UMM ADIYYAH CHAPTER 65 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 65 BY AZIZA IDRIS GOMBE
shi kenan, ita ce take ta duma kanta akan me
zai kasance yake gudana a cikin
ransa idan ya samu labarin tana shirin bawa TJ.
kofar neman aurenta.
Ajiyar zuciya ta yi da ta tuna ta bar TJ. A ciki
yana jiranta.
Da fatan dai komai lafiya, kin ce ki na zuwa
yanzu, na ji kuma shiru, saura kiris! Na
je na ga ko kin bata ne hanyar ki ta dawowa.”
Murmushi ta yi sannan ta ce masa, “Kan batun
ofis ne, amma mun gama magana.”
Ofis kuma?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Eh, wurin da na yi aiki da, akwai abinda suka
tambayeni, shi ne na tsaya masu
bayani.” Ta rasa dalilin me ya sa ta yi karya ba
ta fada masa da Yaya Zaid suka yi
magana ba.
Murmushi ya yi mata ya ce, “Muna magana
dazu.”
Tana kallon kan carpet din falon Abban ta ce
masa, “Uhmm?” Ya kula da hankalinta
ya dan yi gaba kadan.
Don haka ya kalli windon falon ya yi mur-
mushi, ya ce, “Ko dai zan bari sai gobe mu
Karasa maganar, na ga yanzu, kamar han-
han-
kalinki ya koma kan aiki.”
No, ba komai, mu gama yau din kawai, ba
wani abu bane ya wuce.”
“Ki na nufin ki ce ba sai na dawo gobe ba ke-
nan ko me?”
Dariya ta yi ta ce, Ni dai yaushe na ce haka?”
*A to dai na ga kamar take-taken ki kenan, any
way. Bari na bar ki ki huta zan wuce.
Ki kula da kanki, sai mun yi magana anjima.”
“To Allah ya kare, ka gaishesu.”
Girgiza kai ya yi ya ce, “Na ga dai randa za ki
fara kiran sunan nan, kishinki ya yi
miki yawa Ummu Adiyya..”
Rufe idanunta ta yi ta ce, “To kuma don kawai
ban fadi suna ba, sai ya zamo kishi
kenan?'”
Kar dai ki sa na tona. A bar kaza cikin gash-
inta kawai.”
Ai shi kenan, na ga ta kaina, tunda har na yi
subul da baka a gabanka.”
Yana dariyarta har ta raka shi zuwa motarsa.
Inda abokinsa Mahmoud wanda ya
shiga wani kanti a kusa da gidan su Umm
Adiyya ya dawo daukarsa a lokacin.
********
Tana shigowa ta tarar da Safiyya ta tashi a barci,
don haka hidimarta ta shiga yi, don
da ta tashi tahowa daga Bauchi tare suka taho.
Kasancewar Adda Zubaida ta dan
fara nauyi. Nan ta sa ta a gaba da surutun bal-
lagwajenta, kullum Walid na mata
dariya, wai ba ta iya hausa ba.
Washegari suka tashi da shirin zuwan Yaya
Saadik da Aunty Saudah, Maami na
gida don haka tare suka kimtsa, duk abindan ya
dace. Gidan ya yi armashi ranar
kasancewar samarin ma duk suna nan ba su fita
ba.
Koda suka iso ma tare aka hadu ana hira, kafin
Maami ta ce, “Ku sako abincin nan a
ci dai, idan ba so ku ke yi ya yi sanyi ba, hi-
rarkun nan ba karewa za ta yi ba, ku
zauna ku yi ta muhawara kamar za a biyaku
kudi.”
Da gaske Maami, gaskiya muke fada masu,
kashi casa’in na maza sam wannan
fentin fuska ba ta burgesu, mutum duk ya tashi
daga halittarsa. Wata ba ta taba iya
fita sai da shi, randa ka ganta na gaske, sai ka
razana.”
Suna dariya Umm Adiyya ta ce, “To wai dole
sai don namiji za ayi kwalliyar ne? Ai
za ta iya yi don kanta, don ta ji dadi. To meye
laifin idan ta so abin ta?”
“Adda ke dai kawai ki yi shiru, duk mun san
irinsu Wallahi don mazan suke yi.” Faruk
ya fada.
Aunty Sauda ce ta kula da Fa’iz ta ce, “Fa’iz
yau ka yi shiru har ma ya wuce kima,
kamar ba ka falon nan.”
Juya cokalinsa ya yi cikin farantinsa, ya yi
yake sannan ya ce, “Babu komai, kawai
ban jin kaina ne yau din.”
Dai-dai lokacin suka hada idanu da Umm
Adiyya, Kura masa idanu ta yi, shi kuwa ya
ajiye cokalin ya mike zai bar tebur din.
“Wai meye hakan? Koma ka ci abincin nan, ba
za ku bar min shi ba, haka jiya ku ka
bar abincin nan himili guda.
“Maami da gaske zan ci anjima.” Ai ko Maami
ta tsare shi da idanu kamar karamin
yaro, haka ya koma ya daga plate din ya shiga
ci.
“Wai ma me yake damunka ne kwanan nan,
har da wani rama ka yi?”
“Maami Ustaaz ya zama har sallar dare ya fara,
ina ga azumin magana ma yake yi.”
Faruk ya fada yana dariya, ya kuwa samu
rabonsa, inda Fa’iz ya jefe shi da
dunkulen karas. Ya zarce ya bugi gefen kan
Safiyya, ai ko Umm Adiyya ta matsar
da ita gefe tana murza wurin. *Wai ku meye
haka ne? Maami yaranki ji suke yi
kamar su har yanzu kanana ne.”
To Allah ya nuna min randa za ku girma.”
Maami ta fada, tana kallonsu.
Fa’iz ne ya hada idanu da Umm Adiyya, ta
gyada masa kai.
Don haka muryarsa na rawa ya soma fadin,
“Uhmm, Maami na samu aiki.”
Aiki? A ina? Dama ka nema ne?
Kamfanin (Nafada & Sons). Ko (Nafada &
Families) ne ma oho.” Faruk ya fada
yana dariya cikin zolaya.
Kai kayi mana shiru da Allah.”
AZ, amma kamar kwangila ne haka fa ba
wani aikin dindindin bane.” Fa’iz ya yi
bayani, kamar yadda Umm Adiyya ta ba shi
shawara ya yi, bayan ya sameta yana
ba ta hakuri, yana kuka a jiya.
“To Allah ya yi jagora, idan ka dage ka sa
himma sai ka ga ka koma dindindin din ma
ai.” Haka dai aka shiga yi masa murna, shi
kuma dadinsa daya da Umm Akiyya ba
ta fadi abinda ya faru na asali ba, har ya janyo
samun aikin.
************
Ranar Juma’a ta gama shirinta tsab! Cikin wata
doguwar riga mai floral prints
(tambarin furanni), ta shirya Safiyya, tana za-
une a falon Abba tana jiran zuwan TJ.
Ne, sai ta ji tsayuwar mota, a zatonta TJ Din
ne ma. Don haka ta mike ta fito waje,
don ta gani, nan ta yi arangama da Yaya Zaid
yana sanye cikin bakar jamfa wanda
aka kawata shi da zare ruwan gwal ya yi masi-
far kyau, ya kafa hular da ta fi kama
da ruwan kasa mai sheki. Komawa ciki ta yi
saboda, ganin ba wanda take
tsammanin bane, sai da ya shigo gidan ta
gaishe shi.
Daidai lokacin motar TJ. Ta tsaya. Zaid yana
kallo ta sagala jakarta za ta fice, “Umm
Adiyyah.” Ya sa baki ya kirata. Daidai bakin
kofar ta juyo tana dubansa.
Ina za ki je?”
Yau tana ganin karfin hali, wai barawo da sal-
lama, “Unguwa.”
Na ga hakan, wace unguwa ki ke shirin zuwa
ke kadai da mutumin da ba
muharraminki ba?”
Idan ta ce za ta tanka ma, ta san wata kila ba
abinda za su fito daga bakinta. “Na
san da hakan, yanzun ma ai ba ni kadai zan fita
ba.”
Kallonsa ne ya koma kan Safiyyah. “Wannan
ce za tayi miki rakiya? Amma ina da
tabbacin Maami ba ta san da fitar nan ba.”
Idan ka na da matsala da fitata, ka rike tu-
nanin a kanka, saboda na yi niyyar fita na
san yadda kuma zan kare mutumci na. Gidan
Aunty Aisha za mu je.”
Me ya sa su Faruk ba za su kai shi ba, idan
sanin gida ne bai yi ba?”
Girgiza kai ta yi kawai, ta sa kai za ta wuce.
Ki tsaya akwai sakonki a mota.”
Bai sake kallonta ba, ya wuce wurin motar kai
tsaye, masu gadin ya yiwa ishara da
su zo su kwashi kayan zuwa ciki. Yana tsaye a
wurin yana ganin suna fitar da kayan
boot din motarsa ce ya ji muryar TJ. Na masa
sallama, murmushi ya sakar masa, ya
mika masa hannu suka yi Musabaha.
Yaya ayyuka?” Zaid ya tambaya a takaice.
Lafiya Alhamdulillah! ayyuka suna hannunku
ai.” Umm Adiyya kam dai ba ta ga
dalilin da zai sa su zama abokan juna ba, san-
nan dadin karawa Yaya Zaid katon din
cornflakes ya kawo mata, hade da sauran
tarkacen da gabaki daya idan ta duba
abinda take so ne.
Lalle Safiyya dole ta yi kiba, katon din corn-
flakes duk ita kadai?” TJ. Ya tambaya
yana murmushi.
Ai masu shan cornflakes din da yawa, wasu
ma addicts ne.” Zaid ya fada yana
kallon Umm Adiyya a fakaice.
TJ. Ya sani sarai me Zaid yake yi, don haka ya
ce, “Wata kila a da yanzu kam sun
samu waraka ai, ba ta shan cornflakes.”
Wa kenan?”
Sauran jama’ar gidan.”
Zaid ya dube shi yana murmushin gefe, “Trust
me, wasu ababen sun wuce gaban a
bar su. Wasu ababen bazamu iya rayuwa babu
su ba. Y awwa wannan ya tuna min,
ta ce za ku je gidan Aunty A’isha, yanzu ko na
ke da shirin zuwa, can din. Za mu iya
zuwa idan ba wani abu, sai ka ga gidan.”
Murmushi TJ. Ya yi, jikin sa ya dan so ya ba
shi wani abu, duk da iya son da yake yi
na kar ya kawo fassarar komai a ransa, ko ba
komai dan-uwan Umm Adiyya ne,
bayan kasancewarsa tsohon mijinta. Kuma ba
yau kadai zai gan shi ba, dole
mu’amala ta hada su a gaba, idan Allah ya sa
komai ya yiwu. Don haka dole ya koyi
zama da shi.
Okay, ba matsala.” Juyawa ya yi zai yi wa
Umm Adiyya bayani, ya ga ta tsume ta yi
tim! Ta koma cikin gida. Ta tsani cewa Yaya
Zaid ya santa ciki da bai har haka.
Tabbas, ta rage shan cornflakes sau dubu,
amma har yau tana da kwali daya a
wardrobe dinta a daki, cikin dare sai ta tashi ta
sha iya shanta. Wataran tana sha
tana kuka, wataran cikin shiru za ta shanye.
TJ. Ya girgiza kai, suka shiga motar Zaid din
suka kama hanya. A hanya suna hira
jefi-jefi kan sha’anin kasa. Kamar daga sama
Zaid ya ce, “Ka san da cewa ba zan
bar ka ba, muddin ka saka ta cikin kunci daidai
da rana daya ko?”
Ban fahimci a matsayin wa ka ke min magana
ba.” TJ ya fada lokacin da ya
Kankance idanunsa.
A matsayin Yayanta na ke fada maka, kar ma
ka bari na fara akan matsayina na
daya bangaren. Amma saboda adalci, zan fada
maka ka shirya samun wasu tsaiko,
ba ka tsammanin na bar maka ita haka kawai
ko?”
“Ina ga da ace akwai wani abu makamancin
hakan da ba ma wannan maganar a
yanzu, saboda ta kasance ta ka a wata gaba. Ka
yi sake da damar ka. Ina ga ko ka
tsaya ka ga iya yina ko kuma ka sameta, ta
fada maka abinda ba ka sani ba.”