UMM ADIYYAH CHAPTER 83 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 83 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

lattin ofis.”

Harararta ya yi, “Yaya Za ayi ki ce na je ofis

yau?” Hannunta ya riko ya zaunar da ita a

gefensa hade da tashi ya jinginu a jikin allon

gadon. “Yau ne ranar da zan fara

zama da ke, lokacinki ne, ba zan raba shi da

kowa ba kuma. Don haka ki zo ke maa

ki yi zamanki, ko kuma bari na shirya, sai na

fito. Amma ba zuwa wurin aiki ba dai

yau ba kam. Haba ai aka ganni a gun aiki yau,

sai ace ba ki yi sa’ar miji ba.”

Umm Adiyya tana dariya ta ce. “Kowa ya gani

ya sani ai ba na kuma bukatar

mutane su jaddada min komai.”

“Aha, na san dai ba haka kawai na zama ad-

dicted to you ba.” Ya fada yana

shinshinan wani sabon kamshin da ya jiyo a

bayan kunnenta.

“Ka bari,”

“Wannan meye sunansa?”

Lumshe idanu ta yi, “Nafhatul ad-deeb.”

“Hmm! Ina sonshi.”

“Da gaske za ka sa na makara abin karyawa,
yanzu yaran nan idan suka tashi ba su
samu abinci ba, daga ni har kai sai mun rasa
yadda za mu yi. Ga shi za mu wuce
asibiti.”
“Ni ban taba ganin rashin gata ma irin wannan
ba, yaushe aka taba kai yara gidan
amarya tare da amarya?”
“Ana yi idan aka ga irinka ne angon, bai da
sassauci, besides, wa yake tuk1? Wa ya
ce a bar su sai gobe?”
“Allah ya shiryi evil mind dinki. Wai irin ni
zan dan yi kara din nan, na zaci ke ma
Halin Girman gareki, za ki dan mun kara, ki
daga kafa sai na sha mamaki.”
“Oh, yanzu kuma ni ce mai laifi kenan. Don
Allah sakeni na tashi, ka ji?” Ta fada
tana kanKance idanu hade da kifta su.
“Oh, Adiyya. Ina sonki da yawa, ba na son ki
kara yi min nisa, kar ki bari na kara
rasa ki a gefena, koda na dakika ne. Domin na
dade ina nemanki, yanzu da na
same ki kuma ba zan bari komai ya shiga
tsakaninmu ba, koda kuwa ni kaina ne. I
love you, my Twinkle.”
Wani irin dadi ne ya kara ratsa ta, ta kara
shige masa cikin rikonsa.
“Ina sonka fiye da yadda ka ke sona, sau
malala gashin saniya.”
Dadi ne ya cika masa rai, amma ya daga mata
gira daya, hade da cewa. “Kamar da
gaske, a nuna min.” Hakoranta ta sa ta rike
lebenta na Kasa tana murmushi, kafin
ya yi aune wani zafi ya ziyarce shi a yatsarsa.
Sai lokacin ta kwashe da dariya, bin ta
ya yi da kallo ya ga kofin shayi a hannunta.
“Yau idan ki ka shiga hannuna yarinya, ki san
da cewa ba mai kwatarki. Ki na wasa
da wuta, ki san da cewa tabbas za ki kone.”
Cikin dariya ta fice daga dakin, kicin ta shiga
ta duba abubuwan da akwai. Ta samu
ya sayi komai na amfanin gida an jere su tas!
Ta san aikin Rabilu ne jeren, don koda
can ya kan shigo da sayayya idan Zaid ya yi,
ya san ma’adanar abubuwan store da
kicin. Yanzu sai ta ji tana kewar Innayo, da
farkon barinta gidan Zaid tana tare da su
a wurin Maami kafin ta zo ta je gida, yanzu
watanninta biyu da tafiya. Tana ga za ta
nemi ta dawo mata su yi zamansu kawai. Don
ta riga ta saba tana nan din.
Motsi ta ji a bayanta. Ta juya ta ga Safiyya na
mutsuke idanu. “Oh Baby Sofy, wa ya
sauko da ke daga sama?”
“Aunty Mammu, an ci?”
“An tashi da yunwa ne?”
Kai ta daga mata, don haka ta debi dafaffen
dankalin da ta yi ta hada da kwai da
kuma ruwan tataccen lemo da ta matse da
safen. Daukarta ta yi ta ce, “Mu je mu
wanke baki da fuska to, sai Sofy ta ci abinci
ko?”
Murmushi yarinyar ta yi mata, nan take ta ji
zuciyarta ta dagargaje don so. Tana son
yara kamar za ta sace, idan ta gani. Musamman
yaran yayyinta da take jinsu kamar
nata, ba ma idan suka yi mata dariya, komansu
gwanin sha’awa.
Kujera ta ja ta dora ta a kai, sannan ta shiga ba
ta abincin. Ba su gama ba. Walid ya
shigo kicin din da sallamarsa.
“Assalamu-Alaikum a’adkhul?”
Abin ya bawa Umm Adiyya sha’awa, ya kuma
ba ta dariya, don haka ta ce. “Udkhul.”
Ya shigo, ya gaisheta, sannan ya zauna yana
kallonsu har da yin taguminsa.
“Kai ba za ka ci bane?”
“Aunty Ummu ba ki ba ni ba to ai.” Dariya ta
yi sosai, sannan ta ce “To bari na ba ka.”
Ta zuba masa abincin, amma sai ta kula da bai
taba komai ba, taguminsa daya ya yi
nan yana wasa da cokalinsa,
“Ba za ka ci bane?”
Kai ya gyada mata a hankali. “Me ka ke so ka
ci?”
“Cornflakes.”
Dariya ta ji a bayansu ta juya, ta ga Zaid ya
shirya cikin Jamfa fara kar! Da hula fara
da baka, sai agogo na silba a hannunsa, ya yi
masifar kyau har da kyar ta iya dauke
idanunta daga kansa. Wani abu ta hadiya ta
kawar da kanta.
“Yaro ka yi mummunar gado, sai dai na ce Al
lah ya kawo maka sauki.” Yana dariya
ya ci-gaba da cewa “A sako da ni, ni ma yau
shi zan sha.”
“Noorie…” Ta fada cikin tsumewa.
Yana dariya ya ce “Meye? Walid ka ga An-
tinka ko? Wai za ta mana rowar CF dinta.”
“Ga abun karyawa fa na yi, ba za ku sha ba,
abincin gaske za ku ci.”
“Ka ji yau kuma wai CF, ba abincin gaske
bane.” Ya fada hade da tabe bakin sa.
“To a ba mu duka za mu ci.” Haka ta zuba
masu, tana kallo suka yi tseren cinyewa.
Har Safiyya ta nemi kari.
Sai da suka shafe awa daya a shiririce, sannan
suka fice zuwa asibiti, don ganin
Adda Zubaida, daga can za su wuce su ga
Aunty Saudat.
** ********
Can suka wuni tsakanin asibiti da gidan Abba.
Sai zuwa barka ake yi kamar mutane
suna jira, bare wadanda suka zo Walima su
Maryam da Adda Sadiya, duk suna nan
ba su tafi ba, sai da aka ga jariran.
An sa masu sunansu, daga lokacin. Adda
Zubaida ta samu Abbanta, Zubair. Yayin
da Maami ta sake yin mai suna a wurin Yaya
Saadik. Za a kirata Maama ita ma.
To yaya za a gane wace Maama ce, duka
sunansu daya?” Faruk ya tambaya.
“Sai ace Maama karama da Maama babba.”
“A dai zaba mata wani sunan, bai fi ba?”
Faruk ya fada, “Mu za ku zo ku na rudawa, mu
fara mance sunan ‘ya’yanku.”
“Sannu Baba.” Asma’ ta fada cikin gatse tana
hararar sa.
“Mai da wukar, kar azo ne gaba kun yi yara da
yawa azo ana cewa ‘Uncle Faruk bai
gane wace Maama bace, ta gaishe shi, kin san
sha’ani na girma.”
“Fita a nan don Allah. Ni ban ga Fa’iz ba.”
“Ina za ki ga Fa’iz yana can AZ, sun cilla shi
aiki da safe ya tafi Kano.”
“Kai ma da za ka yi abin kai da ka samu, aikin
yin ai.” Umm Adiyya ta fada.
“Wa, ni ai komai seti za a ban, da aikin da
matar duka gaba daya.”
“Allah ya shiryeka to, yanzu kuma auren jari
za ka je yi kenan.”
“A’a ba haka sunansa ba, auren ‘convenience
ake kiransa. Ta samu kyakkyawar
kamili irina, ni kuma na sameta da white collar
job daga Babanta.”
“Kama yi shiru tun kan Abba ya ji batun nan
daga bakinka.” Asma ta fada.
“Adda Ummu ba gaskiya bane? Yanzu idan ba
ka aiki da wani shell ko NNPC ko
wani National Assembly, ka na zuwa gun
yarinya sai ta fara maka gani-gani,
Musamman ‘yan matan Abujan nan. Amma
idan ta dan ga hadadde fes, hakan nan
ta dan mato maka shi kenan, sai ka kaiwa
Baba CV dinka. A wuce wurin.”
“Kai
ina labarin yarinyar da ka je ka yiwa
kanka tambaya?”
“Tana nan, ina aunawa ne, ko za a je da ita, na
ga ta fara wani jan aji ne, tana ga
kamar ba zan iya hakura ba.”
Tsaki Umm Adiyya ta yi, “Idan ka je kar ka
kira sunan gidan nan, don mu za ka
zubarwa da aji. Ka ji wani zance a nan.”
“Kwantar da hankalinki ‘yar uwa, ni da ki ke
ganina, ba zan yi aure ba, sai inda aka
darajani da asalina, ba a raina min abinda zan
iya ba. Yanzu haka wani abu yana
clicking da N-Zuhair, daga baya zan ba ku
bayani na fi son komai ya kammalu ne za
ku ji bayani. Auren gida zan yi kuma.”
Ware idanu suka yi suna kallonsa.
“Cabdijam! Duk yadda kowa ya sanka a dangi,
ban yi tsammanin akwai mai dauka
ba ka dai kara gaba.” Umm Adiyya ta fada,
“Ikon Allah naka ma ba su yi maka shaida ba,
yaya ku ke tsammanin a min a waje,
Allah sarki Umaru bawan Allah.”
Asma’ da Ummu suka kalli juna, suka girgiza
kai.
“Kai tashi ka fita ka sa mutane a gaba da surutu
kamar mace.” Maami ta fada
lokacin da ta shigo dakin. Ba shiri ya mike,
Saudat na masa dariya.
“Kin ci abincin kuwa?” Maami ta tambaya tana
duba kwanonin da aka jero na Mai-
Jegon.
“Na ci Maami.”
“Ah’ah wannan kam ba abinda ki ka ci. Ummnu
miko plate din can a kara mata,
abinci ki ke bukata yanzu ki ci, ki samu karfin
jikinki, idan ba haka ba, daga haka
Karfinki zai kare. Ga shayarwa dole ki maida
hankali da abinci.”
Saudah dai ba yadda ta iya, haka aka karo
mata nama himili guda na farfesu, “Tea
za a hada miki ko kunu?”
Umm Adiyya ta tambaya, Saudat tana mata
ido akan ta bari. Maami ta kama su.
“Oh, mune ba kya so mu ba ki ko? Bari mijin
naki ya zo, sai ki sha,” Ai da wuri

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE