WAYE ANGON CHAPTER 1 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 1 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON?
Rafi’atu ta shizo dakin hannunta rike da plate din
abinci, hannu daya kuma z06o ne a robar ruwa da
ake durawa guda biyu sun dauki sanyi karara.
Tabi inda Mabaruka take kwance da ido ta zauna tare
da aje plate din ta ce “‘Mabaruka!” Shiru bata amsa ba.
Ta kara kiranta ” Nasan idonki biyu ki tashi.” Ta tashi a
zaune a kasalance, kallo daya za kai mata ka gano bata www.dailynovels.com.ng
cikin walwala, ta dauko dankwalin da ya cire a kanta ta
yafa ta dubi Rafi’atun ta ce “Menene?”
Kallonta take tsaf! don son gano wani abu, sannan ta
ce
“Wai meye haka Mabaruka? Kina son damuwa tai
miki yawa ko?”
tayi mata shiru. Ta ci gaba
“Ki
saukakawa kanki don cuta bata da wuyar shiga jikin
mutum wallahi.”
Ta yatsina fuska tanakallonta, ta ce
“To me nayi
kuma?” Ta ce cikin kulawa,
“Ba ki komai ba, amman
kwanciyar da ki kai ba bacci ki ke ba illa tunani da kuka,
tun da na-fita na bar ki a haka na kuma taras da ke a
haka
Ta sunkuyar da kai ba tare da ta ce komai ba. Rafi’an
ta ce “Don Allah Ki daure Kawata ki barwa Allah komai.
ke dai kici gaba da addu’a kurum
Ta dago da tsumamman idamunta Kamar zata yi kuka
tace “To me kike so nayi? Kwana biyu fa ya rage www.dailynovels.com.ng
Tayi
jim sannan ta nisa ta ce
“Na sani Mabarika, amman
na ce fa ki bar masa komai ki gane lokacinki bai
Kure ba
Ta ce, “Ke kadai ki ka zama matsalata Rati’a, Bacin haka
da tuni nayi nisa da garinnan, inda zan sami yanana da nutsuwva.” Tace, “Na gaji da jin haka Maburaka, kin fada
yafi a kirga, na ce miki babu inda za ki je wallahi.”
Ta buda baki zata yi Magana a kasalance ta yi saurin
katseta.
“Ya isa! Matso ga abinci muci muyi sallah,
sannan ma tafi.” Ta kalleta tace, *Ina kenan?”
Tana juya abincin ta ce, “Kasuwa mana, daga nan mu
sauka wajen Anti Farida muyi saloon din, Tun safe na
fad miki haka amman kin kasa rikewa
Ta dubeta da kyau tace. – Nima tun safen nake fada miki bazanjeba
“Wallahi ba ki isa ba, ya zama dole ki matso ma ki gani.
Muna da abubuwa fa da yawa Mabaruka?” Ganin bata
da shirin matsowan yasa ta haye saman katifar da
abincin ta mika mata cokali ta ce, “Karbi muci mu wuce,
yana hucewa ga lokacin sallah yana tafiya.
Ta makale hannu taki karba. Hakan yasa Rafiar ta
Daga murya ta Kwalawa Mama kira. *Mama!” Daga can www.dailynovels.com.ng
Tsakar gida Maman ta ce,
“Ya aka yi ne?”
Ta ce,
“Mabaruka ce mana.”
Jin haka yasa ta taso ta nufo dakin. Ta dubi
Mabarukan ta ce, “Ya aka yi ne?” Ta dago da jajayen
idanunta tana kallon Maman ta kasa cewa komai.
Ta dubi RafI’atun ta ce, “Ya aka yi ne?” Ta ce “Abinci
taki taci.
** Maman ta karasa wajen Mabarukan ta zauna
Gefen katifar ta ce -Ya aka yi ne Mabaruka don me bazakici abinci ba?” Ta ce a sanyaye “Bana jin yunwa ne.
Tace,
“‘To me yasa ko na safe fa banga kin ci wani abun
kirki ba, zama da yunwa illa ne, daurewa za ki kada
damuwarki ta shafi cikinki,
Hmmm yanzu aka fara www.dailynovels.com.ng