WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 6 BY MARYAM JAFAR KADUNA

miki da iyayenki kije ki kyautatawa mijinki, ku zauna lafiya cikin farin ciki da ganin darajar juna, wanna ita ce shawarar da zan iya ba ki.”

Taja tsaki tare da dauke kanta tana cewa “Ba zan iya ba, zan nemowa kaina shawarar abin da zan yi wanda ba zai nakasa rayuwata ba.”

Duk yanda Rafi’ar taso ta ganar da ita da tausasarta sam ta kasa cin nasara a kanta sai dai tasa mata ido.

Suka yi waya da Sulaiman a kan zaizo ya ganta tana ina sam ba shi da nutsuwa a zamanta gidan Mamanta, ta dawo gidan Babanta.

Ta dube shi bayan yazo a sanyaye, to ya zan yi Sulaiman Momyna ba ta min da wasa, ban isa in mata musu a kan abin da tasa ni ba, ban ma ga fuskar tambayarta ba, bare nazo nan na tare.

Sannan shi kanshi gidan Baban ba dadinsa nake ji ba, matsaloli ne dankare cikinsa.”

Yaja tsaki tare da rike kugu ya ce “Me ake da wannan haukan haka nan an hana min nutsuwata, kowa ya sani ya gani nine Angon, amman ana son murkushe zance a bi son zuciya a ba wani sakarai can.”

Ta ce, “Ba kai kadai yake wa ciwo ba, Sulaiman na fika jin ciwo da damuwa ni kadai nasan yanda zuciyata take min daci da radadì, ba in da nake samun sauki da walwala.”

Ya dubeta da kyau yana ganin abin da ta fada a idonta duk ta rame tayi zuru-zuru, idanuwa ko yaushe a rikide jajawur kamar ma suna ciwo tayi duhu, kana kallonta kasan ba ta da sukuni ya dubi mashin dinsa ya ce hau muje. Ta kalle shi da kyau ta ce “Ina zamu je Sulaiman?”

Ya ce, “Ni mijinki ne kada ki tsorata da ni, ina son yau kadai ki sami walwala zuciyarki ta saki ki dan ji sanyi-sanyi kafin zuwa gobe, in dauke ki zuwa gidana.”

Ko ba komai taji sanyi-sanyi a ranta duk da a ganinta in har ba an kawo karshen rikicin ba bata jin akwai abin da zai sa ta walwala saboda zullumin da yake dankare a ranta, tsoronta daya.

Ba musu kuwa ta haye ya tada mashin din suka wuce:

Kai tsaye gidansu ya nufa da ita, ta dube shi ido cikin ido bayan ta sauka ta ce, “Kana nufin nan ka kawo ni?”

Ya dube ta “Eh, wani abun ne?” Ta ce a sanyaye “A’a ba komai hakan daidai ne.”

Duk da tana jin faduwar gaba a tattare da ita, bata nutsu

da zuwansu ba, amman dai bata nuna masa ba, suka shiga tare.

Inna na zaune tsakar gida tana dama, fura, Samira na wanke-wanke, yayin da Nafisa na kitchen tana faman aikin tuwon dare. Inna ta bisu da kallo dai-dai. Ya shige daki ya dauko tabarma ya shimfida ta zauna cikin jin kunya.

Duk bakin Inna sake shima ya zauna kusa da ita, ta dube shi da kyau ta ce, “Sulaiman.” Ya ce, “Na’am Inna.” Ta ce,

“Ina ka samo wannan yarinyar?”

•Ya juyo yana kallon Mabarukar ita ma shi take kallo idanu sun raina fata, sannan ya dubi Innar, haka nan ya ji bakinsa ya yi nauyi yana tunanin fada mata ko wacece.

Ta sake fada “kai da kai fa nake, wacece ita wannan din ka shigo min da ita har da dauko min sabuwar tabarma?”

Ya ce cikin dan tsoro “Inna Mabaruka ce fa.”

Ta ce, “Ta ina? Ni nasan wata Mabaruka ne, ina ka samo ta?” Ya ce da kyar, “Amaryata ce fa.”

Tamkar wacce aka watsawa ruwan zafi, ta zabura har zani na faduwa ta ce, “Amaryarka ta gidan uban wa? Wa ya baka iye?”

Da gashi har ita sun tsorata, suka zuba mata ido ya ce,

“An fa daura min aurenta kowa ya sani.”

Ta ce, “Haka ka ke cewa, amman kowa yasan ba kai za a ba ba.” Ya turo baki cikin fushi “Ni fa matata ce ba me kwace min mata.”

Ta yunkura ta rarumo kara zata dake shi tana cewa,

“Amarsu ba Amarya ba don ubanka, me na fada maka tun yaushe nake cewa ka sakar musu ‘ya?”

Idanun Mabaruka suka fito, ta juyo tana kallon Sulaiman din cikin tuhuma daman haka suka yi da Innarsa amman bai fada mata ba?

Innar ta katseta “Gidan wa kaga ana wannan haukan auren? Ko a garin Mahaukata ban tada jin labari ba sai a nan, shine ka ke Kokarin kawo mana ita nan gidan ta zama tarihi a dinga zuwa kallo?”

•Ya dinga nuna mata da hannu ta bari tana ba shi kunya, ta ce “Na ki na bari don ubanka, in kai kana tsoronta ni ba na tsoronta, da kai da ita sai in hada in zabge ku da wannan karan don ubanku.”

Idanuwansu suka fito suna kallonta baki sake.

Ta ci gaba “To tunda ga ka ga ta sakarta a nan ayi ta ta kare na fada maka ba kai za a ba ba, wahala kadai za ka sha sakarai.”

Daga Samira har Nafisa ido suka sa abu ya zama na

• kallo, ya ce “Ba zan iya ba Inna, ina son matata daga na kawo miki ita ta gaishe ki kafin a kawo ta gobe kin bi kin rude kina zaginmu.”

Tayo kansa “Na zage ku din, sai me? Ko za ku rama ne?” Suka yi shiru ba amsa. Ta ce, “To wallahi sai ka sake to na rantse.”

Ya ce, “Ba zan iya ba kiyi hakuri na . .” kan ya karasa ya ji saukar karan a jikinsa, abin bai tsaya shi kadai ba har da

Mabaruka ta dinga jibgarsu.

Da sun yunkura za su gudu dukanta zai maida su, suka kasa kwatar kansu.

Sai da kyar sannan suka arce ba shiri a wurwurce takalma a hannu, suka tsaya a waje suna haki da maida numfashi, suka baro Inna na cizgar fada tana fadin.

“Za ka dawo ka same ni a gidan, sakarai wahalalle, kai ba ka ma da wayau wa ke shari’a da ma su kudi?”

•Samira ta ce “Kin min daidai Inna, ke din ba ta wasa bace.” Nafisa ko ba bakin magana, bata isa ta ce wani abu ba, abu ya dawo kanta sai dai tayi bakin ciki da aka kora su har

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE