WATA SHARI’A CHAPTER 10
WATA SHARI’A
CHAPTER 10
Washe gari ta kama ranar lahadi babu aiki, Hakan yasa da sassafe Sultana ta gyara gidanta ta bad’e ko’ina da kamshi, D’akin su Hafsa ta shiga ta samu Haydar baya nan sai Hafsa kwance a gadonta, hakan ya tabbatar mata da yana d’akin Safiyya.
Kai tsaye d’akin Safiyya ta nufa, Ta samu Haydar zaune bisa cinyar Safiyya sai zuba mata surutu yake ita kuma tana dariya. Ganin Sultana yasa Safiyya ta sauke Haydar daga kan cinyarta ta tsuguna har k’asa tace “Ina kwana momy?”. Da fara’ah Sultana ta amsa da
“Laflya kalau Safiyya, an tashi lafiya?”,
“Laflya Aunty, ya gajiya?”,
“Ba gajiya, naje dakin su Haydar ne na samu bayanan, na tabbatarda nan yayo”,
“Ehh kuwa nan yayo kam, cikin magagin barci ma yazo, Haydar” ta miyarda kallonta ga Haydar.
Hakan yasa ya fahimci inda ta dosa, “Good morning momy” ya fad’a bayan ya duk’a har k’asa.
“Morning my boy, ka tashi lafiya?”,
“Lafiya momyna” ya bata amsa yanayi yana wasa da warwaron hannun Safiyya.
“My boy anyi sallah kuwa?”, “Ehh momy Aunty Safiyya tasa nayi”, “0k muje ayi wanka” ta d’aukeshi suka tafl d’akinsu.
Tashin Hafsa tayi tayi sallah kafin ta gama har Sultana ta gama shirya Haydar.
Bayan ta gama shiryasu duka ta fita parlor, dama kuma ta gama had’a break fast tun tashinta daga bacci,
Koda ta shiga d’akin Umarta tayarya tashi shima harya shirya,
Murmushi k’unshe a fuskarta tace
“Barka da tashi mai gidana na kaina”.
Murmushin ya mata shima yace
“Yauwa ‘yar aljannah, kin tashi lafiya?”,
“Laflya k’alau honey, break fast is ready, kai kawai mukejira”,
“Alright wifey, idan mun gama akwai maganar da nake so muyi dake”, “0k ba damuwa”. Suka fita daga d’akin tare da nufar dining area.
Bayan sunyi nat Umar yace “Maganar jiyan nan ce, so inaga kamar ya kamata mu koma gidan tare dake, saboda akwai ‘yan tambayoyin da nake so na masu kafin mu shigar da maganar kotu, saboda a
tunanina ba zamusha wata wahala ba a wannan shari’ar”.
“Hakane honey, na shirya muje kawai, amma kumajiya nama su Hafsa laifl, ina so muje tare dasu daga can mu wuce yawo dan in kankare laifina” ta fad’a bayan ta kalli Hafsa ta saki murmushi.
“0k muje?” Ya tambayeta “Ehh muje” ta shiga dakin Safiyya, Abunda zata dafa na rana ta shaida mata sannan ta fito da sauri saboda su Haydar har sun fita parking area ita kawai sukejira.
Kai tsaye gidansu Ummimah suka dosa, A kofargida Umarya tsaya bai shiga ba, sai Hafsa da Haydar ma a cikin mota basu fito ba, Sallamah tayi tare dajinkirtawa har saida aka amsa sallamar.
Kamarjiya ta samu Ummimah tayi tagumi saidai kuma yau babu hawaye, amma kuma kallo d’aya za’a mata a fahimci tsantsar tashin hankali a tattare da ita, Bayan sun gaisa ne tace “Tare nake da mai gidana, Barrister Umar Mohd Bashir”, “Ki shigo dashi ciki mana Sultana” Mama ta fad’a had’e da d’an guntun murmushi.
Fita tayi kuwa babu jimawa sai gasu sun taho harda su Hafsa, Bayan sun shiga ciki Umarya gaishe da Mama ta amsa cikin dattako, Ummimah ma ta gaisheshi bayan ta saka hijabinta,
Ruwa ta kawo masu a tasa mai fadi sannan ta koma mazauninta ta zauna.
D’aukar ruwan Umar yayi yasha kad’an sannan ya ajiye.
“Mama na samu bayanin duk halin da kuke ciki kuma mun d’auki alwashi nida matata insha Allahu zamu taimakeku, kuma da yardar Allah zamuyi nasarah, nazo ne saboda akwai bayanin da nake so na samu daga bakin Aishatu, saboda gobe Monday nake son
shigar da maganar kotu”.
“To babu damuwa Umar, muna saurarenka” Mama ta fad’a bayan ta sauke hannunta daga tagumin da tayi ta fuskanceshi.
“Ummimah tambayarki zanyi, A lokacin da aka kaiki asibiti karo na biyu, kin saurari wani bayani daga bakun Dr. Rafiq?”.
Ajiyarzuciya ta sauke tare da fad’in “Ban saurareshi ba gaskiya, saboda baya da abunda zai fad’a min in yarda dashi duk da
insisting da yayi akan lallai sai ya fad’a min amma ban yarda ba”.
“Kinyi kuskure Ummimah, da kin sani ki saurareshi sai kiji abunda zai fad’a miki, kinga k0 nan da mun samu wata hujja, amma babu komai, shi Dr. Rafiq d’in d’an can Jalingo d’in ne?”,
“Wallahi ban sani ba, na dai san wata private hospital ce yake aiki, kuma da alama tasuce shida abokin aikinshi Dr. Khalid”,
“To yanzu kuna ganin Dr. Rafiq zai iya saurarena idan na sameshi da maganar?”,
“Bazan iya ganewa ba, saboda na kula Dr. Rafiq munafuki ne, yanada canja magana, kaga dai daga farko ga yanda mukayi dashi, daga k’arshe kuma wai daga asibitin takardar shaidar zubarmin da ciki tazo, kaga kuwa ai babu gaskiya”. ’
Kallon Ummimah yayi a karo na farko tare da sauke ajiyar zuciya, “Zan sameshi zamuyi magana dashi, insha Allahu nasan zamuyi nasarah”,
“To shikenan Uncle Allah ya tabbatar da hakan” “Ameen” duka suka fad’a. Sultana tace
“To yanzu ya za’ayi asan address na asibitin?”,
“Sunan asibitin KADRAQ CLINIC, ba zatayi wahalar ganewa ba, batada nisa da Talent University”,
“0k good” Umarya fad’a bayan ya mik’e tsaye yama su Sultana nuni da su tashi su tafi.
Bankwana sukayi sannan suka fita cike da tausayin rayuwar su Ummimah.
Royal bakeries duka zarce daga can, suka kwashi ice cream kala kala da chocolates masu yawan gaske sannan Umarya biya kud’in suka nufi hanyar fita. Suna fita sukaci karo da wasu matasa su biyu a buge da gani sunsha sunyi tatul, Kallo Sultana da Umar duka bisu dashi, “Waiku ya akayi kuke kallonmu ne? Ko kun sanmu ne?” D’aya daga cikin ‘yan mayen ya fad’a cikin maganarsu ta ‘yan maye. D’ayan ma yace “Sai kallonku sukeyi hehe, ga katina ka d’aukeni aiki kaji?” Ya mik’awa Umar complimentry card d’inshi. Da k’arfi d’ayan yaja hannun abokinshi suka k’arisa cikin restaurant d’in, Bin katin da kallo Umaryayi, Degree holder ne kyakkyawa dashi a hoton dakejiki,
Ga phone number a jiki da address d’inshi.
“Rayuwa kenan, Allah ya shirya mana zuri’ah, kinga wannan matashi gashi da iliminsa amma ya kama sana’ar shaye shaye duk ya wulakanta rayuwarsa” Umar ya fad’a cike da tausayi yana k’ara kallon katin.
“wallahi kuwa honey, Allah dai ya shirya, kawo katin in gani” ta mik’a hannunta ta karb’i complimentry card d’in matashin.
“Sulaiman Usman Saraki” ta furta bayan ta kalli katin, “To shi a tunaninshi idan ma d’aukar aikin ne sai a rasa wanda za’a d’auka saishi? Duk mutanen kirkin nan dake neman aiki saishine za’a bama aiki?”, “Wallahi kuwa, mu tafi su Hafsa har sun gaji da tsayuwa” suka isa inda su ka ajiye motarsu, Purse d‘inta ta bud’e ta jefa card d‘in sannan suka kama hanyar gida.
Har suka isa gida basu daina mamakin ‘yan shaye shayen nan ba, suna k’ara tausaya masu.
“To yanzu honey ya kake ganin za’ayi? Zamu fara shigar da maganar kotu ne sannan kaje wurin likitan ko kuwa?” Sultana ta tambayi Umar.
“Nafi so mu fara shigar da maganar har sammaci akaima su Salmah sannan in fara duk
wani bincike” ya bata amsa.
Kamar Sultana tana son yin magana sai kuma ta fasa,
Safiyya ta kawo masu abinci sukaci kafin nan la’asartayi ta shirya Hafsa domin zuwa
islamiyya.
Washe gari da sassafe suka kama haramar zuwa aiki kamar yanda suka saba,
Kai tsaya Gobarau academy suka zarce sukayi dropping d’in Hafsa sannan suka wuce nasu aikin.
Kasantuwar weekend akayi aiki ya taru masu sosai a Office musamman ma Umar, hakan yasa bai shigar da maganar ba sai washe gari,
Safiyar talata kam babu b‘ata lokaci ya shigar da case d’in su Ummimah, aka kuma ce nan da sati d’aya za’a shiga kotu.
Sosai Sultana taji dad‘i ta kuma shirya ta tafi gidan su Ummimah dan ta shaida masu halin da ake ciki.
Masinjan kotu aka aika gidansu Gentle dan yakai sammaci, saboda koda aka fad’i
sunanta da sunan iyayenta kowa ya ganeta, saboda babanta sananne ne sosai kuma yanzu haka ya fito takarar d’an majalissar tarayya.
Kai tsaye gidan Alhaji Abu Abu ya dosa, Sallamah yayi a tangamemen gate d’in gidan amma shiru ba’a amsa ba,
Saida yayi sallamah sau uku sannan mai gadin gidan ya fito yana taunar asuwaki, Hannu masinjan ya bashi suka gaisa sannan yace “Meke tafe dakai bawan Allah?”,
“Sak’o ne daga kotu, sammaci ne akace a kawowa masu gidan nan”.
Cike da mamaki mai gadin ya karbi takardar, “Sammacin?” Ya tambayeshi.
“Ehh sammaci ne, dan Allah a tabbatar da anbawa masu gidan wannan takardar” masinjan ya fad’a tare da juyawa ya tafl.
Kai kawai mai gadin ya kad’a sannan ya zarce cikin gidan domin ya basu takardar.
Bayan yayi sallamah yaga Ladi mai aiki tana mopping, mik’a mata takardaryayi yace ‘ta bama yallab’ai’ sannan ya tafi.
Saida suka fito karyawa sannan tace
“Hajia wai ga wannan mai gadi ya kawo yace a bama yallabai”, Bayan ta karb’a tace
“Alhajina gashi”, Murmushi ya mata yace
“Bud’e ki karanto min inji”.
A zahiri kuwa ta karanto cewa ‘sammaci ne daga kotu ankai k’arar ‘yarsu Salmah bisa laifuka da dama’.
“What!?sammaci? ‘Yata aka kai sammaci?”, ltama Hajiyar tsaye ta tashi tace
“Lallai wannan munafurci ne? Salmah dake makaranta abunta hankali kwance shine dan
rainin hankali za’a kaita kara?”,
“Ko tantama babu wannan cinne ne daga mak’iyana, suna so inji kunya akan takarar da
zanyi ne”, “Kaga wai Aisha Abubkar sukayi k’ararta, ga sunan nan ajiki” Momy’n Gentle ta fad’a
bayan ta mik’a takardar cike da mamakin wannan al’amarin. Karb’a yayi yace “Wacece wannan? Aisha?” Tun bai rufe bakinshi ba momy tayi caraf tace
“Na gane ko wacece, k’awartar nan ce diyar matsiyata ce, saisa tun farko na hanata k’awance da ita amma ta nace lallai sai tayi ita dai tana sonta, wato duk alkhairan da
Salmah ta mata da wannan abun zata saka mata? Lallai d’an adam abun gudu ne”.
Cike da b’acin rai Alhaji yace “Kenan ma ‘yar matsiyata ce ta kai ‘yata k’ara? Lallai kuwa reshe zai kife da mujiya, saboda duk abunda take nuflnta dashi gareta zai koma, wallahi na rantse sai na d’auko
lawyer wanda duk k’asar nan babu kamarshi, sai na nuna masu nafi k’arfisu, su d’in banza!” Ya tofar da yawu bisa center carpet yace
“Sai kun wulak’anta I promised” yajefar da takardar k‘asa.
Mamaki sosai uwar keyi ta d’auki wayarta ta latsa kiran Gentle, bayan ta d’auka ne ta
shaida mata duk abunda ya faru,
Taji tsoro sosai amma a zahiri ta nuna al’ajabinta akan al’amarin,
Harda kukan munafurci tace
“kinga illar talakawa Momy, ba irin maganar da baki fad’a min akan kar inyi k’awance da Ummimah ba amma na nace sai nayi, kinga abunda ta bini dashi ko momy?” Ta k’ara fashewa da kukan munafurci, da haka suka kashe wayar bayan uwar ta shaida mata cewa sati mai zuwa za’a fara zaman kotu, dan haka ta hanzarta dawowa gida saboda babanta yace zai d’auko mata babban lawyer,
Dukda hankalin gentle ya tashi amma sai ta samu sassauci jin lawyer za’a d’aukar mata. ‘
Sosai take mamakin yanda akayi su Ummimah suka samu lawyer wai harma sukayi tunanin kai k’ararta kotu.
Wani shu’umin murmushi tayi tare da furta, “Mugun abunku gareku zai koma maku, wallahi sai kun k’ask’anta, wato na sarara maku
kwana biyu shine zaku d’auki wannan matakin k0? Zakuyi regreting” ta katsa kiran d’aya daga cikin ‘yan iskanta,
Umurtarshi tayi da yaje gidansu Ummimah ya kona baki d’ayanshi, yanda zasu mutu kuma ba za’ayi zargin kowa ba saidai ace gobara ce sukayi,
Da wannan shawarar ta kashe wayarta tana ci gaba da muguwar dariya mai d’auke da ma‘anoni kala kala.
Shi kuwa Umar sosai ya miyar da hankalinshi ga bincike, yaje Jalingo har asibitin su Dr. Rafiq, amma bai sameshi ba kasantuwaryayi tafiya zuwa Lagos, kuma sai nan da sati biyu zai dawo,
Dr. Khalid kawai ya tayar, amma bai tinkareshi da maganar ba yafi so yayi da Dr. Rafiq d‘in, Phone number d’inshi ya karb’a a wurin wata nurse sannan ya juyo zuwa Katsina.
Alhaji Abu Abu kuwa yama commisioner na ‘yan sanda magana an had’ashi da wani Barrister wanda a duk fad’in k’asar nan babu wanda bai sanshi ba,
Ya kware sosai a aikinshi, haka kuma duk shari’ar da zayyi da wasu ba’a winningd’inshi saidai shi yayi winnning mutum,
Baki d’aya karatunshi ma ba’a k’asar nan yayishi ba, hakan yasa yake da experience sosai akan shari’ah, komai rashin gaskiyar mutum indai ya sakoshi a shari’arshi to sai yayi winning.
Sosai Alhajin yaji dad’i saboda yasan yanzu kam asirinshi zai rufu, saboda matuk’ar aka
kama Gentel da laifin da ake zarginta to yasan bazai tab’a samun d’an majalisarjiha da yake nema ba.
Haka Umar ya koma gida ba tare da walwalar kirki ba, sabodajin wai ba yanzu Dr. D’in zai dawo ba, gashi kuma shine kawai hope d’inshi a wannan lokacin, kuma shida dawowa har sai anyi zaman kotu na farko, yasan basuda wani evidence a halin yanzu.
Zama kawai yayi bisa kujera baki d’aya bashida walwala,
Koda Sultana ta ganshi haka tasan akwai matsala,
Inda yake ta zauna tace
“Sannu da dawowa honey, nasan ka gaji muje kayi wanka kaci abinci”, Babu musu kuwa ya tashi yabita,
Ganin a gajiye yake yasa ita da kanta tayi masa wankan,
Bayan sun fito ta fitar masa da k’ananan kaya jeans bak’i da blue shirt,
Fita sukayi ta ringa bashi abinci a baki tana faranta masa rai da labarai masu dad’i,
Saida yayi nat sannan ta goge masa bakinsa da tissue suka koma d’akinta. ‘
Bayan taga ya warware sosai tace “Honey baka samu likitan bane?”, Kallonta yayi yace
“ya akayi kika san haka?”.Murmushi ta sakar masa sannan tace
“Wani abu sai bahaushe, ana tambayarshi shima yana tambayarka”,
Shima murmushin ya sakar mata kafin yace
“wallahi kuwa ban sameshi ba, wai baya nan yaje lagos sai nan da sati biyu zai dawo,
gashi kuma kinga saura kwana biyu mu fara zama kotun, ni yanzu damuwata d’aya zamu
shiga kuma banida evidence ko d’aya”.
Ajiyar zuciya Sultana tayi tare da cewa “Gaskiya kam abun ka damu ne wannan, amma ina ganin ka cire damuwar a ranka, karka
cire hope na smaun nasarah tunda ai nasan ba zama d’aya za’ayi ba, sai ka roka a d‘aga shari’ar har lokacin da zai dawo ku tattauna dashi, kaga duk bayanan da muka samu daga
gareshi nasan zasu amfanemu”, “Ehh hakane wifey, kuma ga lambarshi nan na karb’a so nake sai zuwa dare in kirashi,
saboda nasan ta yiwu yanzu he is busy kinsan likitoci, wata k’ila sai dare ne baya komai”, “To abunma ai yazo da sauk’i, kaga sai kayi magana dashi a waya ka masa bayanin komai, insha Allahu nasan zai taimaka mana sosai, Kuma saida ka tafi na tuna da k’awayen nan nata guda biyu, suma zasuyi amfani garemu, ina so inje gidan su Ummimah d’in yanzu sai ta kwatanta min inda gidan kawayen nata yake”.
Cikin farin ciki Umar yace
“Good idea, ni ai nama manta da maganar kawayen nata, ehh kije ki samo bayanin inda suke daga bakinta” “0k yanzu zan tafi”,
Umaryace “ni wallahi tunanina d’aya ma karsu d’auko mana lawyer’n da zaifi karflnmu”,
Kallo Sultana tabishi dashi kam tace “Bana son jin haka daga bakinka honey, kana tunanin akwai lawyern da zai gagareka ne?
Kaima fa babbane ko a sahun lawyers”, “Hakane, amma fa dole sai mun dage da addu’ah, saboda bahaushe yace ‘in kanada
kyau ka k’ara da wanka , “Barin tafi dai honey, yamma nayi” ta zira hijabinta har kasa ta d’auki makullin mota ta tafi.
Wasu mutanene fuskokinsu sanye da mask kwayar idonsu kad’ai ake gani,
Lab’e kawai sukeyi suna sand’o dan basa son a gansu,
Dukda dare yayi akwai duhu amma suna tsoron a gansu saboda an gargad’esu akan kar su bari asirinsu ya tonu,
A daidai k’ofar gidansu Ummimah suka tsaya su duka biyar d’in,
D’aya daga cikinsu hannunshi rik’e da wata jarka babba ya ringa yayyafawa a baki d’aya gidan ta waje,
Yana gamawa wani daga cikinsu kuma ya k’yasta ashana,
Take duka gidan ya kama da wuta sosai su kuma suka samu nasarar guduwa.
Wuta keci sosai babu sassauci har baki d’aya cikin gidanma ya d’auka da duk d’akunan, Saida ya kone sosai ne mutane suka fara kawo d’auki, Cike da tausayi aka ringa watsa ruwan omo a ciki amma wutarsai k’ara tashi take,
Kowa sai karkad’a kai yake saboda sun tabbatar da inhar akwai mutane a ciki tofa babu
wanda zai fita da rai, saboda yanda wutar ke tashi sosai duk ta fara cinye katangun dukda na k’asa ne,
Wasu kuka suke sosai wasu sunyi tagumi suna kallon wannan wuta,
Daga ganin wutar cinnata akayi ba wai kamawa tayi da kanta ba, saboda da alama daga waje ta fara ci. Wani mutumi ne yace
“Na tabbatar da matar gidan da ‘yarta suna ciki, nasan kuwa wuta ta cisu sosai, barin shiga ciki ko Allah zaisa in dace” ya fara nad’e kafar hannunshi data wando yana k’ok’arin shiga ciki,
Da sauri wani mutumi ya kamoshi yace
“Kar kayi wannan sayar da ran bawan Allah, kana tunanin akwai mai rai anan ciki ne?”,
Duk mutane suka hanashi shiga saboda sun tabbatar da kowa dake gidan ya mutu saboda katangun da kansu suke fad’uwa tsabar wuta da sukasha.