WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 7 BY MARYAM JAFAR KADUNA
Mabaruka ta dora hannu saman kai tare da fashewa da kuka, “Wai wai wai ni Mabaruka na shiga uku, wai ya ake son nayi da raina?”
Ya rasa ma me zai ce, wannan abin kunyar da Inna taja masa har ina? Ya dubeta ya ce, “Ya isa Mabaruka, bana son tashin hankalin nan, ba komai ba ne komai zai daidaita kadaki damu, nasan yanda zamu yi da ita.
Ta marairaice fuska, kwalla ta cika a idanunta ce *Ko ta ina akwai matsala, yanzu kana nufin bata son aurenmu har tana cewa a sake ni Sulaiman?”
Ya ce “Rabu da ita, wannan fadarta ne. Tun yaushe take fama da ni naki nayi sai dai taji ana shigowa da ke.”
Ta zauna dadas kasa ta rafka tagumi ta ce, “Ga shi nan mun sha duka karo na farko kenan ban san me zai kasance gababa
Ya ce, “Na fada miki ba abin da zatayi…” Ta katse shi
• da’sauri “Don me za ka ce haka? Bayan mahaifiyarka ce ta isa ta saka ko ta hanaka har sai da yardarta sannan zan shigo gidanka?’*
Ya durkusa gabanta ya ce, “Ni ne mai aurenki ba ita ba
idan tayi kokarin raba ni da ke zan kaita Kara ga magabatanta.”
Tayi jagwam tare da cewa, “Allah yasa to tsorona kar hukuncin da kotu za ta yi ya ki mana dadi, wallahi ina tsoro Sulaiman.” Ta fada a marairaice tamkar zata yi kuka.
Shi kanshi hakanne a ransa, damuwar kotu tafi ta Inna.
Koda yaushe zuciyarsa na harbawa dankare take da tsoro, Allah ya sani yana son Mabaruka fiye da duk matan da ya aura.
Kai yana jin zai iya sadaukar da komai a kan ya sameta koda ‘ya’yansa karshen zance hatta Inna zai iya sadaukar da ita idan har zai sami Mabaruka bare abin duniya, ko ransa.
Ya kwallafawa ransa ita, Kun ji fa
A fill ya dubeta ya ce, “Koda kotu ta yanke hukuncin da bai mana dadi ba, ina iya daga shari a har sai naje in da za a bani ke tunda kowa yasan uba shi ke da hakkin aurar da
“yarsa ga wanda yaso ba uwa ba, don haka ina da tabbacin ni za a ba mata in dai ana bin gaskiya.
Ta kalle shi kurum, ita ba haka ba ne a ranta, tsoronta ya wuce nasa. Koda ta fada masa ba zai fahirta ba, gwanda ma kawai ta kyale shi.
Ta ce, “Mu bar wa Allah Sulaiman, shi zai shige mana gaba yasan zuciyoyinmu duk wani dabara ko hikima ba zai fishshemu ba.” Ya ce a sanyaye “Haka ne.”
Daga bisani ya dauke ta a mashin dinsa suka shiga yawace-yawace duk don ta saki ranta ta samu nutsuwa.
Ba laifi dai ta dan ji dama-dama, amman da zaran ta tuno tashin hankalin da ke gaba da idan ta tuna gobe kamar yanzu an riga an yanke hukunci.
Dayan cikin biyu sai taji komai ya dagule mata, har goma na dare suna waje.
Tuni take cewa ya maida ta gida amman yaqi, ko da
Momynta ta kirata rikicewa tayi ta rasa me zata ce, sai dai tayi mata karya ta ce tana gidan Babanta.
Ba ta ce komai ba ta kashe wayar saboda ta yarda da ita ranta bai kawo komai ba.
Shi kuwa Imran koda ya tashi yake tambayar Momy ina
Mabaruka? Ta ce Taje gidan su Rafia. Ya nanata, “Gidan su Rafia kuma?”
“Haka dai ta ce, wai.” Ya jinjina kai kawai amman ba haka yaso ba, yaso ya ganta da safen nan yanda ya tashi da kwadayin son ganin matar tasa, har ya gama abin da yake ya fice.
Har dare da ya dawo ya sake nemanta bai ganta ba, a haka dai ya kwanta yana tunaninta.
Sulaiman kuwa gidan abokinsa Mansur ya wuce da ita,
Mansur yana da matarsa da ‘yarsu guda daya.
Sunci sun sha suna tana zolayarsu da sake labarta wannan rikitaccen auren nasu.
Ya dubi Mansur din ya ce “Mu fa a nan zamu kwana sai ku bamu daki daya.
Tayi saurin dubansa tare da cewa, “A nan kuma? Wasa dai kake.” Ya dubeta ya ce, *Wallahi da gaske nake, yau a nan zamu kwana
Ta marairaice fuska ta ce, “Please, kar ka min haka
Sulaiman, wallahi idan Momyna taji sai ta dake ni.”
Ya ce, “Ba za ma taji ba, ba kin ce kina gidan Babanki ba, shi kenan sai ta dauka kina can din, shi kuma daman ya sakankance kina gun Mamanki.
Sannan ba magana suke ba bare ya tambayeta ke ko ita ta tambaye shi.”
Tayi tsura-tsuru, sam ba haka taso ba, ta ya ya ma hakan zai kasance har yana wani cewa a basu daki daya. Masifaffen tsoronta ya taso bata san sanda ta mike ba tsalam! Sai dai ta ganta tsaye tana wawwurga idanuwa suka bi ta da kallo.
Basira matar Mansur din ita ta fahimce ta, tayi dariya tare da mikewa tana ce musu “Ka bar ni da ita minti biyu.”
Da haka taja hannunta zuwa dakinta.
Sulaiman din ya dago murya yana cewa, “Kar fa ki kai min mata wani garin.” Ba ta saurare shi ba suka shige daki.
Mansur din ya yi dariya ya ce, “Kai mutumina ta zama matarka kenan har yanzu fa a babin-badinuhu ka ke, ba ka san tsakaninka da wancan ba, waye me matar?”
Ya dube shi a natse ya ce, “In tambaye ka mana.” Yace
“Ina jin ka.” Ya ce, “A ganinka ni da wancan din waye
Angon?”
Ya yi dariya sosai ya ce, “My friend kenan, ni ba Alkali ba ba Lauya ba, ta ya zan san waye Angon?”
Yace. “A’a a naka tunanin in za ka bi tsakani da Allah a hukancinka wa ka ke gani shi ke da mala?”
Ya nutsu tsawon dakiku sannan ya ce “Kai! I can’t, ban san wa zan ce shi ne angon ba, wannan sai mai shari’a. Ya yi jim sannan yace Ka tayani addu’ a abokina a bani
Hmmm