WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 8 BY MARYAM JAFAR KADUNA
matata, zan iya mutuwa idan a ka ba wancan, ko kuma na kashe shi wallahi.”
Ya buda baki yana salati, cikin tsorata da mamaki yake kallonsa. Ya ce, “A’a kar ka fara wannan tunanin, ka bar wa Allah komai kar ka bi son zuciyarka, Allah shi zai ba mai mata matarsa.”
Bai iya cewa komai ba, ya yi dai jim yana sauraronsa.
Koda suka shiga daki ta zaunar da ita bakin gado tana dubanta.
Ta ce, “Me ki ke tsoro ne?” Tayi shiru tana kallonta ba amsa. Tayi murmushi ta ce, “Na fahimce ki abin da kike tunani ba haka ba ne.
Ki kwantar da hankalinki, Sulaiman dai mijinki ne ba komai yasa ya bukaci haka ba sai don samun nutsuwarki da tasa, don farin cikinku.
Don kin kwana a nan ba wani abu ba ne, kowa yasan kina tare da mijinki ne bare ba wanda yasan kina nan…
Ta katseta a sanyaye “Amman wannan ha’inci ne bai kamata na ha,inci Mahaifiyata ba. Sannan ba ni da tabbacin waye mijina tsakaninsu.
Ina Tsoron Mahaliccina, haka nan idan
Mamana taji ina tare da Sulaiman bare na kwana da shi na rantse sai ta karya ni.”
Ta zauna tare da da fa kafadarta cikin lallashi,
“Ba abin da zai faru dake, kiyi tunani tun yaushe ku ke cikin rashin nutsuwa da fargaba? Yau kadai idan ku ka wuni da juna ku ka kwana za ku sami nutsuwa ku shiryawa tanadin gobe.
Ki nutsu da kyau hakan babu aibu, don shi mijinki ne ya bada sadakinki an kuma daura muku aure yana da ikon fita da ke duk in da yaso.’
Tayi shiru tana tunanin maganarta, wani gefe na zuciyarta yana son amince mata wani gefen kuma yana hanata.
Da dadin bakin Basira da lallashi ta shawo kanta a kan zata kwana din amman a kan sharadi.
Ta dubeta ta ce, “Wane sharadin kenan?” Ta ce tana kallonta “Ba zan kwana tare da shi ba a daki daya, sai dai su kwanta da miinki ni kuma na kwana tare da ke.”*
Tayi dariya tace, “Wayo ko Mabaraka?” Murmusawa kawai tayi ta sunkuyar da kai ta ce. “Shi kenan kadakiji komai hakan za a yi, amman muje muci abinci muyi hira
yau sai mun kai dayan dare muna hira.”
Haka kuwa ta kasancen, sun dade a falo suna labari gefe kuma da dan abin sa wa a baki.
Bai ce komai ba suka shige shi da Mansur din wani dakin su kuma suka shige dakinta.
Can ma suka dasa da ita, musamman hirarmu ta mata da karin shawarwari.
Taji dadi kam da sukuni ta dinga nishadi musamman kasancewarta da masoyinta ga abokanan hira masu mutunci da ban dariya.
Sun ba su shawarwari a kan addu’a ce kadai mafita gare su. Ta kwnata tana nishadi tana cewa a ranta me ake da wnai Imran can! Ina! Ai sai Sulaiman.
Haka zalika ta tashi da farin ciki, sai dai kash! Tuna yau za ayi ta ta Kare yasajikinta ya yi sanyi kalau.
Fargabarta ta dawo sabuwa, addu’ar da su Mansur suka bata ita take ta nanatawa a baki, har suka baro gidan karfe goma.
A hanya Momy ke kiranta ta ce tana kan hanya, Can nesa da gidan ya ajeta a kan sai sun hado a kotu, ya juya ya wace A harabar gidan suka hadu da Imran.
Ya yi kyau sosai yasha dream yard ya yi matual dress, fuskarsa manne da glass fari yana Kokarin shiga motarsa wacce aka wanke masa tana ta sheki.
Suka hada ido biyu ya sakar mata murmushinsa mai kyau. Yayin da tayi saurin dauke kanta ba ta dai harare shi ba ta shige ciki da sauri tamkar wacce a ka ce a kamo. Ya yi siririyar dariya tare da fadawa mota yana ambaton sunan Allah, ya ja motar ya fice zuciyarsa cike da tunanin Mabarukarsa.
A KOTU
Karshen tika-tika-tik!
Kamar yanda Alkali ya ce a yau zai yanke sharia, zai ba mai mata matarsa a yau dinnan.
Kuma koda aka fara tasu, ce kan gaba ya Kara jaddadawa lallai a yau zai yanke hukunci.
‘Yan cikin Mabaruka suka hautsina, zufa ta keto mata,
jikinta ya yi sanyi kalau, gabanta ya dinga dukan tara-tara, fargaba ta cikata dam.
•Har sai da Rafia dake gefenta ta riko hannunta tana cewa, “Ki nutsu Mabaruka ki ta ambaton sunan Allah, za ki samu nutsuwa.”
Ba ta iya amsawa ba sai dai ta daga kai saboda yanda bakinta yai nauyi ta baza kunnuwa da idanu tana kallon Alkali
Imran kuwa da Sulaiman ban san wa ya fi shiga fargaba da zullumi ba, sai kallon kallo suke.
Ita kanta Momy a zulumce take, tana tsoron kar ‘yarta ta shiga gidan Sulaiman ko ba lallai Imran ba tana tsoron matsalar gidansa, sabanin Babanta da fargabarsa ba wata bace.
Da farko Alkali ya faro da nasiha da wa’azi, ya kawo ayoyi da hadisai a kan yanda aka ce mu Musulmai muyi aure.
Maza an ce su aura daga bibbiyu zuwa uku har hudu, idan sun ji tsoron ba za su yi adalci ba to su tsaya ga daya.
Babu wata aya ko hadisi da aka ce mace ta auri fiye da miji daya, sai dai ko in auren ya mutu ko mutuwa ko
Hmmm