WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 10 BY MARYAM JAFAR KADUNA

wurin da motarsu, suka bace masa bat!

Ya dinga kuka yana dake-daken duk abin da ya tari gabansa, tamkar zai cinye mutanen da ke gurin, idan kaga yadda yake yi kamar wani sabon hauka.

Asibitin suka nufa da ita, da zuwansu a ka ba su gado, ba da jimawa ba ta farfado kasancewar bata yi nisa ba a sumar.

Ba kowa dakin sai Rafi a ta shiga wuwwurga idanu don son gano a ina take, ta daga kai ta kalli karin ruwan da akasa mata, ta gane a asibiti take sai a sannan komai ya dawo mata. Ta dubi Rafi’ ar cikin yanayin mutuwar jiki.Ba da gaske ba ne ko Rafia?” Ta ce, “Ba da gaske ba me?” Ta ce, “Sulaiman shi a ka ba ni ko ba Imran ba ne?” Tayi shiru. Sam ta kasa cewa komai bata san me hakan zai jawo ba, idan ta fada.

Kafin ta ce komai Momy da Sharifa suka shigo suka hau mata sannu, binsu da ido dai take tana, son karyata abinda zuciyarta ke son tuna mata.

Kamar hadin baki Daddy da Imran suka shigo suma.

Da zuwansa ya hayo kan gadon a dan birkice yana mata sannu ta bishi dai da ido ta kasa amsa masa, so take a bata amsar abinda take zargi.

Ya hau rawar jiki da ita me take so me zata ci ba dai in dake mata ciwo? Sam taji bakinta ya kulle, sannan idonta ya kasa daukewa daga kansa.

Likita ya shigo ya duddubata tare da tambayoyi gareta, jikin ba wata matsala, amman ya. ce tana bukatar hutu sai gobe zai sallame ta.

Ya rubuto wasu magunguna da za su sa ta kuzari da

karin lafiyarta. Imran din ya fita don nemo. su.

Dady ya dubeta ya ce, “Sannu my doughter ta daga kai ta kalle shi tare da amsawa a hankali.” Ya ce, “Kin tabbata ba wani abu da yake damunki ko?”

A can Kasan makoshi ta ce, “Eh Daddy.” Ya ce “Good,

idan kina bukatar wani abu ki sanar da ni kin jiko?” Ta

daga kai alamar ‘To.’

Ya ce, “To zan wuce sai anjima zan dawo.” Ta ce, “To a

dawo lafiya.

” Ya dubi Momy yana cewa “Zanje wani guri

Idan na dawo zan biyo ta nan.”

Ta ce, “To shi kenan a dawo lafiya.” Ya amsa amin.

Sharifa ta mike tana cewa “Nima zan bika Daddy.” Yanayin fuskarta ba annuri, ya ce “Don me ke da za ki zauna kuyi jinya. Ta yatsina fuska tare da turo baki ba tare da ya ce komai ba. Mommy ta riga ta gama fahimtarta, sam ba son auran take ba da Yayanta, duk saboda yanda Mabarukar take nuna kiyayyarsa a zahiri kuma bata da laifi, waye zai so dan uwansa ya cutu? Tayi murmushi ta ce, “Me yiwuwa ta gaji ne tun safe fa.”Ya ce, “Amman ai dole ce zata sa ta tsaya din.” Ta ce, “Ka barta dai taje din da dare ta dawo.”

Yayi jim sannan ya ce “Shi kenan muje.

Tayi dariya ta dubi Mommyn ta ce, “Thanks Momy.” Ta rufawa Daddyn baya.

Ita ma tayi dariya ta fita don raka su.

Dakin ya rage daga Rafi’a sai Mabarukar ta juyo ta kalli Rafiar, ta ce “Fada min gaskiya Rafia, waye Angon? Wa kotu taba?”

Tayi jim tana kallonta, dole ne ma ta sani yau ba sai gobe ba, ta kamo hannunta cikin kulawa ta ce, “Komai ki ka ga ya faru ga dan Adam daga Allah ne, Mabaruka me kyau ko akasinsa.

Ba kuma don ba ya sonka ba sai don ya jarabaka kuma me yiwuwa shi ne mafi alkhairi gare ka.

Ta katseta “Ki fada min kawai bana son sharar fage, duk nasan wannan, ki fada min waye mijina”

Ta kalleta da kyau, ido cikin ido ta ce, “Mabaruka Allah ya yi miki baiwa, ya zabe ki a cikin dubban mata, ya azurta ki da miji na kwarai mai addini da kamala.

Ba kowacce mace ba ce take samun irin mijin da ke ki ka samu ba, kin yi miji ba ki da bakin cikin gidan aure, za ki yi rayuwa mai kyau da dadi.”

Ta dai tsura mata ido tana kallo, ta kasa cewa komai. Ta ci gaba da magana a tausashe, duk a kokarinta na kwantar

• wa kawar tata hankali don ta nutsu ta gane abin da take fada mata gaskiya ne.

“Mabaruka! Imran shi ne Angonki, shine kotu ta ba.’ Tamkar wacce a ka dasa, ta zamo a kan gadon tare da

kurawa Rafi’ar ido tamkar yau ta fara ganinta.

Ita ba tunani ba ita ba kallonta ba, ba ta ce kuma komai ba. Har sai da ta taba ta, amman ko motsi.

Sai da ta jinjigata daidai zubowar wasu hawaye masu dumi daga idanunta wadanda ba su nuna alamar zuwansu. ba Ta ee, “Mabaruka kuka kuma?”

• Ta kalle ta ta ce, “A tunaninki dariya zan yi ko shi yasa har ki ka yi mamakin ganin hawayena?”

Ta ce, “In ba ki dariya ba kuka bai kamace ki ba, godiya za kiyi wa Allah, don hakan ya fi dacewa.”

Ta ce, “Daga yau na fara kuka a rayuwata Rafi’a, har daukewar numfashina na har abada. Kukan zahiri kukan zuci wanda za a gan shi ko ba za a ganshiba.”

_Ta ce, “Don me Mabaruka? Sai ka ce wacce a ka hadata da mugun abu?”

Ta ce yayin sakkowar wasu hawayen.

“Ai wannan yafi mugun abu a guna, gwanda a hada ni da mutuwata a kan nayi rayuwa da shi saboda bana sonsa! Ba na sonsa!! ” Ta fada tare da fashewa da kuka, sannan ta kife a nan tana rizgar kukan.

•Hankalin Rafi’ar ya tashi, ta birkice ta dinga Kokarin dagota.Haba Mabaruka, kina son jefa kanki a tashin hankali? Duk fa abin bai kai haka ba. Meye laifin Imran da har za ki

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE