WAYE ANGON CHAPTER 19 BY MARYAM JAFAR KADUNA

WAYE ANGON CHAPTER 19 BY MARYAM JAFAR KADUNA

 

 

Yace,Sakar min mata nine Angon.” Shima Sulaiman din yana rike da ita ya ce cikin

tsawa, har jijiyar wuya na fitowa, ya ce

“Karya ka ke nine Angon.

.” Suka fara janta wannan yaja wannan yaja,

kamar za su cira ta. Yayin da ita ke kuka wannan ya jata wannan yajata

mutane suka taru suka rasa me za suyi, kowa dai kan gaskiyarsa yake.

Tsawon mintoci suna haka, kowa ya nace shi ba zai sake ta ba tashi ce. ‘Yan bikon Imran iyayansa, daga ciki har da Sharifat ganin abin ba zai kare ba tazo ta dube shi

ta ce,Sakar mana mata, kowa yasan mu muka aure ta ba kaiba.Haushi ya turnike Sulaiman din yazo iya wuya, ya

daddage iya karfinsa ya kai mata naushi a baki. Idanuwan Imran ya fito ya dubeta da ta duke baki fashe

jini na zuba idanunta sun kada jajir, ai shi ma sai ya nade hannun riga ya kai masa naushin a baki. Kan kace me tuni dambe ya kaure tsakaninsu, jika ke tim! tim! suka dinga nausar junansu, nan da nan jini ya bayyanajikinsu.

Ganin sun kaure da fada yasa ‘yan bikon Sulaiman suka jata za su shige da ita gida, yan bikon Imran suka gani suka yo kansu. Nan ma abu ya rincabe tsakaninsu, wannan ta daki wannan wannan ta daki wannan:

Sai ga jini suma yayin da abokan ango suma tsakanin na Sulaiman da Imran suka kaure, ji ka ke tim-tim sai su kuma mata dum-dum dudum! Ma su dundu kenan da ma su cizo, su kuma angwayen tuni sun buda fili dambe suke ba ji ba gani.Yan uwa suka yo kansu, yawan mutanen ya gagara a raba su saboda sun fi ‘yan rabon yawa nesa ba kusa ba.

Amarya ko ta koma gefe tana rusar kuka, ta rasa me zata yi. Sai dai ta kalli wancan group din sai ta kalli wadancan. Sharifa ta hango ta, don haka da gudu tayo kanta zata turata mota, habawa ita ma ta dafe keya ta

shige gidan Inna.

Jin hayaniya kofar gida yasa Inna ta dauko ‘yar fitilarta tana haskawa tayo wajen don taga me ke faruwa? A zaure suka ci karo da ita, habawa tuni sai ga

Inna wanwar a Kasa, fitila a tarwatse.

Suka yi cikin gida ba su saurara ba, bare su san me yake faruwa. Jikin Inna ya hau rawa ta kasa mikewa sai dai ta shige da rarrafe cikin gida a tsorace, cewa take “Yaki ake.ne

.” Ta shige daki fitsari tararara yana binta.

Suma sauran matan suka yo cikin gidan aka ci gaba da dauki-ba-dadì. Inna tayi mutuwar zaune ta kasa Kwakkwaran motsi, idanuwa waje ta garkame daki har

zuwa lokacin bata fahimci me ake ba.

Bata kawo wa ranta ‘yan kawo amarya ba don bata san ya akai auran ba, tunaninta yaki ake ko tashin kiyama ne yazo.

Fitsari tayi shi, anan zaune yafi a kirga, ‘yan cikinta sai hautsinawa suke, suna kokowa da zawo yana son kawo kai , irin bugawar da gabanta yake zai iya shafar zuciyarta ta buga.

Ko ya taji tim sai ta zabura, Samira bata nan. Yayin da su kuma suka ci gaba da fashe-fashen duk abin da yazo musu gaba daga kayan Inna an yi tatar kokon gobe

aka dauke shi aka juye wa amarya jikinta wajen zubawa wata. Ruwa kuma tun daga na girke har kan na butoci sai da suka karar da su, tukwananta na kasa duk aka fashe

su da bokitai.Amara ta dinga kuka tana yarfe jikinta da kullun Koko,bata ita kanta Rafi’atu taci duka dukda ba da ita ake ba.

Can mazan ma suka shigo, Sulaiman, jikinsa face- face da jini, ya shigo cewa yake *Kan ubannan, gidan namu’ne ku ka birkita haka? Ina uwata?” Ya dinga daga murya

“‘Inna! Inna!! Kina ina?

Habawa su Inna ana can idanuwa sun yo waje sai da taji muryar Sulaiman din sannan murya can kasa kamar wacce ke gadon asibiti tana jin jiki ta ce,Sulaiman gani

nan a daki.”Ya tura dakin, warin zawo da zarnin fitsari suka dake shi a hanci, ya dode da sauri yana cewa “Meye haka?” Ba ta saurare shi ba ta ce, “An gama yakin?” Ya ce,

“Wane yaki?” Ta ce, “Rigimar me ake?”

Ransa a bace ya ce,Kokari suke su kwace mini

mata, bayan ni ne Angon,

‘” Daga haka ya fice yana cewa Ki zauna nan kar ki fito.Ya rufo Kofar.

Gabadaya gidan sun birkice shi sun yi fatsa-fatsa da komai,

Koda Samira ta dawo taga gidansu haka ta ce Kam bala’ in nan, ku su waye ku ka mana haka?” Daga cikin masu bikon Imran daya tace “Mu ‘yan gidan ubanki ne.”

Habawa, nan ma sabon fada ya kara hardewa, suka ci gaba da kicimilli, mota guda ta ‘yan sanda tazo saboda kai mata rahoto da aka yi, sai zuwan ‘yan sandan sannan

aka saurara, kowa jiki yayi laushi likis, ba Bata lokaci aka tattara su a mota sai ofishin ‘yan sanda. A wannan ranar duk a ofishin ‘yan sanda suka kwana.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE