UMM ADIYYAH CHAPTER 85 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
Washegari da safe ya tashi da shirin zuwa
wurin aiki. Ta tashi latti wannan ya sa ta
yi tunanin yin wanka tukun, saboda ba ta cika
son shiga kicin ba ta shirya ba. Ta
dade da sanin kuma Yaya Zaid baya son mu-
tum ya tashi busu-busu ya wuce
kitchen, amma kallon agogon da ta yi, ya sa ta
canza shawara ta shirya cikin
doguwar riga, sannan ta sauka ta hada masa
abincinsa.
Ta koma sama don ta yi wanka ne, ta tsaya ga-
ban kwabanta don cire kayan da za ta
sa, lokacin Zaid ya shigo cikin shirinsa. “Sorry,
na yi latti, na sa mana abun karyawwa
ka fara bari na shirya.”
Tsuke idanunsa ya yi yana kallonta, “Ki shirya
zan jiraki.”
Har ya kama hanyar fita daga dakin ne ya
dawo da baya da ya ga rigar hannunta,
daure fuska ya yi ya iso inda take tsaye, “Meye
wannan?”
“Kayana ne, yanzu zan shirya na sauko, ka yi
hakuri yau na makara.”
Sa hannu ya yi ya karbi rigar hannun nata.
“Seriously? Har yanzu ba ki bar sa
wadannan kayan ba? Na tsanesu. Da gaske za
mu yi fada idan na sake ganin ki da
su.”
Bude baki ta yi tana kallonsa, tabdijan! Bai
san yadda take masifar son rigar soya
koyinta ba.
“Amma ina jin dadinsu Noorie.” Ta fada cikin
turbuna fuska za ta yi masa kuka,
“Me ki ke nufin jin dadinsu? Ki na nufin ya fi
daya dama ki ke da shi?”
“Eh! Mana, ba ka ganin ina sawa ne?”
“Eh! Kullum, lokacin da ki ke gasani, ki ke ba
ni wahala, ki ke tsume min, wannan
bakin kaya ne, na tsani masu kamfanin da suka
fara kirkirar kayan ma, bari ki ji,
kwaso sauran ki ban.”
Ware idanu ta yi. “Da gaske kawai ina sa su
don shan iska ne.” Boye rigar roba-
robar nata ta yi ta bayanta don kar ya karba.
“Idan ki ka sake sa kayan nan na rantse da Al-
lah zan kona su, ki tattaro kawai ki ba
ni.”
Haka ta shiga kwaban kayan nata sumui-sumui
ta fiddo rigunanta masu roba roba
kala shida da mai zanen damisa da na zaki da
mai baki zalla da mai fari mai digo-
digon baki, sai kuma wata baka zalla. Kallonta
yake yi tana fitowa da su tamkar
jumanji.
“Kin cuceni Wallahi, yaya za ki sa wadannan
kayan, ki zauna min a gida? Matsa ki
ga na zaba miki, na ga alama along with your
head, kin rasa fashion sense dinki.”
“Su Yaya Zaid fashionistas, yaushe ka san
gayen mata?”
Juyowa ya yi ya dan harareta kadan, “Kar ki
gwada ni, yanzu ki ga aiki da gamawa.”
Kayan ya zubar a kasan kafafunsu ya janyota
jikinsa, ta saki kara. “Allah za ka yi latti ni dai ba
ruwana.”
“Yaushe za ki koma ofis?”
“Ai ba aikin gado bane, da zan yi resigning sau
hudu ina komawa.”
Sa hancinsa ya yi cikin wuyanta yana shinshi-
nan kamshinta, “Ke da kamfaninki duk
yadda ki ke so, hakan za ayi. Da gaske ina ke-
warki a ofis, da farkon tafiyarki, sai na
tashi da karfin gwiwa zan shiga na dan ganki a
ofis dinku, sai kawai na ga wayam ko
kuma na tuna kafin na isa cewa kin min nisa.”
“Hmm! Dama ka yi kewata tun lokacin?” Ta
fada tana matsawa baya, don ta samu
sararin ganin idanunsa.
“Eh! Mana, koda yaushe na fada miki, ki na
raina ko a farke ko a mafarki, amma
dole ta sa na dan matsa kadan saboda ki samu
sararin tunani da kyau ki kwantar da
hankalinki, duka mu natsu, mu fahimci abinda
muke so na gaskiya.”
Gira ta daga masa, “Yanzu ka fahimci ni ka ke
sO na yi gaskiya kenan?”
“Dama fa? Kin tab tantaar hakan ne? Tabbas,
banda lokutan da ki ke borin Yaya
Zaid baya so na… Blah blah blah, bayan ki na
hira da zawarawanki, 1dan na zo wurin
gaba daya idanunki suna kaina har ma ki na
kwarewa.”
Zaro idanu ta yi ta bugi faffadan kirjinsa. “No!
Ba ka ga wannan ba. Au, sam hakan
ba tai faru ba, ni ban taba satar kallonka ba, me
ma zan yi da kai a lokacin?”
Riko hannayenta duka biyu ya yi yana dariya,
“Asirinki ya dade da tonuwa yarinya
kallonki kawai na ke yi, ina jiran randa za ki
shigo hannu. sannan an taba fada miki
cewa ki na da hannu kamar guduma?”
“Ka san zan rama ko?”
“Affaffariyaf! Bismillah, ta ina ki ke so?”
“Sau biyu ka na fada, kuma ni hannuna sun fi
komai laushi, da taushi, da kyau. Da
luwai-luwai.” Ta yi masa fari da idanunta.
Dariyarta ya yi sosai, sannan ya ce, “Oh, na
san wannan ba shakka, zan bada
shaida ma idan ki na so.”
Kumatunsa ta yi tsalle ta ciza, sannan ta gudu
zuwa kofar bandaki tana dariya. “Kin
sayi na kudinki, bari ki ga na dawo.”
“Ba za ka karya ba?”
“Na koshi dam.” Ya fada hade da daga mata
gira. Rufe idanunta ta yi ta shige
bandakin da gudu hade da kullo kofar. Tana
jin sautin dariyarsa, kafin ya fice daga
dakin.
****k ****k *****
“Ke Hajiya, amarcin bai kare bane? Kowa yana
zuwan defense ke kin makale gefen
Noorie ko?”
“Hahhaha! Sharri kayan kwalba, haka na ce
miki? Da gaske na kusa dawowa, ina
dan jira ne a min rakiya, na ce zan tafi, an ce
na jira, yaya zan yi?
“Ah to, ba yadda za ki yi kam, sai jira, idan da
rabon biyan sabon kudin rajista ne
kuma to. Na hadu da Malam Yusuf ya ce min
kawarki ta kammala karatunta ne?””
Umm Adiyya ta sa dariya, tana so ta ga
fuskarsa, idan ya ji labarin ta yi aure.
“Me ki ka ce masa?
“Na ce ki na nan tafe wasu ‘yan al’amura ne
suka dan sako miki kai, amma za ki
dawo kwanan nan. Gyada kai kawai ya yi bai
ce komai ba kuma.”
“Ka ji min tsoho, ya tattara lafiyar tsufan shi ya
ji da matansa biyu, zai zo ya
addabeni, ke ya zaci zan ji tsoro ne, tunda yana
rike da sakamakona.”
“Bai san waye Ummu A. Ba kenan.”
“Au ke ma kin fara fadar haka ko?’
“Zama da su Adda Asma’ ne duka, sunan
kuma da dadi.”
“Ku
“Ku kuka sani dai, tana tambayata ke ma
shekaranjiya, na ba ta lambarki hala ta kiraki, na
ga alama za ta sace min kawa.”
Maman Abul ta yi dariya, suka karasa hirarsu,
sannan suka kashe wayar. Hakan
nan jininsu ya hadu tun zuwan Umm Adiyyan
digirinta na biyu a Bauchi, duk da
Maman Abul ta fita a shekare hakan bai sa ta yi
mata girman kai ba, tare suke zamaa
a dakin ddaukan lakcas haka tare suka karatun
gwaji da jarabawa, har Malamai ke
tambayarsu ko su Ya da kanwa ne ko kuma gi-
dansu daya? Saboda da wuya ka ga
daya ba ka ga daya ba, kuma kullum a gefen
juna suke zama, a jarabawa kullum
ana cikin watsa su.
Ta gama shirin dawowar Zaid tana zaune tana
sauraren karatun Alkur’ani da muryar
Abubakar Shatry, ta ji an danna kararrawa.
Agogo ta kalla, ta san ba Zaid bane ya
dawo, don haka ta nemi Hijabinta ta bunjuma,
sannan ta isa kofar gidan. Tana leka
ramin jikin kofar, ta juya da sauri ta jinginu da
jikin kofar idanu a ware, kirjinta dafe
da hannunta.
“Me suke yi a nan?”
Sai da ta yi ajiyar zuciya biyar, tana mayar da
numfashi, sannan ta saki ranta, ta
kirkiri fara’a kan ta bude kofar.
“Sannunku da zuwa. Aunty Rahma. Uncle TJ.
Bismillah ku shigo.”
BABI NA HAMSIN DA DAYA
Kan ta ne ya kulle, yaya aka yi suka san gidan?
Sannan babban tambayar ita ce me
ya kawo su?
Fara’ar nan dai tana manne a fuskarta, ta shiga
kicin sai lokacin ta saki zuciyarta, ta
hado masu kayan tarba lodi-lodi, sannan ta
dawo ta ajiye masu komai, wurin Rahma
ta wuce ta sa hannu ta karbi Minaal, “Baby
Minaal, oyoyo.”
Sai da ta koma gefe suka dan taba ballagwajen
wasansu da Minaal, sannan ta
dubesu ta ce “Ina wuni?”
“Lafiya kalau, amarya, yaya gida?”
“Alhamdulillah.”
“Kullum muna wakar zuwa da Baban Minaal,
ba mu samu mun zo biki ba, ayi mana
afuwa, har gida Maman Walid ta aika mana
kuwa.”
“La, ba komai, ai komai sai Allah ya nufa.”
TJ ne ya ajiye kofin hannunsa ya ce, “Na kira
shi ai ya yi mana kwatancen gidan, ya
ce shi ma ya kusa isowa.”
Umm Adiyya kam mamaki ne ya daskarar da
ita, wato dama Yaya Zaid yana waya
da TJ. Ko kuwa abokai suka zama?
“Eh! Yana hanya ko wani lokaci. Gaskiya mun
ji dadin wannan ziyarar. Ban ganki a
sunan Abba ba?”
Rahma ta yi dariya ta ce, “Kin gan shi nan, wai
shi baya son yawan shiga taro, sai
dai na je barka, haka na gama kumburina yana
kallona, bai ce komai ba. An taba
haka ayi ta hana shiga taro?”
Ah Uncle TJ mu ma ba za mu zo naku ba
ashe.”
“Gwamma ana yi ana hutawa dai ko? Bare ma
kawai za ta daura ki ne, biki suka yi
na kaninta a satin tana dawowa gida Asabar.
Lahadi wai za ta je suna, na ce ai koo
ita ce Amara kirjin biki ta hakura nan.”
Umm Adiyya tana dariya ta ce, “Kai dai kawai
ka nuna mata mulkinku na masu
gida.”
Suna cikin hirar da har yanzu Umm Adiyya ta