WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 3 BY MARYAM JAFAR KADUNA

abin da ya canja.

Alakata da shi ta rushe haka, alakata da Sharifa bayan tazo bikin, yayin da soyayyarmu da Sulaiman take Karuwa tsakaninmu mahaifiyata ta dage a kan lallai sai na aure shi.

Yayin da shi ma Babana ya dage lallai sai na auri

Sulaiman, saboda shi ya ba aurena.

A tunanina jahilci ne ke dawainiya da su har suke son aura min maza biyu da kafiyarsu, sam ba sa jituwa motsi kadan zai zagi Mamana, duk bakin cikinsa ta bar gidansa ta koma gidan wani Alhaji tana more rayuwarta me dadi da nishadì ta bar shi a wahala da talauci.

Ita kuma take jin haushinsa a kan wuyar da tasha gidansa da wulakancin da ya mata, kamar yanda take fada min kullum, amman bata taba fada min ya aka yi suka rabu ba, amman takan ce ta sha wuya gidansa.

Nayi iya bakin Kokarina na fahimtar da su a kan abin da suke kokarin yi ba kyau, ba a taba yi ba, sam ba su saurarona kowa ya dage a kan burin shi a ganinshi shi ke da gaskiya.

Hakan yasa nayi yunkurin kai su Kara kotu, tunda ba su da magabatan da za su musu fada, kawata Rafi’a ita ta hana ni sannan naso na gudu shima nan ta hana ni ta tsare ni a gidansu.

Yayin da su kuma suna can kowa na kokarinsa suka kuma sa ranar auren duk rana daya. Har dai suka daura min aure da maza biyu har zuwa yanzu.

Ta kalli Alkalin ta ce, “Wannan shine cikakken ko ni wacece da yanda abin ya faru gare ni.”

Nan fa kotu ta hau kace-nace.

Bayan an nutsu Alkali ya fito da angwayen, Sulaiman da Imran, kowa yai ma kotu bayanin wanda ya ‘daura mai aure, kuma ya bada sadaki.

Duk tambayoyin da ya kamata kotu tayi musu tayi ta gamsu da duk bayanansu.

Ta bukaci a bata kwana biyu kan ta yanke hukunci, don haka a haka aka tashi kotun.

Wannan karon ma gidan Momy ta koma, a mota ta ci gaba da yiwa Rafia, korafi kamar zata yi kuka.

“Wallahi na gaji Rafia, na kagara a yi ta ta Kare, in san matsayina, na gaji da jelangen nan na kotu.”

Ta ce, “Haba! Kada ki damu, jibi ne fa kawai. A jibin kai tsaye gidanki za a zarce da ke, magana ta kare ko gidan Sulaiman ko gidan Imran.”

Idanunta suka fito hankalinta ya tashi, idanunta suka yi rau-rau, ta ce “Ya Allah kada kasa aure tsakanina da Imran, Ya Allah kà sa Sulaiman shine ANGON Ya Allah.”

A haka suka isa babu kuzari jikinta, ta haye gadonta tayi lamo zuciyarta da sake-sake dankare da zullumi.

A nan suka wuni da Rafia tana Kara kwantar mata da hankali, sai gaf da Magriba sannan Rafi’ar ta tafi gida.

Bayan ta rakata ta dawo, daidai Rofar falo suka ci karo da Imran ya tare mata kofar yana kallonta fuskarsa dauke da fara’a.

Tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata taba dariya ba, ranta ya baci matuka ta dago tana harararsa, yayin da shi yake dariya shi kansa yasan ya jawa kansa fada ne.

Ta ce cikin fushi “Matsa ka bani guri.” Ya dage kafada alamar a’a bata saurare shi ba tayi kokarin rabewa ta gefensa ta wuce.

Nan ma ya tare, ta dawo ta dayan gefen nan ma ya fake.

Tazo iya wuya, ji take kamar ta shake shi ta huta gabadaya.

Tsawon mintoci suna haka, ganin da gaske yake ba zai matsa ba ga wani tukuki da take ji a ranta tsayawa kusa da shi da tayi, kawai ta juya baya abinta.

Ya bita da kallon ina zata je.

Gefe ta koma ta zauna a harabar gidan tana ‘yan harare-harare da fushi, bai daddara ba ya Kara binta can din.

Tsugunnawa ya yi gabanta har suna jin numfashin junansu, Kamshinsu ya hade da juna ta dago tana kallonsa cikin tsananin tsanarsa shi ma ita yake kallo cikin yanayi na kaunarta ya ce da ita.

“Wai menene haka Mabaruka? Guduna kike don ba kya sona ko?”

Kai tsaye ta ce, “Eh, amman ka kasa gane hakan bare ka kale ni na huta, zuciyata ta huta da matsananciyar tsanar da take maka.”

Ya yi shiru yana kallonta zuciyarsa tana masa ba dadi, ya ce “To me yasa? Meye aibuna me na rasa da har zuwa yanzu na gaza zama masoyinki.

Kullum kina furta min kiyayya, ina ganinta a idonki me yasa Mabaruka?”

Idanunta suka kada kamar zata yi kuka ta ce, “Haka nan babu wani dalili Allah ne yasa min haka ba daga ni ba ne amman ka ki fahimtar haka ka kyale ni don ba mu dace da juna ba sam bare zamantakewar aure ta yiwu tsakaninmu.”

Zuciyarsa ta Kara yin daci bakinsa ya yi nauyi da kyar ya. iya cewa “Mabaruka, Allah ya jarabce ni da matsanancin sonki ban san ya zan misalta miki ba bare ki tausaya min yanda zuciyarki take miki ba dadi da . azalzalarki a kan kiyayyata.

Haka nima tawa take azalzalata da sonki, a kullum Kara min sonki ake, wallahi Mabaruka ba zan iya rayuwa idan ba ke ba, bare na iya hakuri da ke ta harararshi tamkar ta kife shi da mari, sannan ta ce “Kana Kara wahalar da kanka ne ka sawa kanka hakuri da dangana, aure tsakanina da kai ba zai taba yiwuwa ba, har abada saboda Allah bai rubuto hakan ba tsakaninmu.”

Cikin Kwarin gwiwa ya ce, “Ni kuma ban taba sawa raina ba, ba zan same ki ba a kullum ganina nake tare da ke muna rayuwar aure tare da ‘ya’yanmu cikin farin ciki da walwala.

Ta kalle ‘shi da kyau ta ce “Ba za ka taba ganewa ba, zuciyarka na yaudararka da mahaukacin tunaninka, ni dai nasan ba zan aure ka ba, kaje kai ta haukanka.”

Daga haka ta mike ta wuce cikin gidan da sauri tamkar

wacce za a kamo.

Ya bita da kallo cikin sha’awar tafiyarta, musamman da take saurin nan sai tai masa kyau a ido matuka, yayi murmushi tare da mikewa ya wuce inda motarsa take yana

cewa, “Zan kama ki yarinya.” Ya shige abinsa ya fice daga gidan.

Da dare wajen karfe tara har ta gota sannan ya dawo.

Momy ce a falo, ita kuma Gimbiyar tana dakinta ita ba bacci ba ita ba kuka ba.

Haka zalika ba tunani ba, zuciyarta taqi ta barta ta huta

saboda zullumi bata san me jibin zata haifar ba, meye a cikinta? Farin ciki ko bakin ciki, rayuwarta ko mutuwarta? Ba abin da ke mata dadi tun tsawon ranar bata sa ko

Kwayar ruwa a bakinta ba bare abinci, haka take. Ko kadan ma bata jin yunwar.

Ya zauna cike da gajiya yana fadin wash! Ya cire hula

yana sosa kai, Momy ta bishi da kallo tana cewa “Gajiya ko?”

Ya ce, “Wallahi amman yunwa tafi yawa.” Ta ce, “Ah

lallai kam ai ga abinci can a dinning ba ma wanda ya taba shi tunda aka gama.”

Ya dubeta yana cewa “Saboda menene ba kowa a gidan, ina Mabaruka?” Tace, “Tana cikin daki, tun dazu nake fama da ita taci abinci,taqi har na gaji na kyaleta, idan ta tantance ta fito ta nema don kanta.”

Sam bai ji dadi ba, jikinsa ya Kara mutuwa.

Mikewa ya yi yana cewa zan shiga ciki in dan watsa ruwa, ki sa Mabarukar ta kawo min abincin da dan lipton, ta ce, “To.”

A daki ta samu Mabarukar kwance ta taso ta suka fito.

Tana zama kan kujerar ta ce “kije ki hado abinci a tire da lipton.

Ta kalli Momyn fuskarta da fushi ta ce nifa bana jin yunwa. Ta ce, “Na sani daman ba ke nace ki hado kanki ba, kije kiyi abin da na saki.”

Ta amsa da “To.” Sannan ta wuce.

“Tayo yanda ta sata, ta kawo mata. Ta dube ta ta ce “Kije kikaiwa Imran dakinsa.”

Ta kalleta da sauri cikin tsoro ta zumburo baki tamkar zata yi kuka “Ni fa Momy…” Ta katse ta “Ba dole, idan ba za ki je ba aje ni sai na kai masa.”

Tasan gatse ta mata. Ji take tamkar ta fasa ihu wai me

yasa ita aka tsaneta ake son kusantata da wannan makiyin nata? Ko dai ba a san numfashinta.

Yanzu abincin ma sai an sa ta ta kai masa bayan a dinning ya saba ci kawai don a bata mata rai. Ta wuce kamar zata yi kuka, idanunta sun taru da kwalla, ta shiga kwankwasa kofar.

Ya fito daga wankan daga shi sai short niker yana sane ya ki suturta jikinsa sabanin da da ba zai taba yarda ta same shi a hakaba, yanzu ta zama matarsa, kun ji fa!

Ya zo ya bude mata fuskarsa dauke da murmushi, bata ko kallonsa bare tasan ya yake ta zunguro masa tiren tana kumburi ta ce, “Gashi ya yi tsayen yana kallonta ya ce

“Kije ki aje ciki mana, ai ba lallai sai na karba ba.”

Ranta ya Kara baci yana raina mata wayau. Ina laifin da ta kawo masa ma yasa hannu ya karba ba zai yi ba, sai ita ta Karasa masa da shi bai ma ga kokarinta ba? Don haka taji bazataiyaba.

Tsugunnawa tayi tana Kokarin dire masa a nan bakin

Kofar, kafin ta aje ya ce, “Wallahi ki ka aje shi a nan ba zan dauka ba, a nan zan bar shi har sai wacce ta turoki ki kawo tazo ta gani inda ki ka aje na gwammace na kwanta ban ci komai ba.”

Kwallar da ta taru a idonta ta sauko, tasa hannu ta goge ta riga ta barwa kanta ba a sonta, so ake kawai ta mutu ko ta ina muzguna mata ake ana cutarta.

Ba ta ce komai ba ta mike da abincin bata ko kalle shi ba, ta rabe ta gabansa ta wuce cikin dakin.

Ya yi dariya yana kallonta gefe kúma ya ji tausayinta, amman duk da haka bai fasa abin da ya shirya mata ba.

Ya datse kofar tare da sa mata key ya dauki dan key din ya cillar bayan wordrove.

Ta aje kan table din da ke gefen gadon, ta mike ta wuce abinta zuwa Kofar, ta jawo ta ji ta gam da ta lura da kyau taga ansa mata key ta ji cak ranta na Kara mata daci, to me yake nufi kenan?

Tamkar ba za ta masa magana ba, amman dai tunda so take ta fita ya zama dole ta sauke girman kan ta tambaye shi, ya bude mata.

Shi kuma ya yi zaune kan gadon yana kallonta da son ganin kokarinta. Bata juyo ba ta ce “Ka bude min kofar ina son in je in kwanta dare yayi.” Ya yi mata banza tamkar ba ya dakin. Ba ta gaji ba ta sake tambayarsa din, sai sannan ya yi magana in bacci ki ke son yi ki zo ki kwanta a nan ga gado nan.

Sai a sannan ta juyo cikin fushi da bala’i zata yi magana, ganinsa a haka tamkar ba kaya jikinsa yasa bakinta ya kulle ta kasa maganar.

Ta sunkuyar da kai wani tsoro na shigarta ga kofa a rufe wato dalilinsa kenan na rufe kofa? Tsoro ya kamata, jikinta ya dauki rawa, idanunta suka yo waje, sam ta gagara daga ido ta kalle shi.

Sosai ya fahimce ta ya yi dariya ya ce, “Ina jin ki, me za ki ce da?” Tayi shiru ta kasa magana. Ya sake nanatawa lokacin da ya mike jikinta ya kara rawa.

Bakinta na rawa ta ce, “Ka. ka…ka bude min…min kofabar…barcinakeji.”

‘Ganin ta tsorata ainun yasa ya yi tsaye cak ya ce “Shi ne na ce ki zo ki kwanta a nan mana ga shimfida nan.

Yana rufe baki ta dauka “Momy zata yi fada ai bai dace na kwanta a nan ba.”

Ya ce, “Waye zai tuhume ki don kin kwana a dakin mijinki?” Tsoron da ke ranta ne ya hanata ba shi amsa,

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE