UMM ADIYYAH CHAPTER 78 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 78 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

“Eh! Sorry yanzu za mu dawo. Ki kwanta da

hankalinki, Twinkle.”

Ajiyar zuciya ta yi ta koma ta zauna a cikin ku-

jerar, amma ba wani zancen

kwanciyar hankali’ har yanzu cikinta juyi

yake yi. Daman ya iya wasa da mota haka?

Gefenta ta dan kalla a fakaice, ta ga a natse

yake tafiya ko a jikin sa, kamar ma ba

shi bane ya kusa wurgar da su a titi yanzu.

“Noorie, wane wata aka haife ni?”

Juyowa ya yi ya dubeta, goshinsa a tattare

cikin alamar rudani, “October, Me ya

faru?”

“Ba komai, kawai ina dubawa ne ko ka na

cikin hayyacinka.”

Dariya ya yi ya girgiza kai. “Za ki san wannan

cikin kankanin lokaci.”

Ba ta amsa masa ba, suka ci-gaba da tafiya,

tana kallon hanya hade da sake-saken

abubuwan da ya kamata ta yi tana komawa

gida, saboda shirin liyafar da za su yi

nan da kwanaki hudu.

Kallon gefen hanya take yi lokacin da suka
fara rage tafiya, suna shiga tsukun
unguwar, ta muskuta a kujerarta, suna tsayawa
a gaban gate, ta hango Rabilu. Sai a
lokacin tajuyo ta dubi Zaid.
“Me muke yi a nan?”
“Akwai abinda na tanadar miki, za ki sauko?”
Tsare shi ta yi da idanu, tana fatan ya fada
mata koma menene, ganin bai da niyyar
Magana, ya sa ta sauke ajiyar zuciya, da kansa
ya bude mata kofar motar.
“Ka san dai wannan baya cikin tsari ko?” Ta
fada suna tafe zuwa bakin kofar gidan.
“Ke kam ba gidanki ki ka zo ba?”
Shan gabansa ta yi bayan sun hau dan dan-
damalin kofar gidan nasu. (Porch).
“Eh! Duk da haka, idan aka ga mun dade fa?
Ko aka zaci wani abu ne ya same mu?
Gwamma dai na yi waya na ce mun bi wani
wuri ne… Ka ga Aunty A’isha na jirana
za mu je kasuwa… “
“Shut up, Adiyyah.” Ya fada dai-dai lokacin
da ya sa makulli a jikin kofar gidan, don haka ta
bar gabansa ta juya tana fuskantar kofar, tana jira
ya gama budewa.
“Me za ka nuna min?” Ta kasa hakura, ta sake
fada tana fuskantarsa.
Tura kofar gidan ya yi, inda kayataccen
mashigar gidan ya yi masu sallama.
“Mashaa Allah!” Abin da ya fito daga bakin
Umm Adiyya kenan, ta juyo ta dan dube
shi, shi kuwa ya sakar mata da murmushi.
Komai na cikin wurin ya canza, daga yadda ta
sansa lokaci na karshe da ta bar
gidan a baya. Yanzu komai ya koma Grey da
ruwan silba an kawata shi da madubi
da Katon tangaran a kusurwa guda, bai tsaya a
nan ba, ciki ya kara shiga, tana biye da shi kamar
yaro a gidan Zu. Tana shiga falonsa na ciki kuwa
ta juyo ta dube shi,
sannan ta ce.
“Gidanmu muka shigo?”
Kai ya gyada mata hade da lumshe mata
idanu, hannunta ya riko cikin nasa ya ja ta
barin jikin sa suka wuce gaba kadan, ya bude
mata kicin dinta. Da sauri ta saki
hannunsa, ta toshe baki cikin mamaki, sannan
ta sa ihun murna tana ta tsalle kamar
karamin yaro ya ga kayan wasa. Sai a lokacin
ta tuna da Balcony din falon sama.
“Don Allah ka ce min ba ka taba Balcony dina
ba, ka ce ba ka canza komai ba.”
“Me zai hana? Akwai wani abin da ba kya so a
taba ne?” Ya fada, bayan ya sani
sarai me take nufi. Amma ya ki ya ba ta amsa.
“A’a, a’a banda Balcony.” Da sauri ta juya ta
nufi hanyar sama, ya bi bayanta yana
dariya. Tana haki ta bude kofar falon da ya
bulla zuwa Balcony din. Tana budewa ta
ji bugun zuciyarta ya rubanya. Ba ta san me za
ta ce ba, hawaye ne kawai suka
shiga zarya a idanunta.
Juyawa kawai ta yi ta fada jikin sa ta rungume
shi.
“Na gode Noorie, na gode! Na gode!! Allah ya
biyaka, ya ba ka aljanna
madaukakiya. Allah ya bar min kai har iya
rayuwa duniya da lahira. Ya kuma sa ka fi
haka.”
Kanta ya sumbata.
“Kin san ana cewa mutane su kan mance soy-
ayyar mutum, su ci-gaba da rayuwa?
Za su iya rasa soyayyarsu, su kuma iya sake
samun wata? Adiyya ina tabbatar miki
hakan ba za ta taba iya faruwa da ni ba. Sa-
boda nan.” Ya sa hannunta a saman
kirjinsa ya shafa gurbin zuciyarsa, “Da ke
kadai yake bugawa. Ba zan iya jure
bayanke ba Twinkle.”
Idanunta ne suka ci-gaba da ZUBAR
KWALLA, ta kara shigewa jikin sa, tana jin
kamshinsa, kafin ta kai fuskarta kusa da shi
daf, ta sumbaci kasan wuyansa, “Ba sai
ka yi duka wannan ba ma, ina nan tare da kai
Inshaa Allah.”
Sun dade a wannan yanayin kafin ta sake shi.
Ta juya idanunta su kara komawa
kan dan filin da ke gabanta, wanda yake cike
da dimbin tarihi. Gabaki daya abinda
ta sani ne a wurin da kujerar lilonsu, zuwa
teburin gilas din da ke wurin da kujrerun
zama biyu da suka kewaye shi. Da ‘yan
Kananan fulawowin da suke makale jikin
karfen da ya kange Balcony din. Abin da ya
karu shi ne wani zane na rana tana
faduwa a magangararta. Ta kasa an rubuta:
“Twinkle you will forever be loved. Zaid”
Take kalamansa da ya fada mata lokacin da ya
fara fayyace mata sirrin zuciyarsa, a
daidai wannan wurin ne ya dawo mata sabo.
“Kin ga yadda ranar nan ta dauko gangarar
faduwa? Abinda ki ke min kenan Adiyya.
A hankali, son ki ya bi jiki na, ya dauke han-
kalina, har ya kai ban san lokacin da ya
gama mamayeni ba, ya kasance ko wane
motsina, ina yinsa ne tare da ke a cikin
raina, ko a sani na ko a rashin sani na, ko a
farke, ko a barci… I love you, my
Twinkle.” Kalamansa kenan a wancan lokacin.
Sama ta kalla idanunsu suka hadu, ta sakar
masa da mafi kyan murmushinta.
Hannunsu ya sake sargafewa cikin na juna.
Sannan suka fita daga falon, ta rinka bin
ko ina tana kallo tana santin sabon gyarar gi-
dan, tana farin-ciki. Zaid kuwa ita kawai
ya shiririce yana kallo.
“Uhh! Twinkle kin san duk yadda na ke son jin
muryarki yau, zan fi so ki yi shiru ko?
Goshinta ne ya tattare cikin rashin fahimtar
zancensa. Kafin ya yi murnmushi ganin
yanayin yadda fuskarta ta shiga rudani.
Daga mata gira ya yi ya ce, “Na gwammaci na
yi wannan.” Ba ta yi aune ba ta ji labbanta cikin
mafi lausasshiyar sumba, mai rikita kwakwalwa.
A hankali yake bi da
ita tamkar yana da duka lokacin duniya, domin
yin hakan. Riketa da ya yi ne yaji
jikinta na rawa, hannu ya sa ya tsayar da ita,
yadda yake so. Sai da ya yi iya isarsa,
ba don ya gama ba ya saketa, ya yi mata mur-
mushi hade da shafa gefen fuskarta.
Barka da dawowa, Twinkle.”
Lumshe idanunta ta yi ta sa goshinta a kan kir-
jinsa, hade da riko rigarsa cikin
hannunta don ta daidaitu, ji take yi kamar za ta
fadi Kasa, kafafunta rawa suke yi,
tamkar wata sabon shiga. Ta mance da
abubuwan da wannan mutumin kan iya
haddasa mata, a yau ba ta da buri irin ta yi ta
sawa iyayensu albarka da har suka
nuna masu sanin darajar juna, har suka amince
suka mayar masu da aurensu.
Domin tabbas ta sani wannan abin da yake
tsakaninsu, ba guguwar so bace, ba
muguwar alaka bace, tsagwaron kauna ce zal-
lah, Kauna daga Allah.
Kara kankame shi ta yi a jikinta, hawaye daya
na bin daya, ba ta san iya abinda
take ji ba a lokacin, ita dai ta san yanzu da takee
tare da shi, ta rayu. Numfashinta ya
kai mata rayuwa, yanzu ne ta cika Umm
Adiyyah, domin Zaid shi ne rayuwarta.
Da sauri ya sa hannu ya riko fuskarta, “Uhm-
uhm! Ba aikinki bane.”
Ba ta fahimci me yake nufi ba har sai da ya
sumbaci kasan idanunta daya bayan
daya yana share mata hawayenta. “Ko kin
manta na ce ki yi iya kukanki, amma aiki
na ne share miki hawayen?”
Maimaita abinda ya yi dazu ya yi a hankali ya
gangaro kan labbanta, “Kin san an ce
labban da hawaye ya sauka akai, sun fi komai
dadin dandano. Don me za ki goge
min abina?”
Umm Adiyya kam kunya ta ji kamar ta nutse
cikin kasa.
“Noorie, ka daina.” Hannaye ta yi saurin
sakawa ta rufe fuskarta, shi kuwa yana
murmushi, ya sa hannu ya zare nata daga
fuskarta.
“Na gode Umm Adiyya, kin kasance wata jigo
a rayuwata da ki ka nuna min fuskokin
rayuwa da dama, da dadi da ba dadi, na san ke
ce kawai don ni. Haka ni ma domin
ke. Ban san me za ki daukeni ba, idan na fada
miki wannan, amma ba na jin zan iya
misalta abinda na ke ji game da ke, fatana shi
ne zuwa yau kin san koma menene.
Yau a ofishin Doctor, na kara samun haske a
game da ko ke wace ce Adiyya, ba
lallai bane duniya ta gane ko ma ta yarda,
amma ki na daga cikin mata ma fi karfin
hali da juriya a duniya. Allah ya yi miki al-
barka, ya hada kanmu cikin aminci. Ya
kuma ba ni ikon kyautata miki, iya rayuwata
da ke da zuri’armu.”
“Ameen Noorie. Allah Ya yi maka jagora a
kan kudurinka, zan kasance a tare da kai
Inshaa Allah har ka cimma burinka. Gidanmu
ya yi kyau, amma na fi sonka.”
“Na sani, na san kuma dama sai na dan ingiza
ki kadan kafin ki fada.”
Ware idanu ta yi ta make hannunsa, “Ouch!
Ke, an fada miki ba kyau dukan miji
ko?”
Kara make daya gefen ta yi, “Ouch! Ina ga ba
a taba fada miki hannunki na da nauyi
kamar guduma bane, shi ya sa. Ki ji ki fa mu-
tum dan firit, sai aukin karfi.”
“Ka yiwa kanka ai kuwa,”
Ta fada hade da juya masa baya ta harde han-
nuwa a kirji, “Ka kai ni gidanmu.”
“Haba Twinkle, my babydoll, dan juyo mana,
na isa na kaiwa Maami ke a haka? Na

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE