WAYE ANGON CHAPTER 18 BY MARYAM JAFAR KADUNA
WAYE ANGON CHAPTER 18 BY MARYAM JAFAR KADUNA
karkashin Kafar Imran, ci sha sutura wajen zama ya koma wuyan sa, sai da amincewarsa zata fita komai in zata yi sai ya amince, ta zama halaliyarsa ta zama tashi.
Kamar daga sama taji ana cewa “An daura auren Imrana da Mabaruka a kan Sadaki dubu dari lakadan ba ajalan ba, ya biya.
Taja wani dogon numfashi kan ta sauke sai dai ta fadi nan sumammiya.
Koda waliyyan Sulaiman suka zo ba bata lokaci suka daura aurenshi shima tare da Mabaruka. A takaice dai an daura auren a tare lokaci daya, nan
fa abu ya zama surutu, hayaniya tayi yawa, mutane sukai dandanzo al’ajabi da mamaki da tir da wannan zuri’a ake yaushe ake haka?
Shin Musulmai ne kuwa? Nan a aka yi yuu kowa na tsegumi aka dinga tururuwar ganin Baban amaryar da angwayen.
Nan da nan ‘yan Jarida suka bayyana, masu dauka suka ci gaba da yi. Sun yi nasarar ganin Babanta, sun zo suji ta bakinsa inda suke cewa Baba ya aka yi wannan abu ya kasance ka daura auren ‘yarka ga maza biyu?”
Ya ce, “Nine mahaifin Mabaruka, kuma ni sadakin mutum daya na karba, shine Sulaiman kuma da shi na daura mata aure a matsayina na ubanta. Ban san wani ba can. Wannan shine abin da zan iya cewa kawai
.” Suka koma Bangaren Ango.
«Ya sunanka Malam?”
Ya ce yana gyara malum-malum (babbar riga)
“Sunana Sulaiman.Suka ce, “Shin ko ka san ku biyu a ka daurawa aure da matar da ka aura?”
Ya ce,Eh na sani.
” Suka ce “To me za ka ce?” Ya ce,
“‘Abin da na sani ni ne angon ban san wani ba, kuma zan dauki amaryata nan ba da jimawa ba, saboda Babanta
shine ya daura min aure da ita, shi na ba sadakina kawai nasan nine angon.
Suka koma Bangaren Imran. “Alhaji Imran me za ka ce game da wannan auren, ko
ka san ku biyu ku ka auri matar da aka daura aure?”Ya yi murmushi tare da gyara tsayuwa ya ce, “Yes, na sani.
“Suka ce “To me zaka ce?” Ya ce,
“Nothing to say, ni dai nasan nine Angon.
” Sun yi-sun yi da shi ya kara
cewa-wani abu amman ya nace a kan hakan.
Kun san ‘yan Jarida da shige-shige, sai da suka bemo gidan Mamanta shi ma cike yake dam da mutane, hankula ya tashi lokacin da suke tambayarta ya akai haka ta kasance?
Tace, Ni Imran shi na sani na ba ‘yata kuma na karbi sadakinta, Babanta Kanin mahaifinta shine ya daura mata auren, sadakinta na hannunshi.?? Suka ce,
«To amman kun san hakan babban sabo ne
da abin tir da tozarci gare ku?”
Ta ce, “Ni ban san wani ba, Imran shi ne mijin yata da shi aka daura.Abin da ta iya cewa kenan
Sun so suga Amarya amman amarya na can a birkice sai ihu take tana tirje-tirje, bayan farfadowarta. Don haka ba su sami ganinta ba.Rafiatu ta ce, “Wai Mabaruka ba za ki nutsu ba,
wannan haukan shine mafita gare ki?”
Tana kukan ta ce,
“Ai gashi nan abin da nake fada
miki da gaske suke sun daura min aure da maza biyu,
kina kallon dandazon mutane ana zuwa kallo da ‘yan Jaridu, duk duniya sai taji, shi kenan ni sun tozarta rayuwata sun wulakanta ni.” Ta ci gaba da kukan.
Mutane yawansu kamar ana arfa a wannan layin har dare ana abu daya, a ka zo daukar amarya, ‘yan biko
suka zo daga gidan su Sulaiman.
Baban da kansa ya shigo inda Mabarukan take har ta gaji da kukan, sai ajiyar zuciya. Ya riko hannunta har bakin mota, ya dubeta da kyau ya ce, “Mabaruka!”Ta ce, Na’am Baba!”
‘Ya ce, “Ni waye gare ki?” Ta
ce, “Mahaifina.” Ya ce To na aura miki Sulaiman, kije gidanshi kiyi zaman aure, kin jiko?”Tace, “To Baba.Ya ce, “Allah yai miki albarka.TaCe, Amin Baba.
Ya sata motar angwayen, kawayen amarya da ‘yan biko duk suka shisshiga suka wuce.
Suna fita kan layin sai ga su Imran da abokanansa yan daukar amarya, aka ce musu ai an zo an dauki amarya. Da gudu suka yi ribas suka take musu baya, basu sami cimma su ba har sai da suka isa kofar gidan
Sulaiman din, wato gidan Inna.Suka fiftito aka fito da amarya, Imran din da kansa
ya tare wadanda suka riko amaryar ya dube su ya ce,Ina za ku kai min mata, bayan nine Angon amaryata ce?”
Suka bibbishi da kallo, yasa hannu ya jawo ta, ya ce Ni ne Angon ba gidan da zata je sai gidana.” Imran ya hango abin da ke faruwa.Da gudu ya iso ranshi a bace ya ce,
‘”Mallam lafiya za ka rike min mata? Ni ne Angon ta.Yasa hannu ya riko
ta shima. Ran Imran din ya baci matuka, kishi ya turnike shi. A
kan me zai rike mishi mata? Idanunsa suka kada jajir ya
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe