WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 4 BY MARYAM JAFAR KADUNA

amman dai ta ce “Kayi hakuri dai don Allah ka bude min.”Ya ce, “A ‘a ban yarda ba, a nan za ki kwana musamman da naji labarin duk yau ba ki ci komai ba, shi yasa na ce a ba ki ki kawo min da kanki, kinga sai muci tare sannan muyi kwanciyarmu a nan ga gado can.”

Sai sannan ta iya dagowa ta kalle shi a marairaice tace,

“A’a ba zan iya ba, don son Annabi ka bar ni na tafi dakina kar Momy ta jiyo ni a nan dakin.”

Tunkarota ya yi yana cewa, “Ba abin da zata ce, nasan zata yi farin ciki idan ta ji ki a dakin mijinki, kada ki damu kina tare da Angonki.”

Ganin yana tunkarota ne yasa ta Kara tsorata, idanunta suka fito ta fara ja da baya har ta dangane da jikin kofa.

Shi kuma bai fasa ba ya ci gaba da tahowa yana dariya, har ya tsaya gaf da ita suna jin numfashin juna, tayi saurin sunkuyar da kai jikin nata kuma bai fasa rawa ba.

Ya ce, “Wai meye duk ki ka tsorata, me ki ke tunani? Ta ce da sauri ba komai. Ya ce, “In ma kina tunanin wani abu nasha masifarki da ki ka saba min zata kwace ki.”

Tayi shiru dai ta gagara hada ido dashi, kamshinsa ya baibayeta ganin ya daga hannu ne yasa tayi saurin datse idanunta da Kankame jikinta gam.

Ya yi dariya yayin da ya ke dora hannunsa, saman Kofar wato bayanta sai ya sata tsakiya tsakanin jikinsa da hannuwanta jilkinsu har yana taba juna.

Jikinta ya Kara rawa, ya ce yana kallonta “Calm down my angel, ba zan miki komai ba, kawai da naji baki ci komai ba ne yasa hankalina ya tashi, naji ba dadi shi yasa nake son muci abinci in ba ki tunda Momy ta ba ki kin kici.

Ba zan iya jurar zamanki haka ba, ba tare da kin ci komai ba, don nima ba zan iya ci din ba.”

Ita dai ta datse idanunta gam bakinta yana ta’ salati, jikinta bai fasa rawa ba bayan zufar da ta lullubeta.

Kamar wasa taga ya daga rigarta yana cewa, “In ga cikin ma?” Ba shiri ta bude idon tana kallonsa, anya yana cikin hankalinsa?

Kan ta gama wannan mamakin taji hannunsa saman cikinta yana shafawa yana cewa “Kin ga ni ko cikinki a shafe yake alamar ba abin da kika ci.”

Ta kalle shi cikin bacin rai ta ce, “Imran!” Ya amsa yana kallonta. Ta ce “Ka dauke hannunka daga jikina.” Ya tsareta da ido ya ce “Why?” Ta ce, “Ni matar aure ce matar wani.”

Ya yi dariya ya ce, “Ni ba?” Ta ce, “Na dai fada maka ka cire hannunka a jikina.” Ya ce, “Idan ba haka ba…”

•Kan ya gama rufe bakinsa a fusace zata ture hannunsa, caraf taji ya rikota yana kallonta, ta kama kiciniyar kwace kanta gabadaya ya rikota ya hadata da jikinsa ya riketa gam.

Tayi iya kokarinta ta kasa, har da cizo ta cije shi ba . iyaka amman ko motsi bata ga ya yi ba bare ya saketa.

Ta hau botsare-botsare, idanunta sun taru da kwalla, tsawon lokaci tana kokarin kwatar kanta ta kasa, ya rike ta gam. Sai kawai ta fashe masa da kuka har da shure-shure.

Yayi tsaye yana kallonta har cikin ransa yake jin kukanta sam ba ya masa dadi ga wani sonta da ke Kara damunsa, ya ce “Mabaruka wai menene?”

Cikin kuka ta ce, “Ka sake ni in tafi.” Ya ce, “Ba zan iya ba, ina sonki ina son na kasance da ke a yau don Allah Mabaruka.”

Ta Kara fashewa da kuka ta ce, “Ni ma ba zan iya ba, ina da miji kada ka keta min haddi don Allah Imran “

Ya ce, “Ke ba matar wani ba ce matata ce, nine Angonki ba waniba.” Ta cigaba da kallonsa tana kukan.

Ya ci gaba, “Kin san yanda zuciyata take tafarfasa na

• sonki Mabaruka son da nake miki wallahi wanda kike so baya miki ba zai baki kulawar da zan ba ki, ba zai tattale ki ba kamar yanda zan miki ni zan gatanta ni in ba ki farin ciki da jin dadin rayuwa ba

Saboda ni ke sonki tsakani da Allah, kuma na fi shi sonki, a gidana za ki fi jin dadi. Don Allah ki tausaya min Mabaruka ki bani hadin kai muyi soyayya me dadi, ba abin da zan miki a nan har sai kin zo gidana.

Ta kasa cewa komai, illa kukan da take har kanta ya fara ciwo ta gaji da yi masa bayanin bata sonsa, ta furta masa ta masa a aikace amman ya gagara fahimta, to me zata ce masa ya fahimta kuma?

•Ta ci gaba da kukan tana kallonsa, ya kalleta cikin tausayawa ya ce, “*Ya isa! Ya isa! Is ok, bana son kukan nan, kiyi hakuri.”

Taki dainawa ta ci gaba da kukan dai tana kallonsa, shi kuma har lokacin yana rike da ita.

Ya ce, “Kina son nima in yi kukan ko ba kya son farin cikina ba kya tausayina ko?”Daga kai tayi alamar eh.

Ya yi murmushi ya ce, “Ok, naji zo muci abinci sannan kita fi. ” Ta tirje ita ba za ta tafi ba, ya ci gaba da lallashinta da yaga ba za ta je ba, ya jata da karfinsa suka wuce ya zaunar da ita bakin gadon kusa da jikinsa.

Ta dinga kiciniyar kwace kanta.

Ya dubeta ya ce, “*Wallahi idan ba ki tsaya ba a nan za ki kwana, kinga gadon nan?” Ya nuna mata. Tabi gadon da kallo.

Ya ce, “To a nan za ki kwanta, ni da ke kuma babu mai tambayata dalilin hakan, don haka gwanda ki nutsu ki ci abincin nan sai na bude miki kofa ki fita salin alin abin ki, kije dakinki ki kwanta.”

Tayi narai-narai da ido, kukan ya tsaya cak sai zare idanu, ganin ta nutsu ne yasa ya saketa yana kallonta.

Ya yi tunanin zata tashi amman sai yaga tayi dai zaune, don haka ya jawo abincin yana zuba musu shi da ita. Yaja table din tsakiyarsu ya debo a cokali yana kallonta ya yi dariya.

Ya ce, “To haa bakin in ba ki.” Ta juyo ta galla masa harara tare da dauke kai tana jin wani takaici a ranta da Karin tsanarsa.

Hmmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE