UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

cakulkuli, idan na yi dariya labour zai tashi.”

Cak! Ya tsaya ya daina murza dunduniyar

kafafunta.

Don Allah, kar ya tashi yanzu ki bari dai mu

koma inda muka fi wayo, a nan ba

barina za su yi na zauna kusa da ke ba, idan ya

tashi a can kuma kin ga muna tare

abinmu.

Umm Adiyya ce ta toshe dariyar da ta taso

mata ganin shigowar Hajja Ku.

Sannu mai mata, mu din ai ba mutane bane

da za a haihu a hannunmu, ku wuce

Abuja idan kun tashi haihuwar.”

Hajja Ku am me ya yi zafi, ni idan kun ce na

damka maku ita ma yanzu sai na

tattara na tafi.”

Umm Adiyya dai kafafunta ta janye daga han-

nunsa ta koma gefe, kai a kasa.

“Rashin kunyarka sai kai, ku tafi can gidanku

ku karaci abinku ku bar min daki ni na

yi bakuwa.”

“Haja Ku, Umm Adiyya ba ta son can yana

wari, mun bude windows turaren da
Fadeela ta sanya, ya fita sai ya gama fita za mu
koma, ku zauna a daya dakin kawai
da bakuwar.”
Adiyya kam zare idanu ta yi cikin mamaki,
Yaya Zaid!”
Rabu da mijinkin nan ganin damar kowa yake
yi, shi wai zai yi da ka yi ka gama, sai
sun maka mafiyin haka ai.”
Yana dariya ya ce, “Da wannan bakin
gwamma mun koma cikin warinmu. Twinkle
tashi mu tafi.” Hannunta ya kama zai tayata
tashi.
Hajja Ku ta ce, “Idan ma taya ne ba Tinkle ba,
ku ku ka jiyo. Ka na nan bini-bini sai
aukin bin mata, ba za ka bar ta ta huta ba. Nan
za ki zo ki zauna, idan kin haihu, sai
ka yi wata biyu ba ka ga keyarta ba.”
Umm Adiyya dai dariya ya ki sakinta, ta kalli
Zaid ta ce “Zan iya tashi.”
Don haka ya dan matsa mata ta mike, suka yi
gaba, yana bin ta a baya, Hajja Ku
kam murmushi ta yi tana ganin ikon Allah, ba
abinda ta tuna irin lokacin da suka rabu
yanzu kuwa soyayya kamar ya lashe matar ta
sa.
Allah dai ya zaunar da ku lafiya haka nan.”
****k********
“Da gaske za ka sa Hajja Ku ta sani a gaba da
tsiya, kullum sai ta tuna min idan mun
hadu.”
Ina ruwanki da ita, sun mayar wasa na ke yi
ai. Tunda Saadik ya iya kowa ma ai zai
iya, tare za mu yi labour ki sha kuruminki.”
Harararsa ta yi, “Ka na gefe ba ka san me na ke
ciki bane za ka ce min tare za mu yi
nakuda? Ni yanzu mu ma bar maganar, don ji
na ke yi kamar na cire bebin na ajiye,
na gama gajiya.”
Da safe za mu wuce ai, gulmarku dai ke da
Maryam, kamar a kanta aka fara suna
ke sai kin zo, ba an yi an gama ba, hankali ya
kwanta?2″
Na gode dai da aka bari na zo din. Ni kun yi
magana ne da Faruk?
Faruk? A’a wani abu ne?”
Murmushi kawai Umm Adiyya ta yi ta ce,
“Shi kenan, idan kun yi maganar sai mu yi.”
To shi kenan.”
************
Zaid Abdur-Rahman yana tsakiyar Scrum
Meeting (taron gaggawa) da suke yi
kowane bayan kwana uku a ofis, domin sanin
inda aka kwana akan kowane aiki da
duka bangarorin kamfanin su ke yi, lokacin ne
wayar ta shigo. Don haka ya nemi ayi
masa uzuri, ya koma gefe domin amsa wayar.
Innayo ba ta wayar.” Ya fada bayan Innayon
ta fada masa akan cewa Malam Bala
zai je gida ya ajiyesu a asibiti, haihuwa ta
tasowa Umm Adiyya.
Gaba daya hankalinsa ya tashi, ya yi gaba
zuwa wurinta. “Twinkle, sorry ku wuce asibitin
yanzu zan gama na taho. Ki jirani, kin ji?
Ce maka aka yi jiran mutum take yi haihuwar.
Kawai idan za ka zo ka zo.”
Goshinsa ne ya tattare, “To, to to kwantar da
hankalinki yanzu ina dakin taro zan..”
Kar ka sake kirarmu, ka tabbata a dakin
taron!” Ta fada sannan ta kashe, girgiza kai
ya yi, ya san tana cikin wani hali, don muryarta
ma kamar ba tata ba.
Excuse me, please.” Ya fada hade da jan
Femi gefe, ya fada masa uzurinsa,
sannan ya fice daga ofishin, cikin sauri yake
tafiya, kai tsaye asibitin da suke zuwva
ya wuce.
Sai dai gaba ki daya halin da ya samu Umm
Adiyya a ciki ya daga masa hankali,
gefenta ya je ya zauna, yana mata sannu, juy-
owa ta yi ta dube shi.
“Yaya Zaid, idan za kayi min addu’a, kayi
min, idan ba za ka yi ba, ka tashi a nan.”
Addu’ar na ke miki ai Twinkle. Allah ya raba
lafiya.”
Ciwo dai sai gaba yake yi, tun Zaid na iya
mata sannu har ya ce, “Sister ba allurar
rage jin ciwon ne a mata?”
Oga, allurar ciwo daya ne shi ne ta haihu,
kuma ta yi kusa, ko za ka je ta waje. Idan
ta haihu, sai ka shigo?”
Don Sister kam dai gani ta yi idan ba ayi sa’a
ba, anjima kadan zai iya saka mata
kuka gaba daya tashin hankali ya bayyana a
fuskarsa.
Kada kansa ya yi kawai ya ce, “Gwamma dai
ina nan din.” Don yadda yake ganin
tana shan azaba, gani yake yi yana juya baya
za ma ta mutu ne kawai ta tafi ta bar
shi.
Hankicinsa ya ciro ya share gumin da ya
tsattsafo a goshinta. “Bayana za ka matsa
ba fuska ba.” Ta fada, sai kuma ta koma cewa.
Subhaanallah.”
Bayan kusan minti sha biyar ne. Anti A’isha ta
kankwsa kofar dakin, ya tashi ya isa
wurin saboda Sister ta ce, ba me gurbata masu
dakin haihuwa da kwayoyin cuta, shi
ma har da takalma da riga aka ba shi kan ya
shigo.
Anti A’isha ta ce, “Malam, tashi ka fita daga
nan.”
Ko kulata bai yi ba, ya san su Maami suna
waje, amma ranar fa koma waye ne sai
dai ya yi hakuri, ji yake yi kamar shi ma zai
mutu.
“Nurse din ta ce ta kusa fa.”
“Yau na ga ikon Allah, Zaid, ba inda za ta je,
ka je ana bukatarka a waje.”
Ba yadda ya iya, musu da suruka. Hakan ya sa
ya cire kayan ya fito waje, can
masallaci ya wuce kawai ya daura alwala. Ya
yi nafifili, ya sake shigowa daga bakin
kofar dakin haihuwar, yana jin nishin Umm
Adiyya.
Maami har yanzu ba su ce komai ba? To ko
dai ciro baby din za ayi ne? Tana ta
shan wahala tun dazu, na mayar da an zo sai
haihuwar fa. Yanzu ta yi kusan awa
biyar a ciki.”
“Kai ka tafi ka ba mu wuri a nan.
Dole yaja baki ya yi shiru. Wani dogon nishi
suka ji ta yi, sai kuma tsit! Komai ya
tsaya ba motsi ba kara, gaba ki dayansu
bakinsu motsin addu’a yake yi.
Bayan kamar sakanni talatin, sai suka ji karar
baby ya callara ihu. Wata ajiyar zuciya
Zaid ya sake, ya lumshe idanunsa, sai ga
hawayen jin dadi sun gangaro daga
idanunsa.
Wadannan mintocin da aka dauka kan a fito da
baby, ji yake yi kawai kamar ya
banke kofar ya shiga ya ga matarsa. Ba
ruwansa da wata dokar rashin shiga dakin.
Amma kamar wasa, sai ji suka yi ta sake wani
dogon nishi, ai kawai sai ga Maami
ma idanunta sun ciko da hawaye. Yanzu kam
ita ma a tsaye take ta gagara zama.
Innayo dai tunda aka fito aka karbi kayan
baby, take tokare da bango suna jira.
Mintoci kadan bayan nan, sai ga Sister Jidda ta
fito da yara biyu a hannunta. Zaid
kam daskarewa ya yi yana kallon ikon Allah.
Hannu ya sa ya shafo fuskarsa ya ji ko a cikin
mafarki yake.
“Alhamdulillahi-Kasiran Dayyiban
Fi-hi.” Ya fada cikin ransa.
Mubarak
Ta sauka lafiya, bari a gyarata sai ta koma
dakin gefe.” Su Maami har da yiwa
Sister sannu, tana rungume da jika daya, Anti
A’isha na rungume da daya, aka juyo
aka nemi Zaid aka rasa a wurin.
*”Ikon Allah, yanzu fa yana tsaye a nan.”
Bayan mintoci sai ga shi ya shigo, ashe masal-
laci ya je ya sake wata nafilar. Yana
shigowa Umm Adiyya na fitowa daga dakin
haihuwar, kai tsaye ya wuce wurinta ya
rungumeta a jikin sa. Dariya su Anti A’isha
suka saka. Maami ko kallon inda suke ba
ta yi ba tana ta murmusawa jikanta da ke han-
nunta.
“Sannu, Twinkle.Na gode kwarai da gaske.”
Shi ya riketa har suka karasa dakin da za ta
zauna, wanda daf yake da dakin
haihuwar, Sai da ta kwanta, ya karbi yaran
daya bayan daya yana kallonsu yana
masu addu’o’i.
Lokacin su Abba suka shigo dakin.
“Haba ni ma dai na ce mata ta je a sake duba
cikin natan nan girman ya kai.” Aunty
A’isha ta fada da kowa yake ta mamakin ganin
yan biyu. Faruk ne ya ce, “Haba
Aunty A ‘isha, jini ai ba wasa ba. Dole ayi gado
ai.”
“Eh! Lalle fa. Da wannan ma don wannan.”
Umm Adiyya kam jinsu kawai take yi, domin
ta dade da sanin ‘yan biyu ne za ta
haifa ba ta fadawa kowa bane ta yi shiru abin
ta.
%***********
BABI NA HAMSIN DA UKU
Har dare kafafu ba su dauke ba wurin zuwa
ganin su Umm Adiyya da jariranta duka
biyu maza. Sai wuraren karfe tara, sannan
Maami ta kada kan kowa ya wuce gida,
don a bar Mai-Jego ta samu hutun da take
bukata.
Innayo tana nan ita aka bari a wurinta, sai
lokacin Zaid ya samu kebewa da matarsa
da yaransa. Zama ya yi a gefen gadon da take,
ya dauki Baby A. Yana kallo yana

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE