UMM ADIYYAH CHAPTER 82 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
iya numfashi, bare magana. Wannan shi ne
babbar magana, wai dan sanda ya ga
gawar SOja.
A hankali ta juyo tana fuskantarsa, shi kuwa ya
hada kansa da nata, idanunsa a
lumshe, “Za ka ci abincin ko ka koshi?”
“Zan ci, amma kar ki matsa.” Yau tata ta
sameta.
“Noorie..” Ta fada a sanyaye, gaba daya jik-
inta ya mutu, “To yi hakuri, ka zauna sai na gama
da wuri na zo, ka ji?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kin ga alamar zan ji rarrashinki yanzu?” Ya
tambaya cikin wata raunanniyar murya.
Ba ta ga alama ba kam, hakan ya sa ta kunna
soket din ruwan zafin da ke gefensu
kawai ta ajiye masu kwanon kayan fulawa,
dangin su cake da dublan a gabansu
Kujerar kicin din ya zauna ya ja ta jikinsa,
suna cin kayan fulawan, suna shan
shayin, koda yake shi ke ba ta Tea din a baki.
“Uhm! Idan na yi motsi za ka iya kona mu.”
“Idan za ki yi motsi, sai ki yi magana, na
ajiye.”
“Da gaske ka ke jin yunwa.” Ta fada tamkar
sai yanzu ta fahimci me ya fada mata
tun dazu.
“Da kin dauka wasa ne?” Ya fada yana mur-
mushi kasa-kasa. Shiru ta yi tana cin
cupcake din hannunta, kafin daga sama ta ce
masa, “Ina son kicin din nan sosai, na
gode da ka kara gyara mana.” Ba don komai ta
yi maganar ba, sai don ta dan seta
balli-ballin da take ji a kwakwalwarta da zuci-
yarta da cikinta.
Zaid ya yi murmushi, “Ni ma ina sonsa sOsai,
saboda kkyawawanababen da suka
ta’allaka da shi, too many beautiful memories.
Na fi sonsa akan ko ina a gidan nan,
a nan ne kawai ba mu taba yin fada ba da ke.”
Dariya ta yi sosai, hakan ya girgiza shi har
ruwan zafin hannunsa ya dan zuba masu,
da sauri ta matsa. Zaid ya yi saurin ajiye kofin
hannunsa, yana duba ko ta kone.
“Na gaya maka, akwai hatsari, zama da ruwan
zafi a hannu.”
Maimakon ta ga ya yi magana, kallonta ya
tsaya yi. Daga karshe ya ce, “Kiyi hakuri,”
hade da sunkuyawa, ya hura saman hannunta,
inda ruwan zafin ya taba.
“Ki na jin zafi?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kifta idanu ta yi, “Baya zafi…” Ita ma dai
yanzu kam kawai ga ta nan ne. Ganin
maikon da idanunta suka yi, ya san hawaye ta
boye, ko kuma wani abin daban.
Hannu ya sa ya jawota cikin wata irin
runguma, mai haddasa bugun zuciya, ya
dauke numfashi, hakan ne ya faru da Ummuu
Adiyya, domin sai da nufashinta ya
sage, kafin ta san indaa kanta yake kuwa,
labbansa sun kai ga nata. Sun dauki lokaci
suna narka zukatan juna. Umm Adiyya kam ji
ta yi kamar ba ta ma duniyar nan.
Yana tsagaitawa ya ce, “Ina ga yanzu kam na
koshi, za mu shiga?”
Ya kula har lokacin numfashinta bai gama da
wowa ba, don haka yana dariya cikin
daukewar numfashi, ya ce “Just nod (ki girgiza
kai) idan eh ne.”
Kai ta daga masa, kafin ta sake wani tunani, ta
ji babu kafafunta a kasa. Ya dagata
cak! Daga inda take tsaye cikin rikonsa, ga
dumi ga kamshi mai juya kwakwalwa,
tuni ta narke a cikin rikonsa. Nan ma kawai
riketa ya yi.
“Ka san na kara nauyi ko?” Ta fada a shag-
wabe.
“Kar ki damu, za mu gyara wannan. Kwanan
nan na fi son ki fi haka nauyi.”
Dariya ta yi ta rufe idanunta cikin jin kunya.
Kansa na cikin sakon wuyanta yake tafiya, ita
kuwa idanunta a lumshe ta cusa kanta
a cikin jikin sa. A cikin shiru suke, amma ji
suke yi kamar sun isa wata duniyar,
saboda sukunin da zukatansu suke ciki.
A kan gadon dakin sa ya zaunar da ita, sannan
ya durkusa a gaban gadon ya
kwantar da kansa kan kafafunta hade da
rungumeta tsantsam!
“Noorie, Ka hau sama ka kwanta da kyau to.”
Hannunta na kansa tana shafa saman
gashinsa mai laushi, domin irin laushin gash-
inta da yaukin sa haka na Zaid yake.
Shi kuwa ji ya yi tamkar, idan ya bude idanu
mafarkin sa zai kare.
“I missed you so much Adiyyata, don Allah
kar ki sake barina, ban san yadda zan yi
ba.”
Kwantar da kanta ta yi a saman nasa ta rike shi
da kyau, daidai kunnensa ta ce, “Ba
inda zan je, Noorie, ina nan tare da kai.”
Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu, sannan ta ce.
Nima nayi kewarka, sosai, da
yawa, wataran, ina kuka na jika filona.”
“I know. (Na sani.)”
Tsayar da hannunta ta yi daga shafa kansa da
take yi, ta dago daga kwanciyar da ta
yi. “Yaya aka yi ka sani?” Ta fada hade da
zaro idanu. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Saboda ni ma haka ya sameni, na san kuma ba
zan kasance ni kadai cikin sonki
ba, Na yarda da mu, na yarda da son da muke
yiwa juna. Saboda haka na san, idan
ki ka tuna ni, ina jinki a jiki na, haka idan na
tuna ki, za ki ji ni a jikinki. Aladarmu na
da wannan karfin Adiyyah.”
Dago kansa ya yi yana kallonta, ta sa hannu ta
riko fuskarsa kamar za su shige
cikin juna, don kaunar da idanunsu ke fayy-
acewa. A hankali ta duka daidai fuskarsa,
ta sumbace shi, daga nan komai ya kwance
masa, ya gaza karasa dauriyarsa.
Ya yi nisa cikin shakar kamshinta daban-da-
ban ne, suka ji kamar magana kamar
motsi. Sai da suka tsaya cak! Sannan Umm
Adiyya ta zabura.
Kamar muryar.. “Safiyya ce, ta tashi tana
kuka!”
Zaid kam dagowa ya yi yana kallonta, kafin
abin da ta fada ya shiga kwadwalwarsa
ya fahimta, komawa ya yi ya kwanta a saman
filo hade da runtse idanunsa, da fitar
da hucin numfashi cikin jin takaici.
“Ina zuwa yanzu, don Allah, ka ji?’ Ta kalle shi
cikin ba shi haduri. Kai kawai ya
gyada mata, sannan ta tashi ta fita daga dakin.
Tana zuwa ta samu Safiyya na ta tsallara ihu,
tana An je Mamana.”
‘Shhh Sofy, yi shiru ko? Ga nan Aunty Ummu
za mu je Mama anjima, kin ji? Zo mu
kwanta mu yi barci, yanzu Baba zai zo ya kai
mu wurin Mama mu ga baby. Yawwa
Sofin Aunty Ummu.”
Ina! Yarinya kamar wacce aka karawa Vol-
ume, sai kyallara kara ta sake yi, har da
bori da birgima. Umm Adiyya sai ta koma ta
buga tagumi, kafin dabara ta fado mata,
“Za ki sha ruwa ne?”
“Uh’uh,” Ta fada cikin kuka.
“Ki na jin yunwa? Za ki ci abinci?” Nan ma taa
Kara sautin ihunta kamar na algaita.
“Me ki ke so to?”
“An je ma…mmana.” Umm Adiyya ta yi rar-
rashin duniyar nan, sun fi minti sha biyar a
haka, amma ta ki ta yi shiru, sai ta rage sauti
sai ta kara.
“Kaniyarki, kwanan nan ki ka yi kwanaki ba ki
ga Maman naki ba, ba a wurina ki ke
kwana ba? Za ki wani ce min Mama, ki min
shiru maza, mu kwanta ki yi barci.” Sai
da ta gama masifarta ne, sai ta tuna da yarinya
mai shekara biyu da dori take
magana.
Hannunta ta kama ta yi bandaki da ita, ta
kunna ruwan zafi, tai mata wanka ta sa
mata kayanta, sannan ta ce, “Hau gado mu yi
barci, anjima kadan zan kai ki da
kaina wurin Mama ko?”
Yarinyar tana ajiyar zuciya, ta gyada mata kai.
Don haka ta kwanta a gefenta tana
shafa kanta tana girgiza ta, har barci ya dauke
ta, sai ajiyar zuciya take yi saboda
ihun da ta sha. Www.bankinhausanovels.com.ng
A hankali ya shigo cikin dakin, yana kallonsu.
Walid na kwance kan shimfidar da
Umm Adiyya ta yi masa da barguna Umm
Adiyya kuma tana kwance da Safiyya a
jikinta, hannunta alamar tana girgiza yarinyar
ta yi barci.
Zuciyarsa ce ya ji ta matse wuri guda, bai taba
ganin abu mafi kyau ba irin haka.
Ganin Umm Adiyya tare da yara, nan take ya
ji yana fatan Allah ya nuna masa ranar
da zai ga yaransa da Ummu haka, tana kula da
su, tana nuna masu kauna.
Dukawa ya yi ya sumbaci kanta, hade da rufe
su da mayafi ya gyara setin AC.
Lokacin Umm Adiyya ta motsa cikin barcinta,
hakan ya sa ya dan saurara kar ya
tashe ta. Bai fice a dakin ba. Kujerar dakin
doguwa ita ya je ya kwanta a kai, yana
kallon su, ya yi addu’o’insa a nan ya kwanta,
koda ace wani yaron zai sake tashi,
baya son ta katse barcinta, don ya riga ya sani
a gajiye take likis!
Kiran sallah a kunnensa, don haka yana tashi,
ya taba Umm Adiyya. Don kar ta
makara. Da ya yi sallah a masallaci, dakin sa
ya shige don ya samu barci sosai, don
jiya barcinsa ragegge ne.
*******x***
“Ina kwana?” Sansanyar muryar Umm Adiyya ta
fada. A hankali ya bude idanunsa
suka sauka a kanta, lallausar fatarta mai sheki
ne ya dauki idanunsa, kafin su koma
kan fuskarta da ke cike da annuri ga lobawar
kumatunta, sun bayyana a dalilin
fara’ar da ke fuskata.
Murmushi ya yi mata, ya mika mata hannu ala-
mar ta isa gare shi. Sai dai maimakoon
hakan, make kafadarta ta yi ta ajiye masa
madaidaicin kofin tangaran mai fadi a kan
durowar gefen gado.
“Me ya sa ki ka kawo Tea yanzu?”
“Saboda lokacin da ya kamata a tashi kenan.”
Gaskiya wannan coge ne, ki zo mu kwanta,
ban yi barci ba jiya sam, yaran nan…
Aww.”
Ya fada yana riko kansa da ya ji ya masa
nauyi.
Murmushi ta yi, ta ajiye masa tablet din ciwon
kan a gefen kofin shayinsa, “Ka tashi
kar ka makara, ka sa ‘yan ofis su lika min su ce
daga aurenka da sati guda, ka fara
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG