UMM ADIYYAH CHAPTER 77 BY AZIZA IDRIS GOMBE
UMM ADIYYAH CHAPTER 77 BY AZIZA IDRIS GOMBE
atamfa yruwan tsanwa mai ratsin ruwan
gahwa, kayan sun dinku sosai, telanta na
Bauchi aka bawa ya yi mata dinkunan express,
tunda aka sa lokacin auren a kure,
amma gaba daya ba na yarwa saboda yadda ya
kware a aikin sa.
Gidan Baffa suka je suka gaida su Mama tukun
na, nan suka samu wata hidimar
guda, an yi soye-soye da gashe-gashe, duk nan
tanadi ne na tafiya. Yanzu ta Www.bankinhausanovels.com.ng
karasa fahimtar inda Zaid ya saba da tanadin
abinci.
Anti ma da nata guzurin na turarurruka. Umma
ko kayan yaji da na su miya kaya
guda ta shake buhu da shi, duk wai nasu ne,
tamkar daga nan gidan za ta wuce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Akwai wasu bakin da suka zo za su koma Jos,
nan aka hada Zaid da su, shi ko ya
kumbura fuska, ya so su yi tafiyarsu, daga shi
sai matarsa, yanzu ba dama ya sake
ya yi hira da ita yadda yake so.
Umm Adiyya koda suka dauki hanya, idan
banda kokarin gimtse dariyarta ba abinda
ba. Sanye da rigar sama ta likitoci, numfashinta ne ta ji yana fita wani iri, a take
fuskarta ta yi dumi. Don na lokaci
Kankani ta mayar, kashe motar zai yi a tsakiyar
hanya, yadda ya kurawa labban
nata idanu.
“Yaya Zaid!” Ta fada da sauri, dai-dai lokacin
da ya shiga kwanar gabansu.
“Na san hanya ba za mu bata ba dai.”
“Saura kadan, ka yar da mu da gaske. Ka kalli
gabanka mu isa lafiya, son samu kar
mu mutu yanzu.” Idanunta sun yi narai-narai!
Don tsoro. Ba ta gama lafawa ba, ta ga
ya kwashesu a kwanar gaba ya yi U-turn yana
tafiya.
“Inshaa Allah ba yanzu ba. Duk da ko ta riske
mu, ina da yakinin zan tafi a mutumin
da ya fi kowa farin-ciki. Sai dai fatan Allah ya
gafarta mana kura-kuranmu.”
Ina! Ita kanta juyawar da yake yi, ya fi karfin
ta fahimci yaren da yake yi. Cikin
tsayayyen numfashi ta samu ta furta.
“Mantuwa ka yi?”
faffadar murmushi ta gaishesu, sannan ta yi
masu izinin zama.
Cikin muryarta a tsanake ta yi masu maraba,
“Finally, Mr Zaid is here, Ive heard a
lot about you actually. (Yau dai ga Mr. Zaid ya
zo, na samu labarinka sosai.)” Dr.
Astha ta fada tana murmushi, ganinta ya koma
kan Umm Adiyya wacce ta boye
fuskarta jikin kafadar Zaid, shi ko ya
dan
matse hannunta da ke cikin nasa, yana
fara’a shi ma.
Dr. Astha ta ci-gaba da magana a harshen tu-
ranci, “Na yi maku murna kwarai. Umm
Adiyya ta fada min yanzu kun koma tare. Na
ji dadin hakan kwarai.”
“Mun gode da kokarinki sosai, in fact, mun zoo
miki da I.V ma karshen wannan satin
akwai taro da za mu yi na murnar aurenmu, za
mu so kwarai ki samu halarta”
Dr. Astha ta karbi katin, tana dubawa cikin
fara’a. “Na ji dadi sosai, dole ma na zo
ai.”
cikin alakarku?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shiru ya yi na yan dakiku, sannan ya ce,
“Bayan abinda na rasa, na zo na sake
samu ba na tsammanin zan iya sake ganin
Umm Adiyya a cikin wani yanayi na
cutarwa bare har na haddasa mata hakan da
kaina. A’a, Likita ba zai sake faruwa
ba.”
“Ya yi kyau, na ji dadin jin hakan daga gareka.
Ummu has been an exceptional
patient, growing by the day. (Ummu ta kasance
marar lafiya mai karfin hali, kullum
akwai canji dangane da ita.) Inda don ta ni ne
da na dade da sallamarta, amma ina
so na tabbatar da cewa ko bayan ta sake aure,
ba za ta kara fuskantar matsalar
baya ba, saboda haka da wannan na ke so na ba
ka shawara, ka bi da ita a hankali
ko yaushe, cikin nuna nmata kulawa da soy-
ayya.
Ba zan iya cewa ta warke gaba daya ba, ammma
akwai wani mataki da ake isa a irin
wadannan cases din da za ace abin ya daina
dadin yadda ka tsaya mata, zan kuma
so kowane miji ko abokin rayuwa ya tsaya ya
kuma tallafawa matarsa a irin wannan
yanayin kamar yadda ka kwatanta. Allah ya
Kara maku son junanku.”
“Ameen. Sai dai Doctor, ina da tambaya…”
Umm Adiyya tana duba wayarta ne, ta ji karar
bude kofa. Zaid ne ya fito. “Kun
gama?”
“Eh, amma ki shiga ku karasa sai mu je ko?”
Kai ta gyada masa, sannan ta shiga ofishin.
Suna tafiya a mota ne, ta juyo ta dube shi,
yanzu ma idanunsa a kan nata suka
sauka. tana ganin yadda yake kallonta. “Meye?
I’m not fragile. (Ba zan karye ba dai)”
“Kin ji na yi magana ne? In fact, idan ma ak-
wai wani abu, yanzu kimarki ta karu
sOsai a idanuna, saboda na san irin juriyarki).”
Hannunta ya rike cikin nasa, suka ci-gaba da
tafiya cikin shiru. Har sai da suka kusa Www.bankinhausanovels.com.ng
duk wannan ba. Me ki ke ganin ya dace?”
“Hmm! Akwai abinda ke raina.”
Murmushi ya yi, sannan ya yanki kwanar
dama. “Ni ba za a fada min ba?”
“Za ka gani, kawai ba ni lambarsu.”
“To shi kenan, an yi an gama Hajiya,”
Juya bakinta ta yi ta gefe ta yi fari da idanunta,
don idan ya so tsokanarta hakan
yake kiranta.
“Na ga abinda ki ka yi.” Ya fada ba tare da ya
juyo ya kalleta ba.
“Ka sa min idanu Wallahi, ba daman na yi
kwakkwarar motsi sai ka ce wani abu.”
“Ina da damar na sa miki idanu son raina, na
kuma yi abinda na ke so, na fadi
abinda na ke so game da abinda na gani. Ka-
mar yanzu idan na so zan iya fada miki
cewa, pink lipstick yana miki kyau, ki rinka
sawa akai-akai. Ranar aurenmu kin yi
kyau sosai, haka yau ma…”
Umm Adiyya kam an bar ta da kyafta idanu da
zuciya mai gudun famfalaki,
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG