WATA SHARI’A CHAPTER 12
WATA SHARI’A
CHAPTER 12
Zama tayi a kusa dashi jin wayar da yakeyi, hakan yasa ya kalleta ya mata murmushi
kafin yaci gaba da wayarsa, Ganin wayar bata k’arewa bace yasa Sultana ta mike ta bud’e wardrobe d’inta,
Ta samu kaya wanda zasuma Mama daidai harda supopinta da lasuka masu tsada.
Har ta fita ta kaima Mama kayan ta dawo Umar bai gama wayar ba, Kwanciya tayi akan k’irjinsa tana wasa da ‘yan yatsun hannunta tana kara tuno da gobe
ne fa zasu shiga kotu.
Tashi daga jikin Umar tayi jin ya gama wayar, “Ya kukayi dashi honey?” Ta tambayeshi.
Tashi zaune shina d’in yayi yace “Munyi magana dashi yanada kirki sosai, Ya shaida min cewa sai next week Friday zai dawo, Ya min bayani cewa wallahi shi kanshi baki daya kanshi ya daure da wannan maganar, Saboda yasan ya ajiye takardar asibitin Ummimah wadda ta nunar da cewa fyade aka mata sannan kuma tana dauke da cutar hawanjini. Amma kuma wai daga baya ya nemi takardarya rasa, Saidai wai yaji magana ta fito cewa ciki aka zubar mata, Baki daya ya rasa yanda akayi hakan ta faru kuma yaso ya mata bayani tun a lokacin taki saurarshi, ya rantse ya kuma rantsewa da Allah akan baisan yanda akai hakan ta faru ba, Yadai san daga shi sai abokin aikinshi ne suka san da maganar, kuma abokin aikin nashi shi yasan yanda komai ta kasance, Kuma da zararya nufi abokin aikin nashi da maganar sai ya noke akan baya son maganar, Shidai wai yana zargin Dr. Khalid d’in akan yasan komai ko kuma da hadin hannunshi a wannan maganar, Amma yamin alk’awarin cewa idan ya dawo zai sake tuhumar abokin nashi da maganar ko za’a dace, ya nunar min da farin cikinshi sosai akan tsaya masun da mukayi domin k’watar masu hakk’insu, kuma shima ya tabbatar min da zai bada gudummawa d’ari bisa d’ari dan ganin mun samu nasarah”. “
Cikin farin ciki Sultana tace “Allah sarki ashe mutumin kirki ne, shi,isa akeso idan mutum yace ka saurareshi to ka saurareshi d’in, gashi kuwa gaskiya ta fito, Ni kaina ina zargin wancan likitan, to idan bashi ba waye zayyi haka? Su biyu ne kawai suka san halinda ake ciki”, “Hakane wifey, dare nayi mu kwanta kinga gobe sammakon fita zamuyi”, “0k dear” ta fad’a tare da mikewa ta kashe wutar d’akin.
‘KOTU“
Kotu ta cika makil wasu na kara shigowa wasu kuwa fita sukeyi saboda rashin halartar alk’ali, Tsabar cika da kotun tayi yasa har wasu basu samu wurin zama ba saidai a tsaye suke.
Shigowar alk’ali ne yasa kowa ya natsu akayi shiru har lokacin daya isa mazauninsa ya zauna.
Daga can gefe na hangi Mama da Ummimah sunyi zuru zuru hankalinsu ya kara tashi dan suna matukarjin tsoron ganin idon mutane ace wai dukyawansu sai sun tashi sunyi magana cikinsu.
Mai gabatar da kara ne ya tashi yace
“A yau d’aya ga watan d’aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai ne kotu zata fara sauraron k’arar da Aishatu Abubakar ta kawo Salmah Abubakar akan wai tasa an mata fyad’e wanda hakan yayi silar korarta daga makaranta” ya mika File din ga alk’ali tare da rusunawa sannan ya dawo mazauninsa.
Alk’ali ya gyara zaman gilashinsa tare da yin gyaran murya yace “Idan akwai Iauyoyi ko zasu gabatar da kansu?”.
Tashi Umar yayi bayan ya gyara rigarsa yace
“Sunana Barrister Umar Mohd Bashir, a tare dani akwai”,
Sultana tayi saurin mikewa tsaye tace
“Barrister Sultana Saddam Bakori”
“Mune masu kare wadda take kara” Umarya fada sannan suka koma suka zauna.
D’ayan Barristern yace “Sunana Barrister Sa’eed Bebeji, lauya mai kare wadda ake kara” yama Umar shu’umin murmushi sannan ya koma ya zauna.
Alk’ali yace “Lauya mai kare wadda ake kara, ko kanada hujja?”.
Tashi Umar yayi ya fuskanci alk’ali yace “Ehh inada ita ya mai shari’ah”, “Kotu tana son ganin” ya fad’a bayan ya zare gilashinshi.
“Zan iya ganin Salmah Abubakar?” Barr. Umar ya tambaya bayan ya miyar da kallonshi ga sauran mutane.
Cikin daburcewa Gentle ta mike a susuce take taku harta iso inda aka tanadar domin tsayuwar wanda ake tuhuma.
Kusa da ita Umarya matsa ya kalleta cikin ido yace “Kotu zatasojin cikakken sunanki daga bakinki?”,
“Sunana Salmah Abubakar“ ta bashi amsa a takaice. “Salmah kadai? Babu wani lakani da ake miki?”. Cikin in-ina tace
“Ana…ana cemin Gentle”,
“Good malama Gentle, ko zaki fadawa kotu alak’arki da Aisha Abubkar? Ina nufin wadda tayi kararki”,
“Ehh Aisha kawata ce sosai tun a Secondary School, mun shaku sosai da ita hakan yasa harjami’a muka cike daya a JAMB d’inmu kuma course iri daya, tare muke karatu kwatsam naji ance wai an koreta daga makaranta saboda an kamata da case din ta zubar da ciki”.
Har cikin ran Ummimah taji wannan maganar,jin hawaye tayi suna zarya a kumatunta.
“Wane irin yanayi kika shiga a lokacin da kikaji wannan maganar? Ina nufln kin yarda da maganar ko kuwa kin musa?” Ya tambayeta.
“Nayi mamaki sosai, amma kuma daga baya sai na cire mamakin saboda mutanen yanzu abun tsoro ne” Gentle ta bashi amsa.
“To duk yanda kike kawance da ita har baki san tana yawon banza ba? Kuna rabuwa kenan?”,
“Ehh a’a, da dai bamu rabuwa da ita, amma kuma lokaci d’aya ta canja halinta, batada aiki sai yawon banza, idan na mata magana tace babu ruwana da ita, kowa yaji da kansa”.
“kina nufin bakiji damuwa ko kadan ba a lokacin da akace an koreta daga makaranta? Amma a yanda kuke da ita ya kamata ace ko yaya kinyi mamaki saboda ace babbar kawarki wannan al’amarin ya faru da ita abun mamaki ne“.
Cike da gadara Gentle tace “Nikam banji komai ba gaskiya, saboda dama ta dade da canja halinta, kuma ta nuna tafi karfina”, “malama Gentle kuma bakya tunanin ko wasu kawayen ne ta canja yasa ta rabu dake? Saboda kinsan zaman da kuke zaku iya gundurar juna, sannan kuma kina nufin ke kullum kina zaune cikin daki daga can sai School area kawai kike zuwa? Kenan bakya zuwa wurin kowa?”.
“Objection my lord!” Barr. Sa’eed ya fad’a a fusace, “Wannan kuma rayuwarta ce bai shafi shari’armu ba, bai kamata barr. Umaryana yima Salmah irin wannan tambayar ba”.
“Barr. Umar a kiyaye” Alk’ali ya fada bayan yayi rubutu a takarda.
“Malama Gentle ko kinsan wasu kawayen Aishatu masu suna Zarah BB da Rabiatu Sk? Sannan kuma bakya tunanin ko wurinsu ne take zuwa wani lokacin shi,isa bakya ganinta?”,
“Ehh nasan tana dasu, amma ni bansan ko wurinsu take zuwa ba, saboda suma din wani lokaci suna zuwa wurina nemanta idan ta tafi yawon darenta”,
Murmushi kawai Umar yayi saboda a yanayin kalaman dake fita daga bakinta ma kadai ya isa ya tabbatarwa mutum da rashin gaskiyarta.
“Zaki iya komawa ki zauna har sai na sake nemeki nan gaba” Umar ya fada tare da
komawa mazauninsa ya zauna.
“Kafin ta koma ta zauna, k0 Barr. Sa’eed yanada tambayar da zayyima Salmah Abubkar wacce yake karewa a wannan shari’ar?” Alk’ali ya tambaya.
Bayan ya sunkuya kasa yace “Ehh inada ita ya mai shari‘ah” ya matso inda take yace “Salmah inaso ki fad’a mana yanayin alakarki da Aishatu a tak’aice”, “Alak’ata da ita mai karfi ce, saboda gidansu talakawa ne ni kuma gidanmu munada hali sosai, So wani lokacinma ni nake taimaka masu da abunda zasuci a gidama barin a School idan tayi broke, komai nata nice kuma tana nuna minjin dad’in hakan, Amma kuma lokacin data fara canja hali na fahimci har abinci idan na dafa bata ci, bama ta zama barin taci, wani lokaci idan tayi dare zatazo da abincin restaurant mai rai da lafiya taci ko kallon inda nake batayi” Gentle ta sharara karya hankalinta kwance.
“Barin dan miyar dake baya, naji kincema Barr. Umar suma kawayen nata wani lokaci suna zuwa nemanta, hakan ya tabbatar da cewa ba kowane lokaci take tare dasu ba kenan, to kina nufin bataje wurinsu ba kenan suma?”,
“Ehh lallai bataje wurinsu ba kam, tunda inda ace taje wurinsu ai ba zasu zo nemanta inda nake ba”.
“Objection my lord!” Barr. Sultana ta fada bayan ta buga teburi,
“Yanayin yanda suke magana bai kamata ace suna yinta ba ya mai shari’ah! Wannan zai iya zama cin fuska ga wadda take k’ara”.
Jinjina kanshi alk’alin yayi yace “Barr. Sa’eed ka tausasa kalamanka”.
“Iyakacin tambayarda zan mata kenan ya mai shari’ah, ina neman kotu ta bani dama domin kiran Aishatu Abubakar, wato wadda take kara domin akwai tambayoyin da nake so na mata” Barr. Sa’eed ya fad’a hade da sunkuyawa kasa yana kallon alk’ali.
“Kotu tana son ganin Aishatu Abubakar” alk’alin ya fad’a yana kallon ta inda zata fito.
A hankali cike da natsuwa ta taso kanta sadde a kasa ta tsaya inda Gentle ta fita.
Cikin izzah da takama Barr. Sa‘eed yace
“Aishatu shin a cikin kalaman da Salmah tayi ko akwai maganar data fada wadda kike da ja akanta?”,
Da hannunta ta share hawayejikinta ya fara rawa saboda yanda taga an tsura mata ido,
“Ehh…ehh a..akwai” ta fad’a cikin rawar murya.
Murmushi Barr. Sa’eed yayi yace “Ki kwantar da hankalinki ki daina rawae murya indai da gaske kinada gaskiya ba karya zaki fad’a ba“.
“Objection my lord!” Barr. Sultana ta fada k’ufule, “Bai kamata Barr. Sa’eed yana fadin wannan kalaman ga Aishatu ba,ya kamata yayi la’akari da yanayin yawan mutanen wurin nan ne yasa take rawarjiki da rawar murya“, “Barr. Sa’eed a kiyaye” alk’ali ya fada yaci gaba da kallonsu. “uhm, ke nake sauraro” ya fad’a a hankali.
“Kusan duk maganganun data fada karya ne, nasan dai tana yimin wasu abubuwan idan taga inada buk’ata, amma maganar da tace ita ke daukar nauyinmu wallahi karyane, babana bai rageni da komai ba, kusan duk wata ko baya da kud’i sai ya ranta ya turo min, sannan kuma da tace na canja hali wannan duk halayenta ne, babu inda nake zuwa, idan ma na fita daga room d’inmu to bazan wuce room na kusa da namu ba inda kawayena Zara da Rabiatu suke ba”.
“Ina su kawayen naki suke a halin yanzu? Inda gaskene ai ya kamata ace sunzo nam kodan su bada wannan shaidar ga kawarsu”.
Jikin Ummimah ya hau rawa saboda rashin halartar su Rabiatu kotun, tasan ba lallai bane a yarda da maganarta.
“Gamu” Zarah da Rabiatu suka fada daidai lokacin da suka shigo cikin kotun.
Ajiyar zuciya ta sauke farin ciki bayyane a fuskarta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da suka iso inda ake son ganinsu.
Qur’ani aka basu sukayi rantsuwa da zasu fadi gaskiya sannan cikin rashinjin dad’in zuwansu Barr. Sa’eed yace “Kune kawayen nata?”,
“Ehh mune” suka hada baki wurin fad’i.
Baki daya yama rasa tambayar da zayyi masu, saboda sam bayyi tunanin zasuzo ba, dan saida ya tabbatarda babu su a cikin kotun sannan ya nemi yana son ganinsu.
Sai daga baya wata fasaha ta fad’o masa yace
“Wai da gaske wurinku Aishatu take zuwa wani lokaci?”,
“Ehh da gaske wurinmu take zuwa duk lokacin da Gentle ta fita tayi dare, wani lokacin ma a d’akinmu ‘take kwana saboda tace ba zata iya kwana ita kadai ba” Rabiatu ta bashi amsa. Shiru ya d’anyi kafin yace
To idan da gaske ne mesa wani lokacin idan bata d’akinku kuke zuwa ku tambayi Salmah inda Aishatu taje? Kenan hakan ya tabbatarda ba kowane lokaci kuma din kuka san inda take ba”.
Zarah tayi caraf tace So daya ne tak hakan ta kasance, kuma ranar ma ta fita neman Gentle ne akan tazo suyi karatu dan exam d’in da zamuyia washe gari mai wahala ce, tun fitar da tayi shine bata dawo ba har mukaje nemanta room dinsu”.
Kallonshi ya miyar ga alk’ali yace “Ya mai girma mai shari’ah, da wannan bayanin da kawayenta sukayi ya isa ya tabbatarwa kotu da cewa ba kowane lokaci ne take tare da kawayentan da take cewa suna tare always ba, kenan akwai gyara a maganar Aishatu saboda gashi kawayenta sun fada da bakinsu, ta masu karyarzataje ta nemi Salmah domin suyi karatu, amma kuma Salmah ta dawo tace ita batama ga Aishatun ba, wannan ya tabbatar da cewa ta tafi yawo kenan” Ya juya gasu Zarah yace “Zaku iya tafiya ku zauna”.
“Amm kafin su tafi su zauna, ko lauyoyi masu kare wadda take kara sunada tambayar da zasuyi masu?” Alk’ali ya tambaya.
“Ehh akwai ya mai shari’ah” barr. Sultana ta fad’a tare da tasowa cike da natsuwa ta iso inda suke.
“Bayan kun tambayi Salmah inda Aishatu take, zaku iya tuna amsar data baku?”, “Ehh zan iya tunawa,
Saida ta bimu da kallon banza sannan tace ‘idan har bamu kyaleta datambayar inda Aisha take ba wallahi sai ta saka an mana abunda tasa akaima Aisha’, duk da bamu san ko menene ba amma hankalinmu ya tashi, babu yanda muka iya dole muka bar mata dakin baki daya ranmu a dagule yake”.
“Well” Sultana ta fada, “To daga nan ku kuma wane irin mataki kuka d’auka?”. Rabiatu tace
“Babu yanda muka iya duk da tashin hankalin da muka shiga, mun nemeta a duk blocks d’in hostel amma bamu sameta ba, hakan yasa muka koma room d’inmu amma babu wadda ta iya yin bacci a cikinmu,
Washe gari tun gari bai gama wayeba muka fita waje nemanta,
Acan muka tsinceta cikin jini nesa da hostel,
Hankalinmi ya tashi muka d’auketa muka kaita school clinic,
Bayan sun dubata sukace suma ciwonta yafi karfinsu saidai su kaida wata asibiti,
Tare muka tafi da ita ta dad’e bata farfado ba, Likitan daya dubata ya tabbatar mana da fyade ne aka mata kuma an illatata sosai, yace mana ya rubuta a takarda zai bamu mu tafi da ita idan ta samu sauki, Amma kuma sai muka shafa’a, shi bai bamu ba muma kuma mun manta bamu karba ba, Saida aka dawo hutu ne akace wai an koreta, kuma harda gwada mana takardar asibitin anyi amma kuma sab’anin waccan ta farkon wadda bamu san dalilin canzata ba“. Barr. Sultana zata sake magana kenan alk’ali yace
“Kotu zata so ganin likitocin da suka dubata a asbitinsu,
Sannan kuma zataso taga ma’aikatan School clinic dinsu domin su fada mana ‘meyasa sukace ciwonta yafi karfinsu?‘ Saboda ta yiwu su abunda suka gani daban, zamuso jin komai daga bakinsu idan suna kusa”. Cike da ladabi Sultana tace
“Likitan da yayi mata aikin mun bukaceshi da yazo amma kuma yayi tafiya zuwa Lagos, ga wannan takardar” ta mikawa wanda ya gabatarda kara domin ya isar da ita ga alkali,
“Takarda ce wadda ta tabbatar da likitan baya nan, yaje wani course ne amma ya tabbatar da yau saura kwana hudu ya dawo, ranar Friday kenan,
Sannan kuma bamuyi magana da ma’aikatan School clinic d’inba,
Muna rokon kotu mai albarka data daga wannan shari’ar har sai zuwa next week, wanda insha Allahu a ranar ma’aikatan zasuzo, shima kuma likitan kamin nan ya dawo”.
Shiru alk’ali yayi bayan yayi ‘yan rubuce rubuce sannan ya d’ago kanshi yace “Kotu ta d’aga sauraron wannan shari’ar har sai ranar litinin, bakwai ga watan d’aya shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai” Ya buga tuburonshi da guduma tare da fadin “Kooootu!” Yana mikewa kowa ma ya mike
Bayan sun Fita daga kotu ne Gentle ta ringa watsawa Ummimah harara cike da tsana, Zarah da Rabiatu sukayi tsaki tare da fadin “Ta Allah bata mutum ba, kuma insha Allahu sai munyi nasarah,Allah baya goyon bayan azzalumi”.
Kara kufule Gentle sukayi,
Momy’nta taja hannunta da sauri suka tafl dan tasan halin Gentle tsaf zata iya yin dambe dasu a wurin, kuma idan har tayi to mutane zasu tabbatar da cewa da gaske tasa anyima Ummimah fyad’e duk da yanzu ma wasu sun fara gasgatawa.
Kallon Rabiatu Ummimah tayi tace “kawayen kun rufa min asiri sosai da kukazo, inda ace bakuzo ba da bansan yanda zanyi ba, banyi tunanin zakuzo ba gaskiya”. Zarah tace
“Ai dole ne a garemu muzo Ummimah, an cuceki kuma aka nemi a hanaki kuka,
Jiya muna Hostel mukaga text d’in lawyer dinki, ta mana bayanin komai kuma ta nemi in da hali anada bukatarmu a kotu,
Kinsan akwai nisa daga Jalingo zuwa Katsina, tun da sassafe muka taso amma bamu iso
da wuri ba har akayi nisa da shari’ar, Allah yasa daidai muna zuwa mukaji ana nemanmu”.
Ummimah tace “Kuma fa haka kawai na bata number d’inki, saboda kin san yanzu banda waya, A wata takardata ce dana tab’a ajiye number’n sanda zan miki call me back, Lokacin da zamu baro gida na hadata cikinjikarmu, Ashe da rabon zatayi amfani”.
“Aikuwa dai kin gani”. Da wannan firar Sultana ta samesu, Takardar dubu d’aya ta zaro a jakarta Ta mikawa Mama tace “Mama ku hau napep da wannan ku tafi gida, ni inada aiki da yawa a Offlce”.
Karba mama tayi tace “To mungode sosai Allah yayi albarka, Sai kun dawo din” suka tafi yayinda Sultana kuma ta koma Office d’inta.
Hmm