UMM ADIYYAH CHAPTER 67 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 67 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 


suna motsi, suna kara a kewaya da shi.
Goshinta ne ya tattare cikin tunani.
A dai-dai lokacin abin ya fado mata. Da sauri
ta juya ta fita daga dakin, ba ta tsaya Www.bankinhausanovels.com.ng
inda kowa ke jira a waje ba, fita ta yi can farfa-
jiyar asibitin, ta gangara wurin da wasu
dan
shuke-shuke suke, ta yi zamanta akan dan
dakalin da ke gun.
************
Washegari Ummu da Mama suka taho duba jikin
Zaid, nan aka bar Umm Adiyya da
raba idanu. Ta rasa me yake mata dadi a
duniya, abin da ya rage mata kawai, shi ne ta ba

su dukkan girmawa, ta jira zuwa lokacin da za su
tafi, wanda take fata nan
kusa ne, duk da ta kan kira Mama jefi-jefi a
waya suna gaisawa, ba ta dai zuwa
sha’anin gida da ma wasu abubuwan.
Haka ta rinka buya kamar marar gaskiya, za a
je asibitin da ita, amma tana can
waje, sai an fito take shiga ta duba Yaya Zaid.
Ranar da ya cika kwanaki uku da yin hat-
sarinsa ne, ta shiga dakin da aka maida shi
bayan sun canza asibiti. Wasu ‘yan ofis dinsu
ne ta samu sun je gaishe shi, sai ko
Yaya Nazeef da ya zo duba shi, ganin jama’a
ya sa ta rakube daga gefe tana leko
shi, har sai da bakin da suka zo duka suka fita,
wannan ya sa Umm Adiyya ta tsaya
daga can nesa da gadon tana kallonsa daga
nan, da gani dauriya kawai yake yi.
Allah kadai ya san azabar da yake sha.
Idanunsa ne suka bude kadan yana kallonta,
da yadda ta rakube take lekensa daga
jikin bangon dakin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hannu ya sa ya yafitota. Bude idanu ta yi cikin
mamaki hade da nuna kanta.


“Yaya ki ke tsaye daga can?”
“Yaya Jikin naka?”
Da sauki, sai abinda ba a rasa ba.”
Alhamdulillah.”
“Ke kadai ki ka zo ne yau, ina escort dinki?”
Tura baki ta dan yi kadan hade da kifta
idanu ta san zolayarta yake yi, saboda jiya da
TJ. Ya zo, ita ma ta shigo da shi suka
gaisa.
Yaya, don Allah, ka daina yawan magana, ka
ga ka na bukatar hutu. Ka bawa kowa
tsoro, ka yi ka warke, ga su Mama duk sun
damu. Baffa kamar ya yi me sai sintiri
yake yi a filin asibitin nan shekaranjiya.”
Ke fa kin damu?” Ya tambaya yana kallon
cikin idanunta.
Sunkuyar da kanta ta yi kasa. “Na damu mana
Yaya Zaid. Yaya za ayi ba zan damu
ba?
“Ban sani ba ni ma, ke za ki fada min ai. Kin
canza Twinkle kin daina sona.”
Girgiza kai ta yi, tana kokarin danne hawayen
da take ji suna kona mata bayan
idanu. Ta san yana cikin ciwo, duk da yana kan
kkwayoyin dauke ciwo masu zafi, ba
Karamin buguwa ya yi ba. Har da su targade
an samu, inda Allah ya taimaka dai ba
karaya.
Kafin ta ce komai ne, ta ji ya yi ajiyar zuciya.
“Zo na fada miki wani abu.” Ta ga alama mag-
anin suna son sa shi barci daga
yanayin zurfin muryarsa. Matsawa ta yi ta za-
una a kujerar gaban gadon nasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Duk da ba kya tare da ni Adiyya, amma ina
so ki san cewa kullum zan zo miki a
tunaninki, zan zo miki a mafarkinki. Na san ba
ya hurumina na fada miki hakan,
amma dole na fitar da abinda ke raina.” Wani
irin murmushi ya yi mai sautin da yafi
kama da takaici “Afterall an riga an min
shaidar taurin kai da naci ko?” Ba abin da
take tunowa, sai lokacin da ta taba ce masa ya
mutu man, idan ya ga dama.
Hawayen da suke neman fita a idanunta
ne
suka gaza tsayuwa, duk iya dauriyarta.
Za ta mike ne ya ce, “Adiyyah, dole ki yi
hakuri, ki jure rayuwa babu ni, tunda kin
zabi hakan, ba yadda zan yi da ke. Abu daya
kawai za ki tuna; kodayaushe ki ka
gamu da wani mahaluki mai sonki a duniya, ki
san da cewa ni Zaid Abdur-Rahman
na so ki fiye da haka.”
Yaya
“Yaya Zaid…” Ta fara magana cikin
shesshekar kuka, amma ya katseta “Shhh… Ki
bar kuka haka nan, ban son ganin ZUBAR
KWALLAR Ki, bayan Twinkle dina ta
girma kuma meye hakan? Banda kuka!”
Wani abu ne ta ji ya murdo mata cikin kirjinta,
da can kasan cikinta, nan take ta san
cewa muddin Zaid ya tafi ya bar ta, to ita ma za
ta tafi ta bar gangar jikinta.
Da gudu ta tashi ta bar dakin, can falon tarban
marasa lafiya ta koma ta samu kujera
ta saka kuka iya karfinta, “Duk ni ce silar
tashin hankulan da suke cikin rayuwarmu.
Yaya Zaid, me ya kai ni neman saki a han-
nunka?
Sai meye don kayi min fin karfi? Ni na hanaka
kaina, maimakon ka koma rayuwarka
ta da, gwamma da kayi min hakan, sai meye,
don ba ka so ni a lokacin da na fi
bukatar ka so-ni ba? Na san dole akwai dalili
sai meye, don ban samu abin da na
ke so daga gareka ba na ‘ya’ yan da za su mana
addu’a bayan ran mu? Iyayenmu Www.bankinhausanovels.com.ng
suna tare da mu, kuma akwai gaba. Yanzu ga
abin da na jawo mana, wannan jinyar
mai wahalarwa ce, domin yanzu komai ya
kare. Na zama sanadin komai daya faru.”
Zaman mutum ta ji a gefen kujerarta, ta san ba
ita kadai bace, wannan ya sa ta yi
gaggawan neman natsuwarta, tana juyowa ta
hada ido da jajayen idanun TJ. Da
sauri ta mike za ta bar wurin. Amma ba ta yi
nasarar tafiya ba ya ce.
“Me ya sa Umm Adiyya? Me ya sa ki ka
rufeni kan wannan batun? Wannan ne
dalilin da ya sa ranar ki ka.. Na tambayeki ko
har yanzu ki na son shi, amma…”
kasa karasa maganar ya yi, ya shafo fuskarsa
cikin tsantsar tashin hankali.
Sauke hannayensa da zai yi ne, ya furta abin da
ya rikito mata duniyarta baki daya.
“Na janye batun aurenmu.”
Inna-Lillahi’ wa’ Inna-Ilaihir-raji’ un! Kawai ta
shiga furtawa, a take ta ji jikinta ya hau
bari.
Wani irin abu ne ta ji ya taso mata, wanda ba ta
san shi meye ba. Bakinta na rawa
hawaye face-face a fuskarta ta ce, “Ba ku da
daman wasa da rayuwata haka, ko
kadan. Ba ka ji dalilina na yin abinda na yi
ba.”
Akan me ya sa zan sa idanu ki na gushewa a
kan idanuna, ki na shirin aurena,
amma da sunan wani ki ke numfashi? Akan me
ya sa zan zamo sanadin raba zukata
biyu?”
Daga kanta ta yi tana kallon filin da ke
samansu ta yi, ‘yar dariyar takaici, “Shin cikin
ku akwai wanda ya taba tambayata abin da na
ke so? Shiru ta yi ta ji ko yana da
amsar tambayarta. “Babu, dukkanku kun sa
abu guda a gaba, yadda za ku nuna iya
soyayyarku gareni. Ko kuwa nuna iya kasawar
junanku. Ba ku kyauta min ba, yanzu
da ka yi wannan kalamin, ka na nufin ka
hakura da ni kenan ka yafe?”
Kau da kansa ya yi gefe guda, cikin dacin rai
da tsananin kuna. Saboda yana Allah
Allah ta bar wurin, kafin ya canza ra’ayinsa,
wanda ya dade yana juya al’amarin a Www.bankinhausanovels.com.ng
ransa, kan ya yanke wannan hukuncin.
Adiyya, Allah ya ba ki sa’a a rayuwa, ba zan
miki karya ba, ya yi min ciwo. kuma
Allah kadai ya san iyakar cutar da ke nan.” Ya
fada hade da shafa gurbin zuciyarsa.
Amma I have to let you go… for good. Nan
ne duka za mu samu natsuwarmu,
saboda koda ki na tare da ni, wani bangarenki
ba zai taba iya sona gabaki daya ba,
na dade da kula da hakan. Tabbas ba ma cikin
kaddarar juna ne…
Cikin kuka ta fice daga asibitin gaba daya ta
hadu da su Yaya Saadik da Adda
Asma, amma ba ta kula da kowannen su ba, ta
yi shigewarta.
Ba ta taba tsammanin dan Adam zai iya shiga
halin da take ciki na kunci ba a
wannan lokacin. Cak! Hawayen idanunta suka
kafe, tana so ma ta yi hawayen ko
zuciyarta za ta yi sanyi, amma abun ya gagara.
Koda ta hau titi tafiya kawai take yi, don ba ta
san inda ta dosa ba. Can kan kwanar
fita daga asibitin kawai ta sulale ta zauna kan
wani dan dakali.
**** ********
ARBA’IN DA BIYU
Kanta ne ta ji ya kulle, ta shiga rudani, shin
dama mace tana iya son mutane biyu a
lokaci daya, ko kuwa dai ita ce kanta yake
kwance? Ko me yake faruwa da ita? Tana jin
wani irin fizga, na radadin zuci da rashin nat-
suwa, da wani irin tsantsar bukatar ta
ji ta rayu a duk lokacin da ta tuna Yaya Zaid,
haka nan lokaci guda ta ji zafi da TJ.
Ya furta mata cewa ya fasa aurenta. Ko don ta
sa ran za ta aure shi ne, ta hakura da
Yaya Zaid?
Alakarta da Yaya Zaid cike take da rikita-
rikita, da fada da sanyaya zukata, da
samun rayuwa, wanda take jin kallo kadai
yana mata ta ji kafafunta suna motsi,
zuciyarta tana canza bugu.
A dayan bangaren alakarta da TJ. Ba abinda
ya kai shi samun natsuwa da lumana,
da jin cewa eh yanzu kam hankalinta a kwance
yake. Da kuma mafarkin samun
tsabtataciyar gobe.
A lokacin abin ya zo mata. Idanunta suka ware.
Tabbas soyayyarta da TJ. Ta samo asali ne da
nufin samun wani tsaro da take
tsoron rasawa idan tana tare da Yaya Zaid.
Abinda take ji wa TJ. Ya samo asali ne
da rashin son ta hana shi soyayyarta a karo na
biyu.
Bayan ya nuna mata wannan tsabtacecciyar
soyayyar, kafin ma aurenta na farko,
sannan yanzu duk da ta yi aure ta fito, ko
kadan soyayyarsa ba ta canza gareta ba.
Duk da yana da iyali, bai mance da ita ba, tab-
bas abinda take ji akan TJ. Ya ginu ne
kan tausayin kar ta karya masa zuciya a karo
na biyu.
Yanzu ta fahimci idan ta aure shi zai iya yi-
wuwa ta zo ta rasa kanta a cikin aurensu,
zai iya yiwuwa ya shafe… Kai ina, ba zai shafu
ba. Amma tabbas ta tsani kanta
yanzu da ta bari har ta fara amince masa, da
tun farko ta yi wannan nazarin ta Www.bankinhausanovels.com.ng
fahimci me take ciki da ba ta wahalar da shi a
karo na biyu ba, ko albarkacin yadda
yake sonta tsakani da Allah, bai cancanci ta
masa haka ba.
To amma ranar da Salisu ya zo mata da batun
Yaya Zaid zai yi aure, ranar ta yanke
hukuncin auren TJ. da karbar soyayyarsa. Idan
za ta fadawa kanta gaskiya ta yi ne
don ta nunawa Zaid ita ma za ta iya sake
rayuwa babu shi. Yanzu ga shi a shirmenta
ta kallafawa TJ. Rai, ya kuma ji sirrin zuci-
yarta.
Ga kuma Yaya Zaid… Me Yaya Zaid yake
ciki? Me yake nufi da kalaman da yake
fada mata? Hannu ta sa ta share hawayenta,
lokacin da ta hango mota a tsaye a
gefen inda take zaune.
Yaya Saadik ta hango a ciki, yana zaune kamar
bai san ma tana wurin ba, sai da
suka hada idanu ya bude mata kofar motar.
Tun yaushe yake wurin?
“Gida za ki koma ko cikin asibiti?”
Bayan hannunta ta sa ta goge hawayen hade da
daukar tissue din hannunta ta
mammana kan idanunta, tunda suka rabu da
Yaya Zaid, yau ce rana ta farko da ta ji
tausayi a cikin muryar dan-uwanta gareta.
“Zan je gida na huta kadan.”
Kai ya gyada ya tada motar, sai lokacin ta kula
da Asma’ da ke bayan motar da ta ji
muryar Maama na surutu tana kiranta,
“Mammu.”
Murmushi ta yi, wani dadi ya cika mata zu-
ciya, tamkar yadda take ji, duk lokacin da
ta ga yarinyar. Hannu ta sa ta karbeta tana
mata wasa. Ta matsar da nauyin da take
ji a cikin kirjinta. Ta ji dadi da cikin ‘yan-
uwanta babu wanda ya yi mata magana ko
ya nemi sanin me take ciki.
Suna zuwa gida, wanka ta yi sannan ta sa riga
da zanin atamfarta.
Asma’ na bin ta da kallo ne ta ce, “Meye?”
“Ki na lafiya kuwa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Eh, me ki ka gani?” Ta fada hancinta jazur!
“Kawai na ga yau ba ki sa doguwar riga bane,
amma ba wannan bane, me ya faru a
asibiti? Bayan kin fita, mun hadu da TJ. Ban yi
tsammanin ya ma kula da mu ba.
Ummu A, kwalla muka ga yana yi.”
Gabanta ne ya fadi. Jikin ‘yar-uwarta ta fada ta
ce, “Adda, cewa ya yi ya janye batun
aurenmu,”
“To! me ya faru har haka kuma?”
Nan ne ta fadawa Asma’ maganganun da ya
samu tana fada, “Na manta me na ke
cewa, amma dai wani abu ya ji, ba abinda ya
karya min zuciya, irin kallon na
yaudare shi da ya yi min. Adda I truly felt for
him, zai iya yiwuwa abinda na ke ji a
raina bai yi karfin da zai rikemu tare ya kai mu
har gaban abada ba, amma ba
yaudara bace. Yana da guri har cikin raina a
tare da ni. “Asma dai ajiyar zuci ta yi,
don ba ta fahimci canisancin da Umm Adiyya
take yi ba.
“Kin san irin yadda za ki ji, ki na son ka-
sancewa da mutum, amma kuma daya
da
zuciyarkin kuma tana ga za ki fi sukuni
waninsa? Ban san yadda zan fada ki gane
ba, zan iya kasancewa mai son kai a wannan
al’amarin, amma dukansu biyu ina
Sonsu.”
“Ummu A… Ya kamata ki fita daga rudanin da
ki ke ciki, abinda ki ke ji wa TJ.
Tausayi ne ba so ba, idan ma akwai so din, to
wancan tausayin ne ya bada filin ya
ginu, ki na addu’a ki na neman zabin Allah. TJ
na da matarsa da yarsa, ina ga barin
sa shi ya fi miki tunda har hakan ta kasance,
kar ki janyo masa asara biyu, shi bai
sameki ba, ko bayan kun yi aure, sannan za-
man lafiyar gidansa ya kau. Shin ki na
son hakan ta kasance a kansa?”
“Ban taba ganin mutum irinsa ba Adda, mu-
tum ne shi na hakika mai karamci.”
“Na sani, akwai wanda za ka ga ya cikata ko-
mai ka ke so a abokin rayuwa, amma
ba lalle bane haduwarku ya zamo maku
alkhairi ko kuma ya zamo ka samu abinda
ka ke nema daga rayuwa a wurinsa. Don haka
ku hakuran shi ya fi. Tunda Allah ya
sa ma ba su kai ga kawo goro ba, magana ce ta
baki aka yi tambayar abin ya zo da
sauki. To amma yaya batun Yaya Zaid, shi ya
ce wani abu ne?”
Gyada kanta ta yi, “Adda Asma’ na cutar da
mu, kafiya ba ta da amfani, azabar da
na sha tsawon lokaicn nan, shi ma hakan ya
sha, a tunanina ya hakura ne da ni,
randa zai yi hatsarin nan, ya fada min yana so
a maida aurenmu, lokacin ne na fada
masa maganar Uncle TJ ta je wurin Baffa, to
kin ga bayan nan kuma sai ga abinda
ya faru. Da wani abu ya same shi yaya zan yi
da rayuwata, ban nemi gafarar sa ba?”
“Shhhh! Ba komai, ya isa haka nan. Kin san
nafilolinkin nan da ki ke yi? Yanzu ki
tashi ki yi alwala ki yi raka’a biyu, za ki ji
sanyi a ranki. Allah sa abinda ya faru shi ya
fi miki alkhairi duniya da lahira.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Adda, Abba zai ce ina masu wasa da hankali
ne.”
“Kar ki damu, za mu hadu duka mu yi masu
bayani.”
Zaro idanu ta yi waje, “Ki na ga za su yarda
da… Ehm.. batun…”
Asma’ ta lumshe mata idanu, “Tashi ki je ki yi
alwala.”
Yadda ‘yar-uwartan ta fada, hakan ta yi. Ta
dauki Al-kur’ani ta yi karatu, bayan nan,
natsuwarta ya zo mata. Sai lokacin ta kalli wa-
yarta. Tana da missed calls da

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE