UMM ADIYYAH CHAPTER 90 BY AZIZA IDRIS GOMBE
Www.bankinhausanovels.com.ng
murmushi. Daya bebin na cikin Cot din da ke
gefen gadon.
“Sun ce da kai suka yi kama. Na ce masu ni ma
da kai na yi kama.” Umm Adiyya ta
fada tana kallon yadda ya kurawa Baby idanu.
Juyowa ya yi ya bar dariyarsa, ya tsuke
fuskarsa, ya ajiye baby din. Zai mike ne, ta
yi saurin riko hannunsa, “Ka yi hakuri.”
“Laifin me ki ka yi?”
Rufe idanunta ta yi ta bude, “Don Allah kar ka
hukuntani haka kawai dai ban fada
bane ganin yadda akan daya ma ka damu sosai
bare idan ka san biyu ne hankalinka
sai ya fi haka tashi. Shi ya sa ban fada maka
ba.”
“Uhm! Ya yi kyau Allah ya rayasu.” Abinda ya
fada kawai kenan ya daga baby B
daga dan katifar jariran ya sumbace shi, san-
nan ya ajiye shi, shi ma.
“A huta gajiya, bari na bar ku, ku samu barci.
Sai da Safe.”
Baki ta bude da idanu cikin mamakin fushin
Zaid, dama yanzu hakan zai bata masa
rai?
“Please, Noorie kar ka tafi da fushina.” Ta fada
a marairaice, hakan ya dawo da
hankalinsa kanta, yana mata murmushi.
“Twinkle, ba zan yi fushi da ke ba. Bayan bai-
war da Allah yayi min ta dalilinki. Kawai
dai ban ji dadin boyemin irin wannan babban
albishir da ki ka yi bane. Na zaci babu
wannan a tsakaninmu.”
“Na sani, kuma babun ma. Kawai dai dalilin da
ban sanar da kai ba kenan. Amma ai
yanzu ma ga shi ka fi jin dadi saboda ba ka
sani ba.”
Harararta ya yi, ita kuwa ta shiga gimtse dari-
yarta. “Idan ki ka sake min haka, za ki
gamu da ni, na fada miki.”
Gwalo idanu ta yi waje, “Lallai Noorie, akwai
ka da karfin hali ko himma ne, kai
yanzu har kwatanto wani cikin ka ke yi bare
har haihuwan biyu? Sai na ce Allah ba
ku zaman lafiya, don dai ba da ni ba kam sai
dai wata.”
Dariyar yadda ta hakikance take magana yake
yi ya ce, “Ai sauranki seti hudu nan
gaba, yarinya.”
“Allah dai ya raya wadannan ya bawa wanda
ba su samu ba. Amma Alhamdulillah.”
Kada kai ya yi ya juya zai bar dakin, sannan
ya ce, “Sannan a’a, ba na kama da ke,
na fi-ki kyau.”
Baki ta bude za ta yi fada sai ta ce, “An gode
da aka ga mummunar aka ce ita ake
so. Har aka yi ta ciwo da hatsari a kanta.”
Yana dariya ya bar dakin.
Sai lokacin Innayo ta shigo bayan fitarsa.
Ruwan shayio mai kauri ta hadawa Umm
Adiyya, sannan suka nemi makwanci, wuraren
Karfe daya Umm Adiyya ta ji kamar
motsi, wannan ya sa ta farka kasancewar ba ta
da barci mai nauyi.
Ware idanunta ta yi da sauri, ta tashi ta zauna.
“Yaya Zaid!”
“Shhhh! Koma ki kwanta.” Ya fada, ga baby
nan a hannunsa yana lulawa kadan-
kadan. Alamar rarrashi.
“Karfe daya fa, me ka ke yi a nan? Ba ka tafi
gida bane?”
Kallonta ya yi kamar me tambayar kanki daya
kuwa? “Na bar ku a nan? Ina waje na
shigo ne, wannan mai kukan ya farka.”
Hannu ta mika masa, “Ki bar shi kawai, ya
koma.”
“Ai ba su san rarrashi ba yanzu sai ci.”
Ita kallon mamaki take binsa da shi yadda har
ya kware a rike jariran ma, kamar
wani abinda yake yi yau da gobe.
“Ina Innayo?”
“Tana can falon baki, ta fita kiran Nas ta ganni
sai ta sha zamanta a can, ta yi barci
ba zan tasheta ba ai ko?”
“Ka dai koreta kawai. Kai ma ka na bukatar
hutun ai.” Ta fada bayan ta kalli
idanunsa da suka fara nuna alamar gajiya.”
“Jinki ko gidan na je zan iya barcin ne?
Gwamma dai ina nan anjima sai mu koma
tare.
Kallonsa kawai ta yi ta yi murmushi. Haka ya
zauna a gefen gadon da take, suka sa
yaransu a gaba suna kallo suna bayanin kam-
mani da surori, sai wajen karfe biyu da
rabi ya ce.
“Idan ba ki kwanta ba, zan tafi tunda ni na
hanaki barcin.”
“Ina za ka a daren nan? Ai ga convertable
dinsu can, shi za ka bude ka kwanta
akai.”
“Na yi masu huduba, tunda ba a fada min ba,
ban shirya suna biyu ba, amma yau na
yi tunanin, mu sa sunan Baffa Mai-Kano da
Abba. Abdullah da Zubair.”
Umm Adiyya ta yi murmushi ta ce, “Baffa fa?”
“Ina bin ki bashinsa.”
Wata irin dariya ta yi ta ce. “Ka ma cire rai,
idan za ka yi tun yanzu ka yi, ai na gama
daga wannan.”
“Nan da wata uku sai ki fada min haka mu ji.
Kiyi bacci Adiyyah.”
“Ban jin yin bacci. Idanuna sun bushe.”
Murmushi ya yi, ya ce, “Ba ke kadai ba, amma
anjima jikinki zai tambayeki, kuma da
gari ya waye mutane ba za su bari ki huta ba.”
Haka dai ya tsaya har sai da ya ga ta yi bacci,
ya isa wurin kujerar dakin da ake
warewa da dare, ya ware, ya jinginu akai har
barci ya dauke shi.
Da Asuba ya wuce gida ya samu ya runtsa
kadan, sannan ya shirya ya fito.
Da safen aka sallame su suka koma gida.
Bayan an tabbatar da samun cikakkiyar
lafiyarsu duka. Sai tsiya suke yiwa Zaid wai
sun ji labarin har kwana ya yi a asibiti.
Saadik ne da aikin nan, “Da sauki dai tunda
gandoki bai sa na amshi haihuwar da
kaina ba.”
“Ai koda garaje ba zan sake wannan kuskuren
ba, kai Malam ka ji tashin hankali,
Wallahi ji na yi duk duniya na zama dolo ba ni
da dabara. Ina!”
Zaid yana dariyar Saadik, ya ce “Haba dai, kai
da muke cewa mun samu sabon
ungozoma hankulanmu a kwance.”
Wani mugun kallo ya aikawa Zaid. “Ai na so
da an haihu maka a mota, za ka san me
na ke nufi. Allah tare muka hango mutuwar da
ni da ita tsabar bugawar zuciya,
tunanina daya ta ina zan taro dan. Daga baya
na fara tunanin kawai hala tsintarmu
za a zo ayi mun suma ko mun mutu.”
Zaid dai gyada kansa ya yi ya kurbi Maltinan
hannunsa mai sanyi, “Na fahimceka
akhi, na fahimceka.”
Saadik ma ya daga gwangwaninsa ya kurba ya
ce, “Finally!”
*********
Gidan Bldr. Zubair Nafada dai ba masaka tsinke
ranar da ake taron walimar sunan
‘yan biyu wadanda suka ci sunan Abba da
‘yan
Baffa Mai-Kano. Umm Adiyya ta amince
ayi masa kara idan Allah ya kawowa Zaid
wani, ayi wa Baffa, duk da har cikin ranta ji
ta yi ta gama haihuwar haka nan. Zubair-
Aslam, da Abdullahi-Saalim.
Asma’ dai ba dama ita ke rike da Aslam, “Dole
na tattala uba mahaifi.”
“Ke nan gane wanda ki ka dauka ki ke yi?”
Saudah ta tambaya cike da mamaki
saboda ita dai tun dazu ta kura masu idanu ta
gaza gane waye-waye.
“Ban gane ba, amma na san wa aka sawa jan
safa da safe.” Ta fada tana dariya.
Zuwa yamma gidan ya cika ya batse da yan-
uwa da abokan arziki. Mashkura matar
Salis na kan gaba a shirye-shiryen hidimar.
Adda Zubaida ce ta dauko Malama
Juwairiyya ta zo ta yi bayanai da nasiha wa
mata, inda ta yi filla-filla ga abinda ke ci
mata tuwo a kwarya. Ba wacce ba ta karu ba a
wannan taro. Mai-Jego da yara sun
sha kyau sun gaji, Umm Adiyya ta shirya cikin
shigen lufaya rantsattsiya.
Kafin dai taro ya watse kowa ya tafi, ji take yi
kamar za ta kife don gajiya, ga daukar
hotuna, ga gaisawa da jama’a, ga kuma yara na
bukatarta. Ana watsewa wuraren
karfe goma saura ta bingire ta yi barci, bayan
ta sha wanka da ruwan dumi sosai.
Koda Zaid ya kirata ya samu ta riga ta yi barci.
Don haka sako kawai ya bari a wayarta, san-
nan ya kwanta. Tunda aka yi suna, su
Aslam suka tsiri kukan dare.
Ranar Juma’a kam, daga Maami har Abba sai
da suka taya renon, saboda lokaci
guda suka tashi suna callara ihu. Umm Adiyyya
ta yi rarrashin har ta ji ba dadi, tana
samu ana karbar su, a nan barci ya dauketa
tana durkushe gaban gado.
Hajiya Larai ke zaune a kanta, kamar yadda
suka saba daukota, yanzun ma ita ce ta
zo, saboda da rana watsewa ake yi a bar su,
daga ita sai yaran da Innayo sai kuma
Hajiya Larai din.
*********
Umm Adiyya ta gama shirinta cikin wani Sea
Green Voil ne ta dauko katon kofin
tangaran dinta tana shan abin ciki. Zaid ya yi
sallama cikin dakin.
“Lallai yau bana ka taba, barci suka yi ne koo
kyautar da su ki ka yi?”
Dariya ta yi sannan ta ce, “Ni dai ka san Abba
na Salihi ne, baya ku ka Saalim ke
Son ya bata min shi.”
Dariya ya yi, ya zauna a gefenta inda take za-
une kan doguwar kujerar dakin, “Abin
son kai ne kenan.” Hankalinsa ne ya kai kan
kofinta, ya ga abinda ke ciki. Hannu ya
mika mata.
Umm Adiyya ta ware idanu, “Meye?”
“Ba ni.”
“Noorie don Allah ka bar min, yanzu kadai
idan na sha shi kenan.”
“Ba na ji an ce abu mai zafi kawai za ki sha
ba?
“A’a har da masu dumi kuma wannan na da
dumi.”
“Mutum dai ya zama Addict karfi da yaji.”
Umm Adiyya ta matsar da kofinta daya gefen
ta ce, “Tunda ba na damun kowa, sai
a bar ni na sha kayana.”