WASU MAZAN BOOK 1 CHAPTER 3 BY EL’LADAN

WASU MAZAN BOOK 1 CHAPTER 3 BY EL’LADAN

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Wani irin kuka ta saka mai sauti tana

fadin na shiga uku ni zahra Wayyo allah na

Kuka take tamkar wacce aka aikoma da mutuwa. Ta Miqe ta fara hada kayanta cikin wata yar qaramar akwati Ta cika tab da kaya

Wani gilas baqi ta saka a cikin idanun

nata dan sbd hawayen da sukaqi tsayawa a idon nata Ta kama hanya ta fice daga falon saif

yana wajen insiyyah wacce take ta turashi a cikin motar wasan yara

Yana ganinta yace momi ina zuwa?

anguwa? Ta daukeshi tana fadin kayi haquri kaji saif ba dadewa zanyiba ga anty insiyya nan

Bai wani damu ba dan daman shi

Yafı sabawa da insiyar akan momy tasa

tunda ita ba samun lokacins take ba Dukda gilas din data saka haka bai hana insiyah gane kukan da umman tata tai ba

Cikin tsananin ladabi da kulawa tace

momy kamar kuka kike?

Tai saurin kallon yai tata tace a,a

insiyyah ba kuka naiba idanunane kemin ciwo

Tadanyi jim kafın tace to momy na baki

magani?

Tace bani insiyyah ai daman ke

malamata ce

Malamin islamiyyarmu yace idan kana ciwon ido ka samu zamzam

Ka zuba a hannunka na dama saika karanta. Bismillah daya fatiha uku

Ka sake bismilla ka karanta nas uku falak

uku ka tofa sannan ka wanke fuskarka

dashin Yace in allah ya yarda indai mutun yai

haka

Bada jimawa ba idanun nasa zai warware ya washe yai sarai

Ta shafi kan yar tata tace na gode

insiyyah shiyasa nake sonki fiye da kowa a cikin yayana

izzati

Nasan kedin wata baiwa ce daga rabbi

Yarinyar tai murmushin jin dadi game da yabonda mahaifiyar tata tai mata

Ta amshi saif din tana saikin dawo allah ya kiyaye

Harta kusa fita ta jiyo muryar yar tata tana ki dawo da wuri momy karki rasa sallah

Tace to shikenan babyna

A harabar gidan masu kula da ita harsu shida uku nata uku na mijinta suka

kewayeta sai sojoji biyu daya shike jigilar

yaran daya kuma mai gadi ne sai kuma sauran masu aiki

Tana qarasowa suka taso da sauri daya

ya karbi akwatin dake hannunta daya ya bude mata mota ta shga dreba yaja motar sauran escot din suka rufa musu

baya

Tuni masu gadi suka bude tangamemen gate din suka fice

Tun daga baki bakin gidan sojojine kawai da yan sanda ko wanne ya dana bindiga sai mazurai yake

Zahra. Ta rage gilashin motar danta

samu damar amsa gaisuwar da suke

mata

Dayake macace ita maison jama,a marar girman kai

Cikin gidanma har yafi wajensa tsaro

tabbas duk taurin ranka

idan ka shgo gidan shugaban qasa dole

ka tsorata

Musamman baqaqen sojojin dake saman wata bene duk sun dana bindiga

Sai mazurai suke

Daya ya kalli gabas daya arewa daya

kudu daya yamma

Duk kakin dake qasar nan to akwaishi a

gidan na shugaban qasa kusanma duk sune ma, aikatan gidan

Batun ince zan tsara yanayin gda ba

abune mai yuwuwa ba dan ko a

qasashen waje samun gda mai tsaruwan

wannan sai an tona ta fece gudu gudu

sauri sauri a tsaitsaye take amsa gaisuwar mutanen daketa gaisheta dan

kyautarma data saba yi musu bata samu

daman yin musun ba

Ta wuce faluka da kusurwan gidan kusan nawa kafin ta qaraso wata yar qaramar

hanya data sadata da wanni kanfacecen falo sannan hannunta na hagu wani saurayin benene wanda ba kowa ke

hawansaba dan sojojin dake gadin

benen sunfi goma ta haye suna mata

sannu da zuwa hannu kawai ta iya daga

musu Da gudu ta qarasa saman benen inda ya

sadata da katafaren falon dadin nata

bayanan saitai saurin nufa dakinsa ta

kwankwasa yakai sau uku sannan akace

Who is knocking ? ta amsa nice daddy

Kafınma ta ida ya gane muryar yar lelen tasa yace shigo yar leleta akan wata lumtsatstsiyar kujera ta ganshi ga

jaridunan birjik a gabansa yana dubawa

Ganin daddyn nata yasata fashewa da

kuka da sauri tai masauki a jikinsa Yana fadar Ify maman meya tabamin kene iye?

Yi shiru ki fadamin

Tadan tsagaita da kukan ba tare da hawayen sun daina zubaba tace ina yini daddy

A qagare yace ba wannan na tambayekiba mamana cewa nai ki fadamin abinda ke damunki Kinga kin tayarmin da hankali fadamin

abinda ke faruwa

Tace daddy wai abban saif ne ya matsa a dole saina aje aikina Dan naqi ajiyewa kuma…….

Ta kasa qarasawa Dan batasan yadda zai dauki lamarinba

idan tace yana kawo mata gdan Dan kamar ta tona asirine tayima kanta

tunda ta tona abinda yake boye Daddyn nata ya katseta yace kuma me

maman? Kuma shinema yau yace wai na daina

xuwa aikin ta qara fashewa da kuka

Daddyn nata ya qara janta jikinsa yana bubbuga bayanta yanacewa Am sorry mamana

Karki damu kinji zankirashi yanxu

dolenshi yabarki kici gaba da zuwa

aikinki danme zai takuraki bayan shi

babu wanda ya takura masa Yace yi shiru aiki kam kaman kinci gaba ne

Ta share hawayenta bakinta na qaqaro wata yar guntuwar murmushi

Tace na gode daddy na cikin jin dadi da

nuna kulawar yar lelen nashi

Yace ina amarena kin barominsu a gda ko

Tace daddy ai nur tace ta sakeka insiyyah ce kawai tace tanayi wai itama

tayi yaji sai kazo biko

Yasa daria yace kice mata idan ta gama yajin ta hada da attarugu tayi gaba danni yanxu bana yayinta.

Tasa daria tana fadar kai daddy insiyyah

fa yar gidanka ce me zakai da nur sarkin

tsiwa

Yace itama na fasa sabuwar mata nakeso akawomin shiyasa Na fara kama qafa tun yanxu tasa daria

tana kai daddy abin harda tsokana

Shima dariar yake dan yar lelen tasa tana

birgeshi

Baison ganinta a cikin damuwa ko

yayane dan farincikinta shine nasa ya janyo jaridarsa yaci gaba da dubawa kai tsaye dakin momyn nata ta nufa

Tana bude labulen dakin ta hangosu. momyn tatace da kuma baban saif din a

zaune

Yana qasan cafet ita kuma ta harde a saman kujera

First lady kenan gaban zahran yai

mummunan faduwa tai saurin komawa

momyn tata tace ina zaki yar nemannan dawo kizo nan yanayuin yanayin yanda

taga tadan tsorantanne yaso yabama maman tata daria amman saita daure

danba wasa a. Fuskar tata ta dawo ta

zumbura baki tana kunkuni sallamarma ciki ciki tayi tace gani momy

Tace waye ya baki izinin fitowa daga

gidankki ba tare da iznin wanda ya ajekiba? Meye dalilinki da kuma hujjar datasa kike

jayayyah da mijinki?

Tace kiji tsoran allah fa kibi mijinki ki tunafa zaki mutu ki koma gaban

mahaliccinki ki dogara ga mijinki wlh in kuma ba hakaba to zakixo a banza ki koma a

banza

Nafa ta dinga mata fada da nasiha masu

tsuma xucia

Itadai duqar da kanta tai tana kuka marar sauti Dan basuma luraba saidata dago tace to

nidame na rageshi

Meye bana masa in akwai saiya fadamin

koko taimakon

Daman yana zama laifi ne Momy tace wane irin taimako kuma? Saida ta tsagaita da sheshsheqar kukan

sannan tace aikina ai taimakon masu

Rauni ne mutane nawa suke zube a cikin

Duniya maza sun zaluncesu sbd talauci

da kuma rauni sunaji suna gani suka qale Damme ni allah ya hore min zan

xuba ido

ina kallo ana dannema mai haqqi

haqqinsa.

MAZAN aure suna cutar da matayensy

MATASA suna zalumtar yan mata

MAZA suna keta haddin mata Suci amanarsu a cikin dukiyarsu suci

amanar auratayyah suci amanar

soyayyah suci amanarsu a kasuwanci Su kuma mata sunada rauni ba ko wacce

macece zata iya kwatoma kanta

haqqintaba Tace dole insa qarfina da dukiyata in

kwatoma mata haqqinsu indai ina raye

Ta gama maganar tana goge hawayen

da suka bata mata fuska

Momyn tata ta girgiza kai tace zahra

Su kuma mata sunada rauni ba ko wacce

macece zata iya kwatoma kanta haqqintaba Tace dole insa qarfina da dukiyata in

kwatoma mata haqqinsu indai ina raye

Ta gama maganar tana goge hawayen da suka bata mata fuska

Momyn tata ta girgiza kai tace zahra

kenan har yanxu yarinta na damunki Ai duk kwazonki bazaki iya cin nasaraba

tunda baki tsaya tsakaninki da allah ba

Baki da lada wajen allah tunda kika bar farillah kika kama nafila

Ai wata shari,ar saidai allah shine kadai zai iya warware abinda ke boye Da abinda ke cikin duhu

Kuma bari kiji ai suma

MATAN ba kwallon yadawa bane bane

dan WATA MACEN…….

Saidai allah.

Ki sakki qarya ki kama gaskia zahra ki fita daga cikin duhu ki dawo cikin haske Dan idan wasu MAZAN sun jefaki cikin

matsala to wasu mazan cikin farin ciki

zasu saki marar misultuwa

Ta qara marairaice murya tace momy

maza sun sani a cikin bala’in da bazai iya misultuwaba takaiga har idan naga

NAMIJI koda yaro ne sai naji gabana ya

fadi

MAZA abin tsoro ne duk macen

Data kama da namiji tana tunanin ta kama dahir Ina tunatar da ita tayi kamun kazar

kukune

Ni NAMIJI. Allah daya kawai zaicemin na

yarda dashi

Momyn nata tace ke kinci gdanku

WASU MAZAN zakice Hmmm lol zahra kenan

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE