WASU MAZAN BOOK 1 CHAPTER 1 BY EL’LADAN
WASU MAZAN BOOK 1 CHAPTER 1 BY EL’LADAN
Barister zahra ilyasu bala kafur yar asalin
jahar katsina ce wacce akafi sani da
nurul in tafe take cikin sabuwar motarta
qirar hummer jeep tafe take sannu a hankali kasancewar bajin dadin garin
take ba. Qira,ar abdurrahman sudes ce
ke tashi a. Cikin motar sannu a hankali ta
shgo cikin wata yar kyakkyawar anguwa
inda wasu danqara danqaran gidaje
sukai mata qawanya Adaidai wani wawakeken gate taja ta
tsaya horn daya tayi saiga sojojin dake
gadin gidan sun taso a hanzarce suna
kokawar bude gate din tadan sauke
gilashin motar a hankali a lokacin da take
kunna kan motar ciki Sannu da zuwa hajia barka da dawowa
hannu kawai ta iya daga musu. Ta shge
gdan qatuwar runfar da aka qawata
domin aje motoci ta nufa. Tun daga nesa
ta hango motar mai gdan nata wanda ya
tabbatar mata da ya dawo ta faka motar tata inda ta fito jiki a mace ta bude bayan
motar inda ta janyo qatuwar kot dinta ta
lauyoyi ta sagala sannan ta qara janyo
trabling bag dinta mai dan girma ta nifi
cikin gdan jiki ba kuzari
Ta tsakiyar fulawowi tabi inda zai sadata da. Qofar sitting room din nasu isarta
keda wuya ta latsa wani waje take qofar
ta bude
Wani hadaddaen falone ya baiyana mai
girma kuma hadadden gaske maicin set
din kujeru biyu. Da manyan kayan kallo da senter table
Sai fulawowin qusurwan falon masu
haske kamar lantarki sannan daga gefe
wata na,urace mai kaman fanka wacce
aka cikata da turaren wuta qamshi kawai
yake tashi Ta shiga shikin falon yan yaran dake
zaune akan kafet suna game suka taso a
guje suna oyoyoo momy
Wani farincikine ya ziyarci suciyan nata
ganin yan yaran nata cikin nishadi
Dan autan nata ta daga sama tace ohh my boi u luk so beauty meye sirrinne yace
momy an daddy. Tasa daria daidai
lokacin da takai idonta akan gwarxon
mijin nata. Ta fada kan kujerar dake
fesing din nashi nashi ta sauke yaron
gami da aje kayan dake hannunta a saman kujerar.
Ta janyo yar bebin nata tace come on my
baby zonan naji qamshin jikinki. Ta
zauna saman kujerar tace waya tabamin
kene iye?
Ta zunburo baki tace ba daddy bane yace zai kaini gurin anty mansura kuma
ya qiya ba
Ta kalli mai gdan nata wanda ya dauke
kai saita wutsiyar ido yake kallonta tace
haba abban saif adalci kenan ?
Ya dalla mata harara ta gefen ido wanda ya sanyata yin wani lallausan murmushi
tace jeki abinki my dota da kaina zan
kaiki anjima kinji yar ta daka tsalle
tanama dad din nata gwalo yace ai
bazata kaiki shan ice creen ba. Tai saurin
kallon momyn nata tace wai momy hakane
Tace kyaleshi duk inda kikeso zan kaiki
yanxu dai jeki gurinsu anty insiyyah kice
su kawomin abinci inci dan yunwa nakeji
Tace to momy ai gama na abba can saiki
fara ci kafin na kawo miki Tace to saif wanda ya taye ruwan cikinta
sai surutu yace ta saukeshi yasa kuka
tace dota dan allah tafi dashi wlh a
gajiye nake
Sannan ne dan mulkin mijin nata yace
ajiye mata shi. Nur. Uwar tasu tai saurin miqewa tace wlh na gaji abban saif bari
naje na watsa ruwA ya bita da harara
yace baki gajiba zaki gaji tunda ke bamai
jin magana bace
Ki barmu a gida tun asuba muda yara
munata kewarki amman ke ko oho. Ta shige bangarenta tana fadin kai abban
saif kaidai kullun mita dai mita dai
Tana isa dakinta ta cire kayan jikinta
duka ta daura tawul ta wuce bath room
dinta ta wanke jikinta tas tsawan mintina
shabiyar sannan ta kammala kwalliyar da take dawowa falon datai taga bata
ganshiba tasan yana bangarensa sai
kawai ta wuce dinnin table ta cika cikinta
da abinci dan daman tun tea din safe
bata samu ta qara sa komai a cikinta ba
Bayan ta gamane ta nufi dakin mai gdan nata gashinshi tai zaune akan gadonsa
yana latse latsen laptop. Da sallama ta
shga dakin kallo daya yai mata ya dauke
kansa. Tayi wani murmushi. Saman
gadon ta haye ta kwanta akan bayansa
tana fadin wash allah na gaji da yawa abban saif dan allah kaimin tausa
Bai tanka mataba kuma bai tureta a jikin
nasa ba ta tabbatar da fushin dai yake da
ita sosai. Ta sauko daga kan bayan nasa
ta rarrafo gabansa ta kalleshi taga fuskar
nasa ba yabo ba fallasa duk da bai dauke kansa daga kan laptop dinba
Hakan yasa ta rufe laptop din tana fadin
lfy dai mai gidana laifin me nayi
Tashi yai bai tanka mataba da sauri
itama ta sauka ta tari gabansa. Ta duqa
gami da riqe hannayensa Tana fadin tuba nake my dear kaimin ko wane irin
horo amman karka horani da shirunka.
Tace please kaji tausayina dan allah.
Yaddah take maganar makar zatai kuka
tausayi ta bashi ya duqa ya riqota. Yana
fadar Kin rainani tawan kinamin yadda kikeso
ace kin tafi aiki tun qarfe bakwai ba zaki
dawoba sai shiddah saura wanne irin
aikine wannan
Keda albashin naki ba amfananki yakeba
dakin karbeshi a take kike kyauta dashi. Baki nemi komai kin rasa ba. To meye na
neman aikinnan sai kace na neman zuwa
lahira
Tace dear taimakofa nakeyi na yan,uwa
musulmi musamman mata wadanda
maza ke zalunta. Tunda dai yanxu maza sun zama abinda suka zama.
Ya kuma hatsala yanajin aibanta mazan
da take dan sai yakeji tamkar dashi take
ya kufula yace
Inaso ki sani inda za,a hada mata irinki
dari wadanda zasu ringabin qaidin maza akan abinda sukema mata. To bazasu
taba cin nasara bin hanyar ba. Basuma
santa ba dan WATA SHARI,AR SAI DAI
ALLAH
Miqewa tayi ta shga jikinsa ta kwanta.
Gamida lumshe idanu tace maza kuna kwararmu
Tace insha allahu saina kwatoma duk
wata mai haqqi haqqinta
Juriyarsa ta qare baimasan inda fushin
nasa ya shgaba ya qara matseta sosai
ajikin nashi Cikin wata murya mai laushi yace duk
sanda maza suka gaji suka damko ki kya
gane suma din ba kwallon yadawa bane
Ta ta murmusa gamida qara langwabewa
a jikin nashi tace bana karaya tunda
inada kai a kusa dani. Ya lakace mata hanci yace ni ba ruwana
tunda harni ba,a kyaleba tace kai abban
saif yaushe——
Ya rufe mata baki ta hanya hada bakinta
da nashi ta maida masa da kyautar daya
bata dan tasan abinda yaketama fushi kenan
Sun farantawa juna sosai tana kwance a
jinkinsa tana wasa da lallausan
gashindake jikinsa tace abban saif
Ba tare da ya bude idanuwaba yace
inajinki Tace wallah wata mata aka kawo qara a
kotu gunin ban tausayi wai mijinta ke
qararsa kumafa tun baida komai ya
aureta
Kusanma iyayentane ke daukar
dawainiyar su kasancewar babanta malamin allo ne yanada dan rufin
asirinsa kwasam rannan sai wani mai
neman takarar zama sanata yaxo gurin
wannan malami mai suna abdulrazak na
allah akan ya tayashi da addu,a akan
abinda yake nema. Daya tashi tafiyane yace yanason malam ya kira masa
yayansa wadanda sukai makarantar
boko. Malamin yace aishi baida yaya
amman yanada zakiru cikin dalibansa
dan har digree yayi dan yanxu hakama
yarsa yake aura me neman takararnan yace a kira masa shi ya nema masa aiki
Yana diban albashi mai tsoka amman ko
kadan bai taimakama wannan malami
ballantana yar tasa da yake aure. Kuma
da wannan mutumi yaci zaben bai manta
dashiba dan duk wasu yan kwangida yana bashi da nufin idan ya samu ya
dinga taimakama wannan tsohon
malamin amman ina yaronnan saidai ya
riqe ya cika aljihunsa kawai kwarar dubu
bai iya bama malamin balle yarsa da
yake aure. Saima matsin da yanxu yafi nada. Kwasam rannan sai sanata ya
bashi wata kwangila yaga tayi kyau aiko
sai ya qara mashi ta miliyoyin gaske
DUNIYA INA ZAKI DA MU
Kawai saiya tattara yanasa yanasa yabar
qasar ga cikin da yabar matarsa dashi yaje can qasar waje ya tare abinsa ya
samu wata baturiya ya aura sukaci gaba
da rayuwarsu
Tsawan shekaru ashirin wanda har matar
tasa yar malaminnan ta haife wannan
yaron daya barta da cikinsa ta dauki dawainiyar shayar dashi da karatunsa.
Harya girma ya zama saurayi
RASHIN KUNYAR DA NAMIJI
Wai sai gashi kwatsam waita bashi
dansa
Ira kuma tace batasan wannan ba rigima ta kaure shene ya kaisu harga zuwa kotu.
Harda daukar lauya ita kuma wannan
mata nata da lauya dan ba kudine da
itaba dan alokacinma abinda zasuci dan
natane ke fita yana nemo musu
Yaron shike taimaka mata da abubuwa masu yawa amman wai yakeson ya
daukeshi ya maidashi can qasar da yake
zaune dan kawai wai wacce matar tashi
bata taba haihuwa ba. Ita kuwa tace bai
isa ba ni kuma bayan na gama kes din
wata shari,ar saiga wannan kasanni daman akwaini da daukar aradu daka
nafa nace nine lauyar mai kare wacce
ake qara nanfa Akaci gaba da
gwagwarmaya wanda shine ya kaimu har
yamman daga qarshe dai naci sa!ar
kwatarma wannan mata haqqinta kuma nacema wannan yaron indai harya gana
service dinsa to yaxomin da takardunsa
ni zan nema masa aiki a duk inda
yakeson
Ya bude idonsa ahankali a inda yake
qara kallon kyakkyawar fuskar matar tasa yace shi wani sonta ne ke qara fisgarshi
yace shiyasa ko nayi niyyar hanaki
wannan aikin sai kuma na tuno ga irin
taimakonki ga talakawa
A dole nake kyaleki
Yace amman baby dan allah ki daina mantawa damu dan dani har yara muna
buqatar dumin jikinki
Tana murmushi tana shafar. Fuskarsa
tace an gama my love I love u so much
Tace abban saif ina farincikin
kasancewarka masoyi gareni Tabbas ya zamamin abin alfahari zabin
abbana a gareni
Wanda a farko ya jefani cikin tsananin
rayuwa. Da duhun duniya.
A yanxu kuwa yake shayar dani giyar
soyayyar da babu irinta na gode abban saif”
Miqewa yayi ba tare daya tanka mata ba
domin abin na masa ciwo a duk lokacin
data tuno mishi da abinda ya wuce. A
tsakaninsu yace a ransa mai yasa takeda
riqo ne yadanja tsaki sannan ya fada toilet
Ta miqe tana. Tana murmushi dan
bataga aibun damuwa dan tana tado da
abinda ya wuce ba
Wanda yin hakan tana ganin shine zai
iya sawa su gane suna cikin wata irin rayuwa mai matuqar dadi wanda basu
samuba a baya
Sannan su godema allah daya fitar dasu
daga cikin qangin rayuwar da suka samu
kansu. a da
Ta fice daga bangaren ta nufi wata qofa wacce ta fitar da ita wani bangare da
filine babba da kayan wasa na yara
bulawowi da kuma swiiming pool kayan
wasane kala kala a wajen ga fulawowi
wurin dai ya qawatu
Tana isowa wajen ta kwalama yaran kira nur tayo kanta tace momy naxo falo ban
gankiba kina wajen abba ne ko.
Ta sureya yana fadin me zaki bani. Baby
na ? Insiyyah ta fito tare da saif sai bon
boi a bayanta yana tafe yana cilla ball
sama yana cabewa har suka qaraso gabanta
Insiyyah tace momy tyme din sallah yayi
ko tace eh insiyyah go on tyme yayi
Bon boi yarone dan shekara goma ya
zumbura baki yace kai momy tyme fa bai
cikaba Ta janyo kunsansa tana murdawa tace
wannan meye tace dan gdanku ka
kiyayenifa dan naga kana wasa da ibada
ta jashi sukai cikin yaran ya fara kuka
yana fadin kiyi haquri momy bazan qara
ba tace to muje abbanku na jiranmu sallah sukai abban nasu ne liman bon boi
ladan bayan sun idar
Yai musu tambayoyi akan addini daidai
da fahimtarsa suka bashi amsar wasu
wadanda basu saniba kuma ya tunasar
dasu °°° °°°
Namij indai ba ubana bane allah yasa ya
shiga uku. Namiji bala’I. Namiji masifa.
Namiji abin amai dandai zucia taqi tashi
namiji ya cuceni ya rabani da uwata ya
rabani da ubana ya rabani da kowa nawa namiji ya sakani a cikin bala,I da masifan
da babu mai iya fiddo dani
Na tsani namiji ko yaya yake kai nida
za,a ban bindiga da zan kuma inada hali
da sAina kashe duk mazan dake dunia
kowama ya huta ya zamo babu sauran maza a dunia kowama ya huta
NIDA NAMIJI ai WATA SHARI,AR.
SAIDAI ALLAH
Allah ya isa tsakanina da namiji
Allah kabimin haqqina…………..