UMM ADIYYAH CHAPTER 68 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 68 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

sadonni. Ba ta ko bude su ba, ta kalli abincin

da Asma’ ta kawo masu.

“Adda abincin nan ban jin cin shi.”

“Ke kin koshi da love ko? Sauko ki ci, kafin ki

je ki fadi ayi komai ba ke.”

“Me din za ayi?”

“Tsaya tambayata, auren kuma fa da ke

“Tsaya

tahowa, asibiti za mu koma ki samu bawan

Allahn da ki ka bari a kwance, yana neman

mutuwa mana, saboda soyayyarki.

Abinda ki ka fada min dazu na game da ki na

ji ki na son kasancewa da mutum bla

bla bla. Ki je ki fada a inda yake da muhim-

manci.” Www.bankinhausanovels.com.ng 

Narai-narai! Da idanunta ta yi za ta fara mata

wasu hawayen. “Ina ga an samu

kuskure ne ki ka riga su Fa’iz zuwa duniya.

Komanki shagwaba da kuka. No wonder, ki ka

faye yaranta. Maza ci abinci ki je ki ga rabin

ranki, kafin mu sa ma miki gadon

asibiti a gefen nasa.”

Dariya ta yi ta kulle fuskarta cikin jin kunya.

“Adda Asma!”

*************
“Da gaske ni kam ba zan iya komawa yau ba, sai
dai nayi masa sako.”
“Ke bakauyiya ce Wallahi, idan za ki je ki
sauke katon kanki, ki fada masa abinda ki
ke ji, ki je ki fada masa.”
“Bai yi sauri ba? Dazu fa ya ce min yana so-
na, ko zan yi aure na san ya so ni fiye
da meye.
Kin ga ya hakura kenan ko?.
Ouch!”
Ta fada bayan Wani rankwashi mai rai da
lafiya, ya sauka a kanta. “Ba kyau
mugunta, Allah.”
“Ke wawiyar ina ce?”
“Kai Adda, ki daina fada don Allah.”
“Oya, tunda ba za ki je ba, ki na jin kunyarsu
Maami da Abba, daga waya ki kira shi.”
Tsareta ta yi da idanunta, tana jira ta ga ta
dauki wayar.
Sai da ta yi ringing hudu, sannan ya daga, tana
ga lokacin ne Fa’iz ko Faruk ya
mika masa wayar, don ba a bari a gangan shi,
saboda masu yawan kira gaisuwa an
fi so kuma ya huta.
“Assalamu-Alaikum…” Ya fada cikin sanyin
jiki, don har lokacin bai yarda ita take
kirarsa ba, haka nan kuma bai san me kiran ya
kunsa ba, bayan yadda ta fice daga
dakinsa na asibiti a guje.
“Umm Adiyyah, ki na kan layin?” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Wa’alaikumus-Salam, Noorie, ina nan.”
An dauki kusan sekon arba’in kafin ta sake jin
fitar sauti a wayar. “Don Allah nan
gaba ki bada gargadi, kar ki hada ni da bugun
Zuciya.”
Dariya ta yi tana share kwallarta. “Yaya
jikinka?”
“Yanzu na warke Twinkle. Yanzu na warke…”
Haka suka tsaya da waya a hannu sun
gaza cewa komai, sai numfashinsu da kukan
Umm Adiyya ke fita daga kowani
bangare.
“Ya kamata ki daina kukan haka nan ai, ko so
ki ke yi ki ji na taya ki?” Zuciyarta ce ta
amsa, yau ta ji murmushin Noorinta, lumshe
idanu ta yi ta bar dukkan abinda take ji
a lokacin ya ratsata da kyau. Sannan ta kashe
wayar.
Har dare ba ta jin kanta a kasa kamar mai
yawo a gajimare take jin kanta.
************
“Adda Asma na tsargu sosai, akan duk halin da
Uncle TJ Zai shiga yau. Ba karamar
barna na yi ba, ban san ko zai yafe min ba.”
“Kar ki damu, yana da kafadar da za ta rar-
rashe shi, a hankali zai warke. Da wuya
zuwa wurin. Zai dauki lokaci kan ya manta,
idan ma ya mantan kenan, amma zogin
zai tafi. Kar ki neme shi tukuna. Duk randa ya
sauka, ya huce, za ki gane. Amma kar
ki ce za ki damu kanki akan hakan.
Duk yadda ka so abu. Idan ba rabonka bane, ba
za ka taba samunsa ba. Haka abu
idan rabonka ne, ba wanda ya isa ya hanaka
samunsa. Ki ka yarda da wannan shi
kenan, sai ku samu saudin abin.”
Kai ta gyada, tana ji Adda Asma da Adda
Zubaida suka yi waya ta fada mata duk
abinda ake ciki.
Tana karbar wayar don su gaisa ne. Adda
Zubaida ta ce, “Kin ki dan gidanmu ko?”
“Ah Adda bayan ke har cikin ranki wa yayanki
ki ke yiwa Addu’a ni kadai ki ka bar ni
da dan gidanku.”
“Ki ji sharri za ki hada min gurmi. Allah sa
hakan ya fi alkhairi. Yaushe za ki dawo?”
“Hutuna fa da saura, yanzu idan mun koma
kam ai Thesis ne ya saura na karasa.”
“To Allah ya bada sa’a.”
“Ameen.”
****k *******
Washegari, Adda Asma’ ta share guri ta zuba
tagumi tana kallon ikon Allah. Gaba
daya dakin a haustine yake. “Kin san dai idan
kin gama ba za ki tafi ki bar ni da
gyaran daki ba ko? Don haka ki na yi ki na
nadewa Hajiya, oh ni, da ba ni da mijin
yiwa gayu da na ga kayan kuttu. Ummu A,
awanki daya a nan idan har yanzu baki
san me za ki saka ba, zan baki shawarar ki suri
duk abinda hannunki ya kai ki saka.
Ko Www.bankinhausanovels.com.ng 
kuma na dauki koma meye na baki ki
saka.”
“Uhm, yawwa na sani ma yanzu.” Da sauri ta
makale Adda Asma’ a wuyanta cikin
runguma tana tsalle, ta na fadin “Na goe, na
gode.” Ta kara komawa kan gadon ta
dauki wani leshi mai launin ruwan qahwa da
lilac, an yi masa Kayataccen dinki, ta
saka da siket dinsa ta kafa daurinta gangariya.
Ta karasa shirinta da maya fin da ya
shiga da kayan.
“Da kyau, wani sha’anin sai Ummu A ta koma
gidan Yaya Zaid.”
“Allah Adda Asma zan fadawa Maami.”
“Ai a wannan gaban ko Yayan ki ka fadawa
baki yi laifi ba. Allah Ya sanya alheri.”
****k *****
Ai kuwa tunda suka isa asibitin, idanun Zaid suna
kanta, yana mata murmushi jifa-
jifa, ba na komai bane kuwa, sai irin yadda ya
tuna wayarsu a jiyan, ji yake yi kamar
yana wani mafarki ne ma tukun. Sati daya
Likita ya dibar masu kan ya ce zai
sallamesu.
Can Wuse Fa’iz ya tattara ya koma jinyar Yal-
labai Yaya Zaid, har lokacin bai dai
gama sakewa ba, amma duk wani abinda zai sa
ya ji ya kyautatawa dan-uwan nasa,
to fa a guje yake yin shi, domin ba karamin
sa’a ya taka ba, da Allah ya azurta shi da
dan-uwa irin Zaid, wanda maimakon ya ture
shi, da ya kama shi da gagarumin laifi.
Sai ma janyo shi jiki da ya yi ya nuna masa
kuskurensa, ya dora shi a kan hanyar
gyara, uwa uba ga rufa masa asiri da ya yi.
Wannan ya sa kullum ya yi sallah, sai ya
roki Allah ya rufawa Yaya Zaid asiri duniya da
lahira kamar yadda ya rufa masu.
Ga shi yanzu ba wanda ya kai shi samun nat-
suwa, yanzu ya kara tabbatar da babu
abinda ya fi aikin halas kwanciyar hankali, ba
ka tare da taraddadin za a kama ka, ko
kuma wataran ka kwanta barci ya kaurace
maka.
“Fa’iz, ka fitar mana da mota za mu je gidan
Abba, zaman gidan nan ya isheni haka
nan.” Zaid ya fada da yammacin ranar Juma’a,
yana sanye da jamfarsa fara tas!
A hakikanin gaskiya Twinkle dinsa yake so ya
gani, tunda ya dawo daga asibiti bai
sa ta a idanu ba, a waya kawai suke magana.
Kafin su isa gidan, ya gama tsara duk abinda
ya dace ya yi a cikin satin, idan Allah
ya ba shi iko. Bai sanar da ita zuwansa ba, don
haka lokacin da Fa’iz ya ce ana
nemanta a falo, ta sauko ba ta taba tsammanin
ganin Yaya Zaid ba.
Tsayawa ta yi a falon ta kali Fa’iz, sannan ta
maida kallonta kan Zaid, numfashinta
ne ta ji ya tsaya, sai kuma ta zaro idanu kafin ta
ce, “Oh! Ahm… ina zuwa.” Ta fada ta koma ciki
da sauri, a kitchen ta buya ta gama maida num-
fashinta tukun, sannan ta
ware mayafin kanta ta rufe jikinta. Sannan ta
dau mintuna biyu kafin ta sake fitowa.
Zaid yana ganin ta fito, ya sakar mata da mur-
mushi ya girgiza kai. “Uh… Hajiya kar
ki manta a gidanmu ki ke.”
Kankance idanu ta yi ta ce, “To? Ko a ina
dinku na ke ma dai.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Dariyarsa ya gimtse, ya dan kau da kansa daga
kallonta, ya san ta takura da shi,
kodayake ya fada mata a gidan yake, ba wai
sun saba saka ko wane kaya bane su
yi zamansu a falon kasa da ke yawanci su kan
zo da abokai ga gidan cike da
samari, sun riga sun saba shiga ta mutumci,
amma ya rasa dalili hakan da ta yi na
nuna kunyarsa, ya ji ya Kara masa sonta. Take
ya ji kunyarta ya burge shi.
“Kallo na za ki tsaya yi, ko za ki zauna mu
gaisa da kyau.”
“Ya Salam! Abun ne yayi banbarakwai, mun
yi magana dazu. Ina wuni?” Kanta na
kasa ta fada.
“Lafiya amaryar Zaid.”
Runtse idanu ta yi ta ce, “Yaya ka fara tsoka-
nar ko?”
“Ni dai na dauka an min sabon ragon suna,
amma sai ayi ta min kwange ana lakaba
min Yaya.”
Mikewa ta yi kuma, “Ina zuwa.” Ta fada kafin
ta koma ciki, cikin kankanin lokaci, ta
shirgo abincin ranar da suka yi, ta kai masa kan
tebur da ruwan sha da su lemo, ta
tsaya tayi masa kunun semo mai dan karen
dadi. Shi dai sai bin ta yake yi da idanu.
“Bismillah,” Ta fada masa lokacin da ta kam-
mala, ta ja masa kujera daya a wurin cin
abincin.
“Yau na ga ikon Allah,”
“Na san yunwa ka ke ji, ga abinci ka ci, sai mu
gaisa da kyau.”
Kada kai ya yi, ya san bai isa ma ya ce a koshe
yake ba, bayan sun ci abinci da
Fa’iz, duk da bai kai wannan dadi ba, amma
Fa’iz ya jagwalgwala masu.
To na gode, amma idan ba so ki ke yi ki yi
dariyar dingishina ba, ki kawo mana nan
mu ci.”
Ba ta musa ba ta kawo masa, “Lallai yau ba
tashi kenan.” Ya fada yana mata
lallausar kallo, “Na gode.” Ya furta a hankali.
Ta zuba masa abincin kadan kamar
yadda ya bukata. Yana kai kununsa baki ya
lumshe idanu. “Ya Allah, I miss this.”
“Yanzu kam za ka sha har sai ka ture.”
Kallonta ya yi, ta kasan idanu, yana shan ku-
nunsa. “Ko? A zatona ba zai hau kaina
ba har abada.” Yanzu kam ba tantama, ta san
ba zancen kunu yake yi ba. Tsigar
jikinta ne ta ji ya tashi. Da sauri ta mike ta fara
kwashe kwanukan daya gama da su.
“Ni dai an kawo min abu, tun ban gama ba, ana
kwashewa.”
“Oh, yi hakuri, ban sani ba ai.”
“Haka ake yi ne? Kin ba ni abinci, ni ban ba ki
ba, na kyauta kenan?
Dariya ta yi, don ta dauka wani abin ne daban,
“Yanzu muka gama cin abinci.”
“To zauna mu yi hira.”
Sai da dai ta kwashe komai, sannan ta samu
natsuwva. Www.bankinhausanovels.com.ng 
“Ina son na gabatarwa su Abba da batunmu.”
Ya fada yana kallonta.
“Hmm! Allah ya kai mu.”
“Baki da matsala da hakan ko?”
Kai ta girgiza masa. Wani kasalallen murmushi
ya yi ya ce, “Twinkle talk to me. Ina
Son jin muryarki fiye da komai.”
“Ba matsala.”
“Ba abin bata lokaci bane, amma kafin nan, ina
so ni da ke mu yi magana ta fahimta.
Abubuwa sun faru da dama, mun samu sabani,
abinda ki ka kasance ki na so, ki ka
yarda da shi, ki ka amince da shi, ni kumna
nawa ra’ayin ya sabawa naki ra’ayin, haka
ke ma abin yake a wurinki. Mun gaza samun
fahimtarjuna, wanda ita ce babbar
matsalarmu tun farko, na zo da niyyar cire
wannan gibin a tsakaninmu ne yanzu.
Kin yanke hukunci wanda ya girgiza duni-
yarmu dukanmu, duk yadda na so abubuwa
su kasance, ba su zama haka ba, na so na zama
mai hakuri da tausasa kaina kan
alamarinki, amma na gaza sa kaina na yi
hakan. Ina so a karo na biyu, don Allah duk
lokacin da na bata miki rai, ko ki ka yi fushi da
ni, ki min magana ki fada min. Mu
zauna mu yi magana ta fahimta, ki fadi abinda
ke cikinki, ni ma na fadi nawa, mu samu
daidaituwa kan duk yadda za mu gudanar da
rayuwarmu.
Ba yadda za ayi, na san kuskurena, sai kin fada
min na kuma fahimci abinda ki ke
nufi,” Zaid ya fada yana dubanta.
“Kar ki kara kulle min abinda ki ke tunani ko
kuma ra’ayinki, ba na son wasa, ko
yawo da hankali. Besides, na ji dadi kwarai da
gaske da ki ka canza ra’ayinki game
da ni, duk da ban san yaya hakan ta faru ba.
Dan ba ni, labari na ji?” Ya karasa
maganar cikin zolaya.
“Ka ga ba na so. Allah, Yaya Zaid ka bari.”
“Ha’an to laifi na yi ne, ka ji min yarinya fa.
Idan ban tambaya ba, na sanki sarai, sai
ki yi fushi, ki ce na shareki ban nemi jin yadda
aka yi ba, na tambaya kuma wai ba
kya so don gulma.”
Rufe idanunta ta yi cikin jin kunya.
“Yaya Zaid..” Dagowa ya yi ya dubeta da
lausassan fararen idanunsa, masu
yankan da suke narka zuciya. “Na saba da
tsumammen Yaya Zaid, don Allah kar ka
yi min haka, kar ka sa na kara fadawa cikin
Soyayyarka.”
“Silly girl, that’s the plan (Niyyata kenan).”
***********
BABI NA ARBA’IN DA UKU
Murmushi ta yi, ta rausayar da idanunta, “Ka na
so ka ji ko yana aiki ne?”
“Da baya aiki da ba kya zaune anan, ki na
murza yatsunki, ki na satar kallon
idanuna.”
A razane ta dago idanunta “Hnn! Yaya Zaid,
an taba satan kallon cikin idanu ne?
Cikin ido kam aka kalla ai kai tsaye ne.”
“Kamar yaya? Ni dai na ganki ki na satar kallo,
kuma idan ba haka bane, ki yi mu
gani.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
Girgiza kanta ta yi, wai yau Yaya Zaid ne mai
wasa har da zolaya.
“Ina labarin Yasmeen?” Ita ma ai ba tayan
baya bace.
Tsuke fuskarsa ya yi, “Ke sai an fara zance na
arziki da ke, sai ki koma kuma ki na
abin nan.”
Dariya ta yi ma’ishinta. Zaid na jin sautin mur-
yarta kamar busar sarewa. “I missed
you, Twinkle.”
“Na sani, ka fada sau casa’in da tara.”
“Zan fada sau dubu ma, idan kin ce, ke dai kar
ki kara nesanta daga gareni.”
“Inshaa Allah, na daina. Kai ma Allah ya kara
maka hakuri da ni.”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE