UMM ADIYYAH CHAPTER 75 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 75 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

Suna kammala wayar ne, ta fito falon Hajja

Ku, nan ta tarar ana shigewa daya dakin

da bokitai biyu masu tururi, sai kamshin da ke

tasowa daga hayakin.

“Hajja ce ta ce a shigo miki da shi, idan kin

shirya.” Mai aikin Hajja Ku ta fada.

“Idan na shirya me?”

Muryar Hajja Kubitto ta juyo tana cewa, “Yau

za a fara saka ki a lalle, ba kya dai

tsammanin mu kaiwa miji ke haka, ba gyara ba

kimtsi ko? Mu ba a mana haka ba,

don haka ba za mu sa idanu ayi miki haka ba.

Ga nan wadannan bokitan dafaffen

Lalle ne da ganyen magarya, masu kyau  Www.bankinhausanovels.com.ng da

tsafta, ki surka ga ruwan turaren muski

nan zan ba ki. Idan kin yi wankanki na sabulu,

to wannan ruwan kuma shi za ki yi

wanka da shi a karshe. Hakan kuma za ki yi na

tsawon kwse anaki uku, kafin ki bar nan

gidan.”

Umm Adiyya kam ware idanu ta yi da baki

tana kallon Hajja Ku, tana jin bayanan da

ke fita daga bakinta.
“Wannan kuma jan lalle ne sai da dare, Yalwa
za ta kunsa miki, na ga ku na yin
naku lallen na zamani mai fulawowi, idan shi
kuma ki ke so sai ki yi magana da su
Maryama su samo miki masu yi.”
“Hajja Ku, an shirya sa ranar auren ne, ki ke ta
shirinki ko kuma dama jira kawai ki
ke yi?”
“Ke ban son shirirta, ki wuce ki yi abinda aka
ce ki yi.”
Wanka ai ba zai hada fada ba, haka ta wuce
sumui-sumui ta karbi robar turaren
wankan, ta fada bandakin dakin da take.
Ai kuwa ita kanta ta san ta wanku, har zartsi
take yi, ta yi tas! Ga wani sansanyar
Kamshin da ke tashi a jikinta. Murmushi ta yi a
ranta ta ce, “Ka ji tsohuwa da
dabara.”
****k ********
na cewa wata kila a daura auren
Karshen satin nan, na ga kuma wancan karon,
ba ki samu damar yin hidima ba, na
san za ki so ki dan ajiye tarihi ke ma dai ace
lokacin bikinmu ne, abu kazan nan ya
faru.”
“Wai yaya ake yi ku yi ta abubuwa ne ban sani
ba? Www.bankinhausanovels.com.ng 
“No, nayi miki alkawarin wannan karon ba
Boye-boye, za mu kasance a cikin
kowane mataki na wannan shirin tare. nshaa
Allah.”
“Na gode, na kuma ji dadin hakan, Allah ya
saka maka da alkhairi.” Ta dan yi shiru
ne, sai ta fahimci abinda ya fada, “Noorie, jibi
ne fa ko gata cikin satin nan kam, yau
Laraba.”
“Ehem! Shi ne za ki daga hankalinki?”
“Gaskiya ban shirya ba, yaya za ayi wannan
satin ba za a canza ba’?”
Daure fuska ya yi tamkar tana wurin. “Ban
gane ba, shiri ne a gabanki ko kuma
kasancewarmu tare?”
“A’a ba haka bane, kai ma ka san ka na da
muhimmanci sosai a wurina, kawai dai
na ga lokaci ya kure ne.”
“Kar ki damu, idan ma ba zai yiwu ba, wani
sati sai na shirya mana liyafa a nan
Abuja, na abokai da dangin kusa.”
“Yawwa ina ga hakan da zai fi ma, na gode so-
sai. You’re the best.”
Murmushi ya yi, jin asalin tsagwaron farin-ciki
a muryarta.
Ba ta da niyyar yin wani babban taro, amma
dai abin farin-ciki, idan ya samu mutum
yana da kyau a tayaka addu’a, ka fada kuma
wa jama’a wannan ya sa ta wakilta
Takiyya da Maryam kanwar Zaid su tayata sa
nar da batun auren. Ba ta dai ce da
wani taro ba, saboda bai fada mata yadda
shirinsa zai kasance ba.
Ranar Asabar da safe aka daura auren Zaid
Abdur-Rahman Nafada da Umm Adiyya
Zubair, a karo na biyu. Sai dai sabanin karon
baya, wannan karon babu boye-boye,
kuma zukatan ma’auratan cike dam da dimbin
farin-ciki.
Ana gobe daurin auren aka zizarawa amaryaa
kitsonta yarfi sosai ya Kara fito da kyan
fuskarta, lalle ma haka ba dama ya yi jazur, ga
baki ma ya fito radau, inda ya samu
mazauni a lallausar farar fatar Umm Adiyya.
Ko ina ta gitta kuwa kamshi ke tashi, ka
na ganinta ka ga amarya ziryan.
Duk da ba wani abu za ayi a Gomben ba, baya
ga daurin aure, da yini a gidan Hajja
Ku, yawancin yan-uwansu sun hallara, daga
iyalan Goggo Amina zuwa gidan Baffa
Mai-Kano, har ma su Aunty Firdausi matar
Baffan Legas sun samu hidimar.
Abin nema ne ya samu, nan da nan aka hadu
aka tattauna tamkar yadda su kan yi
ko wace shekara.
Masu nasiha sun yiwa Amarya da Ango, masu
tsiya na masu duka dai, su kam ko a
jikinsu, ba abinda suke yi, sai tsantsar farin-
ciki da kuma godewa Allah. Www.bankinhausanovels.com.ng 
Maimuna ce ta shigo dakin da Umm Adiyya
take zaune da kawayenta, ta shiryu
cikin wasu kaya ruwan toka masu ado da
duwatsu ruwan hoda, an yiwa yadin aiki da
manyan fulawowi ruwan tokar da ya turu, ta yi
kyau sai sheki take yi irin dai na
amare.
“Gaskiya Ummu A. Yanzu kam ki na shiga ya
kamata da ‘yan uku za a yi
compensating dinmu lokacin da aka kwashe
ana mana cogel ko ba haka ba
Fatima?”
“Ai lissafin da muke mata kenan, kan ki shigo
tana yiwa Maryam tsiya, to abin ya
dawo kanta yanzu kam.”
Umm Adiyya na dariya ta ce, “Ban san ba ku
kaunata ba sai yau, dukkan ku yaushe
aka sallame ku daga (Labour Room), shi ne
don mugunta ni za ku min fatan samun
sau ukun azabarku ko?”
“Kar ki damu ki dauka akan daya za ki dauka
biyun Yaya Zaid zai tallafa miki.” Suka
kwashe da dariya gaba dayansu. Saudat din
Yaya Saadik ma tana cikinsu, wacce
ita ma fama take yi da tulelen cikinta, dama ita
da Adda Zubaida ake masu lissafin
wacce za ta riga wata.
Nafisa ce ta shigo dakin ta ce, “Oh! Ni Nafi,
ban taba ganin amarya mara kunya ba
irin Ummu A. Wato ke daga daura auren har
kin baje ki na kirga yawan ‘ya’yan da za
ki haifa, ga can Hajja Ku a cikin gida tana ta
sababi, wai yaran zamani abin mu sai
mu.”
Umm Adiyya, ta toshe baki, ta rufe idanu,
“Wallahi Adda Nafi, kin ga wadannan ne
suka sa ni a gaba tun dazu da tsiya, shi ne na
ke mayar masu da martani, ni kam ba
ruwana.”
“Kya dai ji da gulmarki. Ba a shigo maku da
abinci nan bane? Na ga ku na zazzaune
baki a bushe.”
“A’a Fadeela dai ta fita za ta yi Magana, ban
san inda ta makale ba ita ma.”
“Bari dai na bi sahu, ai rana ta yi ba za ayi ta
zama haka ba.” Bayan fitar Nafisa ne
aka shigo masu da kulolin abinci kala-kala da
ababen sha, dangin su kunu masu zafi
da masu sanyi, ga tsire jibgi-jibgi a wani
rusheshen tire, daya kwanon da ke rufe
kuma na silba, shake yake dam da kaji masu
suyan yaji. Abin dai ba dama, daya
bangaren kuma ga jan jolof, ga salad lafiyayye,
har da kananan fanke da kuma
kwanon Giz Dodo.
Shiri ne sosai aka yiwa amaryar da bakinta.
Maami da kanta ta tsaya ta ga komai ya
yi kyau, sannan aka kwasa aka aiko gidan Haj-
jan, kowaccensu ta debi abinda take
so. Har aka ragewa bakin baya da ba su iso ba.
Bayan sun gama cin abinci ne. Maryam ta
shigo dakin, kai tsaye ta wuce inda Umm
Adiyya take zaune ta jingina bayanta da jikin
gado, tana ta fara’a, sai walainiya takee
yi.
“Aunty Ummu…”
“Ke ban son shegantaka, idan za ki kirani da
sunana, ki kirani.” Www.bankinhausanovels.com.ng 
“An ki a kira din, tsaya ki ji sako aka ba ni.”
“Na me?” Umm Adiyya ta dubeta wani iri.
Kallon fuskarta, ya sa ta fahimci me take
son fada. “Sun dawo ne?” Ta tambaya tun kan
ta ji sakon.
“Eh, tun dazu ai. Yana so ku yi hoto ne, ya ce
ki same shi a falon Modibbo.”
Umm Adiyya ta yi shiru tana duban Maryam.
“To ai ga su Adda Nafisa ma dazu na ji
suna batun hoton, ya shigo kawai ayi gaba
daya, sai a huta lokaci guda.”
“Ke
Maryamn ce ta kwada mata harara, “Ke
bakauyiya ce, to ki tashi ki je ganinki yake Www.bankinhausanovels.com.ng 
son yi, haka kawai anyi awa uku da dauraa
maku aure, bai ko ji muryarki ba, kin kama
kin kashe waya, sannan kuma yanzu kin fara
wani Kabli da ba’adi, ki je jiranki yake yi
ku zanta.”
Ummu A. Ta harari Maryam, “Ke ‘yar sa ido
ce. Yanzu kaf jama’ar tsakar gidan nan
ta yaya za ayi na tsallake kowa na je wurinsa,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG 

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE