
Suna hada ido Imi yace yace ya mutumin you sounded worried fa. Me ya faru ne? Envelop din Junaid ya mika masa. Imi ya rinka dariya bayan ya karanta harda hawaye a idonsa. Can ya daki kafadar junaid…haba mutumina kada ka bada ni mana. Yanzu har akwai wata chick da zata ce kayi mata ciki ka yarda? Matan nan fa sun fi mu tsoron faruwar hakan tunda su ke da wahala. Wani abin kawai take so. Fuskar Junaid babu sauran kwanciyar hankali uhm uhm Imi aure fa zanyi kuma Allah Ya sani ina son yarinyar ina kuma son gyara rayuwata. Kaima Allah Ya baka tagari. Kayya yaro gigin soyayya ke dibanka bari romon ya kare zaka neme ni ne. Bayan ina kallo dazu amaryar taka ta murguda maka baki. Kansa ya shafa yana dariya da irin tsokanar fada ne yaga tana kulashi shiyasa yake mata haka a fili yace Kai kam kamar ana kada maka gangar shaidanu..ya ina cewa zan shiryu kana min mugun baki. To yi hakuri na Hafsa Imi ya fada yana dariya…yanzu dai ka manta da wannan yarinyar kada ma ka sata a rai. Idan ta sake nemanka kaci ubanta da kyau wallahi zata kyaleka. Kada ma ka fara bata kudi don sai tayi blackmailing dinka. Nan suka yi ta shawara sai wurin ukun dare Junaid ya koma gida.
******************
Bacci sam yaki zuwa idanun Hafsi sai tunani take kala kala. Wannan Junaid din dabiunsa na bata tsoro( wai ma don ya rage!) Gashi haka hankalinta bai kwanta da matar da ta bashi envelop ba. Maganar Tilly duk ta tsaya mata a rai wai sun rigata lasar zumar…..ehew abin kyankyami ma zancen ta fada a fili tana yamutsa fuska. Anya ba yan is…sai tayi shiru zargi babu kyau don haka mafitar ta daya shine ta mike ta dauro alwala ta tayar da sallah. Haka tayi ta nafila har asuba tana addua sannan ta yi bacci.
Sai wuraren goma na safe ta farka. Shima Hadiza ce ta tasheta da dundu…to kasa ana shirin fita daurin aure kina kwance kina bacci hankali kwance. Mutssika idanu tayi ta mike…ina ummati ta tafi Yaya? Debo miki ruwan zafi kiyi wanka. Kinsan dai baffa yace karfe biyu zaa bar kano so kiyi da jiki kafin a dawo daga daurin aure. Ta kalli agogon wayarta…Allah sarki nan da mintuna arbain da bakwai kin zama matar aure. Cikinta taji yace kulululu da gaske abin yazo. Kuka tasa wa Hadiza inama basuyi wadannan hotunan ba tun kafin aure da yanzu Saif ta aura. Ummati ta ajiye bokitin hannunta ki gode Allah baa daura dashi ba don yadda aka ce Junaid yayi bayan yaga hotonki da kila a gidan auren zai biyo ki ko ma ya kashe auren. Hadiza tace kyale ta ummati ai tasan wani baya auren matar da ba tasa ba.
Kayan da mama ta dinka da aka hanata sawa daren jiya su tasa ai kuwa tayi kyau sosai. Katon mayafi ta yafa ga kamshi ko ta ina.
Taro yayi taro don manyan mutane na kusa da nesa sunzo bikin dan manya. Junaid yasha cream shadda harda babbar riga da brown din takalmi da hula maroka suna ta sanaar su. Daga karshe dai Liman ya daura auren Junaid Rufai Bukar da Hafsa Aminu Garba.
Mijin Hadiza ne ya bugu ya sanar da ita an daura auren kan sadaki dubu dari gida ya cika da guda da hayaniya. Wata ‘yar makarantarsu tace gaskiya Hafsa Aminu kinyi saa muma Allah Yasa mu a danshinku. Yan Amin kuwa suka amsa.
Ansha koke koke lokacin dasu Hajiyan dangi suka zo daukar amarya. Mama kasa daurewa tayi ta kulle kanta a daki. Baffa ma yana mata nasiha yana sharar kwalla. Bai taba tunanin zata yi auren nesa ba, aure ma irin na gidan Senator Rufai Bukar. Motoci har wajen layinsu Hafsi. Cikin motocin kuwa harda wadda Rosie da Tilly suka dauko haya suka bi ayarin kai amarya. Don karfin hali har mutane uku suka dauka aka dauki hanyar abuja.
TUN KAFIN AURE💐23
Tunda suka hau hanya basu tsaya ba sai a garin Abuja. Motar da Baffa ya hado da kayan da yayi wa ‘yarsa ita ce ta karshe cikin jerin motocin.
Duk girman gidan ba duka motocin bane suka sami shiga ba saboda yawansu. Shima gidan cike yake da mutane gashi basu iso da wuri ba. Dakin mommy su Hamida suka kai Hafsi. Ita dai kanta a kasa taki dagowa ta kallesu. Mommy cike da murna tace nasan kun gaji ga magriba ta kawo kai a kai su masauki suyi wanka aci abinci sai su shirya akwai wata dinner din karfe takwas. Hafsi ta kankame hannun ummati sai Nafisa tace mommy wanan fa aminiyarta ce tare zasu zauna kafin anjima ta dan kanne ido ai sai kamarsu ta Junaid ta kara fitowa Hafsi tayi saurin dauke ido.
Suna idar da sallar magriba akace Hafsi ta shiga wanka. Komai na toilet din daban yake…oh su Hafsi a toilet din matar sanata. Tana fitowa Hajiyan dangi ta tarar suna hira da mommy sai ta kasa fitowa. Hadiza da Nafisa wadanda tuni jininsu ya hadu kamar sun dade tare suka fara mata dariya. To yan nema da girmanku kuna tsokanarta ko. Fito kinji Mamana ni da nake so nan da yan watanni nazo yi miki wankan jego. Ai Hafsi ji tayi kamar ta nutse a kasa Mommy tace Hajiya banda kwacen ‘ya fa. Fita suka yi aka hau shirin amarya. Kwalliyar yau tafi ta sauran events din. Suna gamawa kowacce ta dau ado jiki da fuska aka fito. Motar da tafi kowacce kyau daga tsakiya wani abokin Junaid ya bude mata kofa ta shiga ya rufe. Taso kwarai Ummati ta shigo sai kawai taga angon nata ya bude kofa ya shigo. Ko tari bata yi ba don ganin yadda yake mata wani irin kallo. Ganin abin yayi yawa tace ya dai? Kamar ya, ya bata amsa. Ta dan turo baki kallo dai idan yayi yawa kuma zai shiga babin haramun. Yayi yar dariya Hafsi Hafsi kenan malaman karya. Wa ya fada miki kallon miji ga matarsa yana ciki. Yadda tayi da bakinta yasan sarai murguda masa shi zata yi. Yarinyar nan akwai tsiwa. Yace to basai kin murguda min baki ba idan kina son kiss, you just need to ask. Sakin baki tayi tana kallonsa lallai ma mutumin nan..dole ta fasa ta kara hararsa. Yayi dariya sannan yace karamar mara kunya kawai.Hular kansa yasa ya rufe fuskarsa. Idan mun isa ki tasheni jiya banyi baccin kirki ba. Ko kula shi bata yi ba ta juyu tana kallon garin da bata taba tunanin zuwansa ba nan kusa.
Nicon Hilton suka shiga. Manyan mutane da dama sun halarci taron. Su mommy ma da sauran matan manya sunzo amma shadaya suka koma gida. Sai wurin shabiyu da kwata mommy tayi wa Junaid waya kan su taho gida haka saboda Hafsi da suka yi zaman mota.
Ummati da Hafsi suna ta hira kafin motar da zasu shiga su karaso gabansu idon Hafsi yakai kanta. Tabbas matar da tazo wurin dinner dinsu ta kano ce. Matsowa tayi gaban Hafsi tana tafiya duk jikinta na girgiza amarya mun sake haduwa ko. Ga naki gift din nasan Juni boy da rowa baiyi sharing nashi dake ba. Wai wacece matar nan ne ta tambayi kanta? Tana mika hannu zata karba Junaid ya doke hannun. Da bomb ne ma haka zaki karba ko ya fada yana zare mata idanu. Mota na tsayawa yaja hannunta ya tura ta ya kalli ummati kema shiga zan biyo abokina. Yana rufe musu motar kafin su fara tafiya Hafsi taji yace cikin daga murya what the hell do you want? Suna tafiya a zuciyarta Hafsi ta kara yarda akwai wata a kasa tsakanin Junaid da yarinyar nan.
Ka zama uba ga abinda ke cikina. Ka rabani da rayuwar da nake ciki. Maana ka aureni. wadannan ne amsoshin da Tilly ta bawa Junaid. Imi dake ta yiwa Junaid horn ya shigo su tafi ya fito daga mota ganin yadda abokin nasa ya rude.
Ya mutumina wannan ce akuyar dake neman daga maka hankali? Ai ka barni da ita na farfasa mata jiki kawai. Yana magana ne yana kokarin dauko wani katon dutse cikin wadanda akayiwa wurin ado dasu. Imi baya daukar raini shiyasa Junaid ya tabbatar yana daukan dutsen nan jikin Tilly zai dire shi
TUN KAFIN AURE💐 24
Dakata Imi zanyi maganinta da kaina. Cheque ya bata na dubu dari biyu. Idan na sake ganinki duk abinda ya faru dake ki kuka da kanki. Suna jan mota ta fita ta tari taxi don yau Rosie bata biyo ta ba saboda laulayi daya fara damunta. Murna take sosai don wannan cheque din sabon makami ne a gareta.
Daki aka bawa Hafsi da kawarta sauran yan biki suna wani masaukin. Nafisa ta tafi da yayarta Hadiza gidanta ita kuwa Hamida ta nace tare zasu kwana da amarya kafin washegari a kaita side dinta.
******************
Wani sabon kukan Hafsi da Ummati suka dasa lokacin da aka fito rakasu bakin motocin da zasu mayar dasu kano. Yanzu haka zata zauna da mutanen da bata gama sanin halinsu ba. Ga uban gayyar wato Junaid ko doriyarsa bata sake ji ba tun a wurin dinner. Kamar yasan tunaninsa take sai gashi ya fito da kananan kaya a jikinsa. Yau ma yayi kyau tunda kayan ba oversize bane. Har kasa ya durkusa ya gaishe da gwaggwaninta dasu Maman Ummati. Hadiza ta rungumota tana ta bata baki akan ta dena kuka haka. Kyaleta Hadiza na gulma ne fa kuna tafiya zata sake. Harararsa tayi yace ai gara ki nuna musu halin da kike min. Hajiyan dangi ta kama hannun Hafsi rabu dasu zan miki maganinsu. Anisa ta Amira ma sunyi nasu kukan da alkawarin zuwa idan anyi hutu. Haka dai suka rabu abin tausayi ana janye Hafsi daga jikin Ummati.
Bayan duk sun tafi aka dawo falo. Hajiya da mommy suka yi musu nasihohi da fatan alkhairi. Nafisa da Hamida suna gefen amarya suna kula da masu dada share wurin kafin su kaita. Sai da aka gama fadan Junaid yace to Allah Ya saka da alkhairi amma yaushe zaku bani matata? Mommy ta cire takalminta ta jefa masa to tsohon mara kunya ai gara ka nuna hali. Ya dafe kai Hajiyan dangi tana duba masa…yauwa Hajiya duba ki gani ko kan ya fashe. Hafsi kuwa dariya tayi har sauti ya fito yace kinci bashi Hafsi Hafsi. Nan suka zauna ana ta raha sai kawai suka ji sallama.
Mata ne biyu sunsha hijab daya sai kuka take dayar tana bata hakuri. Dif Junaid yayi ya dena dariyar da yake saboda ya gane mai muryar. Zuciyarsa ke bugun uku uku yaji yawon bakinsa ya kafe. Itama Hafsi ta gane yarinyar ko baa fada ba tasan akwai matsala don ta kula da yadda ya kidime da ganinsu. A fusace ya kallesu ubanwa yace ku shigo har nan? Wai ma waye ya baku izinin shigowa.
Mommy da Hajiya cikin rashin fahimta suke kallonsa. Junaid kana hauka ne zaka ga baki kayi musu irin wannan tarbar? Rosie ta kiyi hakuri Talatu an gama cutarki shine zaa ci mutumcinki saboda baki da galihu. Mommy tace ku zauna muji abinda ya kawo ku. Tilly harda fyace majina ai yafi kowa sanin dalilin zuwanmu. Idanun Junaid kamar an bada masa yaji yayi kanta yana sirfa mata zagi.
Kana tabata zansa a kulleka mara mutumci kawai. Daga kai yayi suka hada ido da Senator Rufai. Alhaji wai me ke faruwa ne? Yace ku zauna muyi magana. Su Rosie aka wani rakube a kasan carfet ita da Tilly. A bakin gate na gansu suna fada da security yarinyar can ya nuna Tilly tana ta kuka. Ganin haka na tsaya aka kirasu tayi min bayani. Cheque ya dauko daga aljihunsa ta mikawa Mommy. Kingani kudin daya bata jiya wai taje a zubar mata da ciki. Kinga goshinta inda ya fashe lokacin da yake dukanta ta fadi. Kamar anyi masa wanka da ruwan zafi haka yake ji. Me tilly ke nema ne a tare dashi? Kokari yake su hada ido da Hafsi ita kuwa idonta na kasa tana kuka a hankali. Salati su Hajiya suka hau yi tace lalacewar taka har ta kai ka bada kudin yin kisa. Kuka ne ya kwace musu ita da Mommy. Junaid yana ta basu hakuri. Hafsi ta mike zata shige daki don taga zancen kamar ba nata bane. Dawo dawo ai gara kada a munafunce ki Hafsa. Senator ne ya kirata ta dawo ba musu. Ya maida kallonsa ga Junaid. Ka san yarinyar nan? Eh na santa amma wallahi ban dake ta ba. Rufa min baki shashasha. Kullum yadda zaka zubar min da mutumci yake nema. Ko tsoron mutuwa baka yi.
Ke ya daka ma Tilly tsawa ta dago a firgice garin yaya kika amince masa. Ta kara jan majina ta fara bada labari. Ni ina sayar da kati ne kusa da wani club da suke zuwa a gidan wannan yayartawa nake da zama shine ya biyoni wai yana sona. Rannan rannan sai kuka….Rosie tace kudin kati yace taje ta karba shine yayi mata fyade. To ganin cewa danka ne bamu daga zancen ba.
Wallahi Álhaji karya suke duk karuwai ne….bakinsa yaji Hajiya ta make. Rufa mana baki. Rosie ta cigaba to da mun hakura sai kuma ga ciki shine muka neme shi kawai jiya sai yazo har gida ya bata cheque ita kuma ta karba don taga bana nan.
Hafsi tayi saurin daga kai tace ba kece kika zo wurin dinner ba kuwa daren jiya? Junaid yace yauwa Alhaji wallahi kaga itama zata min sheda wurin dinner ta biyoni ba raping dinta nayi ba. Mommu tace Hafsa kada ma ki fara kare masa don bakisan waye Junaid ba. Duk abinda akace yayi zan yarda. Allah wadaran iskanci yau mahaifiyarsa ma taki yarda dashi.
Senato Rufai ya kalli dansa cikin bacin rai yace ka taba ganinta? Eh ya amsa masa. Muamala ta shiga tsakaninku? Shiru ya kasa magana. Ya daka masa tsawa kai kurma ne. Hawayen da yake boyewa ya sauko yace eh. Innalillihi wa inna ilaihi rajiun. Koda ba auren so suka yi ba amma ace mijinka yana neman mata akwai ciwo. Hafsi duk auren ya kara fice mata a kai. Senator yace to ke zaa kaiki asibiti a sake miki gwaji idan ya tabbata da gaske yayi wa Junaid wani mugun kallo zamu jira ta haihu a aura maka ita. Mikewa yayi a fusace su Hajiya suka bi bayansa.
TUN KAFIN AURE💐25
Rigar jikin Junaid ta gama jikewa da gumi saboda tashin hankali. Yana ganin iyayensa sun shige yayo kansu ita da Rosie sam ya manta da Hafsi a falon. Ke don ubanki me kike nema ne a tare dani? Idan ciki ne dake ki sa a ranki har abada Junaid bazai taba zama uba ga abinda ke cikinki ba.
Hafsi tana jin furucinsa ta nemi hanyar barin falon rasa wurin shiga tayi don bazata bi su mommy ba a wannan yanayin da suka tashi. tana turo kofar dakin da take tsammani ma na masu aiki ne taji yo Tilly tana dariya…haba Juni boy ai kowa yaci tuwo dani miya ya sha. Ni ka zane a lagos daga na fadi abinda baiyi ma dadi ba. Rosie ta dan dake ta to banza rage muryarki. Ta maida kallonta ga Junaid ai kai karamin dan iska ne don giyar kudi ce ta kaika tashar iskanci mu kowa, ta nuna kanta da Tilly wahalar rayuwa ce ta kawo mu kaga dole mu fika rashin imani. Tsayawa yayi ya rasa yadda zaiyi dasu. Ya juya ya fita daga falon tare da buga kofa da karfi har sai da gaban Hafsi ya fadi.
Masu aiki ya tarar a barin nashi ya ma manta wai shara akeyi da sauran gyare gyare. Get out ya fada cikin karaji har su Nafisa suka fito daga ciki ita da Hamida. Sauri tayi ta dafa masa kafada Junaid what is wrong? Ban sani ba wannan karon hawaye yake sosai. Ku fita wallahi ko wani yaji ciwo. Ba shiri duk suka yi waje shi kuma ya shiga sabon bed room dinsa. Bai taba tunanin first day dinshi da Hafsi zai zo masa a haka ba. Tsakani da Allah yake sonta don a yadda ya tsara ma kansa ma bashi da niyyar takura mata. A hankali zai bita ya koya mata sonshi don yasan yanzu baya gabanta. Gashi yar tsiwarta da fadan da suke suna burge shi. Drawers ya rinka budewa kamar mahaukaci yana neman kayan maye ko yaya ya gusar masa da hankali ya manta da bacin ransa.
Wata taba dogowa ya dauko wacce Imran ya kawo masa tsaraba daga Italy. Kujera ya hau ya rufe idanunsa. Yana kunnawa yaji an fizge ta daga bakinsa yayi saurin bude ido. Hajiyan dangi ce tsaye kansa fuskarta jike da hawaye. Haba dan albarka. Yanzu ashe akwai wani maganin bakin cikin rayuwa bayan ambaton Allah da karatun Quran ko sallah? Ashe duk abinda ake fada maka bayan kunne yake bi. Bakin gado ta zauna dora kansa a kan cinyarta ya saki kukan da yake ta kokarin boyewa. Kyale shi tayi yayi mai isarsa har yayi shiru don kansa. Bai tashi daga kan cinyarsa ba yace Hajiya sai da nake son na canja halayyata kuma sai wannan masifar ta taso min? Kul ta ce masa tana girgiza masa kai. Allah sarki ne mai dinbin rahma da jinkai ga bayinSa. Shekararka nawa kana saba masa Yana hakuri da kai? Meye baka sha ba da aikin neman mata duk sai yanzu don Ya jarrabe ka kake neman kara fadawa ga halaka. Shin ka sani ma ko silar shiga aljanna ce wannan jarabawar? Dago kansa yayi yana kallonta. Hajiya wallahi yarinyar nan karuwa ce. Na rantse miki da Allah ita ta fara nema na a club. Abinda ta fada duk karya ne ya dan sunkuyar da kansa maganar cikin dai bazan karyata ba kila da gaske ne.
Kayi hakuri ka daure kaci jarabawar nan. To Hajiya zancen Hafsa fa? Ya zanyi da ita idan taki ni. Murmushi Hajiya tayi ,kasa Allah a ranka yarona komai zaizo da sauki. Hafsa tayi min yanayi da mutanen kirki idan ka nuna mata kai mutumin kirki ne sai kaga Allah Yasa ta zauna da kai lafiya.
TUN KAFIN AURE💐26
Neman Hafsi aka rinka yi a cikin gidan an rasa ina ta shiga. Mommy sai kuka take ko don taji zancen ciki ne ta gudu. Wata mai aiki mai suna Amaka ce ta tafi bakin gate ta tambayi securities din wurin ko sunga fitarta. Kusan awa biyu ana abu daya har Hajiyan dangi da Junaid suka shigo gidan don ta matsa masa akan yazo ya nemi gafarar iyayensa. Ganin gidan a hargitse Hajiya tace Salma me ya faru ne haka. Mommy cikin kuka tace bamu ga Hafsa ba Hajiya. Kinga har babansu ya fito nemanta.
Tunda akace Hafsi ake nema Junaid ya dena gane me ake fada. Na shiga uku Mommy ta gudu. Tilly da Rosie dake zaune a gefe ko a jikinsu. Ya nufo su cikin tsananin fushi ku sa a ranku indai banga matata ba wallahi kun gama ganin farinciki a duniya. Banzaye Matsiyata, karuwai….kafin ya kara magana Amaka mai girki ta fito daga dakinta da gudu. Madam amariya dey for my room. Bangaje ta Junaid yayi ya shige dakin. A daidai lokacin Senator ya fito yana waya da IG na police kan a baza masu nemanta. Me zai fadawa Mal Aminu? Duk kudinsa mutumin kwarjini yake masa sosai.
A kwance ya sameta kan gado tana ta rawar sanyi. Hafsi me ya faru ya fada yana shirin taba ta. Doke masa hannu tayi da kyar don wani zazzabi ne ya kamata sosai bayan tayi kuka mai isarta. Zuciyarta a cushe take da tsananin bakinciki. Badon abinda tayi ba tun kafin tayi aure tasan Allah bazai hadata aure da mazinaci ba.(don ma bata san yayi shaye shaye ba).
Ganin yadda ta hade fuska ga wasu hawayen sun taro a jajayen idanunta. Kasa ya sunkuyar da kansa kiyi hakuri Hafsi ki bari na taimaka miki ki tashi naga kamar ba kya jindadi. Harararsa tayi tayi tsaki a hankali zata mike. Ke ba kya gajiya da harare harare ne , wata rana sai na tsire miki ido. Duk da suna tare da damuwa da bacin rai amma sai da duk sukayi murmushi. Nafisa ce ta fara shigowa sannan su Mommy suka biyo baya. Hajiya tace mamana duk kin samu cikin damuwa tun dazu ana nemanki. Sai a lokacin suka kula da idanunta. Mommy ta zauna a bakin gadon. Kiyi hakuri yata nasan duk abinda zan fada zakiyi tunanin ko don bani na haifeki ba. Hafsi ta share hawaye ba haka bane mommy. Hamida tace wai ni me ya faru ne shi yazo yana mana fada dazu mun shigo kuma ance ana neman ta.
Babu wanda ya bata amsa. Mommy da kanta ta taimaka wa Hafsi ta tashi. Zazzabi ne a jikinki ko? A’a kaina ne kawai kuma zai dena idan nasha magani. Mommy tace ku zama shaida idan har yarinyar nan tace bazata zauna da Junaid ba sai an raba aurensu. Hajiyan dangi zancen bai mata dadi ba ta kama hannun danta. Muje Allah Ya kyauta.
Kwanaki uku bayan zuwan su Tilly jikin Hafsi ya warware sosai ga kulawar da take samu daga wurin iyayen Junaid. Hajiyan dangi taso komawa kano amma dole ta zauna har a shawo kan matsalar data kunno kai gidan. Su Nafisa kuwa kowacce ta koma gidan mijinta. Kirikiri aka hana Junaid ganin Hafsi gaba daya gidan ya masa zafi. Addua da yawan sallah yanzu kamar sabon limami don tsoronsa baya wuce a raba shi da Hafsi.
TUN KAFIN AURE💐27
Hajiyan dangi ce kadai ke shiga sabgar Junaid. Shiyasa kullum yana dakinta. Hafsi kuwa dakin da aka bata kusa da na Mommy ne ko fita bata yi. Ranar laraba tana zaune a daki duk shirun ya isheta ta fito zata dakin Hajiyan dangi don yau bata leko sun gaisa ba. A bakin bene suka hadu Hajiya tace ina zuwa mamana? Ta dan sunkuyar da kai, dama gaisheki zanzo yi. Tayi mata murmushi to bazan amsa gaisuwar a nan ba. Karasa dakin ina zuwa. Zanje wurin babanku ne muyi magana.
Ba musu ta karasa sauka. Sai dai kuma bata san ina ne dakin Hajiyar ba gashi ba damar ta koma sama ta tambaya. Wani corridor tabi tana tafiya sai ta jiyo maganganu daga dakin. Babu shakka wadannan matan ne ke maganar. Kamar ta wuce sai ta tsaya daf da kofar. Daga ciki ta jiyo daya daga cikinsu tana magana da fada fada…kai banza so nake kawai kayi karyar kaine babana. Ka sami wasu da zaku zame min iyaye. Wallahi babbar harka zan baro mana idan kuka yi kuskure kuma Allah kashimu ne zai bushe. Sai wata tace ke komai akayi dake sai kinyi hauka ki rage muryarki mana. Wannan karon sai da Hafsi ta hada kunnenta da kofar take jin me ake fada.
Bayan dayar ta gama wayar tace ni yanzu Rosie ya zanyi idan suka kaimu asibitin ayi min test. Gashi kece mai cikin bani ba.
Hasbunnallahu wa niimal wakil. Ashe karya suke babu wani ciki. Bata san dalili ba amma har ranta taji dadin wannan zancen. Rosie tace kada ki damu Tilly nasan yadda zamuyi da komai. Ke dai idan kika yi kokarin yaudarata idan kika shigo gidannan sai na koya miki hankali, itama wannan matsiyaciyar amaryar tasa sai nasan yadda nayi aka saketa ko ta nemi sakin da kanta. Ni bani maganin nan na kara sha naji cikina ya fara ciwo ciwo. Gara shegen yayi ya bare kowa ya huta. Tilly ta kalleta ki hakura ki haifeshi ni yanzu da ko shege ne ina so. Ai tunda likitan nan yace mahaifata ta lalace nake jin son haihuwa. Rosie ta tabe baki…wanan dai sai suck away in kin matsu kije gidan marayu.
A sanyaye Hafsi ta cigaba da tafiya. Wata mai aiki ta gani ta tambayeta dakin Hajiya ta nuna mata. Tana shiga ta tarar dashi zaune kan carfet yana shan wani abu a cup. Ganin tayi turus ita bata shigo ba ita bata fita ba yayi dan murmushi mai cike da bakin ciki. Hafsi Hafsi ko na fita ne don ki sami sakewa? Dan kwarin gwiwa da samu data tuna cikin ba nasa bane ta shigo. Ina kwana ta fada tana dan durkusawa. Ajiye kofin yayi yana kallonta cike da mamaki. Hala ta manta abinda ya faru a kwanakin da suka wuce. Kai fa ka fiye kallo kuma na fada maka babu kyau. To ranki ya dade na dena daga yau. Rufe idanunsa yayi ya dauki cup din kununsa ya cigaba da sha. Jin wani daddadan kamshi kusa dashi yasa ya bude idon. Hafsi ce zaune a kasa kusa dashi. Tayi yar ajiyar zuciya. Junaid, bata taba kiran sunansa ba sai yau shiyasa yaji wani dadi. Sai ya wayance. Ke mijin naki kike kira haka ba ko yar alkunya irin na matan hausawa. Komai bacin rai baya rabo da wasa. Kafin tayi magana yace kina hararata fa zan…sai ya kashe mata ido daya tsire miki ido zanyi. Ai kayi kama da mugaye dama. Ya mike tsaye ni din? Ashe baki da ta ido yar nan. Yadda ya rike haba yasa tayi dariya. Duk da yana tare da damuwa ya koyawa kansa hakuri. Har yana tsokanarta. Wani serious look ta gani a tare dashi. Yace Hafsi Hafsi why are u being nice to me? Ta dan kalle shi, saboda i believe you. Bangane ba ya fada cikin rashin fahimta. Bazan miki karya ba nasan Tilly kuma cikin jikinta maybe nawa ne. Na sani ta bashi amsa. Na dai yarda ba…ba raping dinta kayi ba. Tana gama magana ta mike zata gudu.
TUN KAFIN AURE💐28
Fizgo ta yayi har jikinsu yana haduwa da juna. Bata yi attempting ta gudu ba ta dai ki yarda su hada ido. Thank you kawai ya ce mata a daidai kunnenta a hankali ya fice daga dakin. Tunane tunane ta rinka yi barkatai game da feelings dinta akan mijin nata. Karshe dai ta tabbatar tausayinsa kawai take ji. Sai kuma ta koma tunanin yadda zata yi da su Tilly. Ita dai bazata je tace karya suke ba kanta tsaye don tsoronsu ma take ji. Dadin abin ma tunda suka kawo kansu gidan ai sun san abinda suka taka. Ita a wa taje ta karyata su ace garin yaya ta sani. Da kunya aji amarya tana labe.
Tana ta tufka da warawara ita kadai har Hajiyan dangi ta dawo. Bayan sun gaisa tace kiyi hakuri na barki aikin jira ko. Ba komai Hajiya. Flask din kunun ta kalla au ina Junaidu? A nan na barshi fa zai sha kunu. Ya sha ya fita inji Hafsi. Kan wata kujera ta zauna tace Hafsatu. Naam ta amsa. Kin sanar da iyayenki abinda ya faru kuwa? A tsorace ta dago ido. Wallahi ban fadawa kowa ba. A’ah kwantar da hankalinki ai tambayarki nayi. Munyi shawara da su Rufai ne yace zaije har kanon ya sami babanki ya sanar dashi. Domin idan akwai cikin nan dole mu tsaya yarinyar ta haihu mu karbi dan. Gashi ma dai ana tunanin gara suyi aure saboda gori a nan gaba. Ko kadan ba haka muka so ba amma bazamu yi wata barnar ba don mu boye wata. Idan har kinsan bazaki iya zama da Junaid ba a haka kada kiji kunyar sanar dani. Ta dan gyara zama. Nasan iyayenki ma bazasu taba yarda ba. Kuma bazanga laifinsu ba ko nice abinda zanyi kenan.
Duk maganganun da Hajiya take Hafsi ta gane so suke suji ko zata bukaci a raba aure. Ko kadan bata so iyayenta ma su san maganar. Ai idan auren ya mutu wani kashin kazar zata shafa wa kanta. Dama ummati ta fada mata a groups din whatsapp babu irin abinda baa fada a kansu. Da masu zagi da masu kiranta karuwa ma. Ai auren rufin asiri ne gareta sosai. Dan murmushi tayi cikin kunya tace Hajiya in sha Allah zan zauna.
Har ranta taji dadi kuma tayi mamakin saurin amincewar Hafsi. Allah Yayi miki albarka Ya baku rayuwa mai albarka duniya da lahira. Ta kama hannayen Hafsi ta rike. Mungode sosai kuma zan kara jan kunnensa aka neman lahira da gudun duniya. Har hawaye Hajiya tayi tace bari na tashi na sanar da su Salma don su kunyarki ma suke ji. Baki ga baban naku bai neme ki ba. Yace bai san yadda zaiyi ya kalleki bane.
Ranar da Hafsi ta cika sati su Nafisa suka zo gidan zasu yini. Hira suke sosai da Hafsi kamar sun dade da sanin juna. Suna nan zaune Junaid ya shigo dakin. Rabon da su hadu tun a dakin Hajiyan dangi. Wata doguwar riga ce fitted a jikinta kanta ba dankwali Nabilan Nafisa tana ta jagwalgwala mata kai wai zata mata kitso. Yana yin sallama tayi saurin sunkuyar da kanta. Sis ina ta nemanku ance min kunzo sai Amaka ce tace kuna nan. Hamida ta ce ai yanzu mu Hafsi ce yar uwarmu. Ka zama dan karo ko Yaya? Nafisa tace Hafsi baki gaishe shi ba. Kafin ta amsa yace kyaleta bashi take ci. Nabilatu na kice kike ja min kan mata haka ko? Ku kuma duk kun kyaleta sai ta tsige mata gashi. Dariya duk suka yi kaji mai mata donma kayi saa tana mata gyaran gashi. Yace nasan dai kara kike musu to baa yiwa dangin miji haka sai su raina ki. Filo nafisa ta jefa masa. Sannu kanwa uwar hadi tun yanzu zaka fara nuna hali. Ke Hamida dauko min ‘yata mu tafi kai kuma ka zauna ka gyara mata. Nabila sai ihu take da Hamida ta dauko ta…ni kichu kichu anti. Tanayi tana dukan Hamida.
Sai a lokacin tayi magana. Don Allah Hamida ku kyaleta. Ganin basu saurareta ba ta dauki hijab dinta zata bisu. Kafin ta gama sun fice harda rufo kofa.
Suna fita harda tafawa. Bawan Allah Ya Junaid duk ya zama abin tausayi. Kiri kiri anki kai masa matarsa gidansa. Nafisa tace nasan fushi su Mommy suka yi amma ai zasu bari ta koma. Ko ba komai yanzu da kudi Junaid bazai kara bin wasu matan ba a waje. Abinda ya wuce kuma Allah Ya yafe mana baki daya. Amin Ya Allah.
TUN KAFIN AURE💐29
Hannun kofar ta kama amma saboda yadda take hanzarin fita sai ta kasa budewa. Hijab din ma saboda karar jan kofar da Nafisa tayi a baibai ta saka shi. Duk abinda take idanunta na kansa don tsoro take kada ya karaso inda take. Wani irin kallo ya rinka yi mata ko kifta ido baya son yi. A hankali taga yana matsowa inda take. Cikinta har wani sauti yake bayarwa saboda yadda ta kideme. Da kyar ta iya cewa nifa bana son kallo. Bai dakata ba da tafiyar sai da yazo gabanta. Da zaa taba kirjinta sai anji bugun zuciyarta da sauri da sauri. hannunta ya kama ya jawota ciki ya zaunar da ita kan kujerar gaban dressing mirror. Ji yadda jikinki ke bari kamar kinga wani dodo ko irin kinzo yi min sata na kama ki. Yadda yake maganar ne ya sata dan guntun murmushin yake. Shiru tayi tana tsoron kada Hajiya ko Mommy wani cikinsu ya shigo dakin tunda suna shigowar kullum. Ganin yana neman cire mata hijab ta fara kokawar rikewa. Ya kalleta ya sha kunu wai ni da jikina ki rinka rufe min. sai anyi magana ki rinka wani abu kamar wata malama. Ta zumburo masa baki, to yanzu me kake so ayi. Da faraarsa yace ki cire na gyara miki gashinki ko baki ji me Sis ta fada ba. Tayi masa fari da ido ai da ka sani salon ka bude sai ka rinka gyaran gashi. Gaba daya ta ruda shi da yadda tayi masa fari da ido har ya kasa magana. Tana ta surutu ita daya sai gani tayi yana kici kicin cire mata hijab. Ihu ta fara masa wallahi idan ka matso zan bude murya. Ganin duk a tsorace take yayi dariya duk wanda ya shigo taimakonki sai ya tayani cire miki hijab din, bari ma na kulle kofar kinsan leke dakin newly weds hatsari ne. Yana zuwa bakin kofar duk cikinta ya gama durar ruwa sai kawai taga zai fita daga dakin…take care Hafsi Hafsi. Murmushi ta sami kanta da yi bayan ya kulle kofar ta fada gado ta kwanta.
Hajiyan dangi suka gani a dakin Mommy suna ta hira. Suna zama Mommy tace dama jira nake ki fito Nafisa. Lafiya dai ko Mommy? Ta tambayeta. Eh to wannan makociyar taki nurse nake son ki kira tazo gida tayiwa yarinyar can test a tabbatar da cikin. Hamida tace Mommy ana yin scanning fa dashi ake fadar EDD. Nafisa ta buge mata baki to banza wa ya fada miki we are intrested muji lokacin haihuwar. Hajiya tace kunga ni ku nutsu idan kinje gida ki fada mata ko zuwa gobe ne sai kuzo tare. Amma abinda Hamida ta fada gaskiya ne. Idan anyi mata gwajin sai ayi scaning din. Nafisa ta mike bari naje na fada musu don su zauna cikin shiri.
Hafsi tana fitowa zata dakin Mommy ta ga Nafisa tana dawowa daga dakinsu Tilly. Hannunta Nafisa taja suka shiga wani karamin falo. Suna zama Nafisa ta ce Hafsi what do you think of Junaid? Kasa ta sunkuyar da kanta. Tana jin nauyin Nafisa sosai don ma ita din tana da wayewa ta iya jan mutane a jiki. Ta dan taba ma Hafsi kafada ina jinki kanwata. Jin ta sake yin shiru tace nasan Junaid ya taba rayuwa mara kyau irin ta ‘ya’yan masu kudi marasa kwaba amma duk irin halayensa he is not a rapist. Kuma a irin ji da kansa na da fa banda yanzu, bazai kula mai kati ba. Ko da wasa bamuyi tunanin zaiyi aure ba nan kusa amma sai gashi yana ganinki ya canja sosai. Banda degree yana da masters har biyu amma yaki aiki sai kashe kudi. Sai gashi jiya Alhajinmu yace yayi masa maganar yana son fara aiki. Hannayen Hafsi ta kama ki daure ki zauna dashi don Allah na tabbatar he will be a better person. Ganin Nafisa na hawaye Hafsi ta suma kuka itama. Cikin kukan ta fadawa Nafisa abinda taji daga dakinsu Tilly. Murnar Nafisa har zuci tace kada ki fadawa kowa da sannu asirinsu zai tonu. Scanning zan kaita shegiya gayyar tsiya. Har suna da guts din shigowa gidan nan. daga nan suka zauna suna tattauna yadda zasuyi karshe Nafisa tace idan kin amince zanyi magana a kaiki wurin mijinki. Dammmm zuciyarta tayi don tsoro.
TUN KAFIN AURE💐30
Washegari gari da safe Nafisa tazo da Mariya nurse. Ita tayi musu jagora zuwa dakin su Tilly. Senator Rufai tun da suka zo gidan zama ya gagare shi ko kadan baya kaunar haduwa dasu gashi bazai iya korarsu ba har sai sunga yadda al’amarin zai kasance.
Tun daren dama Tilly ta gama tsorata Rosie tace ki kwantar da hankalinki nifa abu irin wannan baya tsorata ni. Zamu sami mafita cikin ruwan sanyi. Ko da su Nafisa suka shiga dakin a kwance suka tarar da Tilly , Rosie tana rirriketa tana ta amai. Laulayi dai kamar gaske. Nafisa ta kawar da kai gefe dama bata sanar da Mariya ainihin alaqarsu ba. Ita ko sunansu ma bata sani ba. Ta yi mata kallon banza ki tashi za’ayi miki test. Rosie ta yi kalar tausayi to bari na taimaka mata ta gyara jikinta. Mariya tace ai fitsari kawai nake bukata ma idan kun shiga ga wannan robar ta mika mata irin sample bottle din asibiti sai ku kawo min a ciki. Kadan ma ya isa. Nafisa tace kiyi mata na jini kawai ance yafi nunawa. Nan da nan suka hada ido a tsorace. Tilly ta fara hawaye don Allah kuyi hakuri bana son allura. Nafisa tace ke da zaki haihu meye abin tsoro a allura. Mariya tace ki bari kawai muyi na fitsarin idan bai zama clear ba sai na debi jinin. Rosie ce ta kamata tana tafiya a hankali har suka shiga toilet suka rufo kofar. Tilly ta gyara jikinta tana tsaki ta sassauta murya kinji waccan yarinyar wai blood test? Idan ta shiga hurumi na bazan mata ta dadi ba. Rosie ta rufe mata baki sai an ji mu. Ungo ni ta mika mata robar data cika taf da fitsari. Kamar ta rike kashi haka Tilly ta karba ta fito ta ajiye a gaban Mariya.
Duk suna kallo ta saka PT strip din a cikin robar ta fito dashi ya nuna layi biyu alamun ciki. Mariya tace ai kinga ma Nafisa ya nuna basai munyi na jinin ba. Nafisa a ranta tayi kwafa dama tunda suka shiga toilet tare tasan akwai abinda zasuyi. Ta kalleta harda dan guntun murmushi sannu Allah Ya raba lafiya. Yanzu gobe zan kaiki asibitin da nake zuwa sai ayi miki ultrasound gara mu gani kila ma biyu ne babies din. Nafisa dai dariyar da take harda ta mugunta suka fice ita da nurse.
Suna rufo kofar Tilly tace na shiga uku ya zanyi ne Rosie gobe asirina zai tuno. Kwantar da hankalinki kamar tsumma a cikin randa. Wannan yar kwailar matar tasa zamu kullawa. Idan zai aureki ai gara ki zauna ba kishiya muci karenmu ba babbaka Talatu. Suka tafa sannan tace akwai dan taimako daga wurin malam fa sunansa makalemata. Idan lokaci yayi zan baki ki yi amfani dashi.
TUN KAFIN AURE💐31
Senator Rufai ranshi duk a bace da aka sanar dashi result din test din. Ya kalli Hajiya ni yanzu ya zanyi da Hafsatu? Duk irin abinda ya faru kafin a bashi aurenta gashi kuma baaje ko ina ba rayuwarsa ta baya tun kafin yayi aure tana dawo musu. Hajiya tace ni dai idan zaka dauki shawarata Rufai kabari yarinyar nan ta tare. Kullum mu kwana mu tashi da ita bata san makomar aurenta ba ai kaga ba dadi. Irin wannan ne idan iyayenta suka sani lamarin sai ya baci fiye da yanzu. Mommy tace anya Hajiya a bar shi da yar mutane kuwa? Bafa kowacce mace bace zata yarda ta zauna da mutumin da yake da da a waje ba. Wata ko dan kishiya bata so bare dan kafin fatiha. Senator yace to ku bani zuwa wata asabar din sai a kaita. Kisa su Hamida su tambayeta irin kalar motar da take so ma. Mtsw Ya danyi tsaki yaron nan bai min adalci ba wallahi. Gara tun da sauran mutumci na naje har gida muyi magana da babanta.
Zaman dakin duk ya isheta tana ta canja tashoshi babu wani abin kallo ta mike ta daga labule tana kallon waje. Tun jiya da su Nafisa suka zo da nurse bata sake fita daga dakin ba, Nafisa dai ta fada mata zasu dawo ta kai Talatu scanning. Tun dazu take jiran zuwansu ko ta sami abokin hira. Su mommy suna iya kokarinsu wurin debe mata kewa sai dai kuma suna cikin damuwar maganar cikin nan. Tana dan tunaninta ne ta kalli kasa suka hada ido da Junaid. Wani abu ne ya ratsa mata zuciya har kafarta. Murmushi yayi mata tayi saurin sakin labulen. Ta koma ta zauna bakin gado. Meyasa take saurin rikicewa ne akan Junaid..abinda take tambayar zuciyarta kenan.
Meyasa zata masa rowar kyakkyawar fuskarta ne. Su Hajiya suna masa gashin kuma gashi yanzu yana cikin jindadin kallonta ta gudu. Girman laifinsa yasa ya danne zuciyarsa bai dami iyayen nasa akan a bashi matarsa ba. Itama yana jin nauyinta sosai a ransa. Ina amfanin badi ba rai? Karamar yarinya tana masa kwarjini saboda ya zubar da girmansa a waje. Ga su Rosie sunyi kane kane a gidansu. Fasa shiga gidan nasa yayi ya koma main house. Mai aikatan gidan suna ta gaishe shi ya haye sama da sauri. Addua yake kada kowa ya ganshi a hanyarsa ta zuwa dakin Hafsi.
Rub da ciki tayi tana karanta wani littafin tarihin Annabawa da Hajiya ta bata taji an bude kofar. Duk a zatonta Nafisa ce tayi saurin juyuwa babbar yaya ina ta jiranki tun dazu yau bani da….kallon da yake mata bayan ta juyu yasa tayi shiru. Ya zaka shigo min ba sallama? Ni da dakin matata har sai nayi sallama? Ya kara kallonta ita duk kayan jikinta suna mata kyau. Dinkin yau ma riga da skirt ne fitted sunyi mata kyau sosai abinka da yar Mama tela. Ya jawo kujerar dressing mirror banda gulma duk wannan kwalliyar kice babbar yaya kike jira? Fada min gaskiya dai ni kika yiwa wannan kwalliyar ko. Bargo ta jawo ta rufe jikinta da sauri ni ba kai nayiwa ba. Kan gadon ya dawo ya zauna a gefenta ya rage murya are you sure? Har fa zuwa kika yi bakin window don na ganki kuma na gani. Daga cikin bargon tace ni Allah ba kai nayiwa ba. Ji tayi kamar ya tashi daga kan gadon sai dai kuma har fuskarta ta rufe yace malaiku na jinki kina cewa yar miji kika yiwa kwalliya ba shi ba. Yau littafinki sai cika da rubutu amma fa daga na hagun. Muryar nan ta shagwaba ta fara yi ni ba haka nake nufi ba…kafin ta karasa magana taji ya daga bargon daga wurin kafafunta ya shigo ciki. Hannuwansa yasa ya danne duka sides din don kada ta bude. Tuni idanunta suka raina fata, they were so close suna shakar numfashin juna. Ya kashe mata ido daya ina jinki wa ma kika yiwa wannan kwalliyar? Ki fadi abinda nake son ji sai na fita salin alin. Kanta a kasa tace kai. Malama ni banji ba fa. Ta sake cewa kai a hankali. Bari na sake matsowa kusa kila zanfi ji. Da karfi tace kai nayiwa. Good girl to ki dan bani chance mana na yaba kwalliyar. Bata ankara ba taji ya janyota ya rungume. Yana shafa mata gashi a hankali. Wata ajiyar zuciya yayi Hafsi Hafsi ki tayani addua yau nayi interview har biyu ta neman aiki. Nasan nayi laifi da yawa shiyasa su Mommy basu da time dina amma don Allah zaki zama friend dina kuma special adviser dina. Dago kanta tayi tayi masa murmushi eh. Thank you so much. Ya mike yau zaki min girki? Ban iya ba ta bashi amsa. Au kin manta da malaikun ne? Itama mikewar tayi na iya, me zaka ci? Kallonta ya sake yi gaskiya kayan nan naki fa suna…kodayake ba komai ki dai rufe jikinki kafin kije kitchen din. Indomie da kwai nake so ina sonta sosai. Idan kin gama ki kirani. Wayarta ya dauka yasa mata number dinsa. Duk ta tsufa anma dena yayin irinta. Itama Gwaggo Zainab ce ta siyo mata irin second hand dinnan. Ki taho dashi daki zanzo na karba. To kawai tace ya fita. Tayi tsaki meyasa idan taga Junaid take zama wata wawiya ne. Ko dan jan ajinma sai ya nemi ya gagareta.
Kasa ta sauka babu kowa sai masu aiki ta dafa masa indomie biyu da daffafen kwai biyu. Tana shiga kitchen Rosie ta hangota ta koma daki da sauri ke Tilly tashi mu jirata a hanya. Akan tray ta dora zata fito wata mai aiki tace madam bari na kai miki Hafsi tayi dariya ai ba nauyi Chinwe nagode. Tana tafiya kamar daga sama Tilly tazo ta bangaje abincin ya zube a kasa plate din ya fashe kawai sai ji tayi Tilly na ihu wayyo Allah cikina.
TUN KAFIN AURE💐32
Wani irin radadi ne ya ziyarci kafafunta duka biyun ta runtse ido ko motsi ta kasa yi saboda duk wurin pieces din glass ne. Tilly kuwa kwanciya tayi wanwar a kasa tana kwarma wayyo cikina, wayyo ta kashe min da na shiga uku. Rosie tace kiyi hakuri Talatu ki mike tsaye. Hafsi ta kallesu tana cewa sannu amma duk kafafunta sun kone saboda zafin abincin harda cikinta don karamin mayafi ta yafa sanin cewa babu ma aikata maza da ake bari su shigo cikin gidan. Ga plate din da ya tarwatse wasu duk sun soke mata saman kafafunta. Duk da haka bata damu ba ta duka tana son taya Rosie ta daga Tilly tsaye. Hannunta taji Tilly ta make tana kara sautin murya. Muguwa azzaluma don kawai ina da cikin mijinki shine kike son zubar min dashi. Wallahi duk abinda ya sami dana kotu ce zata raba mu. talakar banza.
Wawan mari Talatu taji an dauketa dashi. Mommy ta sake daga hannu Hajiya ta riketa yi hakuri Salma muji abinda ya hadasu. Rosie cikin kukan makirci tace Talatu ce ta fito zata sha iska tace dakin yana tayar mata da zuciya. Tana fitowa wannan yarinyar ta nuna Hafsi, mommy kuwa ta make hannun karki sake nuna min yarinya da yatsa wallahi. Rosie ta share ta cigaba da magana kawai tana ganin Talatu sai tace mata zanga yadda zaki haifi dan shege a gidannan. Tray din da plates din da ke kai duk ta tura mata a ciki. Hajiya ko kadan bata gaskata zancen ba ganin yadda Hafsi ke kuka tace mamana me ya faru. Hafsi ta fadi iya abinda ta sani. Mommy ta kama hannunta su koma falo ayi maganar.
Sai a lokacin suka kula da yadda jini ke bin kafar Hafsi ta dama Mommy tace maza a kira mata Junaid yazo ya kaita asibiti.
Da fara’arsa ya shigo falon. Mommy daga nasa yarki dafa min indomie sai ace in kaita asibiti. Ko ta kitse albarka. Gunjin kukan Tilly yaji daga bayansa ya juya da sauri lafiya? Rosie hade rai ka tambayi matarka da take son zubar wa Talatu da ciki. Yace au ashe sunanta Talatu ai na zata Tilly ne. Muryar Mommy yaji tana kiransa. Ya zan aika a kira ka sai kazo kana wani zancen daban. Ka dauko key mukai yarinyar nan asibiti nace. Ya kalle Hafsi duk fuskarta hawaye yayi saurin karasawa gabanta. Me ya faru Hafsi garin yaya kika ji jiwo? Mommy tace ka tashi mana ka zauna kana mata tambayoyi.
Suna shiga motar Nafisa na isowa Hajiya tace ta debo su Rosie su taho tare. Amma ta taho da security don kada su zama su kadai. A motar Junaid kuwa Mommy tana ta balai ya dauko musu masifa har gida. In Allah Ya yarda sai cikin ya zube. Ga Hafsi nan ki saki jiki kiyi ta zuba masa ‘ya’ya tunda su yake so. Hajiyan dangi ta gama waya da senator ta sanar dashi halin da ake ciki sannan ta dubi mommy tana bata hakuri. Junaid kuwa banda sannu babu abinda yake fadawa Hafsi. Hawaye ne wani ke bin wani a idanunta don ita kadai tasan me take ji musamman a cikinta. Ga babban mayafi ta yafa wani karin zafin a cikin.
Suna isa asibiti Junaid daukarta yayi don ganin yadda kafar taki dena jini. Emergency aka shige da ita da Tilly. Kururuwa kawai Tilly take yi ita tasan danta ya mutu. Ai kuwa basu dade ba nurse ta fito tace Tilly tayi bari. Nafisa ta rike baki cike da mamaki wato don sunji yau zaayi scanning suka bullo da wannan abin. Dariya tayi tana gyada kai sai tayi maganin mutanen nan.
Junaid yana tsaye doctor ya zare glass dinda ya shige kafar Hafsi yana ta mata sannu. Bayan an gama cirewa ansa plaster ya lura ta kasa kwanciya da kyau yace Hafsi akwai inda yake miki ciwo bayan kafar ne? A hankali ta daga kanta tace cikina. Fatar ta daye. WHAT??? Shima ya gama tsorata yayi saurin cire mayafin ya nunawa doctor din. Da almakashi ya yanke barin rigar daya kwanta akan cikin yace yi hakuri fatar bata cire ba. Ya dauko magani zai saka mata Junaid ya karba don tuni ya kule da kallon da yake mata. Dr bai ma san me yake ba ya nuna masa yadda zai shafa ya fita.
Ba karamin tausayi ta bashi ba yana shafawa tana runtse ido duk hawaye. Sai da ya gama ya duka yana hura mata cikin tuni ta hadiye kukan. Ya dago kansa sannu kinji Hafsi rabin raina. Ashe tsautsayi ne yasa nasa ki girki. Amma me ya hadaki da waccan. Fada masa komai tayi yace ba komai. Allah Yayi mana jagora.
Dr Sunusi yana fita Nafisa ta ja shi suka yi magana tace dr ina jin yarinyar nan cikin karya gareta. Yace ya akayi kika sani tace yar uwarmuce ce daga garinmu ina jin karya take ta matsu ne ta haihu sai tayi ta kiran cikin karya gashi kwanaki tayi bari baa wanke cikin ba. So nake don Allah kayi mata wankin ciki zan biya ko nawa ne. Bani da burin da ya wuce Talatu ta sami haihuwa. Ta dan matse hawaye. Dr Sunusi yace ba komai Hajiya ki kwantar da hankalinki. Yana fita Nafisa tace shegiya ai karen bana shike maganin zomon bana.
TUN KAFIN AURE💐 33
Tana kwance suna hira cikin nishadi nurse din ta dawo. To angama komai ina kudina? Rosie ta dauko dubu ashirin a jakar Tilly ta mika mata. Ki dai tabbatar babu wani cikin wadanda suka kawo mu babu wanda ya shigo. Nurse Talle ta washe baki tana murna ta ce angama ranki ya dade. Bata dade da fita ba Dr Sunusi ya shigo dakin tare da wata nurse din. File ya bude yana dubawa, ya dan dago kai kece Talatu Jibo ko? Eh ta amsa da kyar tana ta rike ciki ita a dole mara lafiya. Yanzu likita na rasa baby na kenan? Kiyi hakuri mana ki dena kukan Rosie ta fada tana rarrashinta. Dr yace ya naga kina rike ciki ne ko bai gama fita bane? Saurin sakin cikin tayi ya fita duka ni dai ku sallameni kawai na tafi. Ya kalli nurse din kinga ki gyara min dakin can zanyi mata wankin ciki, ya maida kallonsa ga su Tilly. Ai kada ki damu idan nayi miki wankin cikin before you know it zaki sami wani. Yadda kike rike cikin nasan akwai saura. Wannan karon kukan gaske ta saka masa kayiwa Allah likita kada kayi min wallahi cikin baya ciwo ko kadan. Yace ai dalilin wankin kenan idan akayi bari ba ciwo nan ma akwai serious problem. Tana kuka yace a kawo wheelchair a kaita dakin da zai mata a can.
Kankame Rosie tayi bazata tafi ba. Rosie tace kiyi hakuri Tilly kada asirinmu ya tuno. Saboda tsabar kwadayin daya kawo su Tilly tana ji tana gani akayi mata D and C. Likita dai yasha zagi ta uwa ta uba.
Sai dare aka sallamosu duka a gidan suka hadu da Hamida suna jiransu da Senator. Ko daki basu shiga ba Rosie tace yallabai munyi waya da kawu na baban Talatu yace gobe zaizo gari don na fada masa abinda ya faru. Anyi mata fyade kuma anyi sanadin zubar da cikin. Wallahi maganar nan har yan jarida sai na fadawa. Kowa kallonta kawai yake tana rashin kunya Senator ya hanasu magana a cewarsa dansa ne ya ja masa. Tana gamawa yace idan sunzo goben zaa daura musu aure da Junaid. Yana gama magana ya juya zai haye sama zuciyarsa na kona saboda bacin rai. Ta sake cewa ita kuma wadda ta zubar da cikin idan zaayi adalci sai a saketa ko a dau mataki. Hamida tace uban kuturu kuma yayi kadan in fada miki. Hafsi mutu ka raba da Junaid. Hajiya tace ku wuce ku tafi gidajenku Allah Ya bamu alkhairi.
Junaid da Hafsi basu san abinda ke faruwa ba saboda ya wuce pharmacy da ita neman wani magani. Ac ya ware mata ya ja mayafinta can baya yadda cikin zaisha iska. Motar ko radio bai kunna ba yana ta kallon yadda Hafsi take ta zumbure zumbure. Yasan itama laifinsa take gani ya jawo musu masifa har gida an rasa yadda zaayi dasu saboda gudun abinda zaije ya dawo tunda babansa dan siyasa ne. Tarkace da yawa ya siyo mata na kwadayi bayan ya siyo maganin. Ganin bata da niyar kula shi yace Hafsi Hafsi kiyi hakuri akan abinda ya faru. Bansan dalilinta nayi miki sharri ba amma zanyi maganin abin. Tsautsayi ne ya kaini ga saninta amma kisa a ranki wallahi bazan aureta ba don nasan ko wacece Tilly. Cikin takaici yake maganar Hafsi tayi biris dashi. Ba komai ke damunta ba face yadda aka kasa gano karyarsu kuma ita bata da wani shaida akan abinda taji. Tasan Nafisa ta yarda da ita amma idan basuyi wani abun ba suna kallo Senator zai sa Junaid ya auri wannan matar. Wai ma ya akayi suka yarda bari tayi ne? Ko dai da cikin gasken? Ita ta gama zama confused. Har ta fara kokonto akan abinda kunnenta ya jiye mata
TUN KAFIN AURE💐34
Yadda tayi zurfi a tunani yasa Junaid kare mata kallo. Wayarta ce ta hau tsitsi shi ya dawo da ita daga dogon tunaninta. Da sauri ta dauka ganin baffanta ne. Tana masa sallama yace Hafsa ya jikin? Dazu babanku yayi min waya kinji ciwo. Ince ko babu wani mugun rauni..dariya tayi ashe kana sona dai Baffa. Yayi dan gyaran murya kaniyarki wasa nake dake ne. Ta sake wata dariyar baffa babu ciwo sosai glass ne ya shige min kafa amma an cire. To sannu Allah Ya kara sauki, amma ki rinka kula kinji ko. Ga Mamanki duk ta damu itama. Sun dade suna hira da mama da kannenta kowa yana mata sannu. Bayan ta gama wayar yace yanzu tun dazu ina magana kina share ni sai da kika ji muryar su baffa kika yi dariya ko. Yadan bata fuska kamar zaiyi kuka Allah Sarki Junaid babu mai sonka. Har tissue yasa yana goge ido , bata san lokacin da dariya ta kubuce mata ba. Wayarta ya dauka yana juyawa. Ni na gaji da ganin wannan toy din. Idan munje gida kizo ki karbi sabuwar dana siya miki. I hope you will like it.
Bayan yayi parking din motar Hafsi ta bude zata fito yace tsaya ina zuwa. Zagayowa yayi ga mamakinta sai kawai taji ya dauketa. Yau karo na uku kenan yana daukarta. Tana ta mutsu mutsu ya ajiyeta kada wani ya gansu ya share. Da kafa ya tura kofar motar bai tsaya ko ina ba sai a side dinsu dake bayan gidan. Ajiyeta yayi ya bude kofar ya sake daukanta, kan doguwar kujerar falo yasauke ta ya duka hannunwansa duka biyu a gwiwoyinsa yana ta nishi. Wai Hafsi haka kike da nauyi…anya baki kai buhun shinkafa biyu ba kuwa. Filon kan kujerar ta jefa masa wallahi bani da nauyi. Kuma ma ai bance ka daukeni ba. Ya sami wuri kusa da ita ya zauna tare da janyota jikinsa. Gaskiya yarinyar nan idan kika hau kaina buzu na zaa dauka. Mintsini yaji a gefen cikinsa tace ya fa isheka ko don kaji ina shiru. Ya kama gefen cikin ke dama haka kike? Don kin kone a ciki nima nakasa ni zakiyi. Ya danyi murmushi me kama da na mugunta kinsan fatar cikinki zata fi dadin mintsini ko. Tana jin haka tayi saurin tashi sai ta fada jikinsa saboda zafin da kafarta tayi. Rungumeta yayi sosai hmmm su Hafsi wayon ki dan ji dumin jikina shine kika wani fado min a jiki. Maganar da tayi niyar yi ce ta makale mata saboda kunya data kama ta. Zata bashi hakuri taji ya hade bakinsu wuri daya. Cikin kankanin lokaci suka tafi wata duniyar sai dai basu dade ba suka ji bugu a bakin kofa tare da sallamar Hamida cikin daga murya.
Tsaki yayi ya amsa mata tare da mikewa. Tace Yaya munji shigowar motarka amma har yanzu Hafsi bata shigo gida ba. Wani tsakin yayi gata nan zuwa kill joy sim dinta zan saka a sabuwar waya. Hafsi dai gintse dariya tayi don yadda taga yana bin Hamida da harara bayan ta rikota zata taimaka mata su koma cikin gida.
TUN KAFIN AURE💐35
Washegari wayar Junaid ce ta tasheta daga bacci da asuba. Ko da ta dau wayar sai taga an rubuta J dear. Lallaima wato har wani saving sunansa yayi a haka. Ta daga cikin muryar bacci tace waye ne waya da asussuba kamar me karbar bashi. Murmushi yayi yana shafa kansa ai zaki biya bashi ne Hafsi Hafsi amma not now. Yanzu dai ya kika kwana? Ya jikin? Da sauki ta ams itama murmushin take. Wani son Junaid takeji yana ratsa ta. Amma babu yadda zatayi yanzu sai sun kawar da su Talatu daga gidan.
Karfe 9 na safe aka sanar da su Mommy zuwan baban Talatu Mal Jibo da kannensa biyu. Senator ta tayar daga baccin da sai bayan asuba ya sami runtsawa saboda tunani. Doguwar riga ya saka ya mike. Ki aika a kira min Junaid tun jiya ban sanar dashi maganar auren ba saboda kada ya daga min hankali. Shi ya jawo matsalar nan so he has to deal with it. Mommy tace amma yallabai baka ganin kara dulmiya shi zamuyi kaga baya sonta kuma basu da kamanin mutumci. Hannu ya daga ya dakatar da ita…haba Salma duk shi baiyi tunanin haka ba sanda yake bin duk macen da ya gani. Ai duk rayuwar da mutum yayi kafin aure indai ba Allah Ya kare ba sai kiga tana bibiyarsa. Ko kadan ita dai abin baiyi mata dadi ba amma dole tayiwa mijinta biyayya. Haka suka sauka kasa ya fita wani falo ya tarar dasu a zaune sun kusa cinye duk abinda aka kawo musu na tarar baki. Bayan doguwar muhawara Senator Rufai wanda rashin son tonon asiri yasa babu wanda ya iya sanarwa halin da ake ciki cikin abokansa da yan uwa ya tsayar da magana akan zaa daura auren Junaid da Talatu nan da sati biyu. Mal Jibon karya yace ranka ya dade ni dai gara a daura auren nan asabar mai zuwa saboda kada ya lallaba ya sake banka mata wani cikin. Wata irin tsawa Senator Rufai ya daka masa ya mike tsaye…kada ka dauki saukin kaina a matsayin shashanci mana. Ina binku ne a hankali kawai don in tayaku sayawa yarku mutumci. Idan kuka shige gonar da ba taku ba wallahi ina da karfin da zansa duk a neme ku a rasa. Duk abinda nake yi saboda girman Allah nake yi so be careful , be very careful. Yana gama magana ya fita Tanimu yace kai baaba kaji yadda hantar cikina ke kadawa kuwa. Baaba yace ai sai da nayi dana sanin magana ma. Wallahi idan Rosie bata biyamu da kyau ba jikinta ne zai fada mata. Kaga yadda yake muzurai kuwa. GG dake gefe yace ai ni na fiku tsurewa yadda yace zai batar damu gani nake kamar ya gama gane mu ma.
Baffa ya dauki wayarsa dake faman ringing tun yana sallar walha ya duba sai yaya sirikinsa ne. Bayan sun gama gaisawa Senator ya labarta masa dukkan abinda ke faruwa a gidan nasa. Mal Aminu dai yau ya rasa bakin magana saboda takaici yanzu irin gidan da Hafsan sa ta tare kenan. Senator ya cigaba da bashi hakuri da neman shawara. Mal Aminu duk yadda ransa ke kuna yace dole ayi abinda ya dace don a rufa asiri kuma shi yanzu kullum Junaid yana kiransa kuma ya yarda da irin shiryuwar da yake ji tare dashi. Haka suka yi ta shawara Senator yace idan ba damuwa ko zaku iya zuwa zuwa Jumaa kai da Alh Bashir saboda bani da wanda zan iya tonawa sirrina. Lallai rayuwa babu yadda bata zuwa ga bawa. Allah Ya kara rufa mana asiri. Daga nan Senator ya nemi dansa ya sanar dashi shawarar daya yanke. Junaid mikewa yayi cikin rudani yana daga murya…wallahi wallahi Alhaji bazan auri Tilly ba, karuwa ce fa.
TUN KAFIN AURE💐 36
Senator Rufai yace Allah Yasa magajiya ce sai ka aureta. Yau kaine kake kiran wata karuwa? Ka manta irin kukan da mahaifiyarka ta rinka yi lokacin da kake bibiyar matan banza. Yau gashi a sanadiyar hakan Junaid wasu yan iska suna neman bata min suna. Duk rayuwar da nayi a politics ina taka tsantsan saboda abokan gaba. Hajiyan dangi dake zaune a gefe ta dago kai cikin fushi lallai ma Rufai ashe duk abinda kake ba saboda lahirar mu kake yi ba. Dama saboda mutumcin siyasa kake yi. To wallahi ka sa a ranka duk abinda ya sameka kai ka jawo tunda babu abinda kake don Allah. Mommy dai kuka take don abin yayi mata yawa. Hajiya tace Junaidu? Ya amsa mata cikin kuka. Ina so kayi wa babanka biyayya hakan shine shaidar ka shiryu. Kuma da yardar Allah zaka ci jarabawar da Yake yi maka. Tashi ka tafi Allah Yayi maka albarka. Yana fita mommy ta hau rokon a janye maganar aure. Yace kun kasa fahimta ta ne Hajiya. Nasan ina son kare mutumci na amma ki duba ki gani indai yayi mata cikin da gaske kada su sami abin tozarta shi nan gaba. Bani da burin da ya wuce naga iyalina suna zaune cikin kwanciyar hankali amma hakan bazai taba yiwuwa ba sai mun toshe duk wata kofar da wani zai iya samun damar daga mana hankali. Senator yayi iya kokarinsa wurin ganin iyalinsa sun amince da auren don a iya tunaninsa da haka ne kawai zaa iya toshe bakin su Talatu.
Kamar wanda aka jefo daga sama kawai ganinsa tayi a cikin dakinta. Yar tsiwar data yi niyar yi masa saboda ya shigo mata daki ba sallama ma kasawa tayi saboda wata irin runguma da yayi mata. Cikinta ne ya soma zafin wurin da ta kone ta fara neman ya sake ta. A kunnenta taji yana magana cikin muryar kuka har hawayensa na sauka a kafadarta. Hafsi please dont ever leave me. Dole ta hakura ta tsaya har ya gaji don kansa sannan ya ja hannunta suka zauna a bakin gado. Kansa ya dora kan cinyarta sannan ya fara magana. Alhajinmu yace lallai sai na auri Tilly. Dama tasan haka zata iya faruwa sai dai tayi shiru ganin kamar bai gama magana ba. Na fada masa karya tayi min amma yaki yarda. Hafsi ke kadai kin isheni rayuwa ina tsoron hadaki da kwararriyar yar bariki. You are too innocent bazaki iya kishi da ita ba. Gashin kansa ta shafa indai Alhaji ne ya baka umarni to don Allah kayi masa biyayya. Kada ka manta aljannarka tana tare da farin cikin iyayenka a kanka. Tana gama magana yaga ta share kwalla yayi tashi zaune kingani ko tun yanzu kin fara kuka. Sai kuma ya kashe mata ido ko dai kishi ne ya motsa. Kyakkyawan rankwashi ta sakar masa ya dafe kai yarinya baki sanni ba ko. Sai a lokacin ya kula ashe daga ita sai wani towel iya gwiwa. Yayi wata dariya yau zaki gane nima mugu ne. Towel din ya kama daga daidai kirjinta yana ja tana ja. Muryarta na rawa tace zan maka ihu fa? Ai idan kika ji mace tana zanyi ihu ba yin zata yi ba. Besides ba zaki so a shigo a ganki a haka ba. To naji ta ce masa, don Allah kayi hakuri bazan kara ba. Kallonta ya rinka yi cike da so yace come here. Sake rungume ta yayi yana shakar kamshin jikinta. Shima kansa yana mamakin yadda yake iya kasancewa da ita kuma ya iya hakura ba tare da ya nemi biyan bukatarsa ba. Ya amince wannan shine true love.
Haka suka kasance suna nunawa junansu kulawa har ranar asabar ta zagayo wadda ranar Baffan Hafsi da Alh Bashir zasu iso abuja kuma ranar ne auren Junaid da Talatu Jibo Aka Tilly.
TUN KAFIN AURE💐37
Hafsi da Ummati sun kusa rabin awa a waya suna ta shawarwari don yanzu kam Hafsi tasan bazata iya zama haka babu abokin shawara ba duk da cewa su Hamida suna iya kokarinsu. Yayarta Hadiza ma ta bugu sun dade suna magana. Tana wayar Nafisa ta shigo da wata karamar jaka a hannunta ta zauna kan kujera. Hafsi ta gama waya suka gaisa. Nafisa tace kanwata kinga yadda Allah Yake ta jarrabar mu da abubuwa kullum ko? Yauma hakuri dai zan kara baki. Da yar shawara kadan. Kinga wadanan kayan masu tsada ne amma fa idan kika sha baza ayi asarar kudin tara ba. Suna gyara mace sosai sannan ki rika shan fruits musamman kankana. Akwai kunun aya ma da ake hadawa da ita da cucumber, dabino, kaninfari, citta da kwakwa. Zan hada miki da kaina kafin anjima. Munyi magana da Mommy ke zaki fara tarewa sannan bayan sati daya talatu ta tare amma gidanta daban ne. Kiyi iya kokarinki ki zama tamkar karuwa kema a wurin mijinki kinga ya san wasu matan so raba shi da irinsu sai kin dage sosai. Kan Hafsi a kasa duk kunya ta kamata ta kasa magana. Nafisa ta nuna mata yadda zata yi amfani da kayan data kawo mata. Ke ni ki dena jin kunyata bazan taba bari matan banza su rabaki da mijinki ba. Tunda kika auri Junaid kin gama mana komai.
Talatu yar gidan Mal Jibo mai faskare amaryar Junaidu dan sanata. Kirari ne Rosie da ke zaune kan kujera take wa aminiyarta. Tilly tace yanzu fa dole inyi ta amsa sunan Talatu sunan dana manta dashi tun a kauye. Suka tafa sanan rosie ta miko mata kullin magani. Ga wanan kawata ki shafa hannu ne ki taba shegen. Wallahi zaki sha mamaki don watarana ma sai ya gundireki idan ya fara like miki. Wata shewa suka yi tace Rosie ba kyau. Gara tun wuri na fara kiranki Samiranki kada ayi subutar baki a gaban surukai. Hakane, yanzu dai zan kira shi yazo a sunan kina zubar da jini sai ki fara gwada saarki. Bikin ma da akace muyi a garinmu zasu sha mamaki don sai munyi kara’i. Sake tafawa sukayi sannan Tilly wadanda sun koma dakin da Rosie ta kama musu ta dauki waya ta kira shi.
Tun safe ya kasa zaune ya kasa tsaye saboda tsananin farinciki yau Hafsin sa zata tare. Ya fito daga wanka yaji karar waya a zatonsa ma Hafsi ce don tun dare take tsokanarshi da flashing. Tsaki yayi kamar tana gabansa daya ga number din Tilly. Yana dauka Rosie ra kwarma ihu tace yazo Tilly tana ta zubar da jini. Wani tsakin yayi ya ajiye wayar ya cigaba da shiryawa. Sake buguwa suka yi har sau biyar sannan ya dauko a wulakance yace gani nan zuwa. Cikin gidansu ya shigo ya fadawa Mommy inda zashi. Ta tabe baki sai ka dawo. Kada dai ka dade yace to. Shi har a ce masa kada ya dade yadda yake zumudin nan.
Suna jin tsayuwar motarsa Tilly ta kwanta a kasa tana wai wai. Kudi ya jefa mata yana mata kallon banza gashi nan nasan abinda kike nema kenan. Ganin bashi da niyar taimaka mata ta tashi ta mike ta riko shi. Juni boy ka saki jikinka mana ai an riga an daura. Ina jiranka anjima kazo mu tafi namu gidan don a sannu zansa ka manta wannan kwailar. Hankadeta yayi har ta fadi kamar zaiyi magana ya fasa ya fice. Rosie dake kitchen ta fito da sauri tana mata sannu. Tilly tace aikin banza maganin naki baya komai ji yadda ya ture ni.
TUN KAFIN AURE💐38
Rosie tace dadina dake ba kya cin ribar abu. Kin fiye rashin hakuri kamar gudawa. Ki zuba ido yau a jikinki zai angwance. Ki dai sha kaya da kyau don ki kara kama shi a hannu.
Hamida ana ta rawar kafa kamar ita ce zata tare. Nasihohi da adduoi Hajiya da mummy suka yi wa Hafsi. Hamida taja hannunta masu aiki suka bi bayansu da akwatunanta. A ciki suka tarar da Nafisa da yaranta ‘yan mata biyu Ummu mai sunan mummy da Husna. Suna ganin Hafsi suka kankameta suna murna. Nafisa tayi musu tsawa ku sake ta mana haka kada ku kayar da ita. Husna yar shekara biyar tace Mama Hafsa ni a nan zan zauna tare da ke ko. Hamida tace asheUncle Junaid zai kore ki kuwa. Ai ku da gidan nan sai nan da wata tara. Hafsi ta sunkuyar da kai kasa cike da kunya. Haka suka zauna suna ta hira. Ko kadan basa barinta tayi kewar yan uwanta saboda yadda suke janta a jiki.
Tun daga bakin kofa yake jin kamshi mai dadi sai dai zuciyarshi wani irin kunci take masa. Yana shigowa falon yan uwansa suka fara tsokanarshi. Nafisa tace to ya isa haka ku tashi mu tafi. Duk suka yi mata sai da safe suka fita. Dama tun shigowarsa Hafsi bata yi masa magana ba saboda yadda su Hamida ke tsokanarta. jin bashi da niyyar kawar da shirun dake tsakaninsu tace masa ina yini. Lafiya ya amsa a takaice. Can ya sake cewa tashi mu shiga ciki muyi sallah ko. Dadi hakan yayi mata ta kara tabbatar da cewa Junaid ya fara maida hankali a lamuran addini. Fuskar nan tata a rufe ta bi bayansa. Suna shiga yaji hakurinsa ya soma karewa yace mata kiyi alwala ina zuwa nayi mantuwa a mota.
Cike da damuwa yake tuki ya rasa abinda ke masa dadi. Ace ya rasa abinda zaiyi ta tunani a yau sai Tilly, Why ??? Gidan ya nufa yayi saa suna zaune a falo. Mamaki karara a fuskar Tilly yace hado kayanki ki sameni a mota. Yana fita suka sa shewa da dariya. Tilly ta yi saurin dauko jaka ta watsa kaya kadan a jakar ko sallama babu ta fice. Rosie ta koma daki tana cin farar kasa wadda ta zame mata abinci yanzu. Mayen cikin yaki zubewa ita kuma tana tsoron wankin ciki.
Kusan awanni biyu kenan da fitarsa amma taji shiru. Tun tana sharewa har ta kasa hakuri. Lekowa tayi wajen gidan babu daya daga cikin motocin da yake shiga. Komawa tayi ta zauna tana ta sake sake. Gajiya tayi ta tashi tayi sallar isha da nafila ta zauna kan darduma tana karatu.
Hotel ya kama musu don yasan babu mai bashi mukullan gidan da Alhaji ya kama masa kafin ayi masa wani ginin inda zai iya hada matan biyu. Tilly ansha gyara ciki da waje. Ta nuna masa salo salo na kwarewarta a fanin shegantaka. Wayarsa ce tayi kara wurin shadayan dare. Har ya fara bacci Tilly ta dauka taga ansa H dear. Kashe wayar tayi gaba daya tayi tsaki sannan da dariyar mugunta. Yarinya yau zaki bushe ta fada a fili..
Saroro ta tsaya kallon wayar. Yanzu ita Junaid ya kashewa waya? Ko tayi masa laifi ne? A falo ta kwana ranar tana kuka ita wannan wace irin rayuwa ce daga wannan sai wannan kullum. Ta yanke shawarar idan bai dawo ba da safe zata sanar da iyayensa.
TUN KAFIN AURE💐39
Wani azababben ciwon kai ta farka dashi lokacin da taji bugun kofa. Sai bayan asuba bacci ya sace ta, dan goge fuska tayi ta bude kofar. Amaka ce dauke da tray ga wani a kasa shima duk kwanukan abinci ne a ciki. Tace Amariya goodmorning…Hafsi ta dan saki fuska ta amsa tare da daukar tray din kasan suka shigo dashi. Amaka tace Madam say make you tell me wetin you wan chop for lunch. Hafsi tace what? Ita fa bajin pidgin english take ba. Ta dai gane lunch ta ce mata ta tafi kawai zata shigo. Har shabiyu tana jira ganin dai bashi da niyar dawowa gashi wayoyinsa duk ta kasa samu ta fito ta tafi main house. Babu kowa a falon sai akwatuna guda uku daga bakin kujera. Dakin Hajiya ta fara leqawa ta ganta tana daura laffaya. A’a mamana keda kike amarya me ya fito dake kuma. Nima shirin komawa Kano nake yi yanzu Rufai nake jira yazo muyi sallama sai a kaini iyaport. Hafsi tayi dan murmushi tace Hajiya bana son ki tafi. Allah sarki Mamana bakya so naje na gyara nawa auren ne? Tare fa aka kawo mu dake gashi muna neman wata daya. Wasu hawaye masu zafi ne suka sauko mata Hajiya a rude tace haba Hafsatu kada ki karyar min da zuciya mana. Ki kara hakuri in Allah Ya yarda zaku sami zaman lafiya da Junaidu. Kirawo min shi mu yi sallama sannan ki goge idonki kada yace na taba masa mata. Kanta a kasa tace baya nan Hajiya. Dan bata rai tayi ina yaje kuma daga kai masa amarya. Mummy dake tsaye a bakin kofa tace garin yaya kika bari ya fita amarsu. Har kasa ta kai ta gaishe da mummy sannan soma kuka. Duk hankalinsu ya tashi aka suna tambayarta ko lafiya. Da kyar tace musu bai kwana a gida ba. Sai suka fara salati. Mummy ta dauki waya ta kira shi aka yi sa’a a kunne wayar take.
Tilly ta kalli wayar bari na daukar maka Juni boy. Kasan yau rana ta ce so duk mai kira yayi hakuri. Ba musu ya mika mata batare da yasan mai kiran ba. Hello ta fada bayan ta amsa wayar. Mummy a dan razane tace wacece? Ahhh tuni ta gane muryar jarababbiyar babar tashi. Tace matarsa ce Talatu don Allah a dena kira yana bacci ne idan da sako ki fada na gaya masa. Yadda take maganar a ladabce shi yasa Junaid ta kara lafewa jikinta yana mata cakulkuli please ki ajiye wayar anjima na kira. Karaf maganar sai a kunnen mummy tace Junaid da karfi. Tilly bata bare yaji ba ta ajiye wayar ba tare da ta kashe ba tana ta dariya please baby ka bari kaga jiya baka barni na runtsa ba.
Jefa mummy tayi da wayarta tana kuka mai tsuma zuciya. Maganar Junaid ta tabbata karuwa ce yarinyar nan. Suna tare bansan ko a ina ba amma suna tare. Hajiya tace inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Anya zan iya komawa kano kuwa salma? Yarona yana cikin matsala. Mummy tace ki tafi hajiya ai tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa zai daka. Rashin jin maganar iyaye yasa ya kwaso mana balai. Bari na tado Yallabai wallahi a nemarwa yarinyar nan saki tun wuri. Ni bazan iya kallon Safiya ba ina kallo dana yana wulakanta musu ‘ya.
Tunda suka fara magana Hafsi ke kuka Mummy ta jawota ta rungume. A haka senator Rufai ya samesu. Bayan anyi masa bayanin abinda ke faruwa yace su kwantar da hankalinsu zaisa a nemo shi duk inda yake a kasar.
Wasa wasa sai da suka yi sati biyu a hotel suna shan soyayya. Hutu ya ratsa su da kyau don daga ci sai kwanciya. Ko kadan baya son Tilly amma ji yake idan ya rabu da ita komai na iya faruwa. Kashe mata kudi yake kamar hauka tana karbewa. Rosie master planner ma an manta da ita .A rana ta shabiyar Senator yasa aka yi freezing dukkanin accounts din Junaid. Matsayinsa yasa har aka nuna masa statement of account din dan nasa. Ba karamin barnar kudi yayi ba a iya kwanakin da baya gida. Senator Rufai ya shiga rudani sosai yadda junaid yake neman kara lalacewa.
TUN KAFIN AURE💐41
Dakinsa ya shiga ya lalube duk wuraren ajiyarsa ya dauko kudi masu yawa. Yana zuwa wurin parking yaga convoy din Alhajinsu dole ya tsaya suka gaisa zai fita. Senator Rufai bai nuna damuwa ba yace Junaid kafin ka tafi ina son ganinka. Tsaki yayi wanda har uban yaji sautinsa. Tilly ta kira shi ya kai sau ashirin kada yaje taki binsa ko yau ta hana shi kusantar ta.
Yana zaune gaban iyayensa Alhaji ya fara masa nasiha mai tsuma jikin mai imani. Mummy ce ta fara lura da yadda hankalinsa ko kadan baya tare dasu. Duk zancen senator ta bayan kunnensa yake bi. Tana kara kiran wayar yace Alhaji bari nake yanzu dai matata ce so don Allah ku dena daga hankali idan baku ganni ba. Mummy tace Kana da hankali kuwa Junaid ? Bai amsa ba ya mike mummy ba nisa zanyi ba ga keys din gidan ashe suna dakina can zamu zauna. Fita yayi ko waige babu. Ba mummy ba hatta senator yau idanunsa sun kawo ruwa. Ashe da gaske ne idan mutum baya tsarkake dukiyarsa yaran da aka ciyar da ita albarkarsu tana tawaya? Allah Ya dora masa son Junaid har baya son laifinsa. Gashi yau dukiya da dansa sun zame masa silar rashin kwanciyar hankali. Kullum tunaninsa baya wuce kada dansa ya jawo masa abin kunya saboda shi dan siyasa ne. Daga yau zai guji abin kunya saboda shi musulmi ne. Haka suka yi ta saka da warwara kafin daga karshe Senator ya yanke shawarar su dage da addua har Allah Ya kawo musu mafita.
Duk yadda take kokarin boyewa kana ganin Hafsi kasan bata da nutsuwa da kwanciyar hankali. Son Junaid take sosai gashi tana missing din irin wasannin da suke na tsokana. Wataninta biyu a gidan Nafisa hakan ya zama wata uku rabonta da Junaid. Iyakar alkhairi tana samu wurin iyayen wanda bai damu da ita ba. Senator ya siyawa babanta mota ya canja musu gida. Duk sai da aka hada da ban baki Mal Aminu ya karba. Itama Hafsi dubu hamsin ta bawa Ummati saboda bikinta saura wata biyu.
Hafsi da Hamida suna zaune tana ta yiwa hamida tsiyar ciki Nafisa ta shigo falon da faraa. Big sis ta samu ne hamida ta tambaya. Kwarai kuwa yanzu Alhaji ya ce muje ayiwa Hafsi passport dukkanmu zamu umra. Farin ciki mara misaltuwa ya bayyana a fuskarta. tana ta godiya ga Allah. Ta samu damar zuwa yin addua sosai game da Junaid.
TUN KAFIN AURE💐42
Sau uku tana katse wayar tare da yin tsaki. Ya kalleta fuskar nan babu fara’a. Ya rasa dalilin zamansa da ita don ko kadan baya sonta. Bashi da sukuni indai ba kusantarta yayi ba shiyasa take gara shi sosai. Parties kala kala yake dawowa ya tarar ta shirya a gidan samari da yan mata su taru su hole. Idan yayi magana kuwa ranar sai ya kusa kuka zata bashi hakkinsa. Yana dai zuwa gaida iyayensa idan ta gadama amma zancen Hafsi tace ko zuci yayi zata sani kuma tayi rantsuwa ranar sai dai hawayensa su kare bazata bashi kanta ba.
Kallon wayar yayi waye ke kiranki? Mtsw rosie ce duk ta dame ni tana son na taimaka mata da kudi. Ina wanda na baki last week baki bata bane? Ta kara yin tsaki kasan gayyar tsiya na rasa me take da kudin. Yace to bari idan na fita zan kawo ki bata. A ranta tace kyayi kya gama bazan bayar ba don yanzu kam yadda yake yawan hade mata rai tasan magani ya fara ja baya kuma da kunya ta koma gidan rosie. Wata biyu rabon da taje kudin da take karba ma account dinta yake shigewa..
Rosie ta kalli wayarta da katon cikin dake gabanta. Kudin abinci ma yanzu gagararta yake amma Tilly taki taimakonta. Gidan da ta tare ma bata sani ba bare tabi sawu. Shawara daya ta yanke ta neme malaminta a warware abinda takewa Junaid ya dawo hayyacinsa ya koreta.
A kasa mai tsarki hafsi da sauran iyalan senator Rufai Bukar sun dage da yawan sallah da adduoi don nemarwa Junaid shiriya. Shi kanshi senator da ya dage da istigfar ba karamin mamaki yayi ba yadda yake jin canji game da al’amuransa. Idan Junaid ya dawo garesu dole su koma a nemi ilimin addini sosai.idan da asiri a jikin junaid to harda sakacinsa ta bangaren addua.
TUN KAFIN AURE💐43
Kwanansu hudu da dawowa bayan sunyi sati uku a kasa mai tsarki Hafsi ta taje kano tayi sati biyu. Sun sha hira da ummati ta fada mata halin da take ciki. Gashi dai ta kara kyau ga hutu amma babu nutsuwa a tare da ita. Bikin dake gabanta ne duk yasa ta dan manta da halin da take ciki. Ansha shagali don ummati ita kadai ce mace a gidansu. Duk kayan da ta saka da ma wasu abubuwan Hafsi ce tayi mata. Idan aka tambayeta mijinta kuwa sai tace yayi tafiya ne. Haka suka sha biki aka kai amarya gidanta. Bayan an gama biki Alhaji ya turo mata da kudin jirgi tana zuwa mota na jiranta suka wuce gidan Nafisa.
Ya kusa rabin awa yana jiran Imi a kofar super market din sai ga Tanimu wanda yazo gidansu a matsayin baban Tilly yana bin wata mata da kaya niki niki a baya. Tabbas shine don ga uku ukun bakinsa nan. Rufe motar yayi ya fito ya karasa inda Tanimu yake shirin lodawa matar kaya a booth dinta. Assalam alaikum….ai kafin kace kwabo Tanimu ya zura da gudu don kuwa ko a mafarki baya jin zai manta wannan fuskar. Ita kuwa matar kyawun Junaid duk ya dauke mata hankali kana ganinta kasan tana da aure. Wani fari ta rinka yi masa da ido da kwarkwasa. Hafsi ce ta fado masa, gabansa ya fadi. Ya rasa dalilin da yasa baya iya bude bakinsa ya nemeta ko ma yayi zancenta. Hango Tanimu yayi zai tsallaka titi ya bishi da gudu. Wuyan rigarsa ya kama ya fizgo shi. Tanimu duk ya gama rudewa don bai manta yadda senator yace zai iya sa a batar dasu idan suka yi masa karya. Gwiwoyinsa a kasa ya daga hannu sama yallabai kayi min rai wallahi sani suka yi. Junaid yace meye alakar ka dasu? Ya cigaba da magiya faci nake a tsallaken titin gidansu kuma ina hada su da maza. Dama dai yasan matan banza ne amma dai baiyi tunanin iyayen karya ta kawo ba. Sam baya jindadin rayuwarsa yanzu kullum jinsa yake kamar an kulle shi a cikin kwai. Imi yaji ya taba shi ya Juni meke faruwa ne? Junaid ya kalli Tanimu dake zaune gabansa ya fadawa Imran ko shi waye. Imran ya kira waya ba dadewa ta shiga suna zaune police biyu suka zo yace a tafi da Tanimu har ya fadi inda sauran suke. Yallabai ai ba sai an dake ni ba muje na nuna muku su duk abokai na ne. Keyarsa suka tasa a gaba suka tafi shi kuma Imi ya dawo motar junaid ya zauna. Wai meyasa kaki yarda mu hadu a gidanka ne? Wani zafi jikinsa yake yi yace Imran ina cikin problem sosai, wallahi na tsani rayuwata. Ba abinda ke min dadi….yanzu fa ina shiga gida da naga matar nan babu abinda nake so kamar kusantar ta. Tun ana abu da marmari yanzu ya koma kamar cin tuwo. Ita kuma idan ba kudi ta gani ba ta rinka gara ni kenan. Imran yace ai laifinka ne, tun a wurin bikinka nace ka barni nayi maganinta kaki. Yanzu kuma gaskiya na tuba…junaid yayi yar dariya Allah Ya kara shiryamu. Amin dan uwa…ai in fada maka wata shegiya ce. Au wallahi na tuba fa. Hmmm yarinya na dauko bayan an gama abu sai da nayi kwana biyu bansan inda kaina yake ba saboda na kasa fitsari. Wani mugun ciwo tasa min in takaice maka labari sai da aka yi min aiki a Germany. Abinda ya gabata Allah Ya yafe mana amma ni da mace sai matata insha Allah.
TUN KAFIN AURE💐44
Junaid yace kowa ya tuba don wuya fa ba lada. Imran na dariya yace ai wallahi da lada tunda nayi nadama kuma dai ai ba bari saida nazo gargarar mutuwa ba. Yanzu dai abar zancena wane mataki zaka dauka game da Tilly? Gaskiya i cant say for now matsalar tafi yawa idan na ganta. Ita kuma dayar ina sonta sosai amma na rasa me ya hanani nemanta. Bayan dan tunani Imran yace na sama mana mafita. Cikin zakuwa yace wacce? Kana ganin zaka iya hakura da mace indai babu aure a tsakaninku? Jimm yayi na dan lokaci. Tilly ta zame masa jaraba yace in sha Allah. To indai haka ne ka kira ta yanzu a waya. Junaid ya dauko wayar ya kira. Imran yasa speaker kafin ta dauka yace kayi mata saki uku yanzu ka yanke ala…..hello? Juni boy ina ka shiga ina ta jiranka. Imran ya zungure shi yana magana kasa kasa. Saketa mana…a dan tsorace yace Tilly na sakeki saki u..u..uku. wata irin kara suka je imran ya kashe wayar yace to tura mata text don a sami shaida. Jiki ba kwari ya tura Imran yana masa dictating abinda zai rubuta. Yana tura send Junaid yayi wata ajiyar zuciya. Imran yace idan har bazaka iya ba ka barni na biyoka gidan. No ka barni kawai ina zuwa zan koreta.
Hafsi tana ta juya waya a hannunta ta kasa bugawa. Tun a kano Ummati ta bata shawara yanzu ma ta sake kiranta taji ko ta kira tace mata yanzu zata kira. Sai da ta tattaro dukkan courage dinta ta kira. Wayar tayi ringing har ta katse bai dauka ba. Kamar tayiwa ummati Allah Ya isa. Gashi ta zubar da ajinta kuma babu biyan bukata. A lokacin da take wayar Junaid da Tilly fada suke kowa murya a sama don bai ma ji karar wayarsa ba. Nishi take kamar wata kumurcin maciji Juni boy baka isa ba na rantse maka. Ni zaka yiwa wannan rashin mutumcin, saki har uku? Duk da bashi da kwarin gwiwa sosai yace ki fita kawai kafin na kira security. Daki ta shiga da gudu ta barbada dan sauran maganin a hannunta. Saboda kuka bama ta ganin gabanta sosai. Duk duniya babu wanda ya isa ya raba mu. Tana yin kansa cikin zafin nama ya tureta bai san lokacin da ya fara karanta La haula wala quwata illa billah. Zafi sosai jikinsa yayi sosai har yáji kamar kafarsa bazata iya daukarsa ba. Tilly kuwa kan wani muzurunta ta fada daya tureta. Wata kara muzurun yayi tare da yakushin tilly. Hannunta mai magani a jikin magen duk ta shafe masa shi. Ihu tasa sosai tana kuka ganin abinda tayi na shiga uku shine na karshe maganin. Wani irin kallo taga muzurun yana yi mata tare da biyota. Tuni tilly ta dago jirgin badai maganin yana yi jikin kowacce dabba ba. Tsere suka sa ita da muzurun tana gudu yana binta juni help me please. Ko dago kai baiyi ba yadda yake jin jiri na dibarsa. Tilly dai kitchen ta shiga ta rufo kofa tana numfarfashi. Muzuru kowa yana ta meoww daga bakin kofa yana karta iya karfinsa.
TUN KAFIN AURE💐45
Da kyar ya mika hannu ya dauko wayarsa don ya kira imran. Kansa ne yake juyawa saboda tsabar ciwo ga zazzabi da ya rufar masa lokaci guda. Missed call din Hafsi ya gani take yaji zuciyarsa tayi masa sanyi. Kiranta yayi amma har wayar ta kare ringing bata dauka ba.
Tsaki tayi ganin me kiran ta wurga ta kan gado tare da tayar da sallah. Husna ce ta shigo dakin jin waya tana ringing ta dauka ta fita Maama ga wayar Mama Hafsa tana ringing. Nafisa ta ajiye remote din hannunta ta kalli Husna. Yanzu wa yace ki dauko mata waya? Maama sallah take yi. Kinga an sake kira ma. Nafisa ta karba ganin sunan Junaid tayi saurin dauka. Tana jin muryarsa ta mike tsaye Junaidu kana ina? Jikinta har rawa yake yace sis kece? Sautin kukansa taji yace i need you please. Kizo gidana yanzu. Kwalawa Hafsi kira tayi ki fito muje gidan Junaid Hafsi ina jin akwai matsala don maganar da yake ma ya dena. Hafsi najin haka itama kukan ta fara suka dunguma waje driver ya kaisu unguwar maitama inda gidan Junaid yake. A hanya ta kira mummy ta fada mata itama duk ta rude don tasan ko ba a fada ba dan nata yana cikin matsala.
A falo suka tarar dashi yana ta rawar sanyi ga gumi ya gama wanke shi har rigarsa ta jike. Nafisa tace da drebansu yazo ya dauko musu shi asa shi a mota. Hafsi tace bari a rage masa kaya jikinsa yayi zafi sosai. Ina ne kitchen ma, duk ta rude tayi nan tayi can. Nafisa ta nuna mata da hannu tana dago kan Junaid.
Wata irin faduwar gaba taji lokacin da taga Tilly kwance muzuru yana bin jikinta yana lashewa. Ko motsin kirki ta kasa yi don duk inda ta motsa sai ya yakushi wurin. Yanzu ma cinyarta muzurun ke lasa. Auzubillahi minash shaidanir rajim. Abinda ya fito daga bakinta kenan. Tilly cikin kankanuwar murya tace taimake ni…muzuru ne ya dare kan fuskarta yana lasar mata baki saboda ta motsa bakin.
TUN KAFIN AURE💐46
Washegari sai wurin shadaya na safe Junaid ya farka. Koda ya bude idanu iyayensa ya gani da yan uwansa. Hajiyan dangi ma tazo daga kano. Yunkurin tashi yayi yaji hannu ya danne shi ta baya Juni ka kwanta jikinka ba kwari fa. Na shiga uku ce ta subutu daga bakinsa. Don har zuciyarsa saida ta kada don yanzu tilly tsoro take bashi. Yace me kike a nan ba na sake ki ba? Wani murmushi mummy tayi har kana ganin hakoranta, ita kuwa Tilly me kumburarriyar fuska tace dont mind him zafin ciwo ne yake damunsa. Imran da yake asibitin tun safe bayan ya kira wayar hamida ta dauka yace ke bana son iskanci…sai yayi saurin rufe bakinsa Allah na tuba. A gabana yayi mata saki uku wallahi kuma harda text ma shaida. Karya yake Mummy don Allah kada ku rabani da Juni. Nafisa tace idan ma joni ne ke da shi har abada. Kuma idan baki fita ba Allah security zan kira miki. Ta kalli su Hajiya tace ai a kwance muka ganta tana wani tsafi muzuru na lasheta kamar maye. Duk shi yaji mata ciwo. Tilly cikin kuka da daga murya tace wallahi karya ne bana tsafi. A jikin Juni nayi niyar shafa maganin shine na fadi ya goge a jikin mage. Subhanallahi dama asirce shi kike yi. Saurin rufe bakinta tayi jin baram baramar da tayi. Tana girgiza hannayenta da kanta tace ba haka nake nufi ba wallahi. Hamida ce ta bude kofa zata tura Tilly waje sai ga muzuru ya shigo ji kake yana meooowww da yaga Tilly. Bayansa nurses biyu ne da wani cikin masu gadi sun biyoshi da gudu. Jikin Tilly ya dafe yana zazzare idanu harda wani lafewa a kafadarta. Ita dai mutuwar tsaye tayi ko motsi ta kasa. Maigadin yace kuyi hakuri muna binsa yana gudu kamar yasan inda zashi ne. Imran dariya har kasa ta kaishi yace no ka barshi kawai ga matarsa nan ya nuna Tilly dake hawaye ba kakkautawa. Tausayi ta bawa hajiya tace don Allah a raba ta dashi. To dai jikin Tilly kamar me wasan kura da kyar aka rabasu don sai da aka yiwa muzurun allurar bacci ya fado. Tana ta godiya nan ta fada musu duk sharrin data kulla ita da Rosie ta roki gafarar su. Hafsi da ke can gefe akan kujera Tilly ta kalla tace kema sharrin dana yi miki babu ma cikin kawai so nayi ya sake ki.
Nan dai kowa yace ya yafe Nafisa tace ina kudin da kika karba wurin Junaid. Sai lokacin ma ta tuna cikin kankanuwar murya tace yana drawer a gida. Nafisa ta sha kunu to babu ke babu su don har atm din Alhajinmu ya sata yana baki kudi. Daga nan ki san inda dare yayi miki.
Hajiya tace to kuzo mu tafi gida don a kawo musu abinci. Hafsi ce kan gaba Hajiya tace ni bana son gulma zauna wurin mijinki kinji ko. Kamar tayi kuka duk suka fice. A bakin kofar ta tsaya taki juyuwa ma ta kalleshi. Kusan minti goma tayi a haka har kafaŕta ta fara sagewa shi kuwa Junaid dama kyaleta yayi don yaga iya gudun ruwanta. Yana kallonta ta sa nauyi a wannan kafar idan ta gaji ta canja. Murmushi tayi don ta fara bashi tausayi.
TUN KAFIN AURE💐47
TUN KAFIN AURE💐48
1/1/20..
Assalam alaikum Talatu, idan kin sami takardar nan to hakika rai yayi halinsa. Ya yar uwata munyi rayuwa tamkar tumaki marasa alkibla. Nice ma sanadiyar lalacewarki bayan kin baro gidanku a dalilin fyade da kanin babanki yayi miki aka karyata ki. Nima wahala ce ta kawoni ga wannan rayuwar a dalilin maraici kamar yadda kika sani. Sai dai kuma duk tsananin rayuwa ba hujja bace ta iskanci. Nayi nadama mara iyaka kuma naje wurin malam ya warware abinda aka yiwa Junaid. Ki rokeshi da duk wanda kika san muamala ta hada mu ya yafe min. Kema ki tuba don Allah.
Hawaye ta share tace na tuba nima nabi Allah da manzonSa.
Ga abinda Allah Ya bani nasan dai aikin da wahala ki taimaka ki bashi tarbiyar da mu bamu samu ba. Ki koya masa tsoron Allah da azabarSa. Na saka masa suna Abdallah bawan Allah. Allah Yasa muna da rabon rahmarsa.
Ashhadu an lailaha illallah wa ashhadu anna muhammadar rasulullah.
Yar uwarki
Samira Jafaru.
Nima a gefe saida nayi hawaye. Talatu au na manta Safiya ta rungume Abdallah tana ta kuka. Allah Ya gafarta miki Samira Allah Ya jikanki. Haka ta zauna tayi yan kwanaki har dan abin hannunta ya kare. Ga Abdallah ba abinci. Karfe tara na dare Tambai tasa samari suka yi boli da Safiya da kayansu. Babu abinda ta dauka sai kayan jikinsu ta goya Abdallah suka fita daga gidan. Yanzu ina na nufa ta fada a zuciyarta.
TUN KAFIN AURE💐49
Kallon dakin take wanda ya kawatu da kayan more rayuwa kala kala. Zauna mana Hafsi Hafsi ko kauyancin ne ya motsa. Ta sha kunu yau wacece bakauyar eyye. Toooohhh ni kike zarewa idanu? Duk mace mai zarewa mijinta ido fa hukuncinta…….mamaki da jindadi ne suka ziyarci zuciyarsa da gangar jikinsa lokacin da yaji ta hade bakinta da nasa. Sai da suka jima a haka ya rinka kokarin su hada ido taki. Kaji wani sabon salon gulmar kina wani kasa da kai kamar mutuniyar kirki. Ita kanta tayi mamakin abinda tayi. Ya kama fuskarta da hannayensa biyu…Hafsi ki fada min abinda zai karasa cika min farinciki na. Kunnensa ta kama tace I love you J dear. Tana gamawa ta hada da cizo a saman kunnen sannan ta gudu. Binta da zaiyi yaji an buga musu kofa ga wayarsa dake aljihu tana ringing. Hafsi ta dawo tace ni na ga ta kaina. Menene ya tambaya a firgice ta nuna masa hanyar kofa. Kullum aka kawoni sai wani abu ya faru. Kanne mata ido yayi kaga su Hafsi ke kuma kina bukatar kadaicewa da mijinki ko. Dundu tayi masa har yayi kara sannan ya duba mai kiran wayar. Ya nunawa Hafsi kinga ma sis ce. Yana dauka tace fito falo kai da Hafsi.
Hankalinsu duk ya gama tashi ta dauki mayafi suka tafi falon. Suna ganin Tilly Junaid ya kama hannun Hafsi zo mu tafi don yau bansan dame tazo ba. Muryar Senator suka ji yace duk su zauna. Sai a lokacin Hafsi ta gane baby ne a bayan Tilly. Nafisa tace a bakin gate muka ganta securities din wurin sun hanata shigowa. Mummy tace shine kika kwaso mana ita ko. Wasikar da Tilly ta bata ta mikawa Senator ya karanta sannan aka bawa kowa ma ya karanta. Hafsi tana gamawa taje ta rungume Tilly cike da tausayawa tace Allah Ya jikanta. Amin Hafsa nagode don Allah ku yafe mana. Kowa jiki yayi sanyi aka ce an yafe. Mummy tace to yanzu me ya kawoki? Cikin kuka ta fadi matsalarta harda labarin rayuwarta dana Samira wanda ta sani. Duk mai imani zaiji tausayin yadda aka yiwa marayun mugun riko musamman Tilly wadda kanin babanta ya bata ta kakarta kuma ta karyata zancen sai da aka ganta da ciki suka koreta.
Bayan ta gama bada labarin senator yace kinyi karatu ne. Tace eh abinda ya fara sasu bin maza kenan neman kudin makaranta. Yace to ina takardunki? Tace suna gidan da aka koro mu. To gobe kije ki dauko da murna tace to ta sunkuya zata kwance goyon senator yace ah ah ki tashi yanzu zansa dreba ya kaiku asibiti a duba lafiyar yaron. Tayi musu godiya ba adadi Hafsi ta karbi Abdallah ta rungume tana kuka. Tilly tace musu sunanta Safiya yaron kuma ga sunan da mahaifiyarsa ta zaba amma baa yi masa radin suna a kunne ba. Junaid yace khudba aka cewa. Senator ya miko hannu alamun a bashi yaron. Hafsi ta mika shi Senator Rufai yayi masa Khudba. Sannan dreba ya kaisu asibiti inda suka kwana.
Junaid ya kalli fuskar Hafsi bayan sun idar da sallar nafila yace to yau dai Allah yayi ga Hafsi Hafsi ga Junaid a daki daya saura me? Yadda yake mata wani irin kallo tace saura karatu ko. Eh haka ne fa ya mike tsaye zai cire riga bari ki sha darussa kala kala. Can na jiyo dariyarsu suna cike da farinciki.
Washegari kamar yadda yayi alqawari a gaban iyalinsa yace ko bayan ransa su kula da karatu da rayuwar Abdallah. Visa ya tura su aka yi saar samu saboda sunan senator cikin sati daya aka gama komai ya tura su Saudia inda ya samawa Safiya Jibo aiki a Nigerian embassy dake can.
Tayi musu godiya kamar ta ari baki da sake basu hakuri akan laifin da suka yi.
******************
Kowa a gajiye saboda yadda taron yayi jamaa Hafsi bata samu kanta ba sai can dare ta dauki baby Rufai junior suka shiga dakin Junaid. Tana shiga ya rungumeta cike da farin ciki haba maijego ya zaki min rowar matata da baby na. Tayi kasa kiss a kumatu sorry my dear J kaga akwai mutane a gidan kuma duk saboda mu suka zo. Yace haka ne ya karbi junior to yi sauri ki min tausa kada su mama suce me nake miki. Kayi ka gama kai da tausar i just came to say goodnight. Haka zaman su ya cigaba cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Watan Junior shida Hafsi ta fara wani laulayi ga bikin Anisa da Imran abokin Junaid.
Bayan shekara 25
Rahma ce zaune tana koyawa Al-Amin auta assignment amma rabin hankalinta yana kan tv zaa fara musabaqar karatun alquran na duniya baki daya. Ana zuwa kansa ta fara kabbara har su Junior, Ummi da Aisha suka fito. Ta kalli yayyen nata tace kunga Yaya Malam. Duk zama suka yi suka bada attention basu san sadda iyayensu suka zo suka zauna ba. Karatu yake da murya mai tsuma zuciyar mai sauraro. Ga larabci tamkar balaraben gaske. Lokacin da ya gama gaba daya falon ya kaure da kabbara. Hafsa ta kalli yaranta zuciyarta sai hamdala take tace to ku tashi muyi sallah mu taya shi addua. Junaid ya mike da sauri Mama Hafsi nine first ina fata zaki bani kyauta. Al amin yayi saurin tashi Allah nine first yau Abba don tun dazu nayi alwala. Sauran yayyen ma suka tashi kowa yace yau yayi alwala da wuri. Junaid yace kaga yan nema da baban naku kuke tsere? Duk dariya suka yi Hafsi tace zo nan babana yau kyautar taka ce. Junior yace mama dama yau tun safe kike nuna mana wariya akan wannan dan kalen. Filo ta jefa masa duk suka tashi yin nafila su taya Abdallah Muhammad adduar samun saa. Bayan sun idar Junaid yace kullum kyautar mama kuke so to nima ga tawa. Tickets ne na zuwa saudia. Zamuje umra tare da taya Abdallah murna ko baiyi na daya ba zaman nasa ma abin alfahari ne gare mu. Nan da nan gidan ya kaure da murna.
Safiya ta cire glasses din idonta ta share hawaye. Ina ma Samira nada rai ta ga danta gaban manyan malaman musulunci. Mijinta Muhammad Aswadiy yace mata cikin harshen larabci ki cigaba da yi mata addua Safiyya. Allah shine mai gafara da jin kai. Nagode sosai Abu Musab ta fada tare da murmushi. Shekararta biyu a saudia suka yi aure bayan rasuwar matarsa. Ta sanar dashi komai na rayuwarta ya ce Allay shine mai gafara da jinkai. Tare ta hada Abdallah da yaransa uku ta rike. Bayan ya shiga ciki ne Safiya ta tashi tayi sujjada tana kuka tace Ya Allah Ka yafe mana ni da Samira da dukkanin musulmi ka sakawa iyalan Alh Rufai da mijina Muhammad da alkhairi. Amin
Alhamdulillah👏🏾