WASU MATAN COMPLETE BY ZEE SARDAUNA
Zaune take bisa tabarma tana tsintar shinkafar hausa tana sauraron wakar hamisu breaker, a gidan redio da yar karamar salularta. Akalla baza ta wuce shekara talatin da takwass ko Arba’in ba sai mita take yi “ohni saudatu ni wlh na gaji da wannan rayuwa a ce ko yar shinkafar ga ta gwamnatii dai mallam ya sayo mana mu tuka amma yakiya a’a, ko da yaushe sai dai yace babu babu kamar kansa a ka fara talauci ko wurin abokanansan nan yaje ya aro koda bashine dai ya sayo muci kamar yadda su laure kayi, amma sai dai yace Ayi hakuri wata rana sai labari ni gsky na gaji da hakurin nan mssssstwwwwwssss”. Ta k’arashe maganar tana jan dogon tsaki. Alokacin da aka turo kyauren gidan tare da sallama ciki ciki inna saude ta amsa sallamar yayin da naga wata mata shiyar budurwa wadda ba za ta wuce shekara goma sha bakwai ba ta fito a cikin wani dan madai dai cin daki sanye da wata kodaddiyar atamfa, ta yo wurin wannan mutunen da ya shigo wanda akalla zai kai shekara hamsin amma idan ka kalleshi so daya baza kace yakai hakan ba domin irin jikin fulani ne dashi daka gansa zakace tabbass bafulata ni ne ta durkusa tace “bappa sannu da zuwa ya kasuwa?”. Dadai lokacin da yazauna bisa tabarmar tare da amsa mata da cewa “yawwa mamana da fatan na same ku lapiya”. Tace “lpy lau baffah”. Yayin da ta tashi ta nufi wurin tulun su ta kawo mai ruwa mai sanyi, ya karb’i ruwan yace” nagode mamana Allah ya miki Albarka”. “Ameen Baffana”. Ta fad’a tana murmushi.
Bayan ya gama shan ruwan ne yace “Hala ina auta naga bangan ta ba”. wannan yarinyar da ya kira da mamana tace “inna ce ta aiketa gidan su inna laure ta anso mata kuka”. yace “tou”. tare da nufar dakinsa a yayin da ko kallo bai ishe inna saude ba balle ai maganar gaisuwa dan haushinsama take jii yanxu shiya takasa yi masa magana yau kenan ko naman dari biyun bai riko asa a miyaa ba
Guduu kawai yake a mota da’alama sauri yake domin gudu yake shararawa a bisa titi Allah ne kawai yakai shi gida lapiya domin yayi mantuwan wasu files a gida gashi kuma urgently ake bukatarsu yana isa bakin wani makeken gate yai parking ko motar bai shiga da ita cikin gidan ba ya bude marfin motar ya zuro kafafunsa waje da dan sauri sauri mashaallh shine abunda nace a lokacin da nai tazalii da kyakkyawar fuskar sa ma’abociya haiba da kamala matashin saurayi kenan maiji da kyau da kudii Aliyu muhammad Ahmad da daya tilo ga Alhj muhammad Ahmad mai xinaree Shahararren mai kudin da yayi suna a fadin nigeria yana da companies a garuruwa da dama za kujii cikaken labarinai nan gaba
Noking din gate din yayi Ila mai gadi ya bude ya shiga ko saya amsa sallamar mai gadii bai yiba yai cikin gidan direct da sallama ya shiga cikin palon da sallama kamar yadda yasani haknne ko a yanxun zune take bisa kujerun da suka kawata dakin tana charting a wayar ta kirar iphone 12plus karar takalmi da tajine alamun an shigo yasa ta dago kanta tare da daga yan yasunta tayi waving dine maana hiiii taci gaba charting dinta bai kulata ba dan inda sabo yaci a ce yasaba da halin suhailat direct uptchers ya nufa tareda shiga room dinsa after 3mint ya fito tare da files din ya fita ko adawo lpy bata masa ba gaba daya ma bata san ma ya fito ba yaja motarsa tare da nufar A.M.A COMPANY ………………………
Da shigar sa cikin matsakaicin d'akinsa ya zauna .......
yayin da ya nitsa cikin kogin tunani ………
Wai yaushe ne Saudatu zata chanxa halinta, yaushe ne zata san cewa zafin nema bashi ke kawo samuu bah ita a rayuwarta ba ta da godema Allah shi yasan ba haka halimatu ke masa ba, shiyasa idan ya tuna abunda yy mata sai yaji ransa duk a dagule. A ko da yaushe yana k’ara godema Allah da yasa halimatu ba ta mutu ba sai da tayafe masa, shikansa yasan ya yi rashi na mace ta gari mai hakuri da kawaici ga tsafta Allah ya jikanki da rahama matata. Ya share hawayen da baisan ma lokacin da suka sauka akan kuma tunsa ba.
Ako ina Ako wani gurii a gaban kowa yana iya fad’in cewa mata suna suka tara domin wasu matan zuciyar Musulunci garesu wasu matan kuwa zuciyar fir’auna garesu, kamar Saude ita a ko da yaushe ba abinda tasani illa Kud’i sannan taci dad’i tana da tsafta dai dai gwargwado amma bata kai Halima tunsa ba tunaninsa ne ya katse a lokacin da yaji kiran sallah azuhur yafito daga d’akin yayi alwala baiga Saude cikin tsakar gidan ba da’alama tana bayi ya nufi masallaci.
Da isar sa A.M.A COMPANY direct office dinsa ya nufa bai tsaya b'ata lokaci ba yakira waya bayan yan mintutka akayi noking "yes come in", cewar Aliyu wanda ake kira Haidar mik'awa mutumin da ya shigo files d'in yayi ya ce "ya kaiwa accounter bayan fitar", mutumin ya duba time yaga 2:15 dafe goshinsa yay yace "oh Allah!", tare da nufar toilet din da ke cikin office d'in na sa, tsayawa misilta muku yadda toilet din yake bata lokacine domin komi na Aliyu haidar yana yinsa ne a tsari Alwala yayi bayan ya gama ne ya shinfid'a darduma ya kabbarta salla domin tawucesa balle yace yy a masallacin companyn.
“Aleeya! Aleeya!! Aleeya” shine sunan da naji inna Saude na kira kamar mai shela a anguwa da sauri wadda naji an kira da Aleeya ta fito daga dakin su, matashiyar buduwar nan ce ta d’azu da mallam Yusuf ya cewa Mamana “masha Allah fata barakallahu Ahasanul halik’in”, kyakkyawa ce ajen karshe duk da talauci ya nakasar da kyawunta kallo d’aya xaki mata kice wannan ta had’a jinsi da larabawa bai wai dan kyanta yayi yawa bane aa irin sihirtaccen kyawun nan gareta wanda idan mai kallo ya tsureta da ido domin wai ya gano muninta to Allah kyawu zai ga ta k’ara masa tanada round face irin wacce ake so ga zara zaran eyelashes tareda dogon hancii had’i da pink lips, bakinta dan k’arami dashi zaka iya rantsewa hannun ta baza ya shiga ciki ba Allah ya mata diri mai kyau kamar ita tayi kanta shiyasa bata fita da gyale, a rayuwata ako ina take tana saye da hijab wani time ma harda liqab, a yanzun ma hakanne sanye take da hijab d’inta wanda ya wuce mata guiwa ta durk’usa kusa da inna Saude tareda cewa “dan Allah Inna kiyi hak’uri koda kika kirani ina sallah ne shiyasa ban amsa da wurii ba”, tsaki inna taja “msssttwwwssss”, tare da cewa “kedai kika sani kin shige d’aki kin dunkule salon malam yazo yace an maki wani abu nidai dan Allah tashi ki had’a wuta ki d’ora sanwar tuwo kinga uku ta kusa” da “to”, ta amsa tare da nufar wani gun da alama kici ne……………………………………….✍️✍️✍️