UMM ADIYYAH CHAPTER 69 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 69 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Mun tsaya
Shiru ya yi yana kallonta, bayan ya koma cikin
kujerar ya zauna da kyau, “Uhh!
Zubaida ta ce min ki na zuwa ganin Doctor?”
Kai ta gyada masa a hankali, ba tare da ta dubi
idanunsa ba. Abinda ya fada ne na
gaba ya sa ta dago ta dube shi.
“Zan iya miki rakiya?” Ya fada yana magana
cikin muryarsa mai taushi da zurfi.
Murmushi ta yi ta ce, “Zan yi magana da Doc
tor din, idan ta amince next zuwa sai
mu je tare.”
“Na gode.” Daga jin muryarsa ya ji dadin
hakan.
Wannan ya nuna masa cewa ko ba komai,
yanzu wancan zancen ya wuce karkar a
wurinta, ta daina kullatarsa da wancan kalma
mai nauyi da ta shiga tsakaninsu.
Tashi suka yi domin gabatar da sallar Maga-
riba, ba ta fito ba har sai bayan issha. Ya
tabota a waya ya ce ta zo su yi sallama zai
wuce. Umm Adiyya ko duk inda ta gilma
kan idon Maami, sai ta ji kunya ta kamata.
Karfi da yaji Maami ta zamo surukarta.
Wani kallo take mata wanda yake nufin.
“Wa ya fada miki Borno gabas take?”
A bangaren Umm Adiyya kuwa, ko kadan ba
ta gajiya da kasancewa tare da Yaya Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaid, wannan ya sa take ta addu’ar Allah sa
Abba kar su jinkirta, yana ganin Baffa
kawai a daura masu aurensu, ai sun kwala
haka nan. An huta, har an gode Allah.
“Me ya sa ki ke murmushi ke kadai?” Ya tam-
baya lokacin da ya kula ta yi nisa a
tunaninta.
“Kawai ina farin-ciki ne.”
“Mashaa Allah. Finally. Da na zaci ko ni ma
zan bukaci ganin Likitar ne, hala ba na
ganin abinda yake gaba na, da sai na ce ban ji
kin ce komai ba, tun farkon abin
nan.”
“Ina cewa idan da ka saurara da kyau da ka ji.”
“Ai yanzu kam ni ma zan je koyon karatun
(Body Language) din nan, tunda bakin
gimbiyartawa nauyi ne gare shi, ba ta iya mag-
ana sai ta gama wahalar da ni.”
“Yaya Zaid…”
“Na’am…
“Dare fa yana yi.”
“Ke dai ki bar ni na kalleki ma’ishina, ina
ruwanki da daren, idan na ga dama a nan
zan kwana.”
Za ka sa Abba ya koramu a gidan nan ashe.”
“Da kuwa ya yi min dai-dai Wallahi, kin ga na
huta zuwa daukar amarya.” Ya fada,
fuskarsa ba alamar wasa, sai ma nuna cewan ta
gwada shi ta ga ikon Allah.
“Yaya Zaid!” Ta fada a shagwabe, murmushi
kawai ya yi yana kallonta. Kafin ya ce,
“To ki huta gajiya. Sai na dawo za ki ganni.”
“Allah Ya kiyaye hanya.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Ameen.” Ya fada bayan ya mike, don har
cikin zuciyarsa ji yake yi kamar ranar kar
ta kare ya samu abin da yake so. Amma kuma
tafiyar ta sa ma tana da
muhimmanci.
***** ********
Adda Sadiya ce ta tabe baki hade da yin kwafa,
bayan Zaid ya dasa aya, inda ya
tara ‘yan-uwansa kaf a dakin Mama ya yi masu
bayanin sabon al’amarin da yake
faruwa.
“Gaskiya ni dai idan za abi ta tawa, kawai a ba
su hakuri kawai a bari a yadda aka
sa din, ban san me ya sa ma Zaid din ya like
mata ba. Nan fa ta kalli idon Baffa ta
ce bata sonsa, aka zo dai aka yi rufa-rufa aka
lallaba aka yi auren nan, da bakinta ta
nemi saki, sannan ku na kallo, tunda ta tafi
yaushe ta taba tako gidan nan?”
“Adda Sadiya, da gaske ba laifinta bane, Baffa
Zubairu ne baya barin ta je ko nan da
can, iya kanta gidan Adda Zubaida, nan ma
don makaranta ne.” Maryam da ke
zaune a bakin gadon dakin ta sa baki.
“Haa! Ta yaro ba ta karko, gyara kam ai an
wuce lokacin tunda har duniya ta gama
sanin an rabun, za su zo su koma ne, kuma abu
ya sake baci har zumunci ya tabu,
dama tuni, yanzu a cikin dangi wasu suna bin
bayan gidan nan, wasu kuma bayan
Baffa Zubairu da ‘yarsa suke yi. Ga can Hajja
Ku, ina ce har yau fushi take yi da kai
kan batun, shi ne za ka rikitowa kanka sabuwar
damuwar ko?”
Zaid kam tagumi ya zuba da hannaye biyu,
yana bin yan-uwansan da idanu, Adda
Sadiya tana iso wannan gabar, ya sauke tagu-
minsa, ya shafe fuskarsa da tafukan
hannunsa, hade da sauke ajiyar zuciya.
Kun ga an taru a nan ne, ba don ayi wata
muhawara ko meye ba. Magana ya zo
maku da ita kan abinda ya riga ya yanke, ku
dai ko ku taya shi da addu’a, ko ku ja
bakinku ku yi shiru.” Mama ta fada hade da
gyara zamanta ta nade hannu a jikinta.
“Mama, na riga naa fada masu duka lokaci
kawai muke bukata, kuma lokacin nan ya
yi, daga ni har Ummu mun gane matsalolinmu,
kuma a shirye muke da mu gyara, ba
zan maku karya ba, duk wacce ma zan aura
baya ga Ummu, to zan cutar da ita ne
kawai, ita ce zabina, don haka Adda Sadiya ku
yi hakuri, amma ba zan iya canza
ra’ayina ba.”
“Oh, to kuma ka riga dama ka yanke
shawararka, meye amfanin tara mu a nan da
ka yi?” Murmushi ya yi mai sauti sannan ya ce,
“Maman Amira kenan. Dan-uwa ya
wuce gaban komai, addu’arku na ke bukata, sa-
boda ina wata gaba ce na sake
samun sabuwar rayuwa, zan so a ce a wannan
gaba mai mutukar muhimmanci
gareni ku na tare da ni duka, kamar ko yaushe,
a lokutan da na ke samun ci-gaba ko
jarrabawa ta rayuwa.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Fadeela da take ta mutsu-mutsu, don jin dadin
za a koma da Aunty Ummu A ne ta
ce, “Yaya Zaid yaushe ne auren?”
Daga idanu ya yi ya kalli Mama, ita ko ta dan
kau da kanta. Don haka ya ce “Ba a
tsayar ba tukun, amma ina so kafin koma meye
ne, don Allah dukanku ku dubi abin
nan da Sansanyar zuciya, yadda ku ke tunanin
Umm Adiyya ta bata min, haka ni ma
na saba mata sosai. Idan tana da laifi to Dan-
uwanku ma na da laifi.
Ba zan so kuma dayarku ta shiga irin halin da
Ummu ta shiga ba, sannan kuma mu
juya mata baya. Da fatan kun fahimci abinda
na ke nufi? Tana da rawar da take
takawa a rayuwata, kamar yadda kuma ku ke
da naku bangaren, dukkanku ku na da
muhimmanci gareni. Wannan ya sa na ga ya
dace mu fara, on the same page, cikin
fahimtar juna da dadin rai.” Kannen dai duk
sun yi tsam! Sun kuma amince banda
Zainab, sai kuma Adda Sadiya da ta tsume.
“Ina son ku fada min yadda ku ke so ayi.” Ya
fada, yana kallon Yar ta sa.
Ganin yadda kowa ya sa mata idanu,
yana
sauraronta ne ya sa ta ce, “To mu dai sai
dai mu yi addu’a kawai, tunda ka kallafa rai.”
Murmushi ya yi ya ce, “Na gode. Da fatan
kuma maganar za ta kare a nan. Ki yi
hakuri idan na bata miki rai. kawai ina so na
wanzar da abun da yake dai-dai ne
wannan karon, bare ma Ummu kam ai kan-
warki ce, ke mai kiranta ne ki mata fada,
idan kin ga ta yi ba dai-dai ba, koda ace ba ni
ne mijinta ba.”
“Na gane.” Ta fada a takaice, sannan ta tashi ta
bar dakin. Kallo ya bi kofar da shi
kafin ya sauke hucin numfashi.
************
Can yamma ana zaune ana maida maganar ne.
Amira ta ce, “Mama Wallahi Aunty
Ummu tana ji da Yaya Zaid, lokacin da na je
gunsu hutu, zai dawo daga tafiya, sai
kin ga hidimar da take masa, ga ta da kyauta.
Ga kyau. Mama don Allah ku bar su,
su koma.”
“Ke kuma manya na Magana, me ya sako
bakinki a cikin zance?” Adda Sadiya ta
doka mata harara.
Yi hakuri Mama, na ji kawai nayi maku
bayani ne, kar mu dau alhakinta.”
Adda Sadiya kam ta tsume fam! Don haushi
take ji yadda kaninta ya sha wahala
akan yar yarinyar. Yana Indiya da Amurka
kullum suka yi waya, za ta tsinkayi
damuwa a muryarsa, akwai randa ma cikin
dare ya kirata, ba karya kuka yake mata
kamar Karamin yaro, wai bai san inda zai sa
kansa ya ji dadi ba. Sannan yanzu tana
ji tana gani, ace ta bar shi idanu a rufe, ya sake
fadawa wannan halin bayan an
kwana biyu?
Anti ce ta shigo, ta samu ana yiwa Amira fada,
har ta nemi jin mafarin al’amarin.
Dariya ta yi ta ce, “Sadiya kenan, shi fa lamari
irin wannan na aure ki ka ce za ki
tada jijiyar wuya. Wallahi sai ki ga an zo ana
jin kunya. Ai tunda dai suka ce sun
sasanta kansu, to zance fa ya kare, sai dai fatan
zaman lafiya da samun zuria
dayyaba za ki masu, domin ki ka ce za ki kul-
laci abin a ranki, sai ki ga shi kansa dan-uwan
naki zai ji zafin kin ki abinda yake so. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ke kuma daga nan za ki ce ta raba ki da dan-
uwanki, wannan idan ba ayi sa’a ba,
sai ya dawo abin nan da ake kira gaba ta dan-
gin miji, ko dangin mata. Don haka abu
daya ya dace da ke a matsayinki na babba. Ki
ba su shawarar yadda za su gudanar
da rayuwar tasu, har ma zaman lafiyar ta dore
yadda ba a sake jin kansu ba, bayan
albarkar da zai yi ta bayyana. Sai kuma abu
mafi muhimanci mu bi su duka da
addu’a.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haka ne Anti, ni dama ba wai ba na son
Ummu ba ne, halin da yake shiga kawai na
ke jiye masa, idan aka samu akasi, aka koma
‘yar gidan jiya.”
“Inshaa Allah ba za a koma ba, bare tana da
yayyu irinku? Ai ku ne iyayen ma, sai
dai mu koma gefe, ku ba su shawara.”
Da lumana dai Anti ta tausashi zuciyar Adda
Sadiya har ma ta sake aka shiga hirar
yadda bikin zai kasance, da ranakun da za a
samu kowa na hutu, don a hadu ayi
zumunCi.