WATA SHARI’A COMPLETE
WATA SHARI’A
CHAPTER 11
Saida wutar ta gama cinye gidan kurmus sannan mutane suka fara shiga Clki dukda gumin dake tasowa daga cikinshi, Alamar gawa ma babu a ciki, hakan yasa wasu suka fara tunanin ko wuta ta cinye
gawarsune? Cike da tausayi suka ringa fita daga cikin gidan wasu haryanzu basu daina hawayen tausayi ba.
Sultana ce kejan motar a sukwane sai faman kara wuta take,
Can daga bayan motar na jiyo murya ana fadin
“Wallahi bansan garinya na manta kayan sakawar mama ba, kuma abun haushi wai duka nawane kawai na hada a jikar bakon, babu nata ko d’aya”
“Ai saisa kikaga ina gudu dan kar dare ya nitsa sosai bamu koma gida ba, amma da yake kayan ne kawai zaki dauka ai da sauk’i ma” Sultana ta fada bayan ta rage gudu da motar.
Murza idona nayi dan tabbatar da muryar wadda naji, ko tantama babu wannan muryar Ummimah ce, to amma garinya hakan ta kasance? Kenan basu cikin gidansu lokacin da wutar ta kama?,
Ku biyoni yanzu zaku samu amsoshin wannan tambayoyin.
Lokacin da Sultana ta nufi gidan su Ummimah dan ta tambayeta address din Zarah da Rabiatu,
Ta samesu itada Mama yanzu sun dan saki ransu akan baya,
Bayan sun gaisa ne ta fada masu abunda ya kawota,
Ko amsa Ummimah bata kaiga bama Sultana ba taji wayarta ta d’auki ruri alamar karar shigiwar text message, D’auka tayi ta fara karantowa
_ina shawartarki daku d’aukesu daga wannan gidan da suke ciki, saboda muguntar waccan nasan komai zata iya aika masu saboda tasan gidansu, amma idan kika daukesu daga ciki kinga shikenan hankalinku kwance kuna tare dasu, sannan kuma ku kanku zakufi samun saukin yi masu tambayoyi ba sai kun tado mota kunzo har gidansu ba. shawarace
Cike da mamaki take karanta sakon,
Kanta ta jinjina alamarta gasgata maganar,
“Ina zuwa mama” ta fada bayan ta mike tsaye ta nufi waje,
Umar ta kira ta shaida masa sakonda aka tura mata,
Suna cikin wayar shima nashi ya shigo a karamar wayarsa,
“Ki d’aukosu kawai idan zasu yarda” ya fada cike da mamakin wanda yake turo masu wannan sakunan wanda su kansu su Ummimah din basu sani ba, nima kam ban sani ba kawai dai ina baza idona don ganin ko wanene wannan amma kuma shiru har yanzu.
Tsinke wayar tayi ta shiga cikin gidan har yanzu bata daina mamaki ba, Bayan ta zauna tace “Dama wata tambayace ta kawoni inyi miki Ummimah, amma kuma sai mai gidana ya kirani yace idan babu damuwa ko zaku bini mu koma gidanmu da zama na wani lokaci?
Saboda zamanku anan zai iya zama matsala koba yanzu ba”.
Ajiyar zuciya mama ta sauke sannan tace “Tabbas maganarki gaskiyace Sultana, ni kaina tunda aka fara maganar kai k’arar nan hankalina ga baki d’aya bai kwanta da zaman gidan nan ba, dan haka mun amince mu tafi
d’in babu damuwa mungode sosai Allah yayi maku albarka, Allah kuma ya mana jagora”.
Dadi sosai Sultana taji da Mama bata musa mata ba, “Ameen mama, sai ku hada kayan da zaku tafi dasu yanzu mu tafi yamma nayi”.
Tashi Ummimah tayi ta nemi ‘yar Ghana most go ta fara zuba kayanta, saida ta gama kuma kwata kwata ta manta bata had’a na mama ba, sai hijabi d‘aya wadda ke rataye a kofa ta saka wadda saboda itane tayi tunanin ta saka kayan mama din, ga kuma sauri da takeyi
kasantuwar Sultana tace suyi sauri tana so ta dauko Hafsa daga islamiya.
Tafiya kuwa sukayi suka d’auki Hafsa sannan suka wuce gida, Saida dare Mama taje canja kaya suka tuna ashe Ummimah bata saka kayan mama ba, Shine Sultana tace tayi sauri suje can gidan su dauko kayan mama din dan bazai yiwu
ta zauna batada kayan da zata saka ba. Wannan kenan.
Koda suka isa k’ofar gidan basu kula da komai ba har Sultana tayi parking suka fito, Hafsa dake gaban mota ma ta fito itama Ummimah din ta fito, Mamaki karara a fuskokinsu lokacin da sukaga yanda gidansu ya kone sosai har wasu
katangu sun zuba, “Ya salam” Ummimah ta fada hannu bisa kai hawaye suka fara mata sintiri, Kamar a mafarki ta d’auki abun, Cikin hanzari suka shiga ciki har a lokacin mutane basu gama watsewa ba kowa na al’ajabin wannan mummunan al’amarin.
Baki daya kallo ya koma ga Ummimah dake kuka sosai tana kokarin shiga cikin dakin, Hamdala mutane sukayi saboda sunji dad’i da bata ciki, amma kuma basu tabbatar da mamanta tana ciki ko bata ciki ba,
“Kiyi hakuri ki daina kuka, kinsan ita kaddara babu ruwanta, idan har abu saiya faru bawa tofa babu makawa sai ya sameshi, ita kuma maman taki data rasu Allah yayi nata rahama” wani dattijo ya fada saboda yayi zaton ko mama tana ciki gobarar ta tashi.
Share hawayenta tayi tace
“Mamana bata rasu ba, bata nan gidan, kamar sun sani sukace mu koma gidansu mu zauna, lallai wannan ikone daga Allah, Allah ya kara karemu”,
“Ameen” kowa ya fad’a tare da yin hamdala ga Allah da yasa wutar bataci kowa ba.
Sultana dai nata kallo ne kawai, tana kuma kara mamaki sosai, Kamar mutumin yasan haka zata faru ya turo mata sako akan su daukesu daga gidan,
‘To kodai aljani ne wai?‘ Ta tambayi kanta.
Ki daina kukan nan ki tashi mu tafi Ummimah, dama haka Allah ya tsara gobara zata tashi kuma komai naki zai kone, abunma yazo da sauki tunda bataci rai ko d’aya ba ai, dan kayan sakawa ko kayan amfani duk mai sauk’i ne za’a iya siyan wasu, rai kuwa kwaya daya ne tak ba‘a aro ko canjin wani, ki tashi mu tafi kawai” Sultana ta fada tare da mikar da Ummimah tsaye duk jininta ya baci da baki inda ta zauna. ‘
Babu musu kuwa tabi bayan Sultana, ranta cike da mamakin wannan abu, ‘Allah dai yasa wannan dinma ba aikenta bane’ Ummimah ta ayyana a ranta wanda tuni Sultana ta gano hakan, kawai dai tayi shiru ne saboda yanda taga Ummimah ta rikice bata
so tayi maganar a cikin mutane.
Shiga mota sukayi haryanzu Ummimah bata daina kuka ba, Hakan yasa Hafsa uwar surutu ta koma baya inda Ummimah take, Dafa kafad’arta tayi tace
“Ki daina kuka Aunty, ai mamanku bata mutu ba ko?”,
Cikin mamaki Ummimah ta daga mata kai alamar ehh
“0k tunda tanada rai ai shieknan sai ki daina kuka, idan kayanku kike mawa zan cema Abbana ya siya maku wasu, idan kuma na momy zasu maku sai ku dauka ku saka, kinga idan baki daina kukan nam ba har muka koma gida zaki saka mamanki ma ta ringa yin kukan, kinga dai ni bana kuka kuma ga momyna ma bata kuka”.
Har Sultanan ma saida tayi mamakin wannan maganganu na Hafsa, “Hafsa dan Allah ki rage surutu maras ma’ana mana, ki barta taji da abunda yake damunta kar ki saka mata ciwon kai”.
Bakinta ta kama bayan ta dawo wurin zamanta tace “Nayi shiru momy, na manta kin hanani yawan magana”.
lta kanta Ummimah saida abun ya bata dariya, saboda surutun Hafsa idan tana yinshi kamar wata babba haka take.
Bayan sunje gida suka labartawa Umar da Mama abunda ya faru, Umar bayyi mamaki ba saboda shi lawyer ne yasan irin wannan abubuwan suna faruwa a case, saidai yaji dadi da Allah yasa saida suka baro gidan sannan abun ya faru.
Mama kuwa hamdala tayi ga Allah tace “Allah mungode maka da saida muka fito gidan sannan wutar ta kama, Allah ya kara
karemu baki d’aya”,
“Ameen” Ummimah ta fada bayan ta cire takalmin k’afarta duk kafar tayi baki kirin.
“To yanzu mama ya za‘ayi da kayan sakawarki? Gashi naki duk sun kone” Sultana ta tambayi mama.
“Haba Sultana ai dan kayan sakawa abune mai sauk’i, ni wallahi basu dameni ba, ke
koda kayan jikina zan iya rayuwa duk dare in ringa cirewa ina wankewa, kinga kafin asubah sun bushe sai in miyar ajikina”.
Dariya suka dauka su duka kafin Sultana tace
“Barin duba ko a kayana inada rigarda zata miki sai in kawo miki masu zani ki saka, kinga
gobe akwai zaman kotu bamuda lokacin siyo miki wasu, sai idan mun samu natsuwa sosai”.
“Masha Allahu Allah miki albarka, hak’ik’a kun taimakemu keda mijinki ko ince kuna kan taimakarmu, Allah kad’ai ne zai iya biyanku, mungode sosai Allah yashi albarka”, “Ameen mama ki daina yi mana godiya, wannan al’kawari ne muka daukarwa gwamnati
cewa zamu taimaki al’ummah baki d’aya, mu taimaki mai gaskiya tare da karen hakkinshi”.
Da wannan maganar Sultana ta tashi domin ta samowa Mama kayan da zasu mata daidai a cikin nata.
Shigarta kuwa ta samu Umar mijinta yana waya da Dr. Rafiq.