UMM ADIYYAH CHAPTER 91 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 91 BY AZIZA IDRIS GOMBE


                Www.bankinhausanovels.com.ng




 “Zan fadawa Maami ta dauke, na san ba ta san

kin boye ba. Yaushe za mu tafi,

gidan can ba dadi.” Ya fada fuska a yamutse,

“Yaushe muka zo? Cab! Ai sai mun kara wata

daya kafin nan sun yi kwari. Yanzu fa

ni kadai, sai Innayo, idan na koma zan yi kara-

mar hauka.”

Amma dai wasa kikeyi ko? Wata daya? Kin

san kwananki nawa rabonki da

gidanmu?”

“Ba yawa, Na ga alama barci ne ya yi makka

yawa, muna zuwa sai ka gwammace

zamanmu.”

Ba lsaifi, bazan damu ba, saboda haka ku fara

shiri kawai zan yi wa Maami

magana, idan ma nauyi ki ke ji ke.” Ya fada

yana mata dariya kasa-kasa.

Kallonsa kawai take yi yana bidirinsa, bai yi

kasa a gwiwa ba ya fadawa su Maami

za ta koma aka kammala duk shirye-shiryen

komawarta, har gidan an je an gyara

mata. Ranar farko da suka koma a tsaye, suka

kwana, don kukan yaran, ba dabarun
da ba su yi ba, amma abu ya gagara.
Sai da suka kai wurin watanni uku. Sannan
suka fara barcin dare. Girmansu har
mamaki yake bawa mutane, saboda ba za ka
gansu ka ce yan biyu bane, ko wanne
ya yi bulbul. Mashaa Allah! Suna samun ku-
lawa ta musamman.
***** ****** ***
BAYAN SHEKARU BIYU.
Ranar Lahadi da dare suna falon Zaid, gaba
dayansu kanta na kan kafafunsa, suna
kallon wani bidiyo na Mufti Menk a wayarsa
ne, idanunta suka kai kan Notifications
din wayarsa. Nan take kwakwalwarta ta dauki
sunan kai.
Wayar ta mika masa, “Ga shi ka na da sakonni
a Whatsapp dinka.”
Karbar wayar ya yi ya duba, ta yi shiru ba ta ce
masa komai ba. Ya gama duba
sakwanninsa, ya kunna mata bidiyon din da
take kallo. Hankalinta ne ta ji ya tashi
daga shaukin son ganin bidiyon.
“Ka bari sai anjima mu karasa, na gaji, bari na
dubo Aslamayn, na ji su shiru.”
Hannu ya sa ya rikota ta dawo jikin sa. “Kin ji
su shiru, wannan yana nufin sun yi
barci, wannan lokacinmu ne, za ki je ki taso
su.”
Dariya ta yi, “Ka koyi son kai kwanan nan.”
“Ba son kai, na ga abin naku ne, idan na biye
maku, sai dai na ji an tureni a circle
din.”
“Na ji ba zan taso su ba, kawai dai na leka na
ga halin da suke ciki ne.”
“Mintuna biyar.” Ya fada hade da sake rikon
da ya yi mata. Murmushi kawai ta yi
masa, sannan ta mike. Dakin yaran ta shiga ta
samu kowa a kan gadonsa ya yi
barci. Innayo ma ta kishingida a kan gadonta
har barci ya dauketa.
Murmushi ta yi kawai ta fito daga dakin, dak-
inta ta shige, ta fada wanka, sai dai
gabaki daya kwakwalwarta ta ki ta toshe mata
abinda ta gani dazu a wayar Zaid.
Gabanta sai faduwa yake yi. Haka dai ta daure
ta ture tunanin a gefe. Ta zura kayan
barcinta, bayan ta kalelaye jikinta da kamshi
daba- daban masu daukar hankali da
Sanyaya rai.
Lokacin da ta kammala, ta riga ta ji hau-
rowarsa sama, don haka dakin sa ta shiga
kai tsaye, kallon da ya yi mata kawai ta san ya
yaba da ita. Murmushi ta yi masa,
sannan ta karasa inda yake.
Rikota ya yi jikin sa yana shakar kamshinta,
“Ya Salaam! Twinkle meye sirrin ne?”
Ya fada lokacin da ya matsar da kansa baya
kadan yana kallon idanunta.
Kallonsa ta yi har cikin idanunsa ba kiftawa,
sannan ta ce “Waye Deena?”
Ya ji tambayar daga sama kuma ba zato ba
tsammani, don haka goshinsa ya dan
tattare kadan cikin mamaki, idanunsa
suka
tsuke.
“Deena?
Eh, dazu na ga naga alamar shigowar sakonni
a wayarka. Sakwaninta ne suka
shigo. Shin ya cancanta na damu?”
Kada kansa ya yi yana murmushi, sannan ya
tallafo fuskarta cikin tafin hannayensa
Aa.”
“Then, wace ce?”
“Wata ma’aikaciyarmu ce.”
“Take maka sakon karfe goman dare, bayan taa
san ka na da iyali. Ba za ta bari sai
gobe ba, tunda za ku hadu a wurin aiki? Me
ma zai sa ta yi maka sako, ina
tsammanin koma meye dai, akwai wanda ya
kamata su sanar, idan ma aikin
gaggawa ne.”
“Kawai kin san sauran ‘Yan Department dinsuu
biyu matan aure ne, so idan da akwai
wani abu, ita ke fada mana.”
“Saboda ita ba matar aure ba. Amma kai ai mi-
jin aure ne, sai ta fadawa mazan da
ba na aure ba, ba na son mu’amalarku gaskiya.”
“Adiyya, fannin aiki ne fa.”
Shekeke ta kalle shi, “Eh, aikin take kewa
ko?” Lokacin ne, Zaid ya bude baki, sai
kuma ya rasa abin fada. Take a wurin Umm
Adiyya ta sa hannu ta cire hannayensa
daga jikinta. “Na ga wani bangare na sakon, A
karo na gaba ka rinka kashe alamar
shogowar sakwanninka, Mr. Zaid Abdur-Rah-
man Nafada.”
Juyawa ta yi za ta bar dakin saboda tafasar da
ta ji lokaci guda zuciyarta tana yi. Ko
ina kuna yake yi a jikinta, daga fatarta har zu-
ciyarta, ta gaza yarda da abinda ta
gani, amma duk da haka, ta ba shi damar ya
kare kansa.
Shan gabanta ya yi, “Tsaya Twinkle, seriously,
kar ki yi tunanin wani abu. A takaice
ga shi bari na nuna miki gaba daya komai ki
gani.”
Hannu ya sa ya daga wayarsa ya bude mata
kan sunan Deena, inda sakwanninta
suka fito, ya mika mata wayar.
Juya wayar ta yi ta mayar masa, “Ni me zan
kalla na yi da shi? Ba sai ka bada hujja
kan abinda ka ke yi ba, kawai dai ka san idan
ka yi mai kyau don kanka, idan ka yi
akasin hakan ma. Allah Yana kallonka. Idan
kuma..”
“Ki tsaya ki ji komai, ba na son sabanin
fahimta.” Jan hannunta ya yi ya kai ta bakin gado
ya zaunar da ita. A gabanta ya durkusa ya ce,
“Kin san dai kowa da yadda
rayuwa take zuwa masa ko? Haka nan kowa da
Kaddararsa ba yadda za ayi abu ya
shigo rayuwarka, sai idan Allah ya zana
faruwar hakan…”
Zuwa lokacin hawaye sun gama ciko idanun
Umm Adiyya, zuciyarta kamar za ta fice
a kirjinta.
“Noorie, ni duk ba wannan bane damuwata, ka
fada min abu daya, ka na sonta?” Ta
rike labbanta da ta ji sun soma rawa a tsakanin
hakoranta.
Kai tsaye ya amsa, “A’a. Na yarda kin ga
sakonta a wayata, amma Billahil-Azeem
ban taba ba ta amsar su ba, tsakanina da Staff
dina, aiki. Amma tun watanni biyu da
suka shige ta fara turo min sakwannin Juma’a,
duk da ban taba bata amsa ba, ta
fara turo min ire-iren wannan sakwannin, na
kirata a waya, na ce ta daina. Amma
duk da haka..”
Ma’aikaciyarka ce, a kasanka take aiki, idan
ka ga damar dakatar da ita, za ka
dakatar da ita, yes na san wasu matan sun
matsu da har za su iya mannewa namiji,
amma sai kun bada kofa hakan za ta faru, ba
yadda za ayi ta yi maka sakwanni dari
ba ka ba ta amsar daya ba, ta ci-gaba da yi,
haka nan ba yadda za ayi ka taka mata
birki sannan ko ba ta da zuciya ta ki daina yi
maka sakwanni a waya.”
“Twinkle, irin wadannan matan abin tsoro ne,
shi ya sa ki ka ga ina bin abin aa
hankali, idan ta ga dama ko wace hanya za ta
iya bi ta cimma burinta, ba na son
abubuwa su kwabe ne, shi ya sa na ke bin abin
a hankali, ina shirin sawa ai
matacanjin wurin aiki zuwa Kano ko Kaduna
office dinmu, kin ga idan ba za ta koma
ba, dole ta bar aikin, yanzu idan na ce zan fito
baro-baro, na nuna fada na ke yi da
ita, za ta iya yin komai.”
“Akwai ma abinda zai daureka kenan?” Ta
tambaye shi hade da tsare shi da
idanunta.
Ajiyar zuciya ya yi, ya kada kansa. “To me zai
daga maka hankali?”
“Idan ki na tambaya ko na koma rayuwata ta
baya ne. Then no, Adiyya tun bayan
aurenmu banda ke, ban sake rike koda yatsar
wata ya mace ba, ko bayan da muka
rabu bare yanzu, so ki kwantar da hankalinki,
ba na tare da Deena, kuma ba abinda
zai faru a tsakaninmu, haukarta kawai take yi,
kuma za ta bari. Kawai dai ina bukatar
ki amince da ni.”
Hannu ta sa ta tallafe goshinta, siririn hawaye
ya gangaro mata, “Ban san abinda ma
zan yarda da shi ba.”
Cikin idanunta ya kalla, “Ina rokonki da ki
yarda dani Adiyya.”
“Matsalar kenan, na gama yarda da kai, ina
tsoron ka karya min zuciya, ban san ko
zan iya daukar hakan ba.” Jawota ya yi jikin sa
ya rungumeta.
“Mun fuskanci abubuwa da dama, ba zan bari
wata ‘zautacciyar Mace ta shiga
tsakaninmu ba. Zan iya sallamarta gobe, amma
dole sai ina da grounds na yin
hakan, idan ba hakan ba, zai iya zama Case, so
ki ba ni time ki kuma yarda da ni.
Inshaa Allah komai zai daidaita.”
Kai ta gyada masa. Hawaye suna bin fuskarta,
tabbas ta san akwai irin matan da ba
matakin da ba za su bi ba, don su ja hankalin
da namijin da suke so garesu ba, bare
Zaid ya tara duk abubuwan da mata suke so, ga
kurucciya ga kyau, ga kudi, ga ilimi
da suna, dole yana cikin hatsari.
A hankali ya share mata hawayenta. “Na
gode.”
Haka dai ta kwanta zuciyarta cike da nauyi.
Wajajen karfe uku ta mike ta yi alwala, ta
fadawa Allah damuwarta, sannan ta samu

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE