WAYE ANGON BOOK 2 CHAPTER 9 BY MARYAM JAFAR KADUNA
rabuwar aure shi ne mace zata sake auren wani namijin. Ba don komai ba kuma sai don adalci ne hakan. Kai kanka ka nutsu kayi tunani a kan abu daya ma kawai mu dauke shi dangane da daukar ciki.
Yau in tana dakin wannan gobe tana dakin wanna sai ta sami ciki, to ta ya ya za a gane cikin wannan ne ‘ya’yan wannan ne? Ba yanda za a yi hakan ta faru.
Don Allah baice ayi haka ba, ba wata dabara ko hikima da zai sa mace ta auri maza biyi, yin hakan kuma babban zunübi ne, rashin tsoron Allah ya shigo da rashin tsoran azabarsa.
Duk wanda ya yi haka kuma ya sabawa Allah da Manzonsa, sannan akwai tsantsar jahilci da isa, don sai jahili zai yi haka, kai ko jahili in dai ba mahaukaci ba ne ba zai yi irin haka ba.
Babu inda ake auren maza biyu, mace namiji daya take aure, don haka iyayen wannan yarinyar sun aikata babban sabo da zunubi, dole ne su nemi gafarar Ubangiji suyi ta istigfari.
Idan rashin jituwa ce su sasanta kansu, an haramtawa Musulmi gaba da junansu, an fi so su kasance ma su yafiya da hakuri ga dan uwansu.
In ita mahaifiyarta tana jin haushinsa ta rike abin da ya mata sai tayi hakuri ta dubi matsayin da Allah ya bata a yanzu ba don yinta ba shi ma yasa wa kansa dangana. Su daidaita da junansu don zaman lafiyarsu da kwanciyar hankalin yarinyar da suka haifa, don a kullum da ba shi da kwanciyar hankali matukar iyayensa ba sa jituwa, ya kan rasa nutsuwarsa.
Sannan duk wannan abin da ya faru rashin jituwarsu da hadin kansu ne ya jawo haka, in akwai jituwa da kyakkyawar fahimta sai su tattauna su shawarta a kan wa ya fi cancanta su ba auren ‘yarsu?
Sai su tantance su aura mata a nutse da aiki da ilimi amman a haka kowa yana ji da kansa shi fa ya haifi ‘yarsa don haka shi zai aurar da ita ga wanda yaso, shi yasa hakan ta faru.”
Alkalin ya dan tsahirta tare da yin wasu rubuce-rubuce sannan ya ci gaba.
“Don haka zamu yanke hukunci mu ba mai mata matarsa,” Dukkansu suka kwalalo idanuwa da kunnuwa, yayin da
ita kuma faduwar gabanta ya karu.
Ya dubi takardun da ke gabansa sannan ya dago yace,
“Imrana Umar shine a ka fara daura mata aure da shi a kan sadakin da ya bayar lakadan, shaidu sun shaida an yi addu’a kuma Kanin Babanta wanda suke Ummi wa Abba shi ya daura mata a matsayin waliyyinta tare da nashi.Don haka ya tabbata lallai babu mai mata face shi, kasancewar shi aka riga aka daura kafin wancan.”
“Innalillahi wa’inna ilair’raji’un! Hasbunallahu wani’imal wakil! Lahaula wala kuwwata illa billah!”
Abin da take nanatawa kenan, ta dora hannu saman kai.
Alkali ya ci gaba.
“Daurin auren da ya biyo baya ya zama shirme, harbin iska ba shi da mata saboda akwai mai matar an riga an kuma daura din. Don haka sai ya nemi wata.
A yau muka kawo Karshen wannan sharia, idan kuma akwai mai son daukakata yana iya daukakata daga nan kotun Musuluncin zuwa wata kotun ta gaba.”
Wannan kenan
Tsalam ta mike ta dubi alkali fuskarta da niyyar kuka
ta ce, “Babana shi ya daurawa Sulaiman aurena, kuma ya ce shi yaba kowa kuma ya san uwa ba ta daura aure, ya za a yi a ba shi?”
Ya kalle ta tsaf ya ce, “Yarinya na riga na yanke hukunci, ga mijinki nan.” Ya nuna Imran. “Saboda Kanin mahaifinki zai iya daura miki aure kuma kasancewar shi ya daura yasa a ka ba Imran din.
Kamar kuma yanda na ce idan bai yi muku ba za ku iya daukakawa.”
Ta fashe da kuka ta hada hannuwa tare da cewa “Don son Annabi don iyayenka ka canza ka ba Sulaiman, wallahi ba na son Imran din.
Bai saurareta ba ya buga abin da ke gabansa alamar ya tashi, duk a ka mike ana amsa masa daga nan ya wuce abinsa. Dogaransa suka bi shi da takaddun da ya bari.
Ai fa nan kotu ta hau kace-nace, ayarin Sulaiman da shi kanshi Sulaiman din sai bala’i suke, yayin da shi gogan ya yi tsaye ya kasa cewa komai.
Sam bai yi tunanin haka zata kasance ba, tuni ya barwa kansa shi za a ba mata saboda uba ke daura aure.
Imran kuwa da ayarinsa sai murn da farin ciki, bakinsa ya kasa kullewa, hatta Momy tana cikin farin ciki sabanin Sharifat.
Daddy da Rafi’a ma ba a bar su a baya ba.
Ita kuwa ta juya nan ta juya can, duk ta kidime ta rasa a ina take, ta manta komai.
Jiri ya dinga kwasarta, ta dinga yi luu-luu ana juyata idanunta suka rufe, kafafunta suka kasa daukarta. Sai dai aka ji rijib ta zube a nan.
Nan fa aka yo kanta a rude, musamman Imran din shi kanshi Sulaiman ya runtumo da gudu da Momy da Rafia ke mata fifita.
Cak! Imran ya daukota tamkar jinjira a gigice ya nufi waje da ita zuwa mota, sauran kuma suka ru fa masa baya.
*Wani abu ya tokare makogwaron Sulaiman, ransa ya baci ya dinga huci tamkar kumurci, idanunsa suka kada jajir.
Ya yunkura zai bi shi ya kai masa duka, abokansa suka rike shi tare da tunasar da shi wancan dukan abin da ya jawo masa.
Sam ba ya jin su ba ta wannan yake ba, ya dinga Kokarin kwace kansa, ko da ya kwace din yana zuwa suna barin
Hmmm