UMM ADIYYAH CHAPTER 76 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 76 BY AZIZA IDRIS GOMBE

               Www.bankinhausanovels.com.ng 

bayan an san ya shigo gidan?”

“Sai meye to? Don su wa aka taru? Abeg, tashi

mu je. Wallahi ko na kira Maami a

waya na ce tun yau kin fara gardama.”

“Ke kaska ce wasu lokutan, Allah.”

“Oho, dai aje a kula min da Yaya.” Maryamm

dai ba ta matsa ba, sai da Umm Adiyya

ta mike ta taka mata baya, suka fito zuwa

sashen Modibbo, wanda dole sai an ratsa

ta tsakar gidan a cimma bangaren, ai

tsiya kam ta sha kala-kala wai za ta

kuwa

ganin ango.

Kanta na kasa har suka isa kofar falon. Ya sha

gyara, kai ba za ka ce falon tsoho

bane wanda ya kai casa’in. Darduma ce a shim-

fide mai laushi, ga fulullunkan

tumtum an kawata wurin da su, sai kuma ku-

jrerun da suka zagaye falon, a bangare

guda kuwa takardunsa ne a jere reras a cikin

kwaba.

Tana shiga idanunta suka fada kansa, take ta ji

duniyar ta tsaya cak! Ta mance da

masu mata tsiya, ba ta jin komai ba ta ganin
kowa sai Zaid Abdur-Rahman, wanda
yake tsaye cikin babbar riga da ‘yar cikinta,
ruwan madara suna sheki kar-kar, da
hularsa ruwan kasa zanna bukar ta kafu a
kansa. Sai kamshi mai dadin shaka da ke
tashi a falon, wanda ya gauraye da kamshin
nata turarurrukan da nasa masu
nagarta.
Murmushi ya sakar mata wanda ya sa zuciyarta
bugawa, kamar ta yi gudun
fanfalaki. Sunkuyar da kanta ta yi cikin jin
kunya hade da yin nata lallausar
murmushin.
Motsi ta ji kafin ta ga kafafunsa, wanda ke
nuni da yana tsaye ne a gabanta daf,
dago kai ta yi ta juya ba ta ga inda Maryam ta
bace ba.
“Amaryar Zaid, kin yi kyau sosai, kamar a
sace, sai dai tunda ke tawa ce, ba bukatar
yin hakan yanzu.”
Rausayar da idanunta hade da girgiza kanta ta
yi, sannan ta dube shi.
“Ina wuni?” Idanunta suka lumshe, ganin ya
tsare ta da nasa idanun.
“Lafiya kalau, yaya fama da baki? Na zaci gi-
dan ba zai cika ba, kawai na zo na
samu ana ta hidima sosai.”
“Eh, mu ya mu ma ai za mu cika gidan bare..
Daga idanunta da ta yi ne, ta ga kallon da yake
mata, ya sa ta yi shiru. Ta hadiye
maganar da ta so fita daga bakinta.
Hannunsa ya sa ya riko nata a hankali, yana
murza ‘yatsunta. Ta kula da yadda
yake kallon zanen lallen da ke hannunta, wan-
nan ya tuna mata lallenta na auren
Adda Asma’ na hannu daya da rabi.
“Congratulations to us. (Ina taya mu murna)
Ya furta kasa-kasa.
Murmushi ta yi kumatunta suka loba, “Na
gode, Kai ma haka.” Ta maida idanunta
kan hannunta da ke cikin nasa.
“Na kasa yarda wai da gaske komai ya wuce..
Sai da ya tabbatar idanunsa na cikin nata, ya
daga hannunta a hankali ya kai bakin
sa ya sumbata.”Kin yarda yanzu, ko ki na
bukatar wata alamar?”
Da sauri Umm Adiyya ta shiga kifta idanu
tana jin bugun zuciyarta, cikin
kunnuwanta, tana kokarin janye hannunta ne
ta ce. “Ahm! Maryam ta ce ka na
kirana za mu yi hoto…”
Riko hannun ya yi ya ki sakewa. Kafin ta ce
wani abu kuma, ya sa daya hannunsa
ya ja ta jikin sa, ya rungumeta gaba daya,
kamshinsa ya dabaibayeta ko ta ina.
“Na jira har gaban abada domin aiwatar da
wannan.” Ajiyar zuciya ta ji ya yi.
Wannan ya sa ita ma ta lafe a jikinsa ba ta hana
shi ba, sai ma lumshe idanunta da ta yi, ta manta
rabon da ta samu irin wannan natsuwar.
Sun
dauki tsawon lokaci a
haka ba me cewa komai, kafin ta ji dirin mur-
yarsa ta cikin kirjinsa yana fita a hankali.
“Kin ci abinci?”
Kai ta gyada masa, “Ba za ki amsa ni ba?”
Girgiza kanta ta yi, haka nan ta ji ta gaza mag-
ana. Sai ma wani damshin hawaye da
ta ji a idanunta, ta san tana Magana, ba tantama
za ta iya yin kuka. Har yanzu dai
wannan dirin na sautin muryarsa na ratsata,
lokacin da ya yi dariya.
“Kar ki ce min kin rasa abin fadi daga simple
hug? Yaya za ayi kenan daga baya,
Uhm?” A hankali ya saketa ya riko kafadunta
yana kallon fuskarta.
“Noorie, ba na so, ka daina don Allah, ka koma
wurin bakinka. Na san ma yanzu
Modibbo zai shigo.”
“Hmm! Idan kin tambayeni, sai na ce ki na so,
bayan ma ko magana kin gagara yi?
Bare ma yau ranarmu ce, Modibbon ma ya
sani, jinki wa ya ba mu aron falon?” Ya
fada hade da daga mata gira. Da sauri ta sunne
kanta cikin jikin sa. Shi ko ya kara
rikota da kyau.
“Don haka ki tsaya sai na gama gaisawa da ke,
za mu yi koma wane irin hoto ne. Gaa
abinci can an ajiye, na zuba mana mu ci?”
Bude idanu ta yi tar, tana kallonsa, don ita har
ga Allah ta zaci wasa yake yi batun
abincin nan. Daman ana iya cin abinci a irin
wanann ranar? Ai ita ji ta yi ta koshi da
wasu abubuwa da suke mata motsi a cikinta.
Duk jeren abinci da a ka yi a dakin zaman
amaren, ita ba ta iya cin komai ba, bare
shi da yake da baki ya kuma fito wurin Recep-
tion.
“Ba ku ci komai bane a wurin Reception din?
Sai ka shigo abinka ka ci abinci ka bar
baki?”
“Wannan daban ne, kin ga laifina, idan na
shigo na bawa Twinkle dina abinci? Na
san ba natsuwa za ki yi ki ci ba, ban yi tsam-
manin Hajja Ku na da guzurin cornflakes
ba.”
“Ina da shi ai.”
Ware idanu ya yi ya ce, “Kar ki ce min a ak-
wati ki ka taho da cornflakes?”
“Noorie, a unguwarmu akwai shaguna.”
Ajiyar zuciya ya yi ya ce, “Da har kin fara sani
tunanin sanya hannun jari a NASCO
na ga alama suna da kasuwa sosai.”
Kifkifta gashin idanunta ta yi tana murmushi
hade da dan turo bakinta a shagwabe.
“Gwamma dai mu ci abincin nan, idan ba haka
ba nan za mu zauna aje ana ta
nemanmu.” Ta zaci zai bar ta ne ta sako
abincin, amma tana nan a gefensa ya rike
hannunta, da daya hannun ya zuba masu
abinci, bayan ya tambayeta abinda take
SO.
Sun shafe kusan minti ashirin wurin cin
abincin. Sai da aka kwankwasa kofar falon,
Zaid ya tashi ya bude da kansa. “Kai Malam
yaya haka, ka mance da jama’a a na ta
jiranka, ina makullin motarka? Fawzaan ya
mance…” Salisu nan da nan ya yi shiru,
ganin Umm Adiyya a zaune kan shimfidar da
suka gama cin abinci.
Fara’a ya sake ya dubi abokin sa, sannan ya
maida ganinsa ga Umm Adiyya, “A’a
amarya ce da girman kujerarta?”
“Ina wuni, Yaya Salisu?”
“Lafiya kalau, ai ban san ki na ciki ba, yaya
fama da jama’a?”
“Alhamdulillah,”
“To ya yi kyau. Allah ya tabbatar da alkhari ya
bada zaman lafiya.”
Juyawa ya yi ya dafa Zaid a kafada, kasa-kasa
ya ce, “Ka yi ka kammala ka fito.” Ya
juya gareta ya ce, “Ki yi hakuri za mu dan
aron angonki na minti kaddan.”
“A’a ba komai, yanzu ma dama zan shiga ciki.”
Zaid ya dubeta yana ware idanu, ita kuwa ta dan
kau da kai kamar ba ta san me yake yi ba, tana
gimtse dariyar da take
jin yi.
“Gwamma dai a tambaya, kar na je gidan
amarya a hanani tuwo.”
“An isa? Muna tare da su Aunty Mashkura a
ciki. Mun gode sosai da zumunci. Allah
ya saka da alkhairi.”
“Ameen-ameen.” Yana fada ya juya zai fice
tare da jaddadawa Zaid suna jiransa.
Umm Adiyya ta mike za ta bar falon ne ya ce,
“Me ki ke nufi?”
“Shiga zan yi. Yaya Salisu ya ce ana jiranka,
kuma da gaske mun dade cikin nan,
mu shiga mu yi hoton su Adda Nafisa duk suna
jira.”
Gyada mata kai ya yi, sannan ya matsa kusa da
ita, “Gobe za mu wuce Abuja
Inshaa Allah, sai ku karasa shirinku, ba sam-
mako za mu yi ba, saboda haka ki dauki
lokacinki.”
“Na zaci zan bi su Maami ne.”
“Eh, gidan Maami za ki, amma wannan ba shi
zai hana mu tafi a mota guda ba ai
ko?”
Kanta ta saddar kasa tana murmushi. Zaid ya
sa hannu ya shafa gefen fuskarta
hade da dago fuskar tata. Gefen kunnenta ya
sumbata a hankali, ya rada mata, “Ki
cewa Hajja Kubitto ina godiya.”
Kunya ta ji kamar ta nitse cikin kasa, ta juyya
da sauri. Nan ya bi bayanta zuwa cikin
gida, inda ya nemi mai daukar hoton ya shigoo
su dauka. Tuni suka samu yana ta
faman daukarsu a cikin gida.
Fatima ta ce, “Ana ta neman amarya ayi hoto,
ashe ango ne ya saceta. Yaya Zaid a
bar mana aronta na yau kadai.”
“Ku dai zumudinku da yawa yake, kuma sai
ku yi ta daukar hoton babu amaryar
dungurungum?”
“A’a mu yaushe za mu jiraku, abinku ba na
Kare ba, har dare ya yi hoton mu ya ki
yin kyau?”
Haka dai aka yi ta barkwanci. Da yamma taro
ya koma gidan Baffa, can ma hotunan
ake ta yi.
Sai dare Umm Adiyya ta koma gidan Abba, ta
kimtsa duk abubuwan da za ta bukata
na tafiya Abuja washegari. Lokacin da ta
kwanta ta gama yin laushi.
Da kyar ta bude idanunta da asuba. Nan ma
motsin su Adda Asma ne ya tasheta.
Kowa yana shirin komawa inda ya fito. Haka
ta daure ta tashi ta shirya cikin wata

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE