WAYE ANGON CHAPTER 11 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 11 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

tana cewa “Kai ka sani ba damuwata ba ce.” Ta buga masa kofar ta fice.

-Ya bita da kallo cikin tsananin kaunarta, hakan da tayi burge shi tayi, ya kasa dauke kansa daga kofar

kamar tana gani. Can ya yi ajiyar zuciya ya ce a bayyane.

«Ya Allah idan har Mabaruka ba alkhairi ba ce gareni, in kuma ba za ta taba sona ba kamar yanda nake sonta

na damu da ita, nake tausayinta. Ya Allah ka cire min sonta kada ka bar aurannan ya yiwu tsakaninmu, ka zaba min mafi alkhairi ga rayuwata, ita kuma ka bata

wanda take so ya zamo alkairi gare ta.

Ya koma ya jingina jikin gadon ya yi lamo yana jin zafin sonta na kara zafafa a zuciyarsa, yana kara yaduwa.

Koda ta shiga dakin ta shige toilet tayi zaune kan abin kashi ta dinga rizgar kuka, wai me yasa zuciyarta take mata zafi har haka? Wallahi ba ta sonshi ko kadan,

tsanarsa ce dankare a ranta. Me yasa ba zai kyaleta da

Sulaiman dinta ba?

Taci kukanta son ranta sai kuma ta koma yi wa kanta fada, to kukan me ki ke don me ba ki fada masa abin da

ya kai ki ba? Ke fa za ki cutu, ki sauke girman kanki ki danne tsanar tasa ki roke shi, me yiwuwa ya fahimce ki,

shi kenan ki huta da kuda.

Amman in ba haka ba ki kai wasa aka daura aurenki da shi.za ki mutu da bakin ciki, kullum za ki dawwama da kuka kina ganinsa kina Kara tsanarsa da takaicin

zama da shi, wai a matsayinshi na mijinki.

Ai kuwa tazo wuya, ba za ta taba yarda tayi rayuwa da makiyinta ba ya nakasa mata rayuwa ba. Lokacinta

na kurewa, daga yau ba wata damar, gwanda taje kawai ta ceci rayuwarta.

Don haka ta nutsu da hakan ta mike ta Kara ficewa ta

tunkari dakinshi, Har za ta tura ta shiga sai kuma ta tuna

yanda ta tarar da shi dazun.

Don haka sai ta fara knocking har ya kwanta amman bacci bai dauke shi ba, ya ji ana bugawa. Ya tambaya

“Waye?” don sam ranshi bai kawo za ta dawo ba, yasan

halinta. Ta yi shiru kamar ba da ita yake ba.

Ya Kara tambaya. Cikin masifa ta ce, “Ka zo ka bude sai ka gani.” Jin ita ce yasa ya mike ya nufo kofar, ya murza key ya bude.

Ya ce,Menene kuma?”

Tayi masa banza tana

kumburi, ganin ba ta da niyyar ba shi amsa kuma ta ki shigowa yasa ya ce,

“To shigo.”

” Ta shigo din ta jingina

da bango har da harde hannuwa a kirji.

Ya bar kofar bude ya tsaya gabanta ya ce, “Menene

wai?” Ta ce a kufule, “Na ce zan yi magana da kai.” Yanuna mata kujerar again, ya ce “To je ki zauna.”Ta dago ta harare shi ta kuma kauda kai don bata iya jurar kallonsa saboda Kiyayyarsa, tsawon dakiku.

Ya ce, “Mabaruka!”

“Tayi shiru, ya kuma cewa “Wai

me ke damunki ba ki jin magana ko?” Ta zumburo baki

tana gunguni. Ya ce, “Na ce kije ki zauna muyi maganar,ina son na kwanta dare yana yi fa.

Ta ce, “Ni ba zan zauna ba.”

“‘ Ya ce, “Ok, to zo ki tafi

mun yi maganar gobe.” Taki tafiyar. Ya dubeta da kyau

ya ce, “Mabaruka!” Ta amsa cikin makoshi. Ya ce, “Meke damunki?” Tayi shiru, ya ce “Kije ki zauna muyi maganar to.

.”‘ Ta ki ko da motsawa.

Ganin za ta bata masa lokaci yasa ya janyo hannunta har gaban kujerar ya zaunar da ita. Tana zama ta mike

tsaye, ya kara zaunar da ita ta sake mikewa tana turo baki.

Ya dubeta cikin ido ya ce, “Kin iya kafiya ko?” Tayi masa banza. Ya saki hannunta ya ce, “Ok, mike din tunda kin raina ni ba ki jin magana.

.” Ya koma ya zauna

•kan gadon ya yi shiru, ransa ya bace amman babu alamar ya ji haushi.

Ba tun- yau take tare da shi ba, ta san shi sosai tasan halinsa lokacinta da yake mutuminta abokinta kan ya ce

yana sonta ya zama makiyinta.

Ransa zai bace a zuciyarsa amma saboda hakurinsa

ba za ka gani ba a fuskarsa. Sai in ya kai iyaka za ka gani a idonsa su sauya launi zuwa ja.

Don haka ta fahimci ya yi fushi ne, don haka a

sanyaye ta koma ta zauna din, Bai ce komai ba dai ya yi shiru.

Ganin hakanne yasa ta ce, “Daman um daman…” ta

kasa fada.Ya dubeta cikin kulawa ya ce, “Fadi mana, kar kiji komai zan suarare ki na kuma yi miki kyakkyawar fahimta.”

*-Don haka ta ce a marairaice, idanunta sun kada, ta ce

“Wallahi ban taba sonka ba, ba na sonka, kai ne namijin

da nafitsana a rayuwata.

Kai maganganun sun masa zafi da nauyi a rai, tamkar ta fesa masa wuta ya ji, duk da ba yau ta fara fada masa

ba amman duk sanda zata nanata sai ya ji yafi sanda ta fada a baya zafi.

Murmushi ya yi a fili ya dubeta ya ce,

“Na sani Mabaruka.” Taci gaba “To me yasa ka nace sai ka aure ni

bayan ka san ba na sonka ko ka aure ni haka zan dawwama za ka cutar da ni ka tauye ni? Kaima ba za ka

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE